← Book details Tabarmar Kashi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 171

Sashe 72

Tabarmar Kashi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

64

* TABARMAR KASHI_*

Page 64

"barka da warhaka yaa toufeeg" daga can daya sashen aka fada cikin d'ari d'ari,kamar me tsoron yin magana

"Barka" ya fada a dake kuma a taqaice

"Ya aiki yaa?"

"'Alhamdulillah" ya sake amsa mata a taqaice,duk sai taji ba dadi,saboda ba haka suka saba yin waya ba,ba kuma da irin wannan yanayin yake magana da ita ba,duk da ta saba da miskilancin sa,amma yanayinsa na yanzu ba dashi suka saba magana ba

"Yaaya upper week zan dawo gida,finally na gama exam dina,zaman canada ya qare"

"Good.....ina miki murna" ya sake amsa mata a taqaice. Marairaicewa tayi zuciyarta na karyewa,tamkar tana a gabansa

"Am sorry yaaya"

"Sorry for what?" Yayi tambayar hankali kwance kamar dai da gaske baisan abinda yake faruwa din ba

"Yaaya,nasan kasan nayi maka laifi,amma wallahi it was not my fault,tanata sakamin pressure akan tanason ganin FADEELA..

"Ki gaya mata,ta sanya a ranta bata haifi wata 'ya ba a duniya kwata kwata,fadeela a yanzun ba jininta bace" yayi maganar cikin zafi tamkar itace a gabansa. Laqwas NADEEYA tayi cikin toro da firgicin jin sautin muryarsa mara hayaniya lokaci guda ta cika da kauri.
Iska yadan furzar yadda nadeeya din tayi shuru ya tabbatar masa ta tsorata da yadda yay maganar ne,sai ya lumshe idonsa yana gogarin yiwa kansa saiti,bayan ratsawar shuru na wasu sakanni sal yace
"Ticket din wacce rana kikayi booking?"

"Sunday" ta fada a sanyaye

"Alright,zan dawo miki da abinda kika kashe,don nayi fushi bashi zai baki lasisin yiwa kanki wata hidima ba,don't tray to buy anything da kudinki,as long as iam alive"

"In sha Allah" ta amsa masa a sanyaye, zuciyarta cike fal da qauna da kuma soyayyarsa,irin zallar soyayyar yan uwantaka,wadda babu algus a ciki. Labarai kadan ta bashi suka katse kiran,don ta fuskanci yanayinsa kamar he's not in mood.
Ya jima da wayarsa a hannu yana jujjuyata ba tare da iya yin komai ba,haka kawai wasu abubuwa na rayuwa suke dauko kansu suna kawo kansu da kansu gabansa,rayuwarsu yadda ta gudana shi da
'yaruwarsa,shekara kusan ashirin da biyar baya.

Ajiyar zuciya hade zazzafar iska ya fesar,ya sake juya wayar a hannunsa sannan ya lalubi number hajiya qarama.

Tashi tayi ta zauna sasai tana cire hankalinta daga lissafin ribar kayan data kawo daga china da suka samu qarewa,ta

bada dukka hankalinta akan wayar ganin me sunan,tayi gyaran murya sannan ta saka wayar a kunnenta.

"Barka da dare"

"Barka kadai,yanzu yanzu na shigo daga gurin mutuniyar,suna can ita da nannynta suna shirin bacci"

"Ummm,yayi,batun nanny dinne dama na kira,nawa ta buqaci albashinta?" Wuyan rigar lace din jikinta ta gyara

"Har yanzu taqi fadin nawa,ni bansan kalar nanny din da muka samo ba wannan karon,nayi mata zancan kudin amma sai tacemin ba komai,aikin yafi kudin muhimmanci" gyara zamansa yayi,shima maganar ta dan bashi mamaki

"'Noo,ta fadi ko nawan ne,sai a yiwa elyas magana,a dinga cire mata on time " yayi maganar ne har qasan zuciyarsa, yana lua hangen canji qarara daga fadeela,a yadda zuciya da ransa sukayi masa dadi,yana ganin ko nawa ne ta bugaci a biyata baiyi tsada ba

"Okay,i will talk to her'

"Yayi' ya amsa a kasalance,tanaso su tattauna wasu abubuwa amma ya bata uzurinta,sai tayi masa addu'a sosai sannan ya katse wayar,ya jefara gefe yana jin dukka gabban jikinsa suna sake zama weak,don haka sai ya kwashe wayoyinsa yabar dukka sauran tarkacen a gurin, saboda akwai wadanda xasu gyara gurin,komai kuma su sanyashi a muhallinsa.
Wanka yasoyi daya dawo amma saboda ya kira fadeelan baiyi ba,don haka yana shiga ya zare kayan jikinsa,ya lullube murdadden jikinsa da babban lallausan towel. Minti talatin kacal ya fito yana qamshin shower gel,da hair shampoo dinsa me tsada da yake amfani dashi waien wanke sassalkan gashinsa da ko yaushe yake cikin daukar idanu da hankulan tarin matan da shi kansa baisan adadinsu ba,saboda mafi yawansu bashi da masaniya akan fadawar da sukayi cikin matsananciyar soyayyarsa. Mintuna sha biyar ya gama shirinsa,a hakan yayi sauri akan yadda ya saba,don shirinsa yana daukar lokaci,sosai yake bawa jikinsa da fatarsa kulawa da mayuka da turaruka masu shegen tsada,ko nawa yana iya kashewa ya siya turare zuwa mayuka,ko a yanzun kudin wasu turarukan nasa sun isa jari a waien mutane da dama. A gurguje ya feshe gashinsa da turaren ka,hakanan beard dinsa da nasa turaren na musamman tamkar wani mace haka yake a wannan bangaren.

Guri na musamman da yake gabatar da ibadunsa ya shimfida lallausar dadduma,cikin daidaituwa da miga dukka tunanin damuwar duniya izuwa bayanka ya fuskanci alqibla,cikin cikakkiyar tsaiwa da daidaito ya kabbara sallarsa.

Dukka raka'o'in daya saba yi babu wadda ya rage a ciki,ya dade saman abun sallah yana addu'o'in sa,bayan ya kammala yana nade abun sallar akayi masa knocking,sai ya waiwaya yana duban wata maqalalliyar na'ura dake nuna masa fuskar wanda ke knocking din. Jibril ne,matsawa yayi gaban bedside drawer ya ciro wasu files,sannan ya zura wasu lallausasan takalma da aka yi da wani gashi me laushi ya buda gofar da zata sadashi da setting room na gidan.
Cikin girmamawa ya rusuna yana gaidashi

"Sir... bakaci dinner dinka ba,ina fatan lafiya" kai ya girgiza yana miga masa files din

"Am too tired,ina bugatar hutu,gobe inaso mu fita da wuri,zan kwanta yanzun,ko meye please kada wanda ya tasheni,zan nemeka idan ina da buqatar hakan" hannu biyu yasa ya karba cikin girmamawa

"Yes Sir,have a goodnight"

"Allah ya tashemu lafiya" sai ya juya a nutse yana komawa dakin.

Saman lallausan carfet din dakin ya yada pillow,ba kasafai yake iya kwana samam shimfida me laushi ko katifa ba,yayi rigingine idanuwansa na kallon roofing din dakin cikin dim light din daya saki,ya kammala addi' o'insa ya shafe jikinsa,ya koma riginginen ya kwanta yana sauraren zuwan bacci.

A hankali jinsa da ganinsa ya fara nisa da wannan duniyar da muke ciki,ya haurawa zuwa duniyar bacci,irin baccin da kake tsakanin wannan duniyartamu da duniyar baccin,zuciya da ruhinsa suka fara haska masa wani abu da ya faru zahiran dazu dazu cikin rayuwarsa ta ainihi. Tana tsaye ta basu baya kamar yadda ya gani a mafarkinsa, dogon gashinta me tsananin duhu da sheqi daya raba tsakiyar bayanta,hips dinta da mazaunanta da suka fita ainun ta shape din doguwar rigar.
A mugun firgice ya bude
idanunsa,sannan yayi wani irin tsalle ya miqe ya zauna sosai saman carfet din,hannunsa ya sanya ya tallafi goshinsa da ya dan fara hada zufa,a hankali labbansa suka motsa da fadin

"Hasbunallahu la'ilaha illa huwa,alaihi tawakkaltu wa huwa rabbul arshil azeem" ya maimaita ta kusa sau goma,sannan a hankali zufar ta fara ragywa tana bushewa da kanta,sai ya daga kansa yana bude idanunsa a hankali

"Meye hadin sa da nanny fadeela da har zata biyoshi cikin mafarkinsa?,me yasa duk yadda yakai ga kame kansa da idanunsa daga kan kowacce diya mace,amma hakan bai rabashi da tarin mafarkan kasancewa da wata diya mace dako fuskarta bai taba samun nasarar
gani ba? mafarkinsa na yanxun ya kusa yin
dai dai da yarinyar dake yawan zuwa debe
masa kewa,duk da baisan saurin murya ko ta
fuskarta ba,ya tsani wannan mafarkin da ko
yaushe idan ya yishi take sake haukatashi ya
maidashi mabuqacinsa,lalurar da ya dauka
yayi adabo da ita,ya tasa ta gofar da zai yaqi
hakan,yawan nauye nauyen da yake dorawa
kansa da ayyuka babu ji babu gani,ya dauka
sun isa su cire wannan buqatuwar daga
jikinsa. Yasan yayi nasara da idanunsa da
kuma zuciyarsa,ta yadda duk tarin matan dake
kai kawo a gabansa dama bayan idanunsa,bai
taba daga kai ya kalli wata yaji shaawar
kasantuwa da ita ko kuma ta burgeshi
ba.amma ta bayan fage, wata mace guda daya
tal da baisan wace ba na neman matsanta
masa,cikin watannin da duka duka basu gaza
biyar na.

Siririn tsaki yaja shi daya cikin dakin,ya
miqe cikin matuqar mutuwar jiki ya nufi toilet.
Alwala ya daura,ya dawo ya tsaya gaban
wardrobe ya cire qaramin towel ya goge lemar
jikinsa,ya saki towel din ya koma makwancinsa na dazu. Duk da bayason kwanciyar rub da ciki ko kadan,amma yau din ta zame masa dole haka ya kwanta a rub da cikin yana qangame dukka pillows din dake kewaye dashi.

****Tsam fadeela dake sanye da uniform dinsu,cikin tsafta kulawa da kuma tsaarin sãahar ta rige hannun sãahar din tana langabar da kai

"Ni ba itace zata kaini ba Allah kece zaki kaini" ta gadi a mugun shagwabe tana daf da sakin kuka. Waiwayowa hajiya qarama tay,tadan hade fuska

"Me yasa bakiji uktie,ta yaya nanny zata kaiki school,shin tama iya mota da kike zancan ta kaiki makaranta? idan kuma kinaso ki makara ne shikenan" labiba dake tsaye riqe da key din tata motar da zata miga fadeelan makaranta,saboda driver dinta da hajiya garama ta aika ta jefawa fadeelan harara,sannan tace

"Ta ina zata iya mota? bayan ba itace dasu ba a gida?‚an saba hawa motor din kasuwa?" A nutse säahar ta dag kai,kallo daya tayi mata ta bawa banza ajiyarta,don tun zuwan labiba gidan ta gama karantarta,ta kuma yi aji guda ta sanyata a ciki.

"Allah mommy ta iya,Allan kuwa"

"Ke ko ta iya bazan bayar da motata ba,saidai ku ira a wanke wata cikin motocin gidan nan sannan a kaiki" ta fada cikin fushi ta juva da zummar komawa cikin gidan

"Zo nan labiba" hajiya garaman ta kirayeta,ta dawo a fusace ta tsaya tana huci

"Bata key din ta tuqaku,saiku tafi tare ki dinga monitoring dinta kada ayi miki barna" fuska ta hade cikin fada take magana

"Allah kune kuke sangarta yarinyar nan,sai abinda takeso sannan za'a yi mata?"

"Waishin ba daga jikin kakanta da mahaifinta kudin motar suka samu ba?" Haiiya garama ta jefawa labiba tambayar. Sak labiba tayi tana duban tsakiyar idanun hajiyan,itama kafeta tayi da kallo. Sometimes kamar yarinyar tana manta waye ita,har suso wuce gona da iri a wasu lokuttan,shi yasa takanyi hakan,saboda makaho yasan cewa fa ana ganinsa.

Jiki a sanyaye ba tare kuma data sake cewa komai ba ta migawa saahar key din.
Kamar ba zata karba sannan tasa Hanna ta karba,tana ji a ranta wasu lokutan wasu mutanen suna da bugatar a koya musu hankali,a kuma basu darasin rayuwa.
Chapter 72 · 0% Book details