← Book details Tabarmar Kashi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 164 OF 171

Sashe 164

Tabarmar Kashi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

_(kowanne yaro a duniya bashi da burin da ya wuce wannan, dukkan yaran da uwayensu ke wani gida suna auren wani tabbas don basu da yadda zasuyi ne amma inda ace son ransu ne ko gaddara ta basu damar rubuta abinda zai wanzu a rayuwarsa,da zasu rubuta tabbatuwar iyayensu guri guda, babu abin alfahari irin ka tashi kaga mahaifiyarka tayi rayuwa kuma ta rasu cikin dakin auren mahaifinka, saidai idan ba yadda ka iya da yadda Allah ya tsara maka qaddararaka, yan uwana mata,mu qara haquri akan wanda muke dashi kan zamanmu gidan mazajenmu, MAZA)MATA a duk sanda rayuka suka baci, muka yanke shawarar rabuwa da junanmu,mu dinga saka tunanin makomar 'ya'yanmu akan gaba kafin komai,Allah ya zaunar damu lafiya ya gara mana haguri da mazajenmu, suma Allah ya qara musu haquri da juriyar zama damu)_

Sai data shiga gidan ta tabbatar gidan yaci sunansa MT JARMA KINGDOM,wani irin fasali da tsarin ginin gidan turawa akayi, kowanne sashe na gidan idan ka kalla zakasan cewa lallai da gaske gidan na masoya ne, an kumayi tanadin wanzar. da soyayya me dimbin yawa a gidan,da rayuwa me cike da ma'ana da sanyayar da zukata.

Wata ravuwa da ko a mafarki dukkansu basu taba zaton akwaita a duniyar ma'aurata ba suka shiga shimfidawa cikin gidan, dukkansu kowa yasan irin bacin rai baqinciki da karayar zuciyar da ya samu,wanann ya qara musu qaimi wajen kula da juna matuqa da gaske.

TOUFEEQ wani irin gold ne a cikin duhu,wanda sai me sa'a ce qwarai zata takashi. Tun asali namiji ne daya amsa sunan NAMIJI bawai muna maza ba, idan nace
NAMIJI ba ina nufin a halitta kawai ba,a'ah, irin mazan da sukayi qaranci a yanzun, wanda yake buda hannayensa ya kuma bude kafadunsa don ya tallafe dukkan nauyi da bugatar iyalinsa,ya bata lokacinsa a kansu,ya nuna musu zallar madarar qauna da kulawa,yayi gyara cikin hikima da iya sarrafa harshe idan anyi laifi ya kuma bada uzuri me nisan gaske a garesu. Ya yarda da maganar annabi da yake fadin mu din an haliccemu daga gashin haqargari na, ko ayi haquri damu aji dadi damu a haka a karkacen da muke, ko kuma ace sai an migar damu, miqar damu kuma yana nufin karya mu,karyamu shine rabuwa damu.

Gefan sãahar kuwa ko daya ciki bata bari va hanata bashi dukka wata kulawa data kamata ba,gasa da wata guda ta gama fahimtar halayya da dukka dabi'unsa wanda batakai ga fahimta din ba. Tayi kuka tayi kuka a sujjada har batasan iya adadi ba bayan data fahimci musayar alkhairin da ubangiji yayi mata,tayi sadaka me tarin yawa dukka tana godewa Allah da bai wofantar da wahalarta ba yayi mata kyakkyawar sakayyar da a nata ganin bata cancanci haka ba, girman rahama jin gai da kuma tausayin bayinsa ne yasa ya mallaka mata toufeeq din. Kamar yadda yake a tsarinta tun can baya,yanzun ma bata wani yarda ta dauki me aiki ba,tanason samun ladan gidanta da hannunta. Daga harabar gida garden na gida da sauran hidimomin gida akwai ma'aikatan da sukeyi acan waie ta cikin gida kuma baba ramatu suka taho da ita,' yar amanarsu,itake gyaran dakuna da bangaran säahar din yayin da säahar din ke rige da ragamar kula da hatta da cup din ruwan da toufeeq zai sha bata dorawa kowa ba. Yayi mitar ta dinga zama tana hutawa shi ya yafe amma tace sammm, saidai idan ya dawo ko yana gida shike tayata su kammala komai tare.

Dalili na biyu da yasa bata dauka me aiki ba,tana ganin a yanzun fadeela ta fara tasawa,shekara takwas tana sanvata fara kovar wasu abubuwan, batason gata da dukiyar mahaifinta ya sanya ta tashi a SANGARTACCIYAR MACE. Yarinyar ita kanta qaunar ace vi abu kaza takevi.don haka ta taso da wani irin qwazo, idan ka ganta tare da sãahar baka isa duk qwaqwarka kace ba ita ta haifeta ba.

Cikin hukuncin Allah cikinta ke girma cikin goshin lafiya,tun a sannan yaso ya kwashe iyalansa subar gasar saboda harkokin business dinsa amma maji tace bata varda ba girma takeyi vanzun tana da bugatar rayuwa cikin ahalinta wanda abaya bata samu wanna damar ba, uwa uba ma bata yarda ya daukar mata yarinya da
'yan jikokinta ba jirgi yana gantali dasu. Yadda tayi lafazin son zama cikin iyalin nata ya taba zuciyarsa qwarai, don haka ya haqura shima ya tattara tafiyar ya watsar, duk da yasan zamansa guri daya a nigeria bazaiyiwu ba,saboda yabar kasuwancinsa a wasu qasashen, don ma bashi da haufi ya hadu da directors 'yan amana,sannan kuma kusan komai dashi akeyi ta na'ura, koda meeting ne dashi akeyi ta conference call.

*****Wani irin gawataccen daki ne da aka yiwa tsari
2) me kyau da wasu irin books shield na glass da wani irin garfe me haske da daukan idanu. An gawata dakin da nau'in kuieru biyu, sofas masu taushi da kuma lounge chairs da suka dace da paint curtains da carfet na dakin.

Takardu ne masu tarin yawa a gabansa da yaketa signing tare da karanta rubutun jikin was daga ciki.
Kana ganinsa zakasan he was so busy hankalinsa kuma yayi nisa sosai.

A hankali aka turo qofar dakin,säahar ta bayyana cikin wasu silk nightgown farare tas in and top,gashinta me tsaho da sheqi yana daure a siririn band da baka ko rya ganinsa saboda cikar da gashin ya qarayi. Ta aje wani irin kyau idan ka dauke tulelen cikinta da take tallafe dashi saboda nauyin da yayi matan, fuskarta a tsuke take sosai, babu alamun walwala ko kadan a tattare da ita.

Sam bai ankara da shigowarta ba sai sheshsheqar kukanta ya ji. Fatali yayi da takardun cinvarsa va mige da sauri yana dubanta,sai kuma ya fara takowa zuwa inda taja ta toge fuskarsa ciks da damuwa

"Ya salam, ya isa cutie tell me me kuma ya faru?" Sake fashe masa tayi da kuka,abinda ya sake rikitashi gaba daya,ya kamo hannunta ya rige sosai cikin nasa ya fara janta ciki a tausashe amma saita cake

"Ka sakeni tunda yanzun baka sona,har suna ma ka canzamin,saboda tsabar baka sona yanzu kake tsokanata da wani cutie,bayan fuskata duka ta kumbura, kyauna dama kakeso ba ni ba,yanzu kuma na zama mummuna ka daina yayi na" matugar juriya kadai yayi bai fashe da dariya ba, saboda yanzun nan cibi zai zama qari. Tunda cikinta ya fara nauyi ta zama mafadaciya,komai akayi mata ba'a kyauta mata ba,ba'ayi mata dai dai ba,ga dan banzan tsarguwa, ko kallonta ya cikayi sai tace muninta yake kalla

"Wallahi kinji Allah kenan, inda zaki zauna a haka zanso hakan bayan kyan da kika qara har tacen wajen ma ko?, ba'a magana" kunyarta har yau tana nan, maganar tasa ta sanyata dauke kanta murmushi na shirin kubcemata, amma tsabar qwarewa a rigima saita fuske

"Ban yarda ba, inda hakanne ai ba zaka barni ina jiranka ba,ni kadai almost one hour?" Wannan karon dai sai da dariyar ta qwace masa,yasa hannu ya juyo da fuskarta yana cewa

"A'ah…ayimin afuwa,ashe duka wannan fushin abun
ake nema?,aikam aiki dai ya gare mun samu babban aiki"

ya fadi yana jin dadi qasan ransa. Shi kam ya daga mata gafa ne saboda cikin kwanaki ukun kamar yaga bata jin dadi sosai, tun ranar data dawo daga sunan afifa wadda ta haifa baby giri dinta qatuwa wadda taci sunan SHIFA(MAJI), suna kiranta da AHLAM, shi dai wannan ciki •) ya biyashi dari bisa dari.

Ko taku daya bai bari ta garasa ba ya dauki abarsa
ya wuce da ita fadarsa, yana tafe yana tsokanarta

"You gain weight moonbeam"

"Kaine ka jawomin" ta fada tana mintsininsa a tsakiyar qirji, tasan yana tsokanarta ne don yasan batason yace tayi nauyi.

Yana alfahari da ita gwarai ta wannan fannin, duk hanyoyin faranta rai ta sansu. Idanunsa a lumshe yana tina irin farinciki da gamsuwar da take bashi yaji tadan tureshi kadan tana guna guni,kunne ya saka da kyau

"He acts like he's the smallest thing in the world but he's freaking huge" dariva ce me garamin sauti ta subuce masa,ya daga fuskanshi yana kallon tata

"Eheenn,wanann grumbling din bashi da ma'ana,kin fada ne don ki rama nace kin qara nauyi, after all ma sai da kika gama kwashe dadin?, kwadayayya?" Kukan kissa ta sakar masa tana dan kai masa duka, shi kuma ya bita da gwalo yana boye kansa cikin boobs dinta. Sai data gaji ta barshi jin tayi shuru sai yakai hannunsa ya shafi gefan fuskarta

"What happened?"

"Am hungry" ta fadi cikin salon ban tausayi. Tashi yayi sosai yadda zai iya ganin fuskarta,da gaske ta bashi tausayi, tana wahala da cikin sosal,bai sani ba ko haka kowacce mace keyi?, ameesha dai baiga bakan daga gareta ba

"But you just eat.

"Need something sweet,am craving" dariya ta bashi,sai yasa yatsusa yadan rufe rabin fuskarsa yana zuba mata ido

"Uhunnn" ta fadi tana kallonsa itama. Da gaske ya fuskanci yau rigimar ce a kanta, don ledar data matsa yayi mata siyayya ma gata a yashe a gasa, da kanta tavi list din komai amma bataci komai din a ciki ba. Baison rigimar tayi tsaho, don haka yayi wuf ya tashi yana dagata

"Go bath"

"Noooo hottie"

"Dole indai kinason maqulashe". Kumatunsa ta riqe da hannunta daya tana jaa

"Having someone who can handle all your moods is such a blessing" hannun ya sunkuya yayi kissing yana murmushi.

Zafafabiyar

"HUGUMA*

_TABARMAR KASHI*

Book 02 Page 71

Tare suka shirya shi da ita, ta saka doguwar rigar abaya wanda yanzun sune suturarta saboda girman cikinta,shi kuma ya Sanya kaftan abaya sassauga suka fice.

"Ina muka nufa?"

"Pizza zanci" ta fada tana tande baki. Dole ta bashi dariya sosai

"Wadan nan babies,wanne irin kwadayayya suka maida ke?"

"Ask them" ta fada kawai tana nuna masa tsinin cikinta wayarta na hannunta tana qoqarin kunnata.
Gurin saida pizza me kyau tsafta da inganci va kaita cikin nasarawa GRA

"A nan fa zamuci" ta fada tana neman gurin zama

"Oh god" ya fada a hankali, mamaki yana sake kasheki, da gaske ake cewa dole ka sake yin karatu na musamman akan mace idan tana da juna biyu, wawayen maza sai suyita cusgunawa matansu a irin wanan yanayin su dauka kome iskanci ke sawa suyi. Tunda yake da ita bai-taba gani ta zauna cin abinci cikin mutane da yawa bama bare waje sai yanzu.
Chapter 164 · 0% Book details