← Book details Tabarmar Kashi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 130 OF 171

Sashe 130

Tabarmar Kashi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kinci darajarta,ki dubi abun kunya wanda kike quntatawa shine yayi silar kubutar dake daga afkuwar wani mummunan abu a kanki" mamaki ya sake kasheta,kanta ya daure tamau, tama kasa cewa komai baki sake take kallonsa har ya miqe ya nufi hanyar soron gidan,har yanzu zallar bacin ran dake saman fuskarsa bata gushe ba. Har yakai bakin qofar sai kuma ya dawo,ya tsaya gaban fauziyya dake zube tana kuka

"Tashi ki wuce ciki". Bai barta ba har sai daya rakata cikin dakinta,ya dan jima ma a ciki kafin ya fito,zuwa sannan shifa ta ja jikinta da qyar ta wuce zuwa nata dakin clkin mawuyacin hali,tare da hasashen me yake ta faruwa da ita ne a rayuwarta haka? tun ranar da fauziyya ta sanya qafarta a gidan da nufin zama dasu,na wata shidda kawai ta samu kwanciyar hanakali bayan zuwan nata,daga bayan wannan watanni shidan bata sake samun sauqi ko salama ba.

Duk wani farinciki nata ta warwareshi tasss ba tare da tasan meye dalilin da yasa taketa aikata hakan ba. A iya saninta,mahaifiyarsu mahmud macace mai kirkin gaske da kowa ke yabonta bayan rasuwarta, zamanta da fauziyya na watanni shidan nan,zama ne na kyautata mata da kula da ita,saboda
tana mata kallon mahmud, mahmud kuwa ba zata manta da soyayyarsa a gareta ba, duk da cewa ba kowa cikin danginta ke son aurensu da shi ba, kasancewarsa shi din dan Nigeria ne, ita kuma 'yar Algeria ce, duk da shi dimma
fari ne tas kalar yarensu da idan ba fada kayi ba za'a
dauka Algerian ne shi dinma, kasancewar ya fita daga
tsatson SHUWA-ARAB wanda asalinsu dama larabawan ne.

Wani irin zama tayi cikin dakin cikin qunci da
kukan zuci,da Muhammad da nadeeya kowa kuka
yake, amma kusan hanakalinta yayi nisa a tunani,taji
alamun kuke sukeyi,amma saboda tsanar tunani da
damuwa bata farga da kukan da sukeyi ba,har sai da
taga fadowar fauziyya dakin kamar wadda aka jeho.
Kafin tayi kowanne irin tunani ta dauke nadeeya dake
tsaye daga bayanta tana kiran sunanta ta hau jijjigata.
Sallamar mahmud da shigowarsa cikin dakin shi ya ankarar da maji dalilin wannan shigowar ta fauziyya ta ba zata,iya saninta ko daya bata iya tayata wahalar yaran,zafi ko sanyi koda azumi akeyi ita zata yi korai dinta fauziyyan na daga kwance, saidai ta fito ta debi abincinta ta koma daki, idan ta gama sabgoginta kuma ta wanke jikinta tayi ficewarta unguwa,ba zata dawo ba sal ta daidaicin lokacin dawowar dan uwanta.
Hannu yasa ya karbi nadeeyan, fauziyyan da ta sake tara wani qwallan ta dubi yaran

"Ku tayani bawa maji dinku haquri, kada tayi fushi da ni,ni din marainiya ce,bani da kowa sai yayana sai ita da nake saka ran ta zamemin makwafin uwa" ta qarasa fada tana share qwallar munafurci. Gaba daya jinin jikin maji so yayi ya tsaya da harbawa,tabi fauziyya dake ci gaba da sharar qwalla da kallo

"Ni kadai na isa na tsaya miki, jeki abinki" mahmud ya fada yana miqa mata leda daya da ya shigo da ita ta takeaway. Har qasa ta durqusa ta saka hannu biyu ta karba tayi masa godiya tana fita.

Wani kallo ya juyo ya watsawa maji, ba komai idanunsa face zallar bacin rai da har yanzu bai gushe ba "Yau na gani da ido na,ansha gayamin yadda yake wulaqantar da yaran nan,hatta a wajen aiki ba wata
Kulawar kirki suke samu ba,saboda baqin hali tun daga waje nake jiyo kukansu amma kin gaza rarrashinsu,to daga rana irin ta yau na soke batun aikinki, ki zauna a gida ki kulamin da yarana da 'yar uwata" yayi maganar yana kamo toufeeq,ya zaunar dashi gefansa nadeeya na saman cinyarsa,ya bude musu daya takeaway din ya fara
basu.

Har yanzu jin komai take kamar a mafarki,sai a lokacin ta samu qwarin gwiwar waiwayawa gareshi

"Allah S W T cewa yayi,yaku wadanda kukayi imani,idan fasiqi yazo muku da labari kuyi bincike a kansa kada ku afkawa wasu mutane cikin rashin sani da jahilci saiku wayi gari kuna masu nadama akan abinda kuka aikata.

Wannan kenan kayi tunani akai,sannan meye hadin matsalar nan da maganar fitata aiki mahmud?" A harzuqe yake kallonta

"Waye jahilin kenan? ‚ni ko 'yaruwata?,ki gayamin?. Ta tabbata kin rainanin d gaske, rainin da ake cewa kinyimin ban sake tabbatarwa ba sai a yanzun,illar mace ta dinga taimaka kenan,koda bakai ka buqata ba wataran sai irin wannan ta gifta a tsakaninku,Allah yasa ba ahaka kika aureni ba da na shiga uku wallahi wallahi, aiki kin daina yinsa,sannan duk wani abu da kikasan kin tallafamin da shi ki zauna ki rubuta daga yau zuwa gobe,tsinke kada ki dagamin qafa,zan maida miki abinki" qas tayi da kanta,hawayen da tun dazu basu zuba ba yanzu suke zuba,maganar da ya gaya mata yanzu tafi zancan barinta aiki ciwo,duk wani fadi tashin rufa musu asiri da takeyi bayan karayar arziqinsa,dai dai da rana daya bata taba jin ta qosa ko ya dameta ba, amma yau da wadan nan kalaman zai saka mata?,komai da tayi musu tayi masa ne saboda tana ganin ya cancanci fiye da haka,namiji ne shi me bala'in kulawa da gida da matarsa,sanda yake dashi babu abinda baiyi mata ba,a lokacin duniya tana kwance, fauziyya bata shigo rayuwarsu ba,sai lokacin ta tuna da kalaman haiia mahaifiyarsu,a duk sanda sukaje borno ba zata dawo ba ba tare da hajjan tayi gorafin fauziyya ba

"Fauziyya, fauziyya,Allah ya shiryamin dai kawai" ba yawan zama take dasu ba,shi yasa a lokacin ba zatace
• ga wani hali nata ba,hakanan ba zatace ga abinda ta taba yi mata maras dadi ba,ashe ita din kara da kiyashi ce daukan mara sani.

Ranar har ta kwanta bata sanyawa cikinta komai ba sai bacin rai da taketa kurba da dogon tunanin ta inda zata kamo bakin zaren. Bayan sallar isha'i tana jinsa shida yara a dakin fauziyyan sunata hirarsu abinsu,kamar ma bata a cikin gidan. Sanda yaran sukayi bacci ya kawo mata su ya shimfide mata su ya juya abinsa ya fice. Kasa haquri tayi,bayan awa daya ta shirya ta miqe ta bishi dakinsa. Tunda ya amsa sallamarta bai sake daga kai ya dubeta ba,gabansa ta tsugunna cikin sanyi da mutuwar jiki

"Ya kamata mu warware sabanin da yake tsakaninmu ta hanyar tattaunawa,bai kamata mu fara yin abinda bamu saba dashi ba" har ta gama maganarta baice ci kanki ba,hasalima shirin bacci ya tashi ya fara yi daya kammala ya haye gadonsa ya kwanta yana fadin

"Idan kin gama ki rufemin qofata" yaja bargo ya lullube har saman kansa. A ranar shifa tayi kuka tayi kuka har taji babu dadi, meye da meye wai fauziyya ta gaya masa haka me zafi? wannan iri fushin koda mahaifiyarsa ta tsinewa albarka ai iyaka kenan.

Washegari saboda bata samu bacci da wuri ba ta makara bata tashi da wuri ba,tana tsaka da baccinta ta dinga jiyo qamshi cikin hancinta,sai ta farka tana salati ganin ta makara,ta shiga toilet tayi brush ta fito tana qoqarin kama ayyukanta na gida,don ko ciwo takeyi babu mataimaki,haka zata rarrafa tayi ayyukan nata, Muhammad na taimaka mata da dauko wannan ajjiye,duk da shekarunsa ba wani kaiwa sukayi ba.

Mamaki ne ya kusa kasheta,don fauziyya ta gyare gidan fes an kintsashi,hatta da yaran tayi musu wanka,hakanan ta kammala breakfast tana ta shiryawa a cooler da take zubawa mahmud abinci, yara nata tsalle hannunsu daya chips daya soyayyan qwai,shi kansa qwai din da chips din batasan ina aka samoshi ba,saboda tasan duk kayan abincin data siya musu wancan watan sun qare. Jiki a sanyaye ta qarasa shiga kitchen din,suka hada ido da fauziyyan tana rufe cooler din,sai ta sakar mata murmushi

"Barka da tashi matar yaaya,nasan tun jiya akwai tambayoyi fal kanki ko?,to yanzun kina da minti talatin zuwa arba'in da zakiyi kowacce tambaya taki zan baki amsarta,saboda yaayan ya fita yomin cefane, zan iya saurarenki kafin ya dawo" kaman majin zata ce wani abun sai ta dauke kanta daga dubanta, dariya ta saki tana cewa

"Bari to na taimakeki na rage miki wasu amsoshin tambayoyin…..nasan kin shiga kogin tunanin meye dalili na na hana yaaya ya sakeki ko? ‚nayi hakanne saboda banason tafiyarki yanzu,nafison saikin gasu yadda ya kamata, idanunki kuma sun gane miki girman matsayina a wajensa da kuma qarfin izzata,ta yadda zaki rayu kina bada labari a duk inda kika zauna"
*HUGUMA*

*_TABARMAR KASHI_*

Book 02 Page 41

Sosai zuciyar maji tayi wani irin nauyi,girman kaidai da dabi'ar fauziyya maras kyau tana ratsata,saidai kuma
ta tuna da wata magana guda daya na cewa
MURMUSHINKA GUDA DAYA TAK NA IYA SANYA
FADUWAR GABA GA MAQIYINKA don haka fa waiwayo tana dubanta da murmushi saman fuskarta

"Kin riga da kin makara,saboda bana tunanin lokacin da za'a rubuta littafin qaddarata kina gurin,na tabbatar da cewa kedin baki da matsayi a wajen Allah da kike da qarfin ikon canza qaddarata,na rigaki tsayawa a gaban Allah,na kuma rigaki ambatonsa" dariya fauziyya ta saki

"To sannu sufiya". Kasa ci gaba da tsaiwa maji tayi a kitchen din,ta juya ta fice a hankali, zuciyarta cike da mamakin wanne abu ta aikatawa fauziyya haka data cancanci irin wannan sakamakon?.

Ranar hatta da yaran basu wuni gurinta ba,sun wuni gurin fauziyya ne tana nan nan da su, sakamakon a ranar mahmud yana gida,saidai yadan fita ya dawo. Fauziyya ita tayi girkin rana da dare, kamar yadda tayi girkin dare,a lokacin idan ka shigo gidan zakayi tsammanin itace matar gidan idan ba kasan cewa matar gidan shifa bace.

Tana daga daki tana sauraren dabdalarsu, yadda suka wuni suka kai kawo haka ta wuni kwance a daki. Sai bayan magariba lokacin da mahmud din yake zaune a parlor suna kallo da yara fauziyya ta shirya komai saman tray ta shigo dashi falon

"Yaaya,don Allah kayi magana da maji,tayi haquri ta tashi taci abinci, yau duka bataci komai ba" dubanta yayi yana jin tausayin fauziyyan yana kama zuciyarsa tare da kallon kyawun halayenta

"Ke kamar baki da zuciya?,kamar baki damu da abinda ta aikata miki ba?,har yanxu fa bandage ne a kanki fa na abinda ta aikata miki" cike da kissa da kisisina tayi gas da kanta

"Bazan manta kyatatawarta a kaina ba,shi yasa bazan iya fushi da ita ba" Numfashi yaja sannan yace
Chapter 130 · 0% Book details