← Book details Tabarmar Kashi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 171

Sashe 42

Tabarmar Kashi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Mamar adam din nan sam bata yimin ba,wai yaushe ta fara sonki ne bestie?" Aafiyan ta jefawa saahar dake driving tambaya.

Dan qaramin bakinta ta bude cikin alamun mamaki sannan ta bushe da dariya,ta san halin Aafiya ba kowanne mutum bane yake mata a karon farko

"Ni banga aibun momee ba,bata da matsala,tana daukata kamar wata qawarta,bata taba takuramin ba,hasalima bata iya boyen duk wata damuwarta,so kuma ni dama bata taba nunamin qiyayya ba"

"K'nnnnn,haka ne" Aafiya ta fada a taqaice tana jawo wasu takardu dake ajjiye gaban motar sahar din ta tara dubawa,shuru ya ratsa motar kafin ta sake dago kai

"Waye zai bude joint account kuma?"

"Adam ne ya karbosu,bai gayan na waye ba yace na ajjiye masa kawai" saita gyada kai ta maida takardun da ba'a kai ga cikewa ba inda ta daukosu,ta gyara zamanta tana dauko wata hirar daban.

Har bakin mota Aafiya ta rakota,saahar tanata mita

"Wallahi wallahi kin bani mamaki,ban taba zaton aure zai nesantamu ba,tsahon shekara biyu cur amma zan iya irga zuwanki gidana da yatsun hannuna?,wanne laifi mukayi miki?,tun adam na min qorafi har ya koma gorantamin kan cewa baki damu dani ba,ni daya na damu dake,ko yaa zain da yake namiji ya fiki zuwa gida na fa" qaramin murmushi Aafiya ta sake

"Ke kuma sai kika yarda da zancan adam?,ki rabu dashi so yake ya hadamu,aiki bestie kema kin sani,amma na miki alqawarin zuwa in sha Allah ending next month" hannu kawai saahar ta sanya tana rufe qofar motarta

"Kice kawai baki shirya zuwa ba,basai kin fitomin ta haka ba"

"Seriouse,Allah da gaske nake miki" ta fada tana dariya bayan taja ta bata hanya,tana nan tsaye har saahar dake galla mata harara ta mirror din motar ta fice daga gidan,Aafiya ta saki ajiyar zuciya sannan ta juya a hankali tana komawa cikin gidan.

Minti ashirin kacal suka kaita unguwar sharada. Saboda ta danyi gudu ba laifi,bataso taje ta samu adam ya isa yana jiranta.

A farfajiyar gidan ta tsaida motarta ta kasheta ta fito,ta fara takawa cikin nutsuwa da takuntan nan zuwa cikin gidan tana gyara laffayarta.

Gab da zata qarasa qofar da zata sadata da ainihin falon gidan mata biyu suka fito,daya a gaba daya a baya,sai tadanja da baya ta tsaya don basu damar wucewa.

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070

VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k

*Al'ummar NIJER ku kira wannan number don yin naku pyment din*

+22799643131

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥

: *H U G U M A*

*_TABARMAR ƘASHI_*💔
https://arewabooks.com/u/huguma

Page 37

Ta farkon macace da aqalla ta doshi shekara hamsin da biyar,saidai a ido ba zakace haka ba,saboda yanayin yadda take,kallo daya zakayi mata ka fuskanci gogaggiyar macace wadda tasan kan rayuwa sosai,idanunta fes suke,akwai wayewa mai tsanani a tattare da ita,gajeriya ce mai gogaggiyar baqar fata,tana da manyan idanuwa da dogon hanci,wannan ya qawata mata fuska sosai,ta bayan nata kuwa doguwa ce,wannan itace momee din adam,wadda suke kama sosai ta fuska.

"Kina hanya ashe?,har na fidda rai?" Ta fada cikin madaukakiyar fara'a,cikin kunya da kara irin wadda kowacce diya keji ga surukarta saahar tadan duqar dakai

"Ina hanya momee.....barka da yamma,ina wuni?" Ta gaida baquwar dake tare da momee din wadda ta kafeta da idanu cikin wani irin kallo na qurilla,har saahar din na jinsa har cikin jininta.

Da sauri ta murmusa cikin nuna kulawa

"Lafiya lou,kina lafiya?" Ta amsa da hausarta data dan baci kadan,da alama su momee din sun fita qwarewa nesa ba kusa ba

"Lafiya lau alhmdlh"

"Ki shiga ciki bari na rakata na dawo" momee ta fada suna juyawa da baquwar

"Ina mamakin yadda adam ya samu kyakkyawar yarinya haka,kyanta na bani tsoro k......" Saahar ta jiyo muryar baquwar,wadda bata qarasa jin abinda take fadi din ba,katsewa tayi ko nisan data fara yi mata ne bata sani ba,ta sanya kai cikin parlor din momee din,wanda a yanzun ya zama abun sha'awa cike da kayan alatu.

'yar budurwar da ake kira da raihanatu ta amsa sallamar saahar din cikin mayalwacin murmushi da kuma tarin kirki da girmamawar da takewa saahar,ta qaraso da sauri tana karbar ledar hannunta hannu bibbiyu har kamar zata kai qasa tana cewa

"Sannu da zuwa anty" cikin fara'a Sahar din itama ta maida mata

"Sannu raiha sarkin aiki,ya gida ya aiki?"

"Alhamdulillah anty,bari na kawo miki ruwa" ta yiwa ledar guri a wajen,ta juya da sauri ta doshi kitchen dinsu dake manne da parlor din,saahar ta bita da kallo.

Yarinyar diya ce ga qanwar momee,momee din ta dauko riqonta,itake mata komai,kamar yadda yarinyar itama itace komai na gidan,yarinyar nada wani irin hankali kirki da kuma nutsuwa,bata da surutu sam,hakanan bata da shiga shirgin da ba nata ba.

Cikin mintin da bai gaza daya ba raiha ta gabatar ma da saahar drinks masu sanyi hade da ruwa,tana murmushi tace

"Mun cinye abincin rana anty,bamu gama kuma na dare ba kiyi haquri" murmushi ya subuce mata

"Ni ba baquwa bace raihana,kada ki damu" ta girgiza kai tana murmushi itama,har cikin zuciyarta tana jin qaunar anty saahar din,saboda sauqin kai kirkinta kyauta da kuma kyautatawarta,matsayinta dana mahaifinta,kyawunta ko iliminta sam bai sanya mata girman kai ba ko jin ita din wata bace,uwa uba kuma yadda ta dauki momee din a matsayinta na surukarta.

Bata taba komai a ciki ba,don ta fito gida a qoshe,har zuwa sanda momee ta dawo parlon ta zauna tana cewa

"Sannu da zuwa,har na cire rai ai" a kunyace saahar ta saki murmushi,tadan sunkui da kai tana murza zoben hannunta

"Ina sane momee,ga saqon nan" sosai ta washe baki cikin fara'a,ta miqe tsam ta dauko ledar da kanta tana budawa.

Manyan kaji ne broilers da suka qanqare saboda dadewa cikin freezer,cikin ma'aikata gidansu ta sanya wata cikinsu ta ciro mata

"Allah dai yayi miki albarka,ai baqi nayi,duka naman gidan ya qare,gashi ni kuma banason girki babu nama ko kadan" saita qwalawa raiha kira,cikin minti daya ta iso gurin,harara ta jefa mata

"Kina abu kamar kazar da qwai ya fashewa a ciki,dauki wannan naman,ki cire wani daga ciki kiyimin farfesu"

"Tom momee" ta amsa a ladance,ta sukunya ta dauki ledar ta wuce kitchen din.

Kamar ko yaushe hira sosai momee ke janta da ita,harda abinda saahar ke ganin bai shafeta ba,to amma tana baiwa momee din uzurin banbacin al'ada da yare dake tsakaninsu,sannan kuma irin wayewarta daban da wayewar sauran surukai data sani.

Mafi yawa saidai ta amsa da eh ko a'ah,ko kuma tayi murmushi wani lokacin,tun tana zuba idon ganin adam har aka kirayi sallar magariba,a sannan raiha tayi mata jagora zuwa dakinta,duk da momee din tayi mata tayin shiga nata dakin tayi sallar amma sai tace a'ah,don ba zata iya sakewa ba.

Sai a sannan ta samu sukunin kiran adam din,amma harta qaraci ringing dinta bai daga ba,ta haqura ta ajjiye wayar zuciyarta na gaya mata yana sallah ne hala.

Tana idarwa ta sake gwada kirannasa,cikin sa'a ta shiga,ta bada dukkan hankalinta ga wayar tana jira ya daga.

Dab da zata tsinke ya daga din,muryarsa can qasa yayi sallama,ta amsa masa cikin kulawa

"Nayita jiranka dear.....kuma baka shigo ba" dan gyaran murya yayi kadan

"Ban samu na fita din bama,throughout yau ina gida" hankalinta ya sake kaiwa ga muryarsa

"Lafiya kake?"

"Me kika gani?"

"Muryanka was so cool.....kaman jikinka ba qwari"

"Yeah.....bacci nayi ban tashi ba har yamma,shi ya kashemin jiki"

"Alright,na taho kenan?"

"No,ai nayi alqawari,zan shigo saimu dawo tare"

"Okay"

"I missed you" ya fada cikin tsananin kulawa, murmushi ya subuce mata

"I missed you too,saika qaraso" daga haka sukayi sallama ta ajjiye wayar taci gaba da lazuminta,lokaci lokaci tunani yana waftar hankalinta ya kaishi ga wani abu na daban,bata bar dakin ba har sai datayi sallar isha'i.

A falo ta samu momee,ta baje dabgen kajin tana kaiwa ciki,tayi d'ai d'ai saman kujera kamar ita daya ta rage a duniyar.

Raihana ta qwala kira har kusan sau uku a jere

"Maza hadawa diyata abinci taci" ta amsa a aladabce,ba jima ta dawo da babban tray ta ajjiye gabanta

"Zauna mana muci" saahar ta yiwa yarinyar tayi,saita girgiza kai,tamkar taga hararar da momee din ke watsa mata ta gefan ido

"Zanci nawa yanzu anty,wannan naki ne".

Batayi nisa dacin abincin ba ta qoshi,dama ita tun tale tale bata cikin sahun mutanen da abinci ya dama,tana rufe warmers din adam na shigowa.

Hannayensa zube a aljihun wandonsa,cikin wasu shirt da trouser yake sanye,shi din gwanin wanka ne,akwai iya daukan ado me jan hankali,idanunsa a kanta,haka yake mata irin wannan kallon ko gaban waye.

Kallo daya tayi masa ta dauke kanta daga sashensa,yayi mata kyau amma jikinsa babu kuzari kamar yadda taji dazu a waya,sai daya iso cikin Parlor din sannan yayi sallama yana laluben wajen zama,saahar din ta miqe tsam da tray din bayan tayi masa sannu da zuwa ta nufi kitchen dasu,duk da yadda momee ke cewa ta zauna raiha tazo ta kwashe.

A kitchen din ta sameta ta gama cin abincin tana wanke plates din,da hanzari ta karba kwanukan tana mata sannu, murmushi saahar din tayi ganin yadda ta tarbeta kamar wadda tayi wani aiki me yawa

"Aike za'a yiwa sannu"sai kawai taja kujerar plastic ta zauna tana bin yadda raiha ke gudanar da aikin nata cikin nutsuwa,batabar kitchen din ba har sai da adam ya leqo yayi mata magana.

Sunyi gaba shida momee din,ta tsaya tana tattara jakarta data gani a bude,ta danyi mamaki,don tasan a zuge tabar jakar,to amma sai wata zuciyar ta bata may be ta manta ne,a buden ta barta,tunda babu wani baqo cikin gidan bare parlor din bare ta zargi wani abun.

"C'mon momee,please kibar maganar nan" muryar adam kenan dake fita a kasalance idanunsa nakan saahar dake fitowa,waiwayowa momee din tayi kafin ta maida dubanta ga adam

"Okay,amma kayi tunani akai ka gani,think twice kafin yanke hukunci"

"Nasan abinda nakeyi fa" ya amsa mata kai tsaye yana dosar motar saahar da key din ke hannunsa,ya buda mazaunin mai zaman banza yana jira isowarta.
Chapter 42 · 0% Book details