← Book details Tabarmar Kashi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 171

Sashe 36

Tabarmar Kashi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai data shafe kusan awa daya sanann ta laluba magani tasha, tayi kuma sallar azahar don tasan zaiyi wuya batayi bacci ba,idan kuma tayin lokacin yana iya kubce mata. Kamar yadda ta zata din kuwa,lokaci kadan baccin yayi awan gaba da ita,saidai dukka cikin barcin ba komai sai mafarkai,wadanda dukka toufeeq ne a ciki da tarin cin mutunci da cin zarafinsa a gareta.

Knocking din baaba rabi ne ya tayar da ita

"Hajiya tace ki fito hakanan kici abincin rana"

"To" ta amsa mata,ta sa hannu ta shafi fuskarta,tana tuna yadda ya zabga mata mari a mafarki,kwatan kwacin marin da ta taba ji ya zabgawa wata,kai ta girgiza ta miqe a hankali ta wuce bandaki. Alwala ta dauro,sannan ta dawo ta cire kayan jikinta. Wata sof cotton shirt ta saka me gajeran hannu royal blue,me adon furanni da gold colour,sai spaghetti skirt daya dace da rigar,tasa comb ta sake gyara gashinta daya hargitse saboda baccin da tayi,ta qara turare a jikinta ta dauki wayarta dake da tarin miscall ta kashe ba tare data tsaya duba kiran waye da waye ba,ta tabbatar dai harda kiran dan anace mahmud a ciki.

A parlor ta samesu,maama da baaba rabi dake gyara freezer din parlor din

"Barka da fitowa farar d'iya" ta fada tana murmushi

"Barka baaba rabi,ya aikin?

"Alhamdulillah "

"Ma sha Allah " ta fadi tana qarasawa kusa maama ta zauna,wadda har yanzun binta take da kallo

"Me za'a kawo miki?" Baaba rabi ta tambaya

"Barshi baaba,zan dan huta ne kadan sannan naci abincin,zan zuba da kaina" ta amsa mata tana daukar remote ta canza channel.

Bayan wucewar baaba rabin kallonta maama tayi

"Kunyi waya da yayanki ne?" Saida gabanta yadan fadi,tasan yaaya muhyiddeen take magana a kai tabbas,batason ko sau daya ya roqeta ta koma aikin nan,don ba zata iya ba muddin wannan mutumin yana a cikin kamfanin

"Bamuyi ba,ko ya kira din inajin bacci nake a sannan" kai ta kada

"Me ya sanya kika ajjiye aiki sãahar?" Shuru ne ya biyo baya na 'yan sakanni,tanata qoqarin hadiye bacin ranta sannan ta motsa bakinta

"Bazan iya ba maama,dansa bashi da kirki sam,baya ganin kima da girman kowa,duk wata mace dake aiki a kamfanin kallon baiwa yake mata,ko wata mara daraja da batasan martabar kanta ba" shuru maama ta danyi sanann ta numfasa

"Amma dai kinsan qarfe daya baya amo ko?,kuma ko meye halin mutum sai k........." Qarar wayarta ya katse mata maganar,sai t maida hankalinta a kai ta daga wayar ta sanyata a free.

Dr mamman girema ne,wanda kafin su gama wayar sun sanya sãahar din cikin tunani,tabbas inda dukka maza irin mahaifinta ne,su kuma mata duka zasu kasance kamar mahaifiyarta ba ko tantama da ba'a samu mutuwar aure ba,koda an samu din ma saboda sabanin da baya wucewa tsakanin bayi,to zaiyi matuqar qaranci.

Tuwon alkama yace yanaso miyar danyar kubewa,batason ta zauna tayita zaman tuna mutumin da a wajenta bashi da wani amfani sam,banza ma ta fishi,don haka sai ta wuce ta debi abincinta taci,tana kammalawa ta shiga kitchen da kanta ta dorawa abban nata tuwon.

Tunda akayi sallar magariba taji yaa muhyi din tare da abba suka shigo gidan ta qule a daki taqi yarda ta fito,saidai ana gama sallar isha'i saiga maama da kanta

"Ki dauki abincin can ki kaiwa abbanku,zan shiga wanka" hakanan ta miqe jiki a sabule,ta fidda hijabinta ta maida gurbinsa da dan qarami ta fito ta debi kayan abincin ta wuce sassan Dr mamman.

A ladabce ta zauna ta gaidasu dukkansu,don yau kafin ta fita basu hadu da abban ba,ta zauna sosai ta fara serving nasu duka su biyun da suketa tattaunawa akan harkokin da suka shafi kasuwancin da suke na hadin gwiwa a tsakaninsu. Ta ajjiye musu komai tana shirin miqewa abba daya gama wanke hannunsa yace

"Dawo ki zauna mana ummin abba" murmushi kadan tayi,ta dawo ta zauna din,sai da ya fara cin abincin sannan yace

"Me ya faru ne yau a MT JARMA?" Kanta ta sunkuyar tana jin rauninta yana dawowa,kamar yanzun abun yake faruwa,amma dole ta bude baki tayi magana da harshen da zasu fahimceta

"Na ajiiye aiki yau abba,ku yimin afuwa abba kai da yaa muhyi na rashin neman sahalewarku kafin aiwatar da hakan,abun yazo a gaggauce ne,sannan kuma a gabar da bazai bada damar yin hakan ba"

"Me ya faru?" Abban ya sake jefa mata tambayar. Bata rufe komai ba ta zayyane musu,tun haduwarsu ta farko har zuwa abinda ya wakana yau din. Ta qarashe maganar tana hawayen takaici.

Ga mamakinta sai taga abban ya saki murmushi yana girgiza kai

"Dake dashi dukka quruciya ce take damunku da kuma zafin kai,tare da wasu memories da suketa hunting rayuwarku,shikenan dai,bakin alqalami ya riga ya bushe,dr jarma ya kirani da kansa,yace bazai tilastaki ba akan ajjiye aiki da kikayi,yace a baki haquri a madadinsa da dukka ma'aikatan,sannan ya tura kudi a baki saboda hobbasar da kikayi kika daga kamfaninsa zuwa matakin gaba,kika gyara matsalar da suke fuskanta kaso sittin cikin d'ari" ya qarashe fadi yana duban fuskarta. Batace komai ba sai kai data girgiza,taji dadi da bai nema alfarmar lallai ta koma ba,don bataso ya roqeta abinda ba zata sake iyayi masa shi ba.

"Dama aiki ba dole bane,aure ne dole" abban ya sake fadi,maganar data bugeta sosai,ta kuma sakata dago kanta da sauri ta kalli abban,shima idanunsa yana kanta,ya jinjina kai alamun tabbatar mata da hakan

"Tunda taqi tsayawa ta fahimci kowa abba bazaiyiwu taci gaba da zama babu auren kuma ba aikin ba,Allah baya barin bawa babu aikin yi,akwai irin aikin da takeso din abba,idan na dawo daga tafiyar nan ta wata daya zuwa biyun nan zan applying mata" kai ya sake jinjinawa yana tsame hannunsa daga tuwon

"Banqi ta taka ba,amma duk da haka ta maida kai ta fidda miji,saboda lokaci tafiya yakeyi,kuma har yanzu ke din yarinya ce qanqanuwa ballantana kice kin girmi yin aure a yanzu". Gaba daya babu abinda maganganunsu sukayi sai dagula mata lissafi,dan ciwon kan data samu ya ragu sosai ya dinga qoqarin dawowa saboda damuwa,ga gidan babu kowa bare ta samu me debe mata kewa,tanaso tayi magana da anty farheen to amma tasan tabbas yaa muhyi yana gidan,don tafiyar tasa sai zuwa wani satin,sai kawai ta hada kayanta a washegari tabi afifan nata zooroad.

Ranar da taje qin cewa afifan komai tayi,itama bata matsanta ba sukaci gaba da hutunsu,har sai data huce,ranar suna ta raka afifa gyaran farce da fuskarta,suna hanya tana driving ta bata labari. Sosai afifa bataji dadin ajjiye aikin ba,duk da itama taji ba dadi akan yadda abun ya faru tsakaninta da toufeeq din,saidai itama ta gaya mata

"Ba kowanne namiji ke iya fuskantar mace ya bata uzuri ba,ya kuma banbance rashin kunya da tsaiwa akan haqqinta ba,bare mutum irin MT da Allah ya yiwa baiwar kyau kudi da ilimi da kwarjini....."

"To hell with his kudi da kwarjinin,ya dauka ina cikin shirgin wawayen 'yammatansa ne da zan dauki irin wannan?,ki daina yabonsa please kina batamin rai afifa.....bakisan wayeshi bane,saboda baki taba mu'amala dashi ba,he was arrogant beyond belief,good look don't always signal kindness" dariya afifa tayi

"Wato kin fahimci kyansa ya janye hankalina sosai ko?"

"chapter close a beg" yatsunta biyu ta sanya tayi signal na zipping bakinta,bata kuma sake cewa komai din ba,sai suka shiga wata hirar ta daban.

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070

VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k

*Al'ummar NIJER ku kira wannan number don yin naku pyment din*

+22799643131

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥
[8/23, 6:15 PM] KYAUTA: *H U G U M A*

*_TABARMAR ƘASHI_*💔
https://arewabooks.com/u/huguma

Page 32

*********K'arfe kusan takwas ne na dare,saman titin dake wadace da fitilu yake tuqin yau da kansa,kuma shi daya,abinda ba kasafai yake faruwa ba. Sanye yake da wata maroon and golden hoodie captan abaya na maza saqar qasa turkiyya,dogon hannu gareta,ya saki hular a bayansa,hakan ya bawa kyakkyawar fuskarsa damar fitowa sosai,cike da wannan turbunewar da kuma rashin fara'a daya zame masa dabi'a.

Kiran dr jarma ne ya fito dashi,don yana zaune shida fadeela a part dinsa suna buga game data tubure itakam yau tare zasuyi,da qyar ya lallabata ya maidata gurin nanny dinta sannan ya fito,tare da alqawarin zai dawo da wuri su qarasa. Baisan kiran na meye ba,amma alamu sun nuna a gaggauce yake neman nasa.

Cikin rukunin gidajen dake sharada NNDC QUARTER,mayalwacin layin dake shimfide da kwalta da kuma fitilu a jere reras,kowanne gini dake layin abun kallo ne,wannan yana wane wancan,a haka yaci gaba da tafiya bayan ya ragewa motar gudu,da alama ya kusa isowa gidan daya nufaci zuwa.

K'ofar wani mansion house dake dauke da ginin bene hawa biyu ya tsaya,ya danna hon na farko, kafin yayi na biyu security din dake sanye da baqaqen uniform da suke kama dana police ya buda masa qofar,a nutse ya sanya hancin motar zuwa cikin makekiyar harabar gidan. Biyu daga cikin security dinne suka bude masa qofar cikin girmamawa da qauna me tarin yawa suke gaidashi,ya amsa musu yana rufe motar,ya jefa key din a aljihun rigar tasa,ba tare daya ciro hannuwan nasa ba yaci gaba da takawa zuwa cikin kamar maijin sanyi. Bawai sanyi yakeji ba,kawai yana jin wani iri ne da yanayin yadda dr din ya kirashi.

Kai tsaye ya kutsa zuwa hanyar da zata sadashi da falon gidan,ya tsaya yayi knocking,duk da cewa gidan mahaifinsa ne,amma hakan ba sakashi shiga kai tsaye ba,duk sanda yazo gidan sai ya tsaya ya nemi izini don cikar dokar addinin musulunci.
Chapter 36 · 0% Book details