Sashe 38
Tabarmar Kashi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Daddy......dadddd......." Maganar ta kasa fitowa gaba daya,saboda yadda harshenta ya lanqwashe,haruffan suka sarqe cikin na juna,a take kuma kowanne sashe na jikinta ya fara wani irin kakkarwa ta soma lanqwashewa zata kai qasa,kafin takai qasan har ya risketa,ya kuma tallafota ta fada jikinsa ta zube gaba daya,ta fara wata irin jijjiga me qarfin gaske. Duk da cewa ba yau ne ciwonta irin haka ya fara tashi ba,amma har yau har kwanan gobe ya kasa sabawa da irin wannan tashin hankalin da yake tsintar kansa a ciki a duk lokacin da EPILEPSY din fadeela ke fuskanta a rayuwarta ta motsa,komai qwace masa yakeyi,kamar yanzun daya rude gaba daya yana kiran sunanta,wanda zuwa sannan ta zama unconscious.
Tuni baaba ramatu dake qwalla ta kirayi hajiya qarama,ganin dosowarta gurin yasa yayi hanzarin yiwa kansa saiti tare da qoqarin dawowa da kansa dai dai,bai jira isowarsu ba ya dauketa don ya sama mata gurin da zata zama comfortable ya wuce sassansa da ita da wani irin sassarfa yana monitoring numfashinta yadda yake kai kawo yana wani irin riqewa.
Sosai ya kwantar da ita saman lallausar sofa,ya kuma tallafi kanta da pillow me laushi yana kallon numfashinta,a duk sanda take irin wannan abun,sai ya dinga ganin kamar zai rasata,kamar zata tafi ta barshi,hannunsa ya sanya ya juyata barin hannunta na dama don daidaituwar numfashinta da yakeyi kamar zai dauke,yaci gaba da kallonta,yana jin inama ace yana da qarfi ko wata dama da zai iya fidda wannan ciwon daga jikinta?,a ko yaushe saidai ya zauna ya kalleta helpless,har sai ta gama ta dawo hayyacinta.
Maida dubansa ga agogo yayi bayan shudewar wasu mintuna,dai dai sanda hajiya qarama data iso tace
"Ta tashi?" Kai ya girgiza ya jawo wayarsa a gaggauce yana neman number Dr anwar,har yanzu idanunsa nakan agogo yana irga mintunan,bata taba daukar mintuna irin haka ba tare data dawo dai dai ba,abun ya fara daga masa hankali.
Kira daya tak ya daga
"Fadeela ce?" Dr anwar ya fada,saboda layi ne da yasa aka tanadar masa saboda matsala irin wannan
"Gani nan" ya fada kawai
"Kada ka matsa daga inda take,ka barta a right side dinta kaci gaba da monitoring dinta da kuma mintunan"
"Alright" ya fada yana ajjiye wayar da sauri,zuwa lokacin hajiya qarama ta koma kujerar kusa dasu ta zauna,ta hada tagumi hannu bibbiyu tana maimaita kiran sunan Allah cikin nuna tsananin tashin hankali,kauda hankalinsa yayi daga maganganun da takeyi,saboda qara masa tashin hankali da kuma karaya kawai sukeyi. Mintuna biyar kacal Dr anwar ya iso,saboda basu da nisa,layi biyu ne kadai ya rabasu. Shi ya dauketa zuwa clinic na cikin gidan,dab da zasu shiga ta motsa tana bude idanunta a hankali bakinta dauke da sunan
"Daddy" miqa masa ita yayi yace ya qarasa masa da ita ciki,suna hada ido ta saki ajiyar zuciya ta qanqameshi sosai,sai taji zuciyarsa na karyewa,tausayinta da tausayin rayuwarta da kuma tsanar mahaifiyarta data jefata a wannan mummunan yanayin yana sake ratsa kowanne sashe na gangar jikinsa.
Sosai Dr anwar yayi checking dinta don gano abinda yasa jijjigar tata ta dauki lokaci fiye da yadda ta saba,ya ajjiye kayan aikinsa gaba daya yana duban toufeeq,hajiya qarama na zaune daga gefe,baaba ramatu kuma na tsaye daga saman kan fadeelan
"Ya kamata gaskiya a qara ninka kulawar da ake bata,akwai factor's da zasu iya ta'azzara epilepsy din,ta qaru daga adadin mintunan da aka saba yinta" idanunsa da suka sauya launi ya mayar kan baaba ramatu
"Ina fatan nanny dinta tana aikinta?" Dan sunkuyar da kanta tayi,ta fahimci me tambayar tasa take nufi,idan ta bayyana masa gaskiya zai kori yarinyar ne daga bakin aikinta,idan kuma ta boye masa taci amanar mutanen da suka bata yarda,har yanzu batajin yarinyar ta samu kulawa dai dai da wadda Dr anwar ke magana akai,ita din ba komai take iya aiwatarwa ba,kamar kula da magungunan yarinyar da sauran wasu kayan qarin lafiyar,abune na wadanda sukayi karatu,ita kuma bata taba halarta boko ba,iya bakin qoqarinta tanayi wajen kula da fadeela tamkar jikar data fito daga jininta,kowa ya shaida hakan,wasu abubuwan hajiya qaraman ne ya kamata tayisu,to amma ita din ba mazauniya bace,koda mazauniyar ce ma,bata ganin alamun.........
"Ko yaushe ciwon zai iya worsening,me zai hana kayi haquri a jarraba yi mata aiki?" Maganar dr anwar ta katse tunanin baaba rabi. Yayi susa ne a inda yake mata qaiqayi,kullum cikin sallolinta na dare addu'arta tafi qarfi akan ciwon fadeela,Allah ya yanke mata,idan da alkhairi Allah ya fahimtar da mahaifinta mahimmancin aikin nan ayi mata ta huta ta rabu da wannan ciwon,tana matuqar qaunar yarinyar kamar jininta.
"Haba likita?,ya zaka ce haka?"
"Hajiya" baaba ramatu a wannan karon ta sanya baki
"Nima ina ganin abarwa Allah a gwada jarrabawa din,ba'a san inda za'a dace ba"
"Dakata ramatu,ashe baki da hankali kema?" Ta fada cikin fushi
"Ke kinsan ma me ake nufi da yiwa mutum aiki a qwaqwalwa?" Shuru baaba ramatu tayi tana sadda kanta qasa
"Allah ya baki haquri" ta fada a sanyaye tana jin ciwon maganar data yaba mata,shi yasa sai ayi abu dubu cikin gidan bata tofa tata ba,wannan shi ya siya mata kima ya kuma sanya ta dade sosai cikin gidan.
"Relax please" toufeeq dake riqe da hannun fadeela ya fada yana rage girman idonsa,dole hajiya qarama ta koma ta zauna tana huci harda qwafa
"Dr,banason azo ayi abinda zai zama nadama a garemu,kaso mafi rinjaye a aikin nan bashi da tabbas na dawowarta normal,if akayi rashin dace ma abun yana iya qaruwa ko kuma a sake samun wata matsalar bayan ya qarun haka ne?"
"Yes,duka akwai probability na samun hakan"
"Mubar zancan"
"Is ok" kansa ya mayar ga takardar ya sake rubuta mata qarin wasu magungunan ya miqa masa
"Aci gaba da kula da magungunanta da muhallinta,and someone who is very knowledgeable is the one who can takes care of her"
"Thanks" ya furta yana bawa dr anwar din hannu sukayi musabaha sannan yayi musu sallama ya fice.
Matsowa hajiya qarama tayi tana shafa kanta a nutse
"Sannu uktie" daga kai yarinyar tayi ta kalleta,saita sakar mata wani dan malalacin murmushi wanda zai nuna maka jikinta duka ba dadi,qarasowa toufeeq yayi ya bata hannu,ta kama hannunsa ya dagota,ya dauketa cak ya azata a kafadarsa
"Ka bani ita mu wuce sashena ta kwana gurina mana?" Hajiya qarama ta fada
"I can take care of her, don't mind it"
"Okay,ke ramatu,ki tattaro magungunanta ki kawo su,a hado mata da kayan baccinta,ki cewa nanny dinta tazo part dina ta fara mata wanka ta shiryata saina miqo maka ita"
"No,tell her to pack her things,gobe driver ya sauketa a inda aka daukota,she's no longer needed,zan canzata with someone better" yana gama fada ya fara takawa a hankali yana fita daga clinic din,yana jin zuciyarsa kamar zatayi melting down,wani irin yanayi na tsananin kewa da tausayin kawunansu yana tsarga masa.
Shi yayi mata komai kamar yadda yace,ya shiryata cikin fararen kayan bacci masu taushi,ya bata abinci taci,tana ci ta kalleshi da fararen idanunta
"Dad,kaima kaci" kai ya girgiza yana qoqarin sauke murmushi akan fuskarsa
"I can't eat" sai ta bata fuska ta rufe nata bakin,ya fahimci me take nufi don haka yace
"Later angel"
"Sure?" Sai ya gyada mata kai yana lumshe ido.
Ci gaba yayi da kula da ita,har bacci yayi awon gaba da ita,ya zauna a gefanta yana qare mata kallo cike da tausayi,zuciyarsa na gaya masa ya ajjiye komai da komai,ya zauna yayita kula da ita tsahon rayuwarsu.
Qarar wayarsa ta katse masa tunanin daya zurfafa a ciki,yanzun yake shirin kasheta, saboda baya buqatar wata hayaniya kuma,ajiyar zuciya ce ta qwace masa sansa yaga sunan MAJI yana yawo saman screen dinsa,sai ya daga wayar a sanyaye ya kaarata a kunne hadi da yin sallama da muryarsa da tayi laushi qwarai
"Bakayi bacci ba?" Ta tambayeshi bayan sun gaisa da hausarta da ta gauraya da sirkin larabci,cikin wani yanayi na nauyin qirji da kuma tausayi dake can qasan zuciyarta yana cinta
"Yanzu nake shiri"
"Ina fadeela?"
"Tayi bacci" shuru na rashin sabo ya gifta a tsakaninsu sannan tace
"Ka yawaita addu'a tare da miqawa Allah al'amuranka,kana buqatar matar aure ta gari kamar yadda fadeela take buqatar UWA" shuru yayi yana saurarenta,ta saba yi masa wannan maganar dake kama da wasiyya,amma kuma a yaudin tayi masa maganar da bata taba yi masa irinta ba. Shurun da yaji yasa ya gane kiran ya yanke sai kawai ya ajjiye wayar gefe,ya zame daga gefan fadeelan ya kwanta rub da ciki yana sauke idanunsa akan innocent baby face dinta.
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k
*Al'ummar NIJER ku kira wannan number don yin naku pyment din*
+22799643131
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
[8/24, 2:11 PM] KYAUTA: *H U G U M A*
*_TABARMAR ƘASHI_*💔
https://arewabooks.com/u/huguma
Page 34
******Tamkar wadda aka yiwa dukan tsiya haka take dawowa cikin dakin,duk wani karsashi data fita dashi babu shi afifa sam bata lura da sauyin yanayinta ba,saboda lokacin da ta dawo din tana amsa waya ne,tana gamawa kuma ta dora mata da hirar da sukeyi dazun kafin ya fita
"Epilepsy duk bahaushen asali yana mata kallon farfadiya,ciwon da aka dangantashi da aljanu,amma kuma mu a likitance ba aikin aljanu bane,aikin daga gazawar qwaqwalwa ne,na gaya miki dalilan dazu da irin yadda akeson a basu kulawa.....yanzu kuma bari kiga w......" Maqale mata maganar tayi,saboda waiwayowa da tayi taga sãahar din dafe da kanta hannu bibbiyu. Da sauri ta ajjiye system din hannunta dake dauke da zanen qwaqwalwa ta nufi sãahar din
"Me yake faruwa?,kin fita lafiya kuma saiki dawomin a haka?" Ta fada tana dafa kafadarta. Kanta ta dago da idanunta da suka cika da qwalla,cikin matuqar sarewa da mutuwar jiki tace
"Inajin kamar na fara gajiya da rayuwar nan"
"Me kuma ya faru haka ana zaune qalau?,ko yaa muhyi dinne?" Kai ta gyada tana sharce qwallar data ziraro mata