← Book details Tabarmar Kashi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 166 OF 171

Sashe 166

Tabarmar Kashi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kuiera nadeeya ta bashi, sai ya jawota gaban gadon ya dora gafarsa kawai akai, fili yake da bugata su bashi,saboda kyakkyawar runguma ce yake gain tafi dacewa da ita. Idanunsa cikin nata yana jin kamar zasu narke su zama abu guda. Cikin hikimar manya maji da baaba ramatu suka mige zasu fice, abinda ya sanya nadeeya fadeela anty farheen da anty samreen suma bin bayansu. Afifa ce dake cikin babban mayafi tana baiwa baby nono ita da sajjad basu fita din ba. A gefansu nadeeya ta jere yaran tana cewa

"Maji din ta fita ai, saiki sake ki qare wa kayanki kallo antyN" ta fadi cikin dariyar tokana tana yin gofa da sauri gudun kada toufeeq din yakai masga.

Hannunsa ya mige ya rige tafin hannunta cikin nashi yana ci gaba da yi mata wannan tattausan kallon

"Yanzu Madam kishi kadai dama ya isa tayar da naquda har a haihu?" Ya fadi cikin salon tsokana kadan. Kai ta langabe tana kallonsa tana kuma satar kallon afifa,ta tabbatar idan afifa taji ta shiga uku da tsokana.

Murmushi ya sake mata yana kanne mata ido d'aya.

"Idan nace sannunki Allah yayi miki albarka batayi kadan ba?" Kai ta gyada cikin murmushi tana kallonsa itama

"Ida nace na gode qwarai, Allah ya sanya mahaifanki cikin aljanna madaukakiya shima baiyi kadan ba?" Nan ma kai ta jinjina tana murmushi zuciyarta cike fal da mahaukaciyar soyayyarsa,sai ta motsa bakinta a hankali itama

"Dukkan wadannan kalmomi naka masu tarin tsada da daraja ne"

"Kamar vadda kike da tsada da darajar da bansan
adadinta ba a idanuna, bude idanunki mu kalli tsarabar
da kika kawomin a tare" ya fadi yana miga hannunsa
cikin takatsantsan da kulawa ya soma bude fuskokin
varan
"Yes!, ma sha Allah, Allah banyi wahalar banza ba" ya fadi
kansa tsaye yana ma mantawa dasu sajjad dake dakin.
Da sauri saahar ta rufe bakinta saboda kunya,sai sajjad
din ya tattara towel din ahlam yana cewa
"Oya let's go, muje ki garasa bata ko cikin mota ne" ai da
gudun tsiya afifan ta rungume diyarta suna ficewa kada
ayi barin zance a gabanta
"Ai da kunyi zamanku" toufeeq ya fadiwa sajjad cikin
gatse sai sajjad din ya gyalgyale da dariya baiko waiwayo
ba
"Bestienkin nan da sajjad original 'yan sanya ido ne" yayi
maganar sanda ya Sanya hannu yana gogarin daukar
babyn ya zauna a gurin
"Ko yaushe gana fadi min muna basu mamaki, basu taba
tsammanin soyayya zatayi mana mummunan kamu har
haka ba"

"Sai gashi tayi mana kamu me kyau harda result" ya furta yana sake bude fuskar dayan baby din, suna nannade cikin wasu lausasan shawl farare gal masu ratsin blue a jiki

Har wani lumshe ido yakeyi sanda yake kallon fuskar varan

"Na yarda ni din jarumi ne, duka vara na ahalina suke daukowa,kiyi haquri ina miki fatan nasara a gaba" kukan shagwaba ta sakar masa, sai ya saki dariya sosai kaman ba MUHAMMAD TAUFEEQ JARMA ba

"Eh, next time ina expecting baby girls twins, zan tayaki addu'ar samun masu kama dake, don nima ina kwadayin* nayita kallon kyakkyawar fuskar nan ta cika kowacce kusurwa ta gida na" sai ya sunkuya a tausashe yayi
U kissing dinsu su duka sannan ya juya kunnuwansu yayi musu khuduba “Muhammad da Mahmud" ya fadi yana kallonta. Farinciki ne sosar ya ratsata, tabbas taji dadin wannan zabin nasa,dama tun asali sunaye ne masu asali

"Allah ya raya dr girema da dr jarma" ta furta a hankali Ameen,let me hug you please ko zan samu sassaucin abinda nakeli na farinciki a zuciyata" ba musu ta bude masa hannayenta,yayi mata kyakkyawar runguma yana sauke ajiyar zuciya idanunsa akan yaran.

Awanni shida kacal aka rubuta mata sallama cikin aminci da goshin lafiya. Tunda yaji maji na zancan tafiya da ita ta kula da ita ya kasa ya tsare. Koda aka rubuta sallamar sai daya kwashesu ya kaisu motarsa sannan ya gaya musu batun sallamar, kafin maji ta ankara tuni motarsa ta dauki hanyar gidansa, don ko kadan bazai iva jumurin rashinsu a kusa ba. Yanzunne yakejin kansa a cikakken magidanci,wanda ya hada dukkan wata falala da farinciki na rayuwa.

Hakanan maji ta gama salatinta ta haqura

"Muhammad ya maidani kakarsa Allah da gaske" haka tayiya mita tana fada. Nadeeya na gefe tana dariya

"Maji, shifa yaa moha har yanzun farin shiga ne,sai yanzu yasan meye dadin family ki bar masa matarsa da yaransa"

"Allah baiko isa ba, dole na gyara diyata, idan yaso su garata,amma dai yara shima yasan bashi kadai ke dasu ba"

"Ah lallai maji akwai kallo kenan,nan gaba kwashesu zakiyi"

"Zasu haifa wasu in sha Allah" ta fadi, don har ga Allah a son ranta ma su koma gidanta da zama.

Wani irin alheri albarka da farinjini yaran sukazo dashi,yadda gidan yake cika kullum saika dauka suna akeyi kullum. Saahar sai yanzu ta sake amanna da gasken gaske 'ya'ya rahama ne,da gaske haihuwa wata falala da baiwa ce daga ubangiji,wani irin budi da alkhairi ita kanta take gani tako ina. Gadan gadan ake shirya I katafaren suna, duk wani taro na biki da basuyi ba toufeeg ya shirya fansheshi a ranar sunan,ya tsara walima ta musamman shi da abokansa, haka bangaren mata da zasuyi nasu cikin yalwatacciyar harabar gidan.

Zafafabiyar
"HUGUMA*

*_TABARMAR KASHI*

Book 02 Page 73

Qarfe takwas na dare ta fito daga wanka,wanka
ne sosai na jego akeyi mata da dalbejiya,jego takeyi na gaske wanda aka sani a qasar hausa,qanwar maama da maji suka tsaya kan hakan, tuwo kunun gyada wankan darbejiya da gasashen nama bata wasa dashi.

Yaran duka na nannade cikin was kayan babies masu taushi da daukan idanu 'yan qasan turkey,gaba daya ubansu ya maidasu kamar shi, kullum shigar fararen kayan babies suke,komai nasu fari qal sai ratsin blue wani lokaci.

Afifa da nadeeya ne cikin bedroom din
nata, fararen hannuwan nan nata da gafarta sunsha jan lallen suna har bayan hannunta,wani irin dan ubansun lalle kamar ka daye shi daga fatarta, kanta ma yasha gyara na musamman sai gyallin da gamshi yake fiddawa,ta cika ta sake yin dam ta zama 'yar duma duma,don da gasken gaske take gyaran kanta.
Tana gogarin shirya kanta nadeeya tace

"Kada na manta na shiga uku,yaa moha ya kira yace ki sameshi a sassansa, kada ki manta ki tafi masa da
Asad(Muhammad) da as'ad(Mahmud)" amsa mata tayi
da to,sannan ta waiwaya a nutse ta fara gyara jikinta.
Cikin minti talatin kacal ta fito cikin lallausan
material baby pink color da kalae sea blue a jikinsa,tayi
sassanyan kyan nan nata da ya cakude da kyan jego,tayi fresh sosai, jikinta sai qamshin turarenta yake fitarwa.
Baki afifa ta saki tana kallonta sanda ta dauki
asad da as'ad
"Anya kuwa? ,kada fa kije ki ballowa kanki ruwa" ta fadi tana dubanta.

"Ruwa wanne iri?" Gyara zamanta afifa tayi

"To don Allah kina jego inake ina buga irin wannan kwalliyar?" Harara säahar ta sakar mata

"Kefa kin cika sharri, har yanzu bakisan an girma ba? ina kikaga nayi kwalliya a nan?" Tabo nadeeya daketa danne danne a wayaa afifa tayi

"Sister nadiya tayani gani, don Allah ko ke bata dauki idanunki ba bare me gida?" Kame kanta nadeeya tayi tana danne dariyarta

"Anty afifa,na rabaki da shiga sha'anin yaa mohaa da ,anty N,wallahi lamarin yafi qarfina, kame kaina nakeyi kafin naji ya moha ya kirani da munafuka" saita mayar da kanta kan wayar ta tana murmushi qasa qasa
"Kanku akeii" säahar ta fada tana rungume yaran ta fice. dasu

"Su sãahar dadi miji" afifa ta fadi cikin dan daga muryar duk dai cikin salon tsokana.

A tausashe tayi sallama sassan nasa. Ya daga kansa daga zaunen da yake, sai ya ajjiye duk abinda yakeyi cikin lallausan murmushinsa ya taso yana takowa zuwa gareta idanunshi a kansu. Sanye da wasu pyjama ruwan sararin samaniya. Har ya qarasa gareta idanunsa suna karakaina a kanta,yana jin wata qaunar ahalin nasa tana gewayeshi.

Hannu ya miga ya shafi gefan fuskarta cikin murmushi idanunsa cikin nata,sai ya miqa hannu yana karbar asad

"Barka da zuwa giwa ta" ya furta cike da wani irin launin soyyaya da ya haifar da murmushi me qayatarwa saman fuskarta

"Barka kadai aljanna ta" itama ta maida masa tana juya qwayar idanunta a kansa. A nutse ya juya yana shiga ciki vana fadin

"Bari nayi hanzarin matsawa, those beautiful eyes..
Sai bai garasa ba ya saki murmushin da sai da ya bata dariya.

Da d'aya da d'aya ya kwantar da asad da as'ad,a nutse ya waiwayo yana kallonta, har yanzu wannan murmushin bai bace a fuskarsa ba. Hannunsa ya sanya ya riqe nata hannun yana murzawa da vatsuntsa a hankali, idanunsa na biye da kowanne zane na jan lallen hannunta da yayi masifar daukar hankalinsa

"This henna..." Shuru ya sakeyi yana cije lip's dinsa. Sai kuma ya daga kansa yana kallonta

"It's been a long day,i need one of those tight hug"
zame hannuwanta tayi, taja baya a nutse, ta buda masa dukkan hannuwanta. A hankali ya sake matsowa gabanta,ya buda shima masa hannayen ya cusasu ta bayanta ya shige jikinta sosai yana kwantar da kansa saman kafadarta ita kuma ta maida hannuwan nata ta lullubeshi tsam. Duk da bata iya ratsashi ba amma wani irin nutsuwa yakeji tana saukar masa,yayi imani da gaske ne babu abinda yakai mace ta gari bayar da nutsuwa da kwanciyar hankalin mazaje.

"Your touch and your kisses are my weakness" ya furta dai dai saitin kunnenta, abinda ya sanya tsigar jikinta tashi. Ta sani yayi missing kiss ne,saboda tasan yana daya daga cikin abinda yakeso yake kuma rage masa zafi. Dan ja baya tayi kadan,abinda ya basu damar ganin fuskar juna sosai

"Please stop being cute,it makes me want cuddle with you forever" ya garasa fada yana cije lip's dinsa. Hannu tasa ta dan ja kumatunsa tana murmushi

"I can't taste my lips, could you do it for me?" Rigota yayi sosai cikin jikinsa vana murmushi
Chapter 166 · 0% Book details