← Book details Tabarmar Kashi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 123 OF 171

Sashe 123

Tabarmar Kashi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"He was elegant" kanta takeson kawarwa amma ya hanata wannan damar,ya kama fuskarta ya riqe da kyau yana mata wani duba dake dauke da tarin ma'anoni masu wuyar fassarawa,wanda yakejin tamkar bakinsa bazai iya fadinsu ba

"Hold me please hold me so close, that your breath become my oxygen" ya fadi numfashinsa na fita da sauri da sauri saboda yadda ya kwadaitu da labbanta. Bai iya controlling kansa ba kuwa sai daya dangane da bakin nata kaman dazun,ya shiga sauke mata hot kisses ya hanata katabus da dukka wani yungurinta na qwatar kanta. Har tsahon wani lokaci kafin ta samu nasarar tureshi, taja baya tana kallon idanunsa da nata idanun da hawaye ya cikasu taf yana gab da gangarowa. Bai wani damu da kalar kallon da take masa ba, yafi damuwa da yadda bata qaunar ya rabi jikinta,wanda a yanzun yakejin cikin zuciyarsa bazai iya wani dogon zamani ba tare da ya rabeta ba,ji yake kamar wani magnetic ne a tsakaninsu. Murmushi ya sauke mata da idanunsa da suka sakeyin wani irin laushi

"Your eyes driving me insane madan ki daina kallona haka" ya furta yana gyara zaman sumar kansa da yatsunsa

"Only you can give me that feeling" ya furta a nutse idanunsa har yanzu cikin nata idanun da bata iya gani sosai saboda qwallar cikinsu.

Ba tare da kowannensu ya sakeyin komai ba sukaji an tura qofar office din, sautin takalma masu tsinin dunduniya ya soma tashi kafin daga bisani muryarta ta bayyana cikin sallama.

Har cikin jinin jikinsa sai da yaji wani abu ya tsarga,lokaci daya gabanin yakai ga juyowa dukka wata walwala da nishadi da ya samu a yanzu suka fara narkewa. Säahar ke fuskantar qofa,don haka da ita idanunsu ya fara jonewa.

Fara tas din mata, wanda har haskenta yaso zarce haske na dabi'a,tana da wani irin kyau shimfidadde akan fuskarta,saidai kuma a gangar jiki, irin matan nan ne da basu da hips kwata kwata,duk kuwa da cewa ita din ba wai siririya bace amma rashin hips din nata bayyananne ne ga duk wanda yasan tsarin halitta a gurin mace. A shape gown ce a jikinta ta wata shadda 'var mali komai na jikinta cike yake da ado da gawa

"Sãahar, nanny N ko?, i see" ta furta tana jifan sahar da wani irin kallo, zallar kyawun da bata tsammaci samunta a tattare da ita ba yana bugar son bugar da ita,tako ina tana hangen wasu qualities kai tsaye daga gareta ta cikin hijab dinta kai tsaye, kyan suffa ciki da waje wanda cikin qasa da minti biyu wani azababben kishinta daya ninka wanda take ji a kanta kafin ta ganta ido da ido va lullubeta.

Farat daya kwanyar säahar tayi mata recalling muryar, take kuma ta fahimci wacece, idanunta ta maida kan toufeeq wanda tashi daya kamanninsa suka canza da wani irin bacin rai da zallar tsana

"Barka da warhaka uban 'yata" ta fada tana rangaji tare da jifansa da wani irin shu'umin kallo da tasan yanaso ada

"Kar ka damu yanxu am single, naje na dawo kuma dukka don saboda kai" zare idanunta sãahar tayi daga kansu,tanaji a ranta bata da bugatar sauraren kowa a cikinsu,bata son jin komai daga bakinsu, don ba matsalarta bane, kowa yaji da matsalarsa, kuma kowa ya rige damuwarsa don haka ta fara takowa da nufin ta isa ga gurbinta na dazu ta dauki takalminta da hand bag dinta.

Cikin jikinsa yaji tahowarta, zuciyarsa kuma ta gama gaya masa abinda zatayin, ficewa zatayi ta barshi da ameesha,fuskar da ya jima da shafe babinta cikin rayuwarsa. Rabuwa yayi da ita har ta garaso dab dashi, bata taba tsammanin yana ganinta ba,sai kawai ji tayi ya tattarata cikin jikinsa yayi mata wata kyakkyawar runguma. Mamaki ya hanata motsawa, sai kuma yadda kunnuwanta suka jiye mata adadin qarfin bugun zuciyarsa da ya qaru matuqa, ala dole tayi luf tana jin bugun sosai cikin kunnuwanta,abinda zai shaida maka lallai yana cikin fushi

"'Baki yarda da gargadin dana yi miki ba?" Duk da zuciyarta ta qone sosai da kalar rungumar da ya yiwa sãahar din wanda ita daya tasan gardinta da dadinta, da
kuma sirrin dake tattare da wannan ingarman girjin nasa
data jima tana kewa,ta kuma gaza samun
kwatankwacinsa acan inda take harin

"Babu me rabani da kai sai Allah moha..... you are mine
forever" cikin nutsuwa ya dauke kallonsa daga
kanta,yasa hannu daya ya jawowa sãahar kujera ya
zaunar da ita a kai

"'Huta a nan" ya fada cikin kulawar da sai da Ameesha
taji kamar numfashinta zaiyi skipping na wasu daqiqu.
Tasan toufeeg ciki da bai fiye da kowa,soyayyarsa
kulawarsa da tsantsar iya ririta mace wani abune da ta
gama lalube daga gurin kaffff mazan data hadu dasu
bata samu wanda yake da koda rabin rabinsa baya
tattara abubuwa masu yawan da sai an tara maza dari
ba'a samu qwaya daya rak irinsa ba.

Wayar da ake kiran security kawai ya danna ya koma
ya tsaya kusa da sãahar kamar wanda yake bata kariya

"Inason ka bani dama mu fahimei juna, nayi maka kuma
bayani mu yafewa juna na dawo na kula da 'yata" runtse
ido yayi,ju yayi kaman ta soka masa wuqa a qahon
zuciyarsa,har bayason ta furta fadeela diyarta ce.

Bazai iya bata yawun bakinsa ma a kanta ba sai yaja waya yayi kira zuwa wajen saima

"Come in" ya fada a kausashe yana ajjiye wayar saima da security uku suka shigo, mata biyu namiji daya
Migewa yayi sosai iyakar tsahonsa yana dubansu,hatta säahar satar kallonsa take ta qasan ido,yadda lokaci daya ya koma Muhammad toufeeq jarma din data sani farkon haduwarta dashi, kaman ba shine yanzun nan ya gama karyar da wuya da murya a gareta ba

"Who allowed that women to enter?" Kallon kallo aka fara a tsakaninsu,kowa yana tsoron magana yana kuma tsoron gaddarar yau ta fada kansa ta kora daga aiki, duk da cewa tunda ya dawo din ko ma'aikaci dava bai kora ba.

"We are sorry sir, don Allah, bamusan bakason ta shigo ba" daya daga cikin matan tayi qarfin halin fada zuciya a karye

"Take her outside, and daga yau,idan na sake ganin gilmawar fuskarta cikin kamfanin nan ku tabbatar kun rasa aikinku" yana kaiwa garshe suka cafketa su biyun,don kuwa ba zata jaza musu asara ba,don kaf fadin kano dama Nigeria basajin akwai company da zasu samu me dadin aiki da kuma albashi me tsoka wanda yayi kamanceceniya da kamfanin MT JARMA.

"Ni ka wulaganta haka?" Abinda ta iya fadi kenan saboda tuni suka garasa yin waje da ita. Sai a sannan ya waiwayo ga saima ,wadda kallon idanunsa kadai ya sanyata taji kamar zata saki fitsari a wandonta

"You are fired" ya fada kansa tsaye. Ya jima yanason rabuwa da zaman yarinyar cikin office dinsa,amma ya rasa da wanne irin laifi zai kamata,sai yanzun da wannan dalilin yazo.

"Nan din ba Bar bane ko club da zaki dinga barin mata anyhow suna shigo min,bayan kin sani tare muke aiki da iyalina a ciki" yayi mata bayanin yana juya baya ba tare dava dubeta ba. Kuka ne ya hanata cewa komai, kawai saita juva da gudu gudu ta fice saboda ta gama tozarta tako ina a gaban idanun matar da take bala'in jin zafinta da tsananin kishinta,wanda ita sam saiman bata cikin damuwarta a rayuwa.

"HUGUMA*

"_TABARMAR KASHI_*®

Book 02 Page 37

Yana jin qarar rufe gofar saima ya tako zuwa gaban saahar din, saman qafafunsa ya tsugunna vana dubanta da wannan zafin da har yanzu baibar saman fuskarsa da kuma zuciyarsa ba. Kauda idanunta tayi daga kansa tana jin wata shakkarsa tana shigarta,scene din da ya gabatar yanzu a nan ya sake tabbatar mata har yanzu TOUFEEQ JARMA shine dai,a gareta ne kawai ya sauya.

Yatsunsa ya sanya ya dawo da fuskarta saitin tata fuskar, sai ta sake kau da kai,ya sake maido fuskar tata ta sake kawarwa,a karo na uku ya sake juyo da ita a zafafe sannan yace

"Idan kika sake juyamin qeya sai na miki hukuncin da na fahimci shi kikafi jin toro,idan baki wasa ba saidai a kawo wheel chair a daukeki, kada ki manta ina da sofas masu taushi a resting room" izzarta ce ta motsa,ya akayi ta bari ya karanci ta tsorata da abinda yayi mata?. So take ta gaggaya masa magana, amma ta sani daga qarshe yamutsatan da batason yayi shi zai aikata mata

"Na kusa kawo qarshen komai" ta fada qasan ranta a fili kuma tana hade rai

"Wayonki da tsiwarki dukka yau na rainasu, saboda baki kishina saiki bar duk wata karya da godiya su dinga tunkarar mijinki gaba gadi ko 'yar shakkarki basa ji saboda sunsan lusara ce MATAR TOUFEEQ?" Da gayya ya kira mata lusarar saboda ta motsa wani abu dake danqare a zuciyarta,yaci nasara kuwa,don take bacin rai ya bayyana

"Ko ba komai ya kamata su dinga jin shakkar tunkarata
haka kai tsaye saboda KE"

"'Ina ruwana da abinda ya shafi rayuwarka?,rayuwarka
daban tawa daban,ka taba ganin anyi kishin abinda ba'a so?, ba'a kuma damu da shi ba?" Ta fada itama gaba gadi. Murmushi ya saki karon farko shima zuciyarsa a yau ta dandana dacin kalmar RASHIN SO da kuma QIYAYYA. Kai ya girgiza

"Tashi mu tafi gida" ya furta yans miqewa tare da ja baya ba tare saya sake bi ta kanta ba. Ranta a quntace itama ta tashi tana jin haushin maganar da ya gaya mata, bataso yabar zancan iya haka ba,sai gashi yayi kamar komai bai faru ba.

Baice mata ci kanki ba a mota har suka dauko fadeela suka wuce gida yana jinsu sunata sabgarsu,bai ce musu komai ba kuma bai hanasu ba. Yau din sun koma da wuri, yana zaune a motar yana kallonsu har suka qule a sassansu fadeelan, kai ya jinjina

"Zanyi maganinki" ya fadi qasa qasa, kafin ya kashe motar,ya barwa jibril key din a jiki ya fito yana cewa

"Kada kayi nisa,zamu sake fita kaman nan da one hour"

"Okay sir" ya fada cikin girmamawa.
Chapter 123 · 0% Book details