← Book details Tabarmar Kashi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 159 OF 171

Sashe 159

Tabarmar Kashi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yadda soyayyar mahaifinsu ke haukata a ranta, haka kullum rana takejin soyyayar 'yan tayin. Duk wannan abun kuma sai taga kamar toufeeq ya fita gaunarsu da nuna tsantsar kulawa. Kullum Allah shine da kullum sai yayi aqalla mintuna kusan hudu ko biyar kunnensa yana saman mararta wai yana gaisawa da biyunsa, hakanan kullum sai ya sanya tape ya auna tsaho da fadin cikin wai yaga sun qara girma?. Tun abun yana bata dariya harma ta riga data saba.

"I love you and your daddy so much"

"'Daddyn nasu shima yana masiliifar gaunar mamansu" taji an fada daga bayanta. Da hanzari ta juyo don bata tsammaci tsaiwarsa a gurin ba. Yana jingine da gofa hannuwansa goye a qirjinsa yana mata wani narkakken kallo. Sosai kunya ta kamata, batasan me yasa yakejin dadin yi mata labe yaji tace masa i love you ba, kunyar ta sanyata jan gefan mayafin boubou din tana sunne fuskarta a jiki.

Dukka hannuwansa va bude mata yana dariya

"Come-on babe bea, ba kalmar da yafi dadi a bakinki irin inji kince I LOVE YOU MY NUGGET the best name da nafiso bayan duk wani suna da za'a kirani da shi idan ka cire MUHAMMAD dina, taho taho" y fada yana sake ware mata hannuwansa.

Iya takun data iss gareshi kawai sun tafi da imaninsa,sanann ya sanya tana isa gareshi ya bata hotties kisses ssman fuskarta wuyanta da goshinta,ya tsugunna sukayi hirarsu da yaransa kamar yadda yake fada sannan ya riqe hannunta suka nufi main parlor na gidan kamar yadda aka sanar masa.

Kamar ma kowa su yake jira,don duk sun samu kowa cikin parlor din, maji na zaune gefe guda ita da nadeeya suna magana qasa qasa, fadeela na cinyar Dr jarma,hajiya qarama haseena na gefanta itama,hakama hajya mansura labiba na zaune daura da ita.

Kallo daya zaka yiwa kowa dake wajen kasan zukata na cike da abubuwa masu tarin vawa da zukatan kadai aka barwa sani akan su. Sallamarsu ta maida hankula a kansu,zukatan maji dr nadeeya da fadeela cike da farinciki da alfaharin ganinsu. Yayin da mansura labiba da hajiya qarama abubuwan da suke zakatansu sun banbanta da na juna.

Wani irin kallo na qurilla hajiya garama takebin säahar dashi, irin kallon da tunda suka je germany har suka dawo bata yi masa irinsa ba sai yau.

Qirjinta yayi wani mugun bugawa sanda sahar din ke kaiwa gasa tana musu barka da warhaka. Idanunta ta maida ta kulle tana fadin

""Na shiga uku" saboda tudun data hanga daga gasan mararta

"Yaushe tayi wani cikin har ya fito?, bayan a yanzun shine lokacin da zanyi kyakkyawan shirin cireta daga jarma family?, fita kuwa ta har abada? ba irin fitar da ameesha tayi ba tabar musu irin FADEELA?, ko dama qarya yakeyi mata toufeeq?, dama ba miscarriage tayi ba?" Wani mugun sarawa kanta yayi, har sai da takai hannunta da ya fara rawa ta dafe kanta tana sake kulle idanunta

"Relax.....relax mana fauziyya‚u are a strong woman" ta gayawa kanta da kanta, saita bude idanunta cike da qwarin gwiwa tana furzar da iska me zafi daga bakinta.

Kowa ya kama gurin zamansa,kamar yadda toufeed ke zaune kusa da säahar din, nadeeya da hajiya mansura ne suke serving, saidai shi din kuma ya kasa ya tsare. Bayajin zai iya barinta taci komai dake wajen, zuwa yanzu mutum uku ya yarda dasu akan säahar din. Maji cs ta farko sai nadeeya sai kuma baaba ramatu.

"Me zakici ne surukata?" Hajiya qarama dake fidda shu'umin murmushi ta tambayi sahar idanunta yana tsakanin fuska da cikin säahar. Motsawa kadan säahar tayi, bagin matar yana sake mamaye zuciyarta,taso ace wannan tambayar tayi mata ita ne lokacin da babu mutanen da takejin nauyi da ganin qimarsu a wajen, tabbas da ta bata cikakkiyar amsar da zata isar da
L sago, ba iya kanta kadai ba,har izuwa kunnuwan gadangarun 'yammatan dakeson shiga rayuwar toufeeq din nata.

"Karki damu da abinda zataci,ke dai ki lura da abinda zai iya zuwa gabanki" toufeeq ya bata amsar da wani irin qwarin gwiwa hadi da wani tsattsauran kallo cikin idanunsa. A hankali ta janye idanunta daga kansa gabanta yana faduwa,iya kallon da toufeea yakeyi mata a yau ya dasa gaqgarfan zargi a ranta

"Akwai abinda yake faruwa" ta bawa kanta amsa.
"Tabbas akwai ayar tambaya,tsahon shekaru sama da ashirin ban taba gain irin wannan kallon daga idanun Muhammad ba" ta sake jaddadawa kanta tana recalling abubuwan da suke faffaru tsahon satittikan da sukayita wucewa.

Zafafabiyar
"HUGUMA*

_TABARMAR KASHI_*

Book 02 Page 66

Maji kamar bata a wajen,saidai tana ankare da komai, dr jarma da hankalinsa duka yake akan majin da duk wani motsi nata,ya dan waiwaya sashenta

"Shifa matsomin da wannan ruwan na gabanki na wanke hannuna" cokalin hannun hajiya mansura ne ya subuce ya fadi, ta watsa kallonta ga dr jarma. Alamu da dama suna mata nuni da yiwuwar faruwar was al'amura

"Meye hadinka da tsohuwar matarka da zata baka ruwan wanke hannu?,duk da nayi kara da alkunyar ciyar da abincin da na girka da hannuna ba tare da nayi qorafi ba"

"'Matarsa dai a karo na biyu ko?" Muryar hajiya qarama ta ratsa hargagin mansura. A gigice mansura ta waiwayo tana kallon fauziyya. Murmushin nan nata dake dauke da tarin ma'anoni ta jefeta dashi

"Af, nayi hanzarin shaida miki maganar da ba'a bakina ya kamata a jita ba ko?, to tunda dai na riga na fada bari na garasa miki.

"Ya isa fauziyya" Dr jarma ya dakatar da hajiya qarama a tsawace

"Da dai ka barni na qarasa yaaya" ta sake fadi tana sakin garamar dariyar da zaka dauka cikin tarin zallar nishadi take

"Da gaske ne abinda fauziyya take gayamin?" Hajiya mansura da tashi d'aya kamanninta suka juye saboda zallar tashin hankali ta furta

"Samu guri ki zauna muyi magana,wanann zaman bana hayaniya bane" dr jarma ya fada cikin nutsuwa da tsare gida

"Ban bugatar zama mahmud,amsa nake nema eh ko a'ah" ta fadi tana rige qugunta wutar bala'i da masifa tana ruruwa saman fuskarta.

Toufeeq da kansa ke duqe,tunda hayaniyar ta fara tashi kansa yake a qasa yana son hadiye nasa bacin ran sal a sannan ya daga kai yana kallon mansura,cikin kakkausar murya yace

"Malama ki zauna akace!!" Ya fada a dan tsawace da bacin rai, ita da hajiya garama din suna cikin sahun farko da a yanzun baisan me ya tsana kamarsu ba

"Karka sake magana toufeeq, ba huruminka bane" mai tace dashi tana tsare gida. Motsawa yayi alamun zai mige yabar wajen, don bayajin zai iya jurewa kallon mansurar tana yiwa Dr haka

"Koma ka zauna, matsala ce da ta shafi kowa da kowa"

Dr jarma ya fadi, sannan ya mayar da dubansa ga mansura

"Shifa matatace ta lalle uwar 'ya'yana,matar da duk duniya tayimin abinda ko.mahaifiyata iya abinda zata iya yimin kenan,wata gaddara da bansan meye silar faruwarta ba ta datse igiyar aurena da ita,na jima ina addu'a da bansan iya adadinta ba,a yanzun haka shifa na matsayin matata ta sunnah, an maida aurenmu a Algeria qarqashin jagorancin kawunta"

"Tabbas!" Hajiya garama ta rufe da fadin haka duk da bata jin ko mansurar tana jin dacin da takeji a zuciyarta akan dawowar maji gargashin igiyar auren dr jarma din.

Saidai a yanzun mansurar ce first target dinta, tanason ta nuna mata ruwa ba sa'an kwando bane.

"Mahmud saidai kuwa ka zaba,ko ni ko shifa wallahi tallahi!" Ta furta tana buga table din gabanta

"'Maji kina gani fa!" Toufeeq ya fada yana yunqurin migewa cikin huci

"Koma ka zauna Muhammad!" Ta sake daka masa tsawa.

Da garfi ya koma ya zaune kan kujerar tasa. Säahar da ta tsorata da irin fushin da take gani kan fuskarsa ta laluba hannunsa cikin tafin hannunta. A hankali ya juyo ya zuba mata jajayen idanunsa, sai ta lumshe idanunta hadi da budesu ta kuma matse hannunsun guri guda, abinda ya kawo wani gwaggwaban gudun mawa,ya sauke wata nannauyar ajiyar zuciya can qasa yadda babu me jinsa yace

“can't take it moon"

"For maji's sake" ta maida masa a taqaice.

"Bazan tsaya doguwar magana ko bata bakina wajen gaya miki na san wacace ke, nasan irin zaman da nayi dake dukka shekarun da muka kwashe ba,amma ina me shaida miki na bar miki dukka dukiyata da kika dinga diba da kadan da kadan kina tarawa….amma kuma ina me farincikin shaida miki,NA ZABI SHIFA, NA ZABI SHIFA,NA ZABI SHIFA, don haka na sakeki saki daya,na sakeki saki biyu....”

"Dr!" Maji ta gwala kiran sunansa da garfi saboda ta fahimci me yake shirin qarasawa aikatawa,saidai kiran sunan nasa da tayi sam bai sakashi ya dakata ba sai daya kai inda yakeso yakai din

"Na sakeki saki uku ni Mahmud jarma, ku shaida" tsaf labiba dake zaune saman daya daga cikin kujerun dining din ta sulale tayi zaman dirshan qasan marbles din dake gurin ta saki wani irin kukan tashin hankali. Cikin izza da tagama da madaukakin farinciki haseena dake daura da ita ta waiwaya tana kallonta,sai taja kujerarta gefe tana tabe baki

"Su ungulu sai a shirya komawa gidan tsamiya ko?, abar masu abu da abunsu, banzar da akazo ci bata samu yadda akeso ba,sai a tashi aje gida". Maganganun haseenan sun sake jefa labiba cikin magurar tashin hankali, don me yasa mommyn zata bari har haka ta faru? me yasa zata janyo mata wanna babbar asarar?, gwara ita ta samu ta abinda ta samu,ta kuma tara abinda ta tara, amma ita fa?,ba toufeeq din, kuma bata tara komai ba.

Kai tsaye mansura ta juyo tana aje kallonta ga hajiya qarama, ta san shaidanci da shu'umancinta,lallai ita fa qulla wanna abun, dawowar shifa da kuma sakin da dr jarma yayi mata a yanzun, saidai batasan cewa har kanta da kanta ta ballowa ruwan ba

"Tabbas kin cika shu' uma,sannan na sake yarda ke kike aura masa mata ki kuma saketa a duk sanda kikaso kamar yadda kikayi igirari...... Mahmud" ta fadi tana waiwaya ga dr jarma. Yadda ta kira sunan nasa yaja hankalinsa
Chapter 159 · 0% Book details