← Book details Tabarmar Kashi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 167 OF 171

Sashe 167

Tabarmar Kashi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Thanks for this beautiful opportunity" bai sake qara koda second biyu ba ya hade bakunansu waje daya.
Hungrily yake kissing nata in and out na bakinta,yanaji cikin jikinsa yayi kewarta sosai. Duk yadda yaji vanason ya wuce ga'ida amma dole ya yiwa kansa birki saboda yasan yanayin da take ciki,ya maida jikinsa ga bango yana maida numfashi, kusan minti biyar sannan ya budesu a hankali. Hannu ya miga mata

"Zo ki gani" ya fada da dakusashiyar murya. A nutse ta tako ta iso gareshi,sai yaja hannunta a nutse suka zauna saman lallausan carfet din dake zagaye da tsakiyar dakin.

Wata kyakkyawar jaka ya jawo ya bude,ya fara ciro abubuwan da suke ciki.

Set ne na gold dan kunne sarga da abun hannu da zobe, muqullin sabuwar dalleliyar mota qirar BMW,sai wasu takardu dake buge da sunanta a sama. Duka ya tattara ya miga mata

"'Bansan da wanne abu zan saka miki ba,bansan meye zan mallaka miki da zai tabbatar da godiyata da jin dadina akan abubuwan da kika yiwa rayuwata ba, inda ana bayar da aljanna tun a duniya lallai da na jima da mallaka miki ita,na baki wannan ne don na nuna kadan daga cikin jin dadin abinda kikayimin,bawai don na biyaki ba" gasa tayi da kanta tana jin wani sassanyan abu yana ratsata tana duban takardun dake gabanta. A duniya babu abinda yafi tsarkin zuciya dadi a lokacin da adam yake dukkan qoqarinsa don gain ya rabata da abinda ta mallaka da guminta qwanjinta da dukka nemanta.....sai-gashi Allah ya aiko mata da wanda ya sadaukar mata da dukiyarsa saboda farincikinta, cikin girmamawa da ) mutuntawa. Adam ya kwashe takardun filayenta sai gashi yau an mallaka mata estate guda, ta mallakawa adam bangles dinta don tsantsar sadaukarwa da soyayya da zuciyar daya.....ya ha'inceta akan hakan,sai gashi yau ta mallaki sarga bangle's da zobba da tasan cewa kudinsu ya ninka abinda ta sadaukarwa da adam.
Adam yaso tattare kudadenta ya gudu,sai gashi ta mallaki motar da ta ninka ninkin baninkin abinda ta tara din,me zata cewa ubangiji banda addu'ar qwarai?, tabi toufeeq tsananin biyayya kamar yadda d'a zaibi uwarsa?.

Hawayen da take zubarwa yaja hankalinsa,ya jawota jikinsa sosai vana shafa bayanta a hankali

"Kada kice komai,all i want is to stay with me forever" gangameshi tayi tana matse ragowar hawayen idanunta tana jin wata qauna me zafi tana Huda qirjinta,a duniya a yanzu batajin akwai wata rayuwa tata da zata iya yiwuwa babu toufeeq.

Zafafabiyar
*HUGU MA*

_TABARMAR KASHI_*

Book 02 Page 74

*_BAYAN SHEKARU UKU_*

A nutse take takawa cikin mansion house din mallakin DR MAHMUD JARMA wanda ko ina kai kawo ne
na jama'a,kaikawon da duba daya zai tabbatar maka da hidima akeyi, hidima irin ta biki.

A nutse MAAMIN SÄAHAR ke takawa cikin dogom corridor din dake qunshe da kebantattun dakin baccin maji,gurin da amintattunta kadai ke ratsashi, kamar saahar nadeeya da afifa da a yanzun ta zama kamar diyar cikinta.

Dakakkiyar shadda 'yar mali ce a jikinta Onion color da yarfin baqi da kima off white, dinkin tea boubou wadda yayi matuqar tafiya da tsari da qirar jikinta.
MRS MUHAMMAD TOUFEEQ JARMA, KHADIJA MUHAMMAD GIREMA, babbar mace hakima da Allah ya huwacewa baiwa masu tarin yawa. Tana sabe da
Mahmud as'ad dake sanye da wata suit ta yara me azabar kyau da daukan idanu,kyakkyawan fine boy wanda kamanninsa ke sake bayyana da babansa shi da dan uwar tagwaitakarsa,kamar toufeeq yayi kaki ya ajiye,bacci yakeyi lakadan a kafadarta,duk da yadda yaketa doki da zakwadin tafiya dinner din SISTER NADEEYA kamar yadda suma suka tashi suna kiranta.
Wani irin sabo sukayi qwarai da ita,suna daukarta babbar abokiyarsu da suke mugun sakewa da ita.

Cikin shekara ukun kacal khadija Muhammad girema ta sauya gaba daya,ta zama wata hakimar mace da idan ka kalleta sai ka sake son ka sake dubanta a karo na biyu,iya 'ya'ya mata kawai kishin kyau da ajin da take dashi sukeyi.

Wannan ya sanya Muhammad toufeeq kishinta sosai da son killaceta hadi da kaffa kaffa da ita,domin ita din rayuwarsa ce kuma mahadin ruhinsa.

Daya daga cikin gofofin ta murda ta bude ta shiga bakinta dauke da sallama. Qamshi da sanyin na 'urar sanyaya daki ne abu na farko da zai fara buso maka. Maji wadda ke a zaune saman carfet din dakin ta amsa. Tana sanye da wata light army green super Holland ta ainihi,fararen hannayenta da qafafunta sun sha jan lalle, ainihin qabilarta da dangantakarta da jinin labarabawa ya fita zammm,gashinta da har yanzu bai surka da furfura ba ya fito ta qasan dankwalin atamfarta.

'A'ah yayar amarya baki tafi ba dama?" Maji ta tambayeta tana miqa hannu zata karbi as'ad. Bata jin nauyin yaran ko kadan,duk da cewa jikin kakansu sukayo

Dr jarma,suna da qiba madaidaiciya da cikar zati

"Ban tafi ba maji,na dai tsaya naga tafiyar kowa"

* "Kedai sannunki, Allah ubangiji yayi miki albarka"

"Ameen ya Allah maji" ta amsa a sanyaye tana qogarin
fidda murmushi.

Sai data gyara zaman as'ad a jikin maji sannan ta mige ta gyara wuyan rigarta,ta miqa hannu tana daukan mayafinta mahadin kayan jikinta ta yafa

"Zamu wuce maji"

"Ke da waye zaku tafi?"

"Yusuf ne zai kaini a motata"

"To Allah ya tsare saikun dawo". Ta amsa da amin tana juyawa maji din kuma ta bita da kallo.

Har takai bakin gofa maji ta kirata,sai ta dawo ta samu gabanta ta zauna

"'Amma me yake damunki maami?" Shuru tayi tambayar maji tana taba zuciyarta,a sanyaye tace

"Ba komai" shuru itama majin ta danvi, ta sani dole ko tsakanin harshe da haqori ma ana sabawa bare miji da mata. To amma tsahon shekarun aurensun nan, ko sau daya daga ita har toufeeq din babu wanda ya taba kawo mata qarar dan uwansa, batason ta cika zurafaf tambaya don tasan a yadda halaye da dab'un sãahar din suke na zurfin ciki ba zata gaya mata komai ba,bata dai jin dadin yadda take gain damuwa saman fuskarta, tun daga shekaran jiya da suka taho biki gidan kawo yau

"Shikenan, Allah ya rufa asiri, amma ki rage sanyawa ranki damuwa ko don abinda yake jikinki" daga kai säahar tayi da sauri tana duban maji kamar me neman garin bayani.

Maji din tasan hakan zata faru saita dauke kai, alamu sun nuna mata sãahar din batasan da zaman cikin ba,shi yasa tayi mata jirwaye mai kama da wanka.

"Tashi kije, Allah ya tsare, ko ba'a tashi ba ki sanya yusuf din ya dawo dake kinsan halin Muhammad"

"'In sha Allah" ta fada tana migewa. Gidan duk an yoye an tafi dinner din nadeeya da mijinta Nader,a hankali maganar maji take dawo mata a kai

"Abinda yake jikina kuma?,maji na nufin wani cikinne dani?" Ta yiwa kanta tambayar dai dai sanda ta iso gaban motarta. Yusuf dan qanwar maji ne da sukazo biki daga Algeria, matashin saurayi ne da duka duka bai wuce shekara goma sha tara ba,amma yana da hankali sosai kirki da kuma son jama'a. Yana matugar son asad da as'ad,duk sanda yazo Nigeria baya rabo da yaran.

Hannunta ta sanya ta shafi cikin nata tana mamakin ace juna biyu ne da ita, kuma har ana iya gani amma ita bata ankara ba?. Shuru ta sakeyi tana wani tunani, kwanakin nan tana danjin motsi a mararta,amma saboda ba cikin nutsuwarta take sosai ba bata ma baiwa ranta komai ba.

"Yaaya another half zaiji?" Ta yiwa kanta tambayar,sal kuma wani abu ya ratsa zuciyarta. Wanne toufeeq din?, toufeeq din da suke tafka rigima yau kusan sati guda kenan?, ko zuwanta bikinma ta taho ne da yawun maii kawai.

Kanta ta kwantar tana dubam fuskar
wayarta,tunda suka taho din ko sau daya bai nemeta ko ya kirata ba,yaransa ma a wayar fadeela suke gaisawa kamar baya qasar, bayan kuma yana nan

"Qila ma yana can suna waya da Hamdiyya" zuciyarta ta raya mata. Ido ta runtse tana jin zafin iya tuna hakan da tayi,cikin ranta tana kiran sunayen Allah hadi da tuna maganganun da ya furta mata ranar da zata taho
"Kije abinki, ban hanaki ba, kome kikayi dai daine,tunda kin gama da zuciyata,kin kuma san soyayyar da nake miki,amma wallahi na gama yarda mace tayi amfani da soyayyar da nake mata ta wahalar da rayuwata, akwai masu sona dake da yawan gaske, zan qara aure na ne, kema kiyi abinda duk kikeso" hawaye ya sauko mata tasa gefan mayafinta ta daukeshi, ashe duk abinda akewa rigimar ma yana tare da ita su duka basu sani ba.

Sanda suka isa guri ya dauki harama sosai, tace yusuf ya riqe key din motar zata kirashi idan ta tashi tafiya,saita wuce ciki. Batasan ya akayi ba tana shiga MC ya kama sunanta lokacin da aka kira ango da amarya,kwata kwata batayi niyyar hawa wajen ba,amma saboda ba yadda zatayi ta mige ta bude jakarta ta fidda rafas guda biyu na dubu daddaya sabbi qal a mige suna daukan idanu.

Liqi sosai takewa nadeeya da nadir,me ya cika gurin da kambamata da kiran sunanta saboda ganin yadda take barin kudi,farinciki da qaunar säahar ya sake lullube nadiya. Cikin sabgar bikin tun daga kamawarta har zuwa yau da za'a gargare säahar din ita ta zame mata uwa kuma babbar yaaya.

Riqota taji anyi ta baya,ta waiwaya kadan sai taga fadeela

"Abby yana motarki yana kiranki" mamaki yadan kamata ta kauda wannan ta migawa fadeela sauran kudin tace ta liga musu,ta soma sauka daga step din a nutse, idanuwa suka sake yawa a kanta MC ya fara kwarara sagon godiya wanda har ya fita daga hall din bai daina zubata ba.

Dukka hannayensa biyu ya saka yana dafe steering motar yana lumshe idanunsa hadi da furzar da iska me zafi a bakinsa. Har cikin tsakiyar zuciyarsa yakejin suya da zafin yadda bakin wani qato ke kiran sunan säahar din yana maimaitawa kamar shi va rada mata sunan, sosai yakejin zafi a zuciyarsa,yana cewa ya hanata zuwa gurin dinner din?, bama ta nadeeya ba, kowacce dinner idan ba tare suke ba, saboda shi kadai yasan abinda yake gani, Allah ya mata ajiyar wani irin kyau me sanyi da daukan hankali,irin kyan dake iya zamewa fitina ga mazaje idan ba'a hadu da mace mai kamun kai da miji mai kula ba. Shi kansa kullum ta Allah ya sake ganinta yake kamar wata sabuwa a idanunsa.
Chapter 167 · 0% Book details