← Book details Tabarmar Kashi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 171

Sashe 34

Tabarmar Kashi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da kallo ta bishi cikin tsananin bacin rai,ya isheta ya kaita maqura,ita ba yarinyarshi bace da zai dinga yi mata irin wannan izzar,tabbas a yau dai baici bulus ba,zata koma aiki amma kuma saita rama abinda yayi mata,tabbas zai biya da farashi me tsada.

Ta qofar baya ta wuce ta bulla sassansu,a parlor ta samu afifa da maama a zaune,bata tsaya ba sai tayi wucewarta ciki,tana kuma shiga daki ta maida muqulli ta rufe qofar,ta zauna tana fidda zazzafan huci daga bakinta,tsanarsa na sake ratsa mata jininta.

Sai da suka daidaita akan hanya sajjad ya dubeshi

"Da ka sanya muka bar gurin,ina fata ba wani abu mara kyau ka yiwa yarinyar mutane ba"

"Kanta na yanke zan siyar" ya amsa masa a taqaice

"A yadda kake da zafin rannan,idan ka fara yankan kai an mata sun shiga uku,kafin shekara 'yammatan garinku sun qare inaga" maganar sajjad din taso bashi dariya,sai kawai yadan murmusa kadan da iya labbansa yana girgiza kai,sajjad din yana ci masa tuwo aka yadda yaga dama,amma ba komai,shi da shi kar tasan kar ne.

***********Cikin karsashi da tare da maido dukka azamarta gangar jikinta ta shiga company din ranar monday,abu na farko data fara yi shine hada dukkan documents da report data fara aiki a kansu,ta tattara dukkan wasi bayanai,harda hardcopie data aikawa office din ceo din bai saka hannu ba,ta zauna cikin kwanaki hudu ta tura zuwa email din Dr ahmad jarma,tace ya duba musu,idan komai yayi,suna buqatar sanya hannunsa zasu fara aiwatar da komai.

A dare daya ya duba dukkan bayanan,bai samu gamawa ba sai kusan qarfe uku na dare. Sosai ya jinjinawa kaifin basira da qwaqwalwa irin na sãahar din,yayi saluting nata sosai,tunanukanta da yadda ta iya tsara abubuwa sai yake masa yanayi da tsari da ra'ayin toufeeq dinsa,tsarikan nata sunyi bala'in burgeshi,don haka baiyi jinkiri ba ya sanya mata hannu a gaba daya guraben da ake buqatar sahalewarsa,don aiwatar da ayyukan da kuma fidda kudade daga asusun kamfanin.

Sanda documents din suka isketa murmushi ta saki,sai taji kanta sakayau,kamar Dr din ya share mata wani fage da zata aiwatar da dukka ayyukanta hankali kwance ba tare data bi ta office dinsa ba har ya samu damar da zai bata mata rai,taci alwashi!,kuma tana da yaqinin wannan itace hanya guda daya da zata qona masa rai.

Sati na gaba ta fara gudanar da komai,aka fitar da kudade akayi hiring mutanen da zasu bada gudunmawar farfado da kamfanin,cikin sati guda ta sauya komai ta kuma fara gudanar da al'amuranta hankali kwance.

Wata guda kacal company ya fara ci gaba,kawo yanzu kusa duk wanda ya kwana ya tashi cikin company din yasan da zamanta,ta maida kanta busy sosai ta yadda zatayi abinda ya dace,wanda zai faranta ran Dr,ya kuma daga kima da martabar yayanta, she's very hard worker,wannan ya qarawa ma'aikatan qwazo da karsashin aiki,ta kuma samu soyayya sosai daga garesu hadi da martabawa,wannan ya fara sanya mata so da qaunar aikin cikin ranta kadan kadan ba tare data farga ba.

********Cikin satittikan da suka biyo baya gaba daya aiki takeyi tuquru cikin kamfanin,duk wani abu daya zama nauyinta ne akafadarta yake tayi qoqarin ganin ya tafi dai dai,gaba daya bata sake bi takan abinda ya danganci office din CEO ba,duk da tana sane da file dinta dake gurinsu,ta zuba idanu ne taga ko zata samu saqo daga gurinsu,yau ne ko gobe ne,shuru dai.

Ba jimawa ta fara samun soyayya daga wajen employees sosai,duk wanda yaga yadda take tafi da aikinta yasan cewa tasan abinda takeyi,da yawa ta tafi da zukatansu,mafi yawansu sun fada a soyayyarta,saidai kwarjininta da yadda bata sakewa mutane fuska musamman maza ya sanya suke shakkar tunkararta. Ta kame kanta sosai,ta kuma sake shata layi ga duk wanda ta fuskanci dan rawar kaine. A hankali sai aikin nata ya fara shiga jikinta,ta fara jin qaunar aikin,saita samu kanta da daura damarar yin dukkan wani abu da zai kawoma kamfanin ci gaba,ko don albarkacin Dr mahmud da ya dauketa kamar diyar cikinsa,don cikin watanni biyun da tayi sai hudu yana kiranta,ya shaida mata yana samun bayanin yadda aketa samun ci gaba daga bakin sajjad. Ba wani sanin sajjad din tayi cancan ba,amma zata iya shaida fuskarsa da kuma nasa muqamin.

Ta bangaren toufeeq aikinne yaso hadar masa,nasa company din da yake shirin kafawa daya baro ana processing budeshi abubuwa sunyi nisa,ana da buqatarsa,dole yayi wani irin busy sosai,yake kasa hankalinsa gida biyu yayi aikin MT JARMA GROUP OF COMPANY sannan yayi na MAHFAD FACTORY,kwata kwata baya samun kansa sai dare,nan ma lokutan baccin nasa bame yawa bane sosai,yana qoqarin yakicewa ya dawo gida ne kadai saboda fadeela bayason abinda zai sanya ta dinga jin kewa,ko ta nemi wani abun ta rasa bata samu ba.

*_RAI DANGIN GORO_*👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070

VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k

*Al'ummar NIJER ku kira wannan number don yin naku pyment din*

+22799643131

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥
[8/22, 7:41 AM] Maman Aslam: *H U G U M A*

*_TABARMAR ƘASHI_*💔
https://arewabooks.com/u/huguma

Page 30

*_RAI DANGIN GORO_*

Yadda ayyuka suka dauki zafi cikin company din,da yadda hadin kai ke samuwa daga dukka ma'aikatan ya sanya cikin satin basu damar samar samar da wasu games don nishadi a kowanne department.

Ranar Monday bata wuce awa daya da shigowa office ba,miss sameera ta shigo,fuskarta dauke da murmushi tace

"Kin samu gayyata daga CSO Chief security officer na MT JARMA COMPANY,yau zasu gabatar da nasu game din na hack day,during break hours". Hannu ta miqa ta karba mini computer din da miss sameera ke duba saqonni irin wannan tana duba saqon da aka aiko din. Kai ta gyada kadan sannan tace

"Babu matsala,ki tunamin idan time yayi"

"In sha Allah" ta fada tana dan russunawa cikin girmamawa,sannan ta juya ta fita. Fitar tata da yayi dai dai da shigowar kiran ahmad gana wayarta.

Har ta dauke kai taci daga da aikinta kamar ba zata daga ba,sai kuma wata zuciyar ta nuna mata kamatuwar yin hakan,koda batason tayi wayar dashi a qalla ta bashi uzurin da zai sanya ta zamewa amsa wayar tasa,tun ranar da yazo gidansun har yau bata sake daga wayarshi ba bare ya sanya ran samun damar sake ziyartar.

Lokacin data daga wayar a zaune yake,amma sai gashi ya miqe tsaye saboda farinciki,maganar gaskiya ya kira ne kawai,bawai don yana da wani tabbacin na zata daga ba, sassanyar muryarta ta saukar masa da kasala lokaci daya,ya koma ya zauna yana dafe wayar qamqam a kunnensa

"Am so sorry,na katse miki aiki ko?,nasan yanzu lokacin aiki ne" ya katsi hanzarinta tun kafin ma tace komai

"Ayimin afuwa,na kasa daina kiranki ne,amma ko iya haka Am really grateful "

"Why did you call me?" Ta tambayeshi kai tsaye

"I want hear you,i missed your sweet voice" ko kadan maganar tasa bata burgeta ba,saima bata mata rai da tayi,ko kadan bata jiran jin yabo daga bakin kowanne namiji a yanzu

"Okay,It's working hours now,can you turn off the phone?"

"Can i call you later please?" Ya fadi cikin kwantar da murya,hakanan taji yau din ta kasa musa masa,sai kawai tace masa

"Allah ya kaimu" daga haka bata tsaya jiran jin amsarsa ba ta datse kiran. Tana ci gaba da aikin amma rabin hankalinta yana kan hanyar da zata bi ta yakice mahmud daga rayuwarta,ta fuskanci wani banzatar da lamuransa da takeyi sam baya damunsa,kamar ma ko a jikinta wai an tsikari kakkausa,qara qaimi kawai abinsa yakeyi. Duk kuma yadda yakai ga sonta bata jin ko kusa ko alama zata iya aurensa,bama shi kadai ba,ta tattara al'amarin aure gaba daya ta rufe shafinsa,bata sani ba ko sai a qiyama.

Sanda miss sameera ta shigo ta gaya mata lokaci yayi saita duba agogo,ta tsaya tayi sallar azahar,duk da cewa akwai sauran lokaci,farkon muhtarinta ne a sannan. Coffee tasha rabin cup,sannan ta gyara yafen mayafinta daya zauna sosai a kanta,ya dace kuma da doguwar rigar atamfar jikinta,wadda dinkin yabi jikinta kamar domin ita aka halicci atamfar da dinkin gaba daya,jikinta sai fidda sirrintaccen qamshin nan nata yakeyi,saika dauka yanzu yanzu ta gama fesa turarukan nata,kabbasa ce me dan karen qamshi data dade da bin jikinta,bayan body mist da sauran turaren kaya da take using dasu masu dan karen tsada da kyau,tana iya kashe ko nawa ne ta siya turare,ba kamar sauran tarkacen makeup ba da har yau saidai a siya mata,don ba wani damunta sukayi ba,gwara gwara powder ma.

Tare suka taho da miss sameera,suna dan tattaunawa akan abinda ya shafi aikinsu. Dab da zasu gifta office dinsa idanunta ya sauka a kansu,can qasan ranta tayi qwafa gami da duke kanta,don ko ta qofar office din bason gifatawa takeyi ba bare wani abu ya kaita,har ya hadata mu'alama da mamallakinsa.

Babban hall din company a nan ta taras da ma'aikata masu yawa,kowa yana saman kujerarun da aka warwatsa a gurin, gurin sama na musamman aka bata ta zauna tana maida hankalinta ga babban allon majigin dake iya nuna yadda kowanne abokin aiki ke qoqarin yin kutse a na'urar dan uwansa amma wancan yana tosheshi. Tun bata jima da zama ba wasan ya dauki hankalinta sosai,bama ita kadai ba,kusan duk wanda yake wajen abun ya matuqar qayatar dashi,mayun na'ura aka hada team dinsu guda kowa yana qoqarin baje fasaharsa.

Sosai wasan ya dauki zafi,ya kuma dauki hankula,har haka ya sabbaba tashin 'yar hayaniya a hall din saboda ana gab da gangara a wasan.

Ba zato ba tsammani sai gashi ya bayyana a gurin,da yawa basu lura da shigowar sa ba,har sai daya fara zuwa tsakiyar hall din,sannan kowa ya fara shiga taitayinsa,cikin girmamawa kowa ya fara duqar da kansa yana miqa masa gaisuwa. Ko gaisuwar mutum daya bai amsa ba,yaci gaba da takowa ciki,cikin izza da qasaitarsa,hannayensa zube a aljihun suit dinsa,fuskarnan a dinke tsaf kamar ko yaushe,murtukewar kuma da bata taba hana bayyanuwar kyansa.

Bai tsaya ba har ya isa ga kujerar da CSO yake tsaye a gabanta,yadan russuna cikin girmamawa
Chapter 34 · 0% Book details