← Book details Tabarmar Kashi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 171

Sashe 54

Tabarmar Kashi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mamakinta ya sake qaruwa lokacin data bude qofar falon,kaya ne a warwatse a qasan falon,ba watsewar kayan bace abun mamakin,gamayyar kalolin sutturar mace da namiji,daya dai tabbas kayan adam ne,yadin data siya masa a dinke a matsayin gift ranar zagayowar shekarar haihuwarsa,sauran kuma ba zata iya tantance suturar waye ba,tasan dai ba tata bace.

Wani abune ya daki zuciyarta,amma saita matse zuciyar tata daga zarge zarge da tunane tunanen data fara debo mata,koma meye a yanzun bata rayuwar adam take ba,ta kanta da tata rayuwar da rayuwar abinda yake cikinta takeyi,koda tana buqatar sanin wani abu akai,tasha maganinta a yanzu shine abinda yafi zame mata me muhimmanci,tanajin mummunar fargabar da kuma mugun bugun zuciya,amma haka ta dauke idanunta daga kan kayan,ta kuma dauke idanunta daga kan sashen dakin adam dinma gaba daya ta nufi dakinta,saidai tana zura key da nufin budewa qofar ta tura kanta da kanta.

Wani irin gurnani da sautin nishi ne abu na farko daya fara kaiwa ga idanunta,kafin daga bisani idanun nata su iya dauko mata hoton abinda ke wakana a tsakiyar gadonta na Sunnah,tare da mijinta na sunnah,cikin gidan aurenta na sunnah.

Ba qaramin dan gajeran yaqi akayi tsakanin ido da kwanyarta kafin qwaqwalwar ta yarda ta kuma tantance mata gaskiyar abinda idanun suka hango mata. ADAM mijinta,tare da wata mace da ba zata iya gane ko wacece ba,suna aikata fasiqanci akan tsakiyar gadonta,dukkansu haihuwar iyayensu,dagashi har ita,ko duvet basu kaarantawa kansu sun rabawa jikinsu ba bare akai ga batun sutura.

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" ta fada da qarfi sanadiyyar fusgota tayi daga cikin bakinta qarfi da yaji lokacin da numfashinta ke niyyar katsewa daga gangar jikinta.

Dif taji sautuka marasa dadin dake tashi sun katse,ta daga kanta da yayi mata wani mugun nauyi tana sake qoqarin bude idanunta a karo na biyu. Tayi zaton ganin kowannensu a wani muhallin na daban yana neman sutura ko maboya,a'ah.......sabanin haka sai ta sake ganinsu a tare da juna,suna ci gaba da aikata alfasharsu hankali kwance,kamar ma basusan ta shigo ba.

"ADAM!!!" Ta kira sunansa da wani irin sauti kamar na mutuwa,waiwayowa yayi yana duban tsakiyar qwayar idanunta da rinannun idanunsa,ba kuma tare da ya fasa aiwatar da abinda yakeyi din ba. Wani irin mummunan fushi da tashin hankali ya rifto mata,ta daga qafarta da zummar kaiwa cikin dakin don ta dakatar dasu,saidai taku biyu kacal tayi!,wani abu me dumi taji ya tsarga daga mararta yana bin qafafunta,abinda ya sanya mata waigi,ta dakata a firgice tana binsa da kallo.

Jini ne jajir yake saukar mata, shigen jinin data gani a wancan lokacin na baya,wanda ganinsa ya tabbatar mata da zuwan qarshen zaminin cikinta,a yanzun kuma me yake shirin alamta mata?. Da wacce jarrabawar zubarsa zaizo mata?, qwaqwalwarta batayi nisan kiwon da zata lalubo mata amsar tambayarta ta fara kokawa da numfashinta,a hankali ta soma gani dishi dishi,dukkan wani jarumta ta gabban jikinta ta fara zagwanyewa,saita fara sulalewa tana yin qasa,inda daga bisani ta kife kif a akan fuskarta kuma saman cikinta.

*******Ba zata iya cewa ga iya adadin awannin data dauka kafin dawowarta duniya ba,iya abinda zata iya tunawa kokawa data fara yi da zuciya da ruhinta,kokawar da batasan a gaske take yinta ba,har sai lokacin da taji ana bada umarnin riqeta,ba jimawa taji an daddanneta,bawai iya hannuwanta kadai ba,harda qafafunta,ta kasa motsa koda yatsarta,a sannan ta yanke shawarar buda idanuwanta taga ko cikin kabari take wannan al'amarin yake faruwa da ita?.

Ba cikin kabari bane,cikin dakinta take,saman gadonta data tabbatar an gama yamutsashi da qazantaccen al'amarin da idanunta suka gani a dazu,hannunta guda daya qarin ruwa akeyi mata,wani dogon baqin mutum dake sanye da lab coat yana tsaye kusa ruwan yana qoqarin zuba wasu allaurai,daga daya bangaren kuma adam ne,wanda ya haye fiye da rabon gadon,kuma shike daddanne da ita.

Wani azababben bacin rai tsana da kuma mummunar qiyayyarsa ce ta zarto tun daga asalin qasan zuciyarta har zuwa saman fuskarta,wani irin qarfi yazo mata,tayi yunquri me qarfi sai gashi tayi nasarar ture adam din gaba daya gefe,saboda ya saki jikinsa,bai dauka zata iya aiwatar da hakan ba.

K'arin ruwan da ake mata tasa hannu ta fincike,take ruwan ya soma zuba a qasa,jini kuma ya ballewa hannun nata,kafin takai ga miqewa adam din ya miqe tsaye yana dosowa inda take

"Karka sake ka matso inda nake,karka kuskure ka qaraso kusa dani,mugu azzalumi,macuci fasiqi,na gama zama dakai har abada wallahi,nayi nadamar saninka a rayuwata,nayi nadamar hada jikina da nayi da naka qazantaccen jikin" tana gama fada ta diro qafafunta qasa cikin fushi qasa,saidai tana miqewa ta jita fayau,kamar iska zata kayar da ita,jini me dumi ya sake zarto mata,amma duk da haka bata dakata daga fita da take niyyar yi ba. Ta tsani ganin koda inuwar adam bare ta hada daki daya dashi,ballantana kuma har suyi musayar numfashi,burinta kawai ta ganta ba a cikin gidan ba kota wanne hali,saidai tana kaiwa bakin qofa taji an fincikota an watsar,kafin ta gama gane ainihin abinda yake faruwa,an saukewa kyakkyawar fuskarta lafiyayyun mari guda biyu,wanda saida kunnenta ya dauke ya daina ji na wucin gadi,idanunta kuwa wasu irin taurari ta gani sun gifta,bata dawo hayyacinta ba adam ya bayyana a gabanta.

Wata irin tsaiwa yayi a kanta,ya raba qafafunsa biyu a tsakiyarta yana duban qwayar idanunta da kyau

"Ina zakije da?,ai yanzu aka fara wasan,wasa ne me kyau dake nuni da kyakkyawan shirin bugashi da kikayi,wanda inda kinsan true color din abokin buga wasan naki da baki tarki yin irin wannan wasan dashi ba" mamaki ya sanya ta daga fararen idanunta da suka taruwar jini a gefe tana kallonsa

"Eh,idan kuma har baki shirya ci gaba da buga wasan ba........hanya guda daya ce gareki,ki fiddomin jakata da kika dauke" kai tsaye babu wani bata lokaci ko dogon ta fahimci abinda yakeson fada

"Jakarka?" Ta fada bawai don tanason musawa ko kokwanto ba

"Yes jakata,wannan ne zai sanya na baki damar tafiya salin alin,ina tsananin sonki sãahar,don ban taba samun mace me zallar madarar kyau da cikakkiyar ni'imar da take iya gamsar dani,da wani irin dandano da dadi na musamman kamarki ba,amma wallahi wallahi nafison kudi fiye dake,kuma nayi imanin su zasu sake samarmin wata macen wadda ta fiki ma wala'alla a wata nahiyar duniyar,matata ba zata taba hanani yin duk harkokin da nakeso ba,saboda itama bai hanata tayi tata rayuwar ba,amma ke muddin zanci gaba da zama dake,duk wata shaqatawata da jin dadina saidai na ajjiyeshi a gefe saboda wai kiyaye mutuncin addini da kuma samun dorewar soyayyarki da zaman lafiya a tsakaninmu,kamar yadda nayi tsahon uku babu kadan a zaman da mukayi......wanda nikam bazan iya ba,inason rayuwa" ya qarashe maganganun nasa yana sakin wani mugun murmushi.

Saita zama speechless,ta narke a wajen tana kallon adam din cikin tsantsar mamakin daya gama daskarar da ita a gurin

"Me kike kallo?,zaki ban jakata na sallameki ko saimun ci gaba da buga game din?"

"Da kudadena halalina zakayi wannan shaqatawar?" Ta jefa masa tambayar da tafi qona mata rai,tafi kuma yi mata ciwo a ranta

"Really,kin fini tarawa da yawa ai,sannan acan gida ma an tara miki wasu ana kan tara mikin ma kinga ya kamata naci gadonki tun kina raye,tunda na taqaita miki wahala ban bari kin haihu dani ba,wancan cikin na saka miki tablet yabi rariya salin alin,wannan ma yana fara girgidi na sanya aka zaquleshi aka watsar,don haka ina binki ladan aiki ma" sosai ta sake razana da bayanansa,ta miqa hannu ya shafo jinin dake bin qafafunta har yanzu ta kawoshi dai dai fuskarta tana kalla,wasu zafafan hawaye suka fara bin kuncinta,shikenan,shima ta rasashi. Wata irin dakiya taurin rai da zafin zuciya ne suka saukar mata a lokaci guda,ta daga fararen idanunta da a yanzun suka rine zuwa jajaye ta kalleshi da muryarta data qara kauri ta kuma cakude da sautin kuka

"Yadda idan mutum yabar duniya sunyi bankwana da ita kenan har gaban abada.......haka nan wannan jakar tabar hannunka har abada,koda hakan yana nufin rasa numfashina ne" miqewa yayi zumbur yana dubanta saboda girgiza da yayi da jin furucinta,yasan halinta tsaf fiye da kima,KHADIJA tana da matuqar taurin kai a wasu lokutan,hakanan ita din kaifi daya ce,idan tace YES tofa YES dinne,hakanan idan tace NO zaiyi wahala ta dawo tace YES. Da qyar ya tattara qwarin gwiwarsa,ya saki dariya ya qara taku biyu zuwa gabanta kamar zai take yatsun qafarta

"Nasan halinki fa,shi yasa na shiryawa dukkan wani taurin kan da zakizo min dashi,wuya da kuma azaba babu abinda bata sanyawa a barshi ko a aikatashi,idan ke qwararriyar 'yar wasa ce to kin hadu da qwararren me buga wasan"

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070

*Al'ummar NIJER ku kira wannan number don yin naku pyment din*

+22799643131

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥

Page 49

*H U G U M A*

*_TABARMAR ƘASHI_*💔

Page 49

Juyawa yayi ga likitan dake tsaye a gefe abinsa kamar ma baisan abinda yake wakana ba

"Me kake jira likita?,ci gaba da aikinka" sai ya waiwaya gareta

"Kika musanta ko kikace zakiyi taurin kai.....zakici gaba da shan baqar wahala ne a hannuna,babu kuma wanda ya isa ya qwaceki".

Zumbur ta sake miqewa ganin likitan ua dosota,har batajin ciwo da zubar jinin jikinta,da gudu ta doshi qofa,amma kafin ta isa adam din ya rigata,ya kankane qofar,daga bayanta kuma likitan yana tsaye yana jiranta,ta duba hagu dama babu ba wani gurin tsira sai qofar toilet,don haka ta kwasa ta nufa can da gudu.

Harta wuce drawer dinsa ta hangi wayarta akai,ta dawo da baya ta finciki wayar ta qara gudu zuwa toilet din,idanun adam suka kai kai,ya baro bakin qofar da wani irin mugun sauri ya biyo bayanta,kafin ya iso ta samu nasarar shigewa bandakin,ta tura qofar,ta kuma danneta da bayanta. Hannunta na rawa ta kunna wayar,ta fara laluben wanda zata kira,zuciyarta tayi mugun karyewa sanda ta tuna a yanzun kusan dukka wanda take saka ran samun daukinsa baya qasar baya tare da ita,daga qarshe ta yanke shawarar kiran ummin afifa.
Chapter 54 · 0% Book details