Sashe 6
Tabarmar Kashi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ki rakani gida mana kiyimin weekend din nan a can?" Farheen ta fada tana duban sãahar,saita bude idanunta tana kallon farheen,cikin zuciyarta tana jin ta gamsu ta bita din,to amma kuma kamar ta kusanta kanta ne da yaa muhyi da take fatan a kwanakin da abba yace taje tayi tunani daga nan har abada zancan da yazo mata dashi yabi ruwa,bata da wani interest akan aikin ko kadan,amma kuma qin amincewarta tamkar ta damtsi qasa ta watsawa idanun yaa muhyi din
"Zaki din?,khalipha nata kewarki" ta fada cikin kwnatar da murya,khalipha shine makami daya da zatayi amfani dashi ta amintar da ita ta bita gidan,Allah ya jarabceta da son yara matuqa da gaske.
Sai da baaba rabi ta kawo mata coffee din taji tana cewa ta hada mata kayanta kala biyu sannan ta fahimci ta aminta zata din
"Miskili kafi mahaukaci ban haushi" anty farheen ta fada a ranta tana murmushi,a hakanma ita daya ke iyawa da sãahar,tana da dadin zama idan ka karanceta,idan ba haka ba kuma ba zaka taba jin dadin zama da ita ba,infact ma ba zaka taba fahimtar tata ba.
Tana rungume da aleena a seat din baya,yaa muhyi da anty farheen na gaba suna hirarsu,komai suke tattaunawa tana jinsu amma bata sanya musu baki ba,ta dade tana kwatanta cewa inama ace dukkan maza nagartattu ne kamar yayun nata,lallai inda addini ya halasta aure tsakanin dan uwa da dan uwa,ta tabbatar cewa bata da sauran matsala a rayuwarta.
Tafiyar da bata wuce minti talatin da biyar ba suka isa unguwar,ya muhyi dake tuqi a nutse ya saka signal,ya shiga layin da ya shiga hannun damansa a hankali. A qofar wani qawataccen gida dake dauke da manyan katangu ya tsaya,a ido kawai idan ka kalleshi zaka san cewa akwai sukunin rayuwa me yawa tattare da me gidan. Ya danna hon,cikin sakannin da basu wuce biyar ba aka wangale masa qofar,daya daga cikin masu tsaron qofar gidan mutum biyu ya rusuna cikin girmamawa har zuwa sanda motar ta sulala ta shige ciki kai tsaye zuwa yalwataccen parking lot na gidan.
Ko kafin yakai ga tsaida motar su fita masu aikin farheen su biyu sun iso,daya nanny dinsu khalipha ce daya kuma tana kula da tsaftace sashen farheen,don sam bata yarda koda wasa me aiki ta karbi wani abu da ya shafi hidimar mai gidanta ba komai qanqantarta.
Cikin girmamawa suke yiwa sãahar barka da zuwa,don dukkaninsu bawai baquwar su bace,kai tsaye ma za'a kirata da 'yar gida,saboda zaman shekaru kusan biyu da tayi dasu,har yanzu kuma bata rufa wata biyu bata zo tayi kwana daya ko biyu ba,daki ne da ita na musamman a gidan.
Baraka ta miqa hannu zata karba aleena sãahar ta hanata,tadai barta da hand bag da kuma qaramar luggage dinta ta wuce ciki rungume da yarinyar dake lafe a qirjinta,don tuni tayi bacci. Bata sauketa ko ina ba sai data dangana da ita har gadonta dake dakin farheen,ta fito Parlor ta samu farheen din na gayawa baraka ta tsaftace dakin da sãahar din zata sauka,duk da fes yake,sannan kuma lubabatu ta tambayi abinda sãahar din zataci a dora mata. Kai sãahar ta girgiza,cikin lallausar muryar ta take fadin
"don't mind,I can take care of myself"
"Really?,kinsan dole a kula da amanar auta" farheen ta fada cikin sigar tsokana kamar yadda ta saba takan zolayeta haka time to time. Dole wani murmushin ya sake kubcewa sãahar,ta motsa bakinta kadan,farheen na daya daga cikin mutane masu matuqar muhimmanci a rayuwarta,ba zata iya fadin adadin yadda taji dadin zama da ita ba a shekarun baya,har yanzun kuma tana jin dadin kasancewa da ita,shi yasa duk duniya ba inda take iya tafiya ta kwana idan na nan gidan ba.
Cikin qanqanin lokaci baraka ta gama kintsa dakin ta kuma shirya mata kayanta, bath set dinta ta fitar,ta zare kayan jikinya ta daura babban lallausan farin towel,ta zare farin ribbom din kanta,yalwataccen gashinta mai tsaho da sulbi ya baje saman lallausar farar fatar jikinta,hakan ya qarawa fuskarta wani kyau da haiba,tamkar ire iren jaruman indai mata,kai tsaye ta dauki kayan wankanta tana takawa a nutsenta zuwa toilet,ta hada ruwan wanka me dumi sosai ta shige,tayi wanka sosai da ruwan ya ratsata, idanunta a lumshe cikin shower din tana qoqarin tattara dukka wasu qananun damuwoyi da taci karo dasu a wunin yau tana watsar dasu daya bayan daya,so takeyi yau din tayi bacci me kyau ta kuma huta sosai,daga qarshe ta dauraye jikinta dake faman fidda qamshin shower gel dinta mai matuqar kyau da tsada,ta nade fatarta daketa sulbi cikin towel ta fito bayan ta sanya pad,kasancewar tana fashin sallah ne.
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k
*Al'ummar NIJER ku kira wannan number don yin naku pyment din*
+22799643131
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*H U G U M A*
*_TABARMAR ƘASHI_*💔
Page 06
*Arewabooks:huguma*
https://arewabooks.com/u/huguma
Sai data fara busar da kanta da ya jiqe,sannan ta shirya cikin wasu cotton kayan bacci masu tsananin taushi,riga da wandon da bai sauka har qasa ba,kadan ya rage yakai idon sahu,ta mulke kanta da turaren gashi kamar yadda ta saba ya zame mata al'ada,hakanan ta shafe jikinta da nau'ikan turarukan da sai zatayi bacci take using nasu.
Cikin sofa bed ta kalmashe qafafunta bayan ta rage haske dakin,ta ja wayarta ta kunna data,tanason shiga media ta karanta news ko zata rage tsahon daren sai taji ana knocking,ta daga manyan idanunta da suka rusuna zuwa lokacin ta kallo qofar sannan ta bada izinin shigowar. Baraka ce,cikin girmamawa ta isar mata da saqon farheen na ta fito taci abinci,kai ta girgiza
"Am okay,kice mata saida safe ma hadu" kai ta jinjina sannan ta juya zata fice
"Ammm,amma idan zan samu black tea ko coffee ina so"
"Babu amma yanzu yanzu saina hada miki"
"Na gode" ta fada a tausashe,baraka ta juya ta fita tana ja mata qofar.
Tana shirin buda wayar saiga kira ya shigo mata,tsaiwa tayi cak tana kallon numbers din dake faman harbawa saman screen din wayar,baquwar number ce don babu ita cikin kaf 'yan tsirarun contact da ta adana cikin wayarta. Ba kowacce number take saving ba,sai number dake da matuqar muhimmanci da amfani a tattare da ita. Wannan yasa taqi daga kiran,har ta gama ruri ta katse,saita sake kunna data din ta shiga abinda tayi niyyar yi tun farko.
Ba'a dauki dogon lokaci ba kiran ya sake shigo mata,taja qaramin tsaki tana jin kamar tayi rejecting,amma saita fasa,taci gaba da kallon yadda wayar ke neman a kawo mata agaji,harta gaji da ɓurari ta sake yankewa,katsewarta da minti daya kacal saqo ya shigo
_"please......do me a favor,ki daga kirana koda na second biyar ne,zan gode da hakan,mahmud abba gana"_
Wani dogon tsaki ta saki kamar zata cire halshenta,wani abu mai tauri yazo ya tsaya mata a wuya,ta lumshe ido tare da danne makashin wayarta yana kasheta gaba daya qirjinta na wani irin dokawa,kenan afifa ta raba number wayarta?,me yasa afifa zatayi mata haka,ta rufe ido kamar batasan komai ba......kamar komai bai faru ba?". Ita daya cikin dakin amma bacin rai ya cikata,haka ta dinga hararar wayar dake ajjiye a gefe kamar itace mahmud din,cikin ranta tana qiyasta gamuwarta da afifa,a haka farheen dake cikin shigar wasu lafiyayyun kayan bacci masu matuqar kyau da daukan hankali ta turo qofar ta shigo dakin, hannunta dauke da coffe din sãahar.
Da kallo sãahar din tadan bi farheen,zamanta da ita ta koyi abubuwa masu tarin yawa,ta kuma gane ashe a baya ita din amsa sunan mace kawai takeyi ba tare da tasan ma'anar hakan ba,sai data zauna da farheen din na tsahon shekaru biyu da Wani abun,taci gaba da kallonta cikin rai da zuciyarta tana jin inama itace farheen din,bata da wata damuwa kaf rayuwarta,Allah ya bata miji irin yaa muhyi dinta,ya kuma azurtata da zuri'a yara lafiyayyu har guda biyu,gidanta tamkar ita ta zabawa kanta shi,duk ko me takeso tana samu,inda itace ita me zata nema kuwa a duniya?.
"Gayamin ta yaya zakiyi kumari,kin kama black tea da coffee kin riqesu tsam" farheen ta fada tana dire cup din saman bedside,idanunta akan fuskar sãahar tana qoqarin karantar yanayinta da take shinshinar kamar ya sauya.
Karamin murmushin da yafi kama da yaqe ta dan saki
"Bana jin yunwa,bazan iya cin abinci kuma banajin yunwa ba" kallonta farheen tayi tayi murmushi
"Koda bakiji yunwa ba ki kamanta ci koda babu yawa" lumshe ido kawai tayi ta gyada mata kai
"Ba wani abu da kike buqata ko?" Kai ta sake gyadawa tana qoqarin zama sosai saman sofa bed din
"To sai da safe"
"Khalipha fa?" Waiwaya kadan farheen tayi
"Kina buqatar dan tayin kwana ne?" Kai ta gyada
"Kin manta ne tare muke kwana dama duk sanda nazo?"
"Haka ne,zan sa baraka ta kawo miki shi,saida safe"
"Allah ya kaimu" ta amsa tana miqa hannu ta jawo mug din tana kaiwa bakinta.
Ba jimawa baraka ta shigo da khalipha wanda keta faman barci,an shirya shi cikin kayan bacci da alama ya jima dayin baccin,ta kwantar mata dashi saman gadon taja mata qofar. Ko rabin coffe din bata sha ba taji ya isheta,ta maidashi saman qaramin plate din tangaran din da farheen ta hado mata dashi,ta miqe a nutse ta shiga toilet tayi brush sannan ta dawo ta rage hasken fitilun dakin,ta hanye gado tana lullubesu da bargo ita da khalipha bayan taja yaron cikin jikinta tana jin tamkar ita ta haifeshi.
Ajiyar zuciya ta saki mai nauyi sanda ta lissafa shekarun yaron,yazo dai dai da shekarun faruwar wani abu daya sameta a baya,ta gyarawa yaron kwanciyar cikin jikinta,tana iya jinsa sanda yake sauke ajiyar zuciya,sai wasu hawaye masu dumi suka ratso ta idanunta,ta sanya tafin hannunta da sauri tana gogesu,qasa qasa bakinta na furta