← Book details Tabarmar Kashi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 171

Sashe 45

Tabarmar Kashi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Na fara iskeka ne don nayi miki kyakkyawan albishir din cewa ka kusa zama uba,babyn naka na dauke da wani babyn naku......i mean matarka nada juna biyu" ta qarashe maganar tana zube dukka idanunta akan fuskarsa,tana fatan ko yaya ta fusgi wani reaction nasa,wanda shi zai bata kowacce irin dama da takeson samu daga gareshi.

Cak komai ya tsaya a falon tsakaninta da adam din,kafin daga bisani ya sakar mata murmushi yana juya key din motar dake hannunsa

"Ban taba zaton ke mutuniyar kirki bace irin yau,kin iya kawo kyakkyawan albishir,duk da naso na fara jin hakan daga bakin baby...... anyways.....ke da ita duk daya ne,ina taya junanmu murna" ya qarashe maganar yana tsareta shima da nasa kallon.

Murmushi ta saki tana murza hannunta

"Haka ne abinda ya kamata ya fito daga bakin kowanne magidanci na qwarai.....shikenan daga yau allurar planning ta qare,saika maida hankali ga kula da abinda yake cikin nata,yadda kake kula da duk wani kudi da zai shigo ko ya fita ta account dinta,da yadda kake kiyaye lokuttan yin salary dinta da sauran komai nata.....ina fatan yaron da ba'a shirya zuwansa duniya ba..... ubangiji ya qaddari zuwan nasa ta silar innarsa afifa......zai samu kulawa matuqa da qauna hadi da soyayya,kwatankwacin wadda ake iqirarin ana yiwa mamansa......yanzu zan turo maka babyn naka,ku sauka lafiya" daga haka ta miqe tana ficewa daga falon,yayin da adam ya miqe tsaye yana rakata da ido,zuciyarsa na suya sosai.

Ya akayi yarinyar ta rainashi har haka?, waye ya gaya mata sirrin rayuwarsu da yadda suka tsara zasu tafi da ita tsakaninsa da matarsa mallakinsa?,me yarinyar ke nufi akansa?,wanne kallo takeyi masa?,akwai maganganu da yawa da yakeson gaya mata don tasan shi din ba sa'anta bane,to amma kuma ta riga tayi nisa ba ta yadda zai iya amayar mata da dukkan abinda yakeson fada din.

Sosai Zuciyarsa ke quna,ransa yayi matuqar baci da maganganun afifan,a zafafe ya fita a falon,ya bude motarsa ya zauna yana jiran fitowar saahar,ya tabbatar banda saahar na sonshi so na gasken gaske,yayi amannar da tuni afifa ta dade da tarwatsa kyakkyawar mu'amala ta fahimtar juna kyautatawa da girmamawar dake tsakaninsa da ita.

Sallamar saahar din kawai ya iya amsawa,ba tare daya waiwayo ya dubeta ba ya tayar da motar ya figeta suka fice daga gidan,saahar da batasan abinda ke faruwa ba ta bishi da kallo galala cike da mamaki

"Na dauka zaka shiga ka gaida ummi ne ai" ta fadi a sanyaye tana mamakin abinda ya canjashi da matsanancin fushi haka lokaci guda.

Shuru baice mata komai ba,sai mamaki ya sake kamata,ta gaza dannewa saboda bata saba ganin irin wannan yanayin a tare dashi ba

"Dear......lafiya kuwa?,ko wani abu ya faru?" Da wani irin gudu ya gangara gefan titi ya tsaida motar,cikin tsawa da hargagi ya soma magana

"Saboda zallar rainin hankali ma ni kike tambaya lafiya?,bayan kinsan komai?,kinsan abinda ya farun?,ki aiko 'yaruwarki ta cikin mutunci ta wulaqantani,ashe yawo kike dani kina bayar da labarin ina karbar dukiyarki,kina gayawa duniya nidin makwadaici ne?,to ki sani ba abinda zanyi da dukiyarki,ki kuma gayawa wannan banzar 'yar uwarki taki afifa ta fit......."

"Ya isa!!" Ta fada da qarfi zuciyarta na wata irin suya,mamakin adam yana cikata,ta dinga kallonsa sosai waiko zataga wani sign na fara shaye shaye a tare dashi,tunda take dashi ko kallon banza bai taba hadata dashi ba bare tsawa har irin haka ba, zata iya jure komai amma banda zagin afifa,don ita din Wani sashe ce ta jikinta

"Ta yaya zaka zo kana hukuntani akan al'amarin da bansan dashi ba?,har kana qoqarin zagin afifa,afifan da bata nufinmu da komai sai alkhairi?"

"Kedai!,amma banda ni,yadda ta tsaneni nima haka na tsaneta,i hate her with passion,idiot....." Saiya finciki motar da kyau,har saahar nayin gaba zata daki gaban motar ta kare da hannayenta, hankalinta ya tashi sosai,bata saba ganin tashin hankali ba,kamar yadda bata taba ganin bacin rai makamancin haka daga gurin adam ba,duk da tasan yana da fushi amma bai taba kwatanta mata ba.

Kuka ta fashe dashi tana dora kanta saman cinyarta,wanne abu afifa dinta ta yiwa adam da zai dauki irin wannan mugun fushin?. Suna isa gidan yaci burki,ya fita yabarta a motar bayan ya kashe. Da hanzari itama ta fita a motar tabi bayansa,saidai bata cimmasa cikin falo ba,tana niyyar binsa daki da take jiyo motsinsa da qarfi sai gashi ya fito,hannunsa dauke da wani file.

*H U G U M A*

*_TABARMAR ƘASHI_*💔
https://arewabooks.com/u/huguma

Page 40

Yana daga tsayi ya wurgoshi kusa da ita,abinda ya baiwa dukka takardun ciki damar fitowa suka warwatsu a falon

"Ga komai naki nan,ki duba dukka abinda babu a ciki ki rubuta zan biyaki,sauran abinda mukayi hadaka kuma ki lissafa nawa ne na cire miki naki" ya qarashe maganar cikin fushi. Iya wuya zuciya tazo mata,sai taji ba zata iya jurewa wannan abun nasa ba,bayan batasan me tayi masa ba,ta miqe a fusace karo na farko a tarihin zamansu data taba maida masa magana

"Basai ka fake da abinda afifa tayi maka ba,zaka iya cin mutuncina duk ta yadda kaso adam,na gode" kuka ya qwace mata ta juya da hanzari ta nufi bedroom dinta.

Sautin kukanta bai hanashi wucewa dakinsa ba yana jan mugun tsaki,amma tsakanin awa daya zuwa biyu sai wayarsa tayi qara,ya kalli wayar yaja tsaki,banda me kiran nada muhimmanci a wajensa ba abinda zai sanyashi daga wata waya a yanzu,shi daya yasan iya adadin yadda ransa yake a bace da kuma irin rudanin daya samu kansa a ciki a iya ranar yau,komai yazo masa a bazata,ya miqa hannu ya daga wayar yana maqaleta a kunnensa.

*_BAYAN AWA DAYA_*

Ajjiye wayar yayi,ya shiga toilet dinsa ya fidda kayan jikinsa yayi wanka,ya dawo ya shirya cikin armless riga da boxer dinta,ya feshe kansa da turare sannan ya wuce dakinta.

Yayi mamakin tarar da ita tana kuka har sannan,yayi tsaye a kanta yana kallonta,sai yaji zuciyarsa ta karyo,ya qarasa kusa da ita ya dora hannunsa saman bayanta

"Awa nawa kikayi kina wannan kukan da bashi da amfani?,bayan kinsan bake kadai bace?" Maganar tasa tazo mata a bazata,sai kukan nata ya tsaya cak,yadda yayi maganar juna biyun dake jikinta kadai ya tabbatar mata shima yana maraba dashi,sabanin yadda tayita tunanin da yadda zata fahimtar dashi. Bata gama wannan tunanin ba taji ya sanya hannunsa duka biyun ya dagota ya rungumeta yana fadin

"Am sorry,raina ne a bace" ajiyar zuciya ta saki tana narkewa a qirjinsa,cikin lokaci qalilan komai ya wuce a tsakaninsu kamar komai bai faru ba,kasancewar basu saba samun sabani a tsakaninsu irin haka ba,sai ya bude sabon shafin tattalinta tare da nunawa abinda ke cikinta zallar qauna muraran,wannan ya wanke komai daga zukatansu.

*********Cikin kwanakin da suka biyo baya komai ya koma normal,hankalin saahar ya sake kwanciya sosai da yadda adam ke tattalinta yana nunawa cikin jikinta qauna,har excuse ya nema mata daga wajen aiki saboda laulayin da take fama dashi,laulayi takeyi sosai,yau lafiya gobe babu lafiya,gaba daya hankalin 'yan gidansu yana kanta,tun daga kan abba har ya zaid da take bi,kowa tattalinta da kuma riritata yakeyi,kamar itace zata haifa musu jikan farko. Saidai duk irin riritar da suke nuna mata bata kai rabin wadda adam ke mata ba.

********Zaune take saman couche,ta miqe qafafunta sosai yadda zata sake,chiffon armless short gown ce a jikinta,wanda rashin tsahonta ya bawa sambala sambalan kyawawan qafafunta damar bayyana.

Waya suke da momee,wadda kullum kwanan duniya sai ta kirata tayi mata sannu da jiki,tun abun yana sata jin kunya da nauyi harta fara sabawa,sukayi sallama da ita dai dai sanda adam ke fitowa daga kitchen,hannuwansa duka biyun riqe da mug dake dan fitar da tururi,qamshin kayan qamshi na tashi a ciki.

Tun kafin ya qaraso ta miqe ta zauna sosai,shima ita yake kallo fuskarsa tana fitar da murmushi,ya soma takowa a hankali saita maqale kafada a shagwabe

"Jan rai ko?"

"Yes" ya amsa mata kai tsaye yana dariya qasa qasa. Kunnuwanta ta kama tana dariya kadan kadan

"Na tuba,don Allah a bani nasha" idanu yadan zubata,yadda tayin tayi masifar burgeshi,kyanta kuma ya sake fita muraran,sai yaji jikinsa yadan saki amma kuma ta wani sashen wata zuciyar ta qara masa qaimi tare da karsashi,ya qarasa gabanta yadan russuna ya miqa mata cup din

"Thanks dear" ta furta da sassanyar muryarta bayan ta saka dukka hannuwanta guda biyun ta karbi mug din cikin zallar kwadayin shan tea din,ta sanya bakinta ta kurba,saita lumshe ido tana sakin murmushi saboda dadin da ya ratsa ta sosai

"Na yarda yau kadai.....ka fini iya hada black tea" murmushi ya sakar mata ba tare da yace komai ba,ba kuma tare da ya dauke kallonsa daga kan fuskarta ba,ta sake kai cup din bakinta ta sake sipping,dai dai lokacin da qaramar wayarsa dake kan wani dan teburin gilashi tare da babbar wayarsa dake charge ta dauki qara,ya qarasa a hankali,ya zareta daga charging ya karata a kunnensa idanunsa har yanzu akan fuskar saahar

"Yanzu?....kamar dai gobe...... alright on my way" ya fada a hankali,saiya cire wayar daga kunnensa ya tako inda saahar take.

Rusunawa yayi yayi kissing goshinta

"Ayimin afwa baby,fita ce ta kamani yanzu,just one hour zanyi zuwan da dawowar...... I hope ba damuwa?" Kai ta jinjina masa tana lumshe kyawawan fararen idanunta

"Babu dear" ciki ya wuce,ba jimawa ya fito,ya canza kaya zuwa qananun kaya,sai zabga qamshi yakeyi,ya mata kyau sosai,ya sunkuya ya sake kissing dinta,har ya wuce ta kira sunansa

"Kayi kyau da yawa,Allah yasa ba zance zaka je ba" ta fada tana langabar da kai. Dariya sosai ya saki,sai ya dawo ya tsugunna a gabanta

"Bayan ke babu wata,idan akwai ma Allah yasa ta makance ta gurgunce koma ta mutu....."baki ta kama tana dariya

"Nidai ba ruwa na,irin wannan mummunan fata haka"

"Eh kuma har zuciyata na fada ba,bazan wuce hour dayan ba zan dawo in sha Allah" ya fada yana miqewa da dan hanzari sanda wayarsa ta qara yin qara alamun ana sake kiransa. Hakanan ta samu kanta da binsa da kallo har ya fice.

A nan falon taci gaba da zama tana kallon wani film da mbc2 suke haskawa,film ne daya shafi soldiers battle,tana son irin films din sosai.
Chapter 45 · 0% Book details