← Book details Tabarmar Kashi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 171

Sashe 37

Tabarmar Kashi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

K'ofar aka bude,labiba ce,sanye da wata doguwar riga da tasha tattara daga qirji,ta bude daga qasa sosai,kanta cike da qananun kitso da gashin doki,sao farata zaqo zaqo data sanyawa hannayenta tamkar wata dabbar daji,amma ita a gurinta hakan ado ne na wayayyun mata masu aji(wallahi wallahi wallahi muddin kinsan daya daga cikin wadan nan abubuwan dabi'unki ne to kiyi gaggawar dainawa tun kina raye kina da lafiya,qarin gashi haramunne koda mijinki zaki yiwa,ko meye zaki sanyashi a kitsonki a qara miki tsahon gashinki haramunne,hakanan saka farce shima haramunne,haramunne haramunne,koda faratan hannunki bai halasta ki tarasu ki barsu baki yanke ba,haramunne barin farce yayi zaqo zaqo bare har kije ki biya kudi a dora miki shi,kina 'yar adam amma kinason kiyi kamanceceniya da dabba?,suke da wanann siffa ta akaifa ko qumba masu tsaho,acikin tsarki na addinin musulunci,bansa aske gashin maara dana hammata harda yankan farce sai yiwa yara shayi(kaciya), ma'aiki baya taba fadar magana wallahi wallahi ta tashi a banza,idan yace abu haramunne mu yarda mubi,ba wani kwaskwarima da malaman zamani masu son zuciya zasuyi ma maganarsa ta koma halak,haram haram ce,halal halal ce,Allah yasa mufi qarfin zakatanmu👏🏽👏🏽).

Sau daya tak ya kalleta ya kauda idanunsa,sannan ya gewayeta ya sanya jikinsa zuwa falon

"Sannu da zuwa yaa toufeeq" ta furta tana bin bayansa hadi da binsa da wani mayen kallo,bai amsa mata ba yaci gaba da kutsa kai,masu aikin dake kai kawo a parlor din suka yi masa barka da zuwa sannan suka kauce daga gurin.

"Abban yana samansa" ta fada cikin yauqi da kwarkwasa,wanda sau tari wani lokaci ita kanta batasan hakan tana faruwa ba,tsabar yadda zuciyarta ne ta afu ason samun soyayyarsa.

"Ya toufeeq" ta kira sunansa,waiwayowa yayi ya watsa mata wani irin kallo daya takura zuciyarta guri guda ya sanyata harbawa,saita duqar da kanta qasa tana wasa da yatsunta

"Yaa toufeeq,am sorry for what happened last time,tsautsayi ne in sha Allah hakan bazai sake faruwa ba" qaramin tsaki yaja,yayi gaba ya fara takawa zuwa stairs din dake cikin falon.

Binsa tayi da kallo har ya bacewa ganinta,hannuwanta ta yarfar kamar zata saki kuka,ta tsani wanann miskilancin nasa,yana matuqar dafaata da dagula mata lissafi,sai ta koma ta zauna saman daya daga cikin qayatattun kujerun falon tana dafe da kanta,dai dai sanda daya daga cikin masu aikin gidan ta qaraso cikin rusunawa

"Ranki ya dade,abincin daren,na kammala fa"

"Dalla matsa ki ban guri" ta fada mata cikin tsawa tana jan tsaki

"Allah ya baki haquri" ta fadi tana janye jikinta daga gurin tunda ragowar mutuncinta,tasan tsaf zata iya ci mata zarafi,ta juya ta koma cikin kitchen din,cikin ranta tana Allah ya qara da yadda toufeeq din yake wajiga rayuwarta. Sake daga kai tayi ta dubi stairs din,gurin mommynta takeson zuwa,to amma ta sani,tunda ya iso ko ruwan giya tasha bata isa hawa saman ba har sai ya sauko,saita kwashe qafafunta ta mayar saman kujerar ta kwanta tana dakon fitowarsa,a ranta tana tsara yadda zasu kebe ita dashi ko na minti talatin ne kacal.

Da sallama a bakinsa ya shiga falon bayan dr yayi masa izini,tana duqe tana zuba masa lemo a cup,kakkaurar mace wankan tarwada me tsaho da jiki,wanda kana dubanta zakasan ba hausa fulani bace.

Da fara'a a fuskarta ta dago tana cewa

"Wata sabon gani,kaine yau a gidan namu?" Dan binta yayi kadan da kallo yana mamakin furucinta,A GIDAN NAMU,sai baice mata komai ba,ya taka a nutse ya isa daura da mahaifinsa,kwata kwata baisan me yasa bai taba jin matar ko daukarta da wani daraja ba,duk da tsahon shekarun data kwashe tana amsa sunan MATAR MAHAIFINSA,sannan dai dai da rana daya bata taba gwada masa wani hali ba,amma haka kawai take takenta baiyi masa ba.

"Ina ka baromin kishiyata?" Ta sake fada cikin fadada fara'arta,maimaikon ya amsa mata tambayarta sai ya buge da fadin

"Barka da dare"yayi furucin kamar ba da ita yake ba,yana maida dubansa ga mahaifinsa,cike da kulawa tace

"Barka kadai Muhammad,ya ayyuka,ya akaji da kacaniyar jama'a" ta tambayeshi cikin nuna kulawa.

"Alhamdulillah" ya amsa mata a taqaice,sam bata damu ba,don ta saba da irin wanna halayyar tasa,saita fara kwashe kayan abincin dake gurin tana dubansa

"Me za'a kawo maka?" Kai ya girgiza,baisan sai yaushe zatayi fushi ba ta daina tambayarsa abinda zaici ba duk sanda yazo gidan,bayan tafi kowa sanin baya cin abinci daga hannun kowa kuma a ko ina ba,sai a wasu kebantattun hannuwa da gurare.

"Alhamdulillah,basai na saki hidima ba" murmushi ta kumayi

"A'ah kace dai ba zakaci ba kamar kullum"

"Yi tafiyarki ki rabu dashi,kada Allah yasa yaci din" Dr ahmad ya fada,wanda tunda ya shigo lemonsa yake kurba yana kuma kallon labarai daga NTA network news.

"Zaici ne wataran ai" ta fada da dariyarta tana yin gaba. Sau daya tak kalmar ta shiga kunnensa amma ya gama fahimtar abinda take nufi ba tare da ita tayi zaton zai fahimta din ba.

"Barka da warhaka" ya fada cikin girmamawa,sauke qafafunsa dr ahmad yayi qasa yana ajiye cup din hannunsa gami da bashi amsa duka lokaci guda

"Kai ya kamata a yiwa barka ai,irin wannan aikin da kayi na cin zarafin yarinyar dana nema alfarmar a bani aronta,ka kuma sanya tabar aiki lokaci guda,to kaga kai ka cancanci a yiwa barka" bai barshi yace komai ba dr din ya tsinke da fada,ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba,daga qarshe yace

"Ka ajjiyemin komai daya shafi company dina kaima na sallameka,na gode da iya taimakon daka bani,ka koma bakin taka dukiyar" daga haka ya miqe ya wuce bedroom dinsa yana bar masa falon.

Kasa motsawa yayi daga gurin,yanajin tamkar ya hadiyi zuciya ya mutu,tsahon tasowarsa bayan shudewar matsalolin da suka sanyo kai a rayuwarsu tun zamanin quruciyarsa,bazaice ga lokacin daya zauna yayi masa fada me zafi irin haka ba,sai yanzu?,a dalilin yarinyar?,ya jima a gurin sannan ya miqe a nutse yana sauka qasan,fuskarsa cike fal da fushi da kuma bacin rai,ta zama silar gurbata kyakkyawar alaqar dake tsakaninsa kenan da mahifinsa lokaci guda?.

Suna zaune a falon,hajiya mansura(matar dr ahmad jarma) tare da labiba,ganin yazo zai wucesu ba tare daya kalli kowa a cikinsu ba,kamar ma baisan da zamansu ba hajiya mansura ta magantu

"Harka sauko?,kun gama kenan?" Da so samu ne yayi wucewarsa,to amma ko babu komai ita din mata ce ga mahaifinsa,zata iya cin darajar mahaifin nasa koda qanqani ne

"Eh" ya amsa bayan ya waiwayo yana dubanta hannayensa zube a aljihun rigarsa. Kwarjini ya mata sosai,tadan daburce amma saita maze ta hanyar sakin murmushi

"Ammm,tafiyarku daya da qanwarka,nace ko ta bika saiku tafi tare?" Ido kawai ya lumshe wanda ke nuna ya amsa kenan,ya juya ya fita a falon.

Da mugun gudu ta sauko daga saman kujerar,ko ina na jikinta yana rawa

"Mommy,ki bada kayana gobe usaina ta kaimin"

"Ki tsaya ki tafi da kayarki,goben akwai inda zan aiketa"

"Tsaf zai tafi ya barni idan na tsaya jiran hada kaya" tayi maganar a lokacin ma takai bakin qofa.

Lokacin data isa tuni ya tayar da motar,abinda ya tabbatar mata inda ta qara wasu mintuna saidai tazo ta tarar da wajen wayam. Gaba ta bude zata shiga,cikin kaushin murya yace

"Koma baya!" Jiki a sanyaye ta maida murfin ta rufe,ta koma bayan ta zauna,ranta ba haka yaso ba,taso zaman kusa dashi,ta yadda duk maganar da zatayi masa ta tafi cikin kissa da kuma jan hankali.

"Yaa toufeeq" ta kira sunansa sanda suka dauki hanya sosai

"I don't want to hear anything from you har mu qarasa gida,if not kuma,i will drop you" kallonta ta maida ga titunan da suke wucewar,yadda suka dauki shuru saboda daukewar qafa da ababen hawa sakamakon dare daya fara yi,marufar asirinta yin shurun,don tasan kadan ne daga aikinsa ya sauketan kamar yadda ya furta. Ranta ya quntata sosai,dukka wani plan nata ya rushe,manufar da yasa tacewa Mommy tayi masa magana ya sauketa ma ya tashi a banza.

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070

VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k

*Al'ummar NIJER ku kira wannan number don yin naku pyment din*

+22799643131

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥

*H U G U M A*

*_TABARMAR ƘASHI_*💔
Page 33

Shuru ne ya wanzu cikin motar,sai satar kallonsa da take tayi ta cikin madubin motar a duk sanda zasu gifta wani guri dake da wadatar haske,ji takeyi kamar taje ta rungumeshi tsam tsam ko zata ji sassaucin yadda zuciyarta ke azalzala da qaunarsa,burinta da fatanta a yanzu shine Allah ya mallaka mata toufeeq din kota halin yaya ne ma.

A nasa sashen kuwa hadiyar wani abu ke tauri kawai yakeyi daya tsaya masa a wuya,tabbas ya sake amanna da kaidin mata babba ne,babu abinda ba zasu iya aiwatarwa ba,fada da kalmomin da Dr ya gaggaya masa kawai ke yawo a kunnensa,yayi qwafa can qasa yadan daki sitiyarin motar kadan yana jinjina kai,ji yake dama ya buda idanu ya ganta yanzun a gabansa. Dan qara speed na motar yayi saboda wani faduwar gaba da yaji ya ziyarceshi,wani yanayi ne da yakan samu kansa a ciki muddin wani abu zai afku ga fadeela,sai duka ya samu kansa tunaninsa ya koma gida.

Tun kafi ya kammala parking yace mata ta sauka,ta fidda ido tana ganin yadda motar ke slow bata qarasa tsaiwa ba,saita langabe kai zatayi masa salo

"Yaa toufeeq idan na karye fa?"

"Keep quiet,will you drop ko sai na fiddaki da kaina?" Jin haka ya sanya ba shiri ta tattare ta tsallake,Allah yasa motar a sannan ta kammala tsaiwa, zuciyarta kamar zata fashe saboda baqinciki,batasan me yasa yake tozartata haka ba,tanason tayi zuciya ta kuma yi fushi dashi amma ta kasa,shi din fushinka banza ne,rashinsa banza a wajensa,wannan bacin ran ya sanya tayi wucewarta ba tare data tsaya ta kalli inda baaba ramatu ke zaune ita da fadeela ba,wadda ta damu baaba ramatun ta rakota su fito su jira dad dinta,dole ta taso suka bar nanny dinta a ciki.

Yana fitowa daga motar fadeela din ta miqe da sassarfa tayi gurinsa cikin murnar ganin ya dawo da wuri
Chapter 37 · 0% Book details