Sashe 142
Tabarmar Kashi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A hankali gofar ta bude, abinda ya kusa tsayar da bugun numfashinta saboda wata qaqgarfar faduwar gaba. Ko ina a jikinta rawa yakeyi sanda likitan ya bayyana a gofar dakin. Zumbur ta mige har wayar hannunta na subucewa ta fadi a gasa, dukkan idanunta a kansa tanason zuwa ta riskeshi taji daga bakinsa amma tsananin tsoron abinda zataji daga gareshi ya hanata aikata hakan.
Lokaci daya kuma gabanta ya sake faduwa fiye da na dazu sakamakon tsintar muryar da bata taba zaton ji ba. Da wani irin sauri ta juya tana kallon qofar farko ta shigowa gurin.
Sajjad ne gefansa kuma toufeeq, nadeeya na biye dasu. Sanye yake cikin wasu lafiyayyun suit da aka saqa da asalin zare me daraja na vicuna giviut fabric.
Kalar suit din data dace da kwantacciyar fatarsa da hutu da kulawa suka ratsata. Idanunta ta sauke kan fuskarsa,abinda ta hanga wani irin shimfidadden bacin rai tare da cushewar fuska,ainihin kamanninsa na cikakken miskili kuma fusataccen MT JARMA take gani muraran, hakanan cikin sassarfa yake takowa fiye da sajjad da nadeeya. Kamar ya sani ko yaji a jikinsa tana kallonsa. Nasa idanun va zube a kanta sanda idanunsu suka sarqe cikin na juna sai taji gafafunta sun fara rawa, bugun zuciyarta ya garu ainun, mararta ta daure tamau yana sake kusantota tana jin kamar ana juyata daga hagu zuwa dama, daga gaba zuwa baya. Sai ta fara gani dishi dishi lokacin da mararta tayi wani mugun murdawa dai dai lokacin kuma da likitan ke magana da harshen jamusanci
"Wo sind Fadeelas Verwandte? Folgen Sie mir ins Büro, es gibt etwas sehr Wichtiges, das ich Ihnen sagen mochte (ina 'yan uwan fadeela?,akwai bayani me matuqar muhimmanci da zanyi muku". Idanunta ta dauke daga kansa tana mayarwa kan likitan dake nufar office dinsa da sauri sauri. Ganinta yana sake zama dishi dishi toufeed na kusantota idanunsa a kanta,lokaci guda kuma taji wani abu me dumi yana ratsa jikinta sannan ya zarto zuwa qafafunta ta cikin lafayar jikinta,sannan ya taba takalminta ya kuma fara sauka a farin marbles din dake shinfide a gurin.
Idanunta takai kai,wani irin abu ya daki
kwanyarta,jini ne, irin jinin da ta taba gani kenan sau biyu a rayuwarta,zamanin rayuwarta a gidan adam,zamanin da take mararin haihuwa da samun iri, yau ga na uku na fita daga jikinta wanda shi kuma wanna bata da tabbacin jinin meye?. Ruf idanunta suka gama fullubewa, tayi baya gaba daya zata zube a wajen,saidai tsananin zafin naman da toufeeq yayi ya hana hakan faruwa.
Cikin zallar tashin hankali ya tarota ta fada a jikinsa. Tuni afifa ta taso kanta, itama nadeeya ta garaso da sassarfa, shi da su kowa na kiran sunanta da garfi hankali tashe, toufeeq din yana jijiga kafadunta,saidai ko alamar motsi batayi ba. Hankalinsa a matugar tashe yake duban jinin dake zuba daga jikinta,sai ya dauketa cak kawai ya wuce office din likitan da gaggawa.
Suna shiga likitan dake rataye lab coat dinsa ya waiwayo,zuwa lokacin tuni ya shimfideta saman gadon dake dakin,cikin rudani ya juye harshen jamusancin shima yana cewa
"'Der Arzt hat ihr schnell das Leben gerettet, ich weiß nicht, was mit ihr passiert ist (Dr ka ceto rayuwarta da hanzari bansan me ya sameta ba)" da gaggawa ya danna wani abu sai ga nurses har biyu sun shigo, ya kalli toufeeq
"Sir, geben Sie uns einen Arbeitsplatz?(sir ko zaka bamu guri muyi aiki?)" Kai toufeeq ya girgiza,yana tsaye qyam a gabanta hannunsa cikin nata,yana jin wani tashin hankali na ratsashi
"Ich kann nicht rausgehen und ihr vor meinen Augen irgendetwas antun(bazan iya fita ba,kuyi mata komai a gabana)". Yadda suka karanceshin sunsan ba zaya fita din ba,abu daya yayi dole ya sake mata hannu don ya basu damar gabatar da aikinsu,ya koma baya kadan hannunsa zube a aljihun suit dinsa, idanunsa da suka sauya launi saboda tsananin tashin hankali qur a kanta tamkar an gaya masa yana janye idanun zai rasata.
Cikin lokaci gangani suka farfado xa ita daga suman da tayi sukayi goqarin tsaida jinin. Bai tsaya ba amma ya ragu,ganin hakan ya sanya likitan ya kunna na'urar scanning ya fahimci ne yakeson yi,sai ya matso gabansa
"Fass es nicht an, lass die Frau es ihrer Tochter antun, ich kann es nicht ertragen, das zu sehen(kada ka tabata,ka bari mace 'yaruwarta tayi mata,bazan jure ganin haka ba)" likitan nada fahimta sosai da kuma saugin kai ya saki murmushi kawai ya matsa baya yana-sakarwa daya nurse din na'urar,har yanzu murmushi yakeyi sannan yace
"Du liebst sie anscheinend sehr, deshalb bist du so eifersuchtig auf sie(kana son ta da yawa da alama, shi yasa kake wannan kishin)" Kansa ya jijiga da qarfi don ya tabbatar masa da girman hakan cikin zuciyarsa
"extreme Liebe(matsanancin so)" ya amsa masa a taqaice.
Idanun likitan nakan allon computer din sanda take scanning din yana kuma yiwa toufeeq din bayani
"Kaine mahaifin fadeela?" Kai ya sake jinjina masa,sal ya waiwayo a nutse ya kalleshi, sannan ya saki murmushi, haka kawai yaji toufeeq yayi masa,ya miga masa hannu yana murmushin
"'Ina tayaka murna,munyi aiki successful irin wanda bamu taba yin kamarsa ba,munyi nasarar cire sashen dake sakata jijiga in sha Allah daga yau zata rayu kamar kowanne mutum, amma zaku kula sosai da qa'idoji da kuma zuwa dubata har ta kammala warkewa duk da dai mun fahimci kamar any amfani da wasu magunguna a kanta da sukaso fadada ciwon ya taba wani sashen daban na qwaqwalwarta,wanda inda hakan ta faru ba zata taba warkewa ba, saidai taci gaba da rayuwa akan magani har qarshen rayuwarta,to sai kukayi dabarar tsaida maganin, abinda yayi nasarar hana afkuwar hakan,kuka kuma yi dabarar kawota akan lokaci akayi mata aikin,Glückwunsch(congratulations)". Wani irin abu me sanyi ne ya sauka saman zuciyarsa tamkar ana sanya sassanyan ruwa ana wanke masa zuciyarsa. Cikin sanyin da mutuwar jiki ya migawa likitan hannu shima
"danke Doktor(na gode dr)". Maida dubansa yayi ga saahar dake numfashi a hankali saboda allurar baccin da yayi mata bayan farfadowarta
"Wanne irin nau'in so zai gwadawa rayuwarta ne?" Ya
tambayi kansa da kansa,shi kansa baisan iya adadin sonda yake mata ba,ga wasu dalilai da suka qara rura wutar qaunarta me tsanani a ransa,shi kam bai sani ba baisanta yadda zai sarrafa wannan soyayya da qaunar da yakej) cikin qirjinsa ba.
"Setzen Sie sich, Herr (zauna yallabai)" likitan ya fada
yana dubansa, koda suka bashi seat din gaban gadontaya maidashi hannunsa cikin nata vana sake kula da dukwani motsinta
"'Zamu bata daki itama,zuwa nan da awa sha biyu zamu tattara bavananta zamu sanar maka" likitan va fadi yana sake nazarin scanning din.
Zafafabiyar
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
"HUGUMA
• TABARMAR KASHI*
Book 02 Page 51
Lokacin da aka fito da ita tana bacci. Afifa so tayi ta rude, toufeeq din ya riga yasan situation din da afifan ke ciki, don haka ya yiwa sajjad din alama na ya jata yabar gurin da ita.
*********Sannu a hankali ta dinga bude idanunta da taji sun dan mata nauyi ga kuma hasken da ya cikasu. Yana zaune a gabanta hannunsa cikin nata,ko motsi baya yi da idanunsa bare hannun nasa dake dame da nata.
A nutse ya miga hannunsa zuwa saman goshinta don tabbatar da farkawarta. Dumin hannunsa dake saman goshin nata ya sakata dauke idanunta daga kan maji dake zaune gefe daya saman kujera ta dawo dashi kansa. Sarqewa idanunsun sukayi cikin na juna,ta dan zuba masa ido tanason tabbatar da shi dinne?, har yanzu akwai fushin nan saman fuskarsa ko kuma yayi qaura?.
Hawaye ne suka fara tsatstsafowa idanunta,idonsa ya lumshe sannan ya bude yana girgiza mata kai alamar a'ah dai dai lokacin maji ta dawo da dubanta kansu,ta matso a nutse tana fadin
"Ta farka ne?"
"Eh" ya amsawa maii din. Qogarin zame hannunta daga nashi takeyi saboda gain maji a wajen, amma saidai bashi da niyyar motsawa daga wajen ma bare ya bari ta zame hannun nata.
"Sannu d'iyata" maji ta fada cikin kulawa. Kai ta gyada mata sannan ta motsa bakinta a hankali
"Yauwa" ta amsa mata,dai dai lokacin likitan ya shigo, bayansa afifa ne ita da sajjad. Dukkansu kayan data gani a jikinsu a daxun yanzu basu bane ba,da alama ta dauki wasu awanni kenan tana bacci ba tare da tasan abinda yake faruwa ba.
Sannu suka yiwa likitan, afifa ta matso tayi mata sannu sannan suka juya dukka suna fita saboda bawa likitan damar dubata, banda toufeeq da ya gara matse hannunsa cikin nata.
Wannan karon cikin harshen turanci likitan yake masa bayani
"'Ina mai baka haguri, ta samu bari na ciki dan sati hudu"
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Allahumma ajirni fi musibati, wa'akhlifni khairan minha" ya furta yana runtse idanunsa.
Har cikin saman kansa ya dinga jin wani abu, sai ya kasa ci gaba da tsaiwar,ya koma a hankali ya zauna saman kujerar yana ci gaba da rige hannunta,kana ya sauke idanunsa a kanta.
Tunda likitan ya fadi maganar taji kamar an sauke mata dutse mai nauyi a girjinta
"Anya tana rabon ganin qwanta a duniya?" Tambayar data yiwa kanta kenan,tana jin numfashinta kamar yana mata wahalar shaqa.
"Akwai abinda yadan raunata qarfin mahaifarta,don haka tana da dan rauni,wanda cikakken motsi ko zirga zirga me yawa,ko kuma razana suna iya kawo mata miscarriage" idanunsa ya mayar kan likitan,yana jin zuciyarsa na quna
"Yanzu sai yaushe zata iya sake conceiving?" Maganar ta sanya likitan dagowa ya dubeshi tare da sakin qaramin murmushi
"Kada ka damu yallabai, indai za'a kula da ita yadda ya kamata, maida wani babyn bazai zama abu me wahala ba"
Magunguna ya rubuta cikin file din sannan ya ajiye yana qara masa was bayanai sannan ya juya ya fita. Ya barshi cikin wani irin yanayi,ya dinga ji kamar laifinsa ne, kamar shi yayi sakacin da cikin ya fita,amma bai sani ba ba shakka inda yasan akwai ajiyarsa tattare da ita ko sama da gasa zasu hade bazai bari tayi tafiyar ba. Shi daya yasan yadda Allah ya jarabceshi da son tara zuri'a,musamman a yanzun a yadda yake,Allah yayi masa dukkan wata ni'ima da sutura ta rayuwa.