← Book details Tabarmar Kashi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 171

Sashe 56

Tabarmar Kashi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk da hankalinta ya kusa gushewa amma bata gaza tantance dacin kalamansa a kanta ba,a sannan tarwai take iya tuno sanda afifa dama maama ke jaddada mata tayi iskhara kafin ta bawa adam damar turo magabatansa, murmushi kawai tauiy,tana ganin tunda har Allah yasa abba ya karbeshi ya amince ya turo,duk da su ya Saifullahi basu gama gamsuwa ba,to ba shakka shi din Allahn ya zaba mata,bata kokwanto,bata kuma buqatar qarawa da istikhara din,kada taje hankalinta ya kasu biyu. Kuka takeson yi amma ruwan allurar yabi jikinta,haka tayi shame shame a gurin,ita bame rai ba,hakanan ita ba gawa ba.

Abu daya da bata sani ba shine,yadda take lissafin ranar dawowar su maama haka shima adam yakeyi,ya kuma gama shirya komai,da dukka wasu allurai masu qarfi da za'a sauya mata dasu,wanda zasu sake sakata cikin bacci da maye mai qarfi,su kuma zabura qwaqwalwarta,ta yadda komai qwaqwafi da hasashenka baka isa ka fahimci lafiya qalau take ba.

A washegari aka shiryo raihanatu aka kawota gidan da sunan zata dinga kula da sãahar,saidai duka hakan wani shiri ne da akayi don amintar da zukatan iyalan dr mamman girema. Da qaqqarfar gargadi momee ta tsare raihanatu akan babu ruwanta da dukkan abinda zata ji ko zata gani a gidan adamu,iyakar abinda akace tayi shi zatayi,wanda ba'a sanyata ba kome zai faru kada ta tsoma hannu ko bakinta,sabawa wannan umarnin nata,dai dai yake data rasa rayuwarta gaba daya,maganar datayi mugun daga hankalin raihanatu kenan,fitsari ya balle mata,ta roqi momee kan tayi haquri,kada ma ta kaita,saboda ta fahimci akwai abubuwa masu muni dake faruwa da anty sãahar din mutuniyar kirki me qaunarta,duk da bata gama fahimtar komai dari bisa dari ba,to amma jikinta da zuciyarta sun bata,kumnuwanta kuma sun tsinci kadan daga cikin wasu qulle qullen da momee din keyi tare da adam din.

"Bakin alqalami ya riga ya bushe,tunda har wannan gargadin nawa ya shiga kunnenki dole zargi xai darsu a ranki,tunda zargi ya darsu kuma dole kici gaba da rayuwa damu harmu cimma gaci" tana ji tana gani aka tattarata aka kaita gidan.

Cikin kwana daya tak ta dinga jinta kamar cikin maqabarta take rayuwa,gunji da buge buge hadi da fashe fashen da takanji duk bayan wasu lokuta daga dakin anty sãahar din yana mugun dugunzuma mata hankali tare da daga mata hankali,kamar afifa,itama a jikinta ta dinga jin cewa tabbas sãahar ba zata haukace ba,Allah bazai taba barin mace me kyakkyawar zuciya irinta ta samu tawaya da naqasa irin wannan ba,idan tace ga sau nawa tayi kuka a kwana biyun nan saboda tsananin tausayin sãahar to tayi qarya,cikin dare bata iya bacci,har cikin ruhinta takejin tashin hankali da kuma damuwa da yanayin da sãahar din take ciki,don haka ta dinga shimfida abun sallah tana miqawa ubangiji kokenta akan ya kubutar da sãahar din daga dukkan kaidi da sharrinsu. (Ita kyakkyawar mu'amala da kuma kyakkyawar dabi'a yado takeyi,a yayin daka shiga tsanani,sai dukkan wanda yake tare da kai ko kuma ya sanka sai ya shiga damuwa me tsanani,wanda bai sanka bama sani na haqiqa labarinka yakeji,sai shina zuciyarsa ta shiga tayaka damuwa da kuma alhini,wannan duka sirrin kyakkyawar zuciya da kyakkyawar mu'amala ce,wannan soyayyar daga ubangiji take,a yayin da ya soka saboda nagartarka,sai ya sanya wannan soyayyar taka a zuciyar dukka bayinsa,suyita qaunarka ba tare da kun hada komai dasu ba,wasu ma baka taba yi musu wani abu na kyautatawa da zasu iya nunawa duniya ba,amma dai kawai suna jin labarinka,sai suji soyayyarka ta shiga ruhinsu,ya Allah,kayi mana baiwa da tsarkin zuciya da kuma kyakkyawar mu'amala 👏🏽 da daukacin bayinka)

*_RANA BATA ƘARYA_*

Inji bahaushe,tunda ya samu labarin a gobe ne ake sakaran isowar jirgin KABO AIR da mahajjatan da suka hada da iyalan Dr mamman girema adam ya kasa zaune ya kasa tsaye,a ranar sãahar taga izaya nau'i daban daban,wata allura data sake birkitata akayi mata,tun safe bata farka ba sai yamma liqis,babu azahar ba la'asar,abinda yafi komai qona mata rai. Tana yunqurin tashi yana sanya muqulli ya bude qofar dakin,idanuwansa da suka canza launi suka kuma zuzzurma saboda bala'in da yakeji rayuwarsa tana ciki ya zuba mata,ya tako ya tsaya a kanta,sai kuma ya kalli agogon hannunsa,ya girgiza kai da sauri

"Nafison allurar da tafi wannan qarfi" ya fadi kansa tsaye,saboda ba tun yau ba,baya shakkar fadin dukka wani shiri nasa a kanta,ta dade da gama haddace koshi waye,ainihin tarihin rayuwarsa da komai nasa da yadda ya shirya faruwar komai kawo yau.

Stool ya jawo zuwa gabanta ya zauna,sai ta miqe taja baya da sauri,duk sanda ya zauna gab da ita tana jin kamar ta cinnawa kanta wuta ne saboda tsabar tsanar data yi masa,duk ranar kuma da yayi kwanciyar aure da ita,ikon Allah ne kawai yake sanyata taci gaba da rayuwa. Takanji zuciyarta ta wani irin kumbura kamar zata buga,saidai bakinta baya rabo da kiran sunayen Allah,ta haka kadai take samun sassauci.

Wani mugun murmushi ya saka ganin yadda taja baya

"Kwantar da hankalinki,yau da gobe bana neman komai daga guriki,so nake sai sha'awata ta taru nayi miki wankin babban bargo,ta yadda tafiyama zata gagareki,da haka sai na sake lanqayawa aljanunki nace sun fara ma kwanciya dake,hanya mafi sauqi da zan rattabamiki sakinki uku qwarara bayan na karbe jakata daga gurinki" maganganun nasa sune abinda suka sake fusata qwarai da gaske,karon farko data saki murmushi ta zauna sosai tana kallonsa.

"indai har yanzu wannan jakar tana cikin mafarkinka,ba shakka ba zaka gushe ba cikin buri da fata har qarshen rayuwarka,kayimin duk iya sharrin da zaka yimin,ka laqabamin dukka ciwon dakaga dama,kayimin dukka iya muguntar da kake jin ka iya,amma karka manta,Alla baya bacci,kuma baya barin zalunci,kuma alqawarin ne yayi rantsuwa sai ya taimaki wanda aka zalunta,bani da baqinciki koda ta sanadinka na mutu,amma ina me sake jaddada maka,daukan fansa daga ubangiji tana nan tafe zuwa kanka,a kusa ko a nesa" dariya sosai ya saki,ya dawo gabanta ya tsugunna

"Waya gaya miki inason ki mutu?,kuma ma a hannuna?,har yanzu ina sonki,ina qaunarki,kodon wannan kyakkyawar surar taki da bata gushewa,bin qwaqwafinki da bincikenki ya sanya kika tono wuqar yanka kanki,idan da ace baki zurfafa bincike ba,cikin biyu za'a yi daya,ko muci gaba da rayuwarmu a gefe ina tawa irin rayuwar dana zabawa kaina na kuma saba da ita,ko ki tashi dare daya ki nemeni ki rasa,amma zaki ci karo da takardar sakinki,salin alin koma gaban iyayenki ba tare da kin cutu da komai ba illa dukiyar kawai da zan kwashe,dukiya kuwa ana iya maida madadinta" kamar yau ta fara ganinsa haka ta zuba masa ido,ta karanci cewa yayi wani mugun nisan nisan da ko kira baya ji,tana zaune a nan idanunta suka fara lumshewa,ya miqe ya tsallaketa ya fice abinsa.

*_W A S H E G A R I_*

Tun daga airport su da motocin da suka daukosu basu saukesu ako ina ba sai gidan sãahar din,tun kan hanya afifa ta fara kuka tana jin tsinkewar gaba da tashin hankalin yadda zata riski 'yar uwarta,hakanan maama daurewa kawai takeyi. Iya su yasu ne,yayyenta maza dukkansu sun wuce Egypt suna laluben asibitin da za'a kawota ayi mata magani,don sunce ba zasu iya dawowa su ganta a haka ba.

Mutum biyar ne a falon nasa,malamin bogin da yake kira da sheik usama,sai almajiran daya hayo guda hudu,bude da qur'ani suka karantawa,shi kuma da baisan ko bihim ba yana zaune a qasa,ya tanqwashe qafa yana faman can tasbaharsa me dubu.

Shine ya fara miqewa da sauri sanda su maama ke shigowa falon ya daga musu hannu alamun suyi shuru.

Page 51

*H U G U M A*

*_TABARMAR ƘASHI_*💔

Page 51

"Mahalan,mahalan(ku kwantar da hankali)" ya fadi da sigar lallashi

"Aiki mukeyi,kuma kukanku zai iya bada matsala,ayi haquri da qaddarar Allah,mijinta yana bakin qoqarinsa qwarai da gaske,kuma ko yanzu ma an fara ganin nasara,son ba ko yaushe suka sakata surutan da bige bige ba".

A nan suka zauna cikin matsanancin halin kuka da jimami,shi kansa gidan gaba daya ya sauya yayi wani iri,dama raihanatu tana bakin qoqarin tsaftaceshi da kula dashi,ita kanta tana zaune rakube daga gefe,tausayin iyalin duka ya kamata ganin tashin hankalin da suka shiga da cutar bogin da aka laqabawa matar da bataji ba bata gani ba.

"Ko zan iya ganinta?" Maama ta fada cikin zallar alhini da tashin hankali. Kallon juna adam da malam usama sukayi,sai ya maida dubansa ga maaman

"Bako yaushe ake shiga gurinta ba,saboda hakan yana sakata yunqurin guduwa,da kuma surutai marasa kan gado,amma yanzu barin na fara shiga nayi mata wasu addu'o'i,yadda ba zata cutar da ku ba koda kun shiga din" ya fadi hakanne saboda allurar da aka danqara mata sunason ta fara aiki,jikinta ya saki gaba daya,yadda ko magana ba zata iya dasu ba barw ta fadi wani abun da zata shanshano ainihin batun.

Lokacin da ya shiga dakin ya isketa allurar ta fara mata aiki,ya hadiyi wani yawu muqut yana qare mata kallo,kullum yaga yarinyar sai ransa ya biya,tana da wani mugun kyau da kyakkyawar suffa,Allah Allah yake wataran ya samu dama kamar hakan nan sanda bata da sauran qarfi shima yadan dandanata,ya rage qishirwar dake ransa,baisan ma wanne irin rashin rabo bane ya sanya adam din yake mata wannan izayar,shikam inda shine ya mallaki zuqeqiyar mace irin wannan,baisan wanne asarar bace zata sakashi yayi sakacin da zai rasata ba,ai shi kam zai iya cewa ma Allah ya sallameshi a duniya dai.

Kamar masu cutar rashin kuzari haka suka shigo dakin,su hudu ciki harda afifa da maama,gaba daya dakin a hautsine yake da fasassun abubuwa,wanda duka setup ne. Wani irin kuka afifa ta saki,ta kuma durfafi sãahar a gigice ganin yadda gaba daya ta koma zararriya sak,dakatar da ita malam usama ke shirin yi yana fadin

"Subhanallahi,karki qarasa gareta,na samu nayi musu addu'o'in kashe jiki,karki zaburar dasu" saidai kafin ma ya qarasa bayaninsa tuni ta isa. Rungume sãahar din tayi cikin jikinta,dumin afifan yana ratsata ta sauke wata iriyar qaqqarfar ajiyar zuciya,ta lumshe idanunta da suka kasa sauka daga fuskar maama dinta,tanason koda motsa labbanta ne ta fadi kalmar da maama zata fahimci diyarta lafiya lau take amma ta kasa furta komai.
Chapter 56 · 0% Book details