← Book details Tabarmar Kashi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 171

Sashe 71

Tabarmar Kashi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

HA
"Mummy bakiga irin kyau da halittarta bane?,bakya tsoron ta rudi yaa toufeeq da kyan nata?" Qaramar dariya hajiya qarama ta saki
"Toufeeq..
. toufeeq dai? ke bakisan halinsa
bane halan har yanzu?,kin taba ganin idanunsa bisa fuskar wata mace da zummar so ko sha'awa?,bare har yaji tayi masa? inama yake toufeeg din?" Shuru labiba tayi tana juya maganar mommy din. Tabbas ko ita din iya tsahon rayuwarta zata iya irga sau nawa ya daga kai ya kalleta,kallon da mafi yawan lokuta yana mata shine don hukuntata idan tavi wani abu daya saba da nasa ra'ayin,sai taji wannan case din kamar ya mutu ne
"Mommy haseena zata dawo ne?" Sai data buda murfin motar ta saka qafarta waje sannan ta amsa mata Ад
"Ba yanzu ba" ta fara qoqarin fita sai kuma ta dakata,shuru tayi kamar me nazarin wani abu,sanann ta fara magana da labiban a hankali
"Toufeeq allura ce cikin ruwa,me rabo ka dauka,so ki dinga sassautawa kanki wasu abubuwan kinji daughter" daga hakan ta saka gafafunta waje ta fita a motar tabar labiba a ciki.
Shuru tayi gumi na dan tsatstsafowa daga goshinta,mommy din tayi magana cikin kwantar da murya da kuma nuna kulawa,to amma kalaman dake qunshe cikin maganarta....sunyi mata wani iri,me rabo ka dauka?,allurar cikin ruwa?,duka me hakan yake nufi?. Shuru ta sakeyi tanason lallai saita fahimtar da kanta,amma ta gaza gano komai,tunda tace dawowar HASEENA ba yanzu ba,ta toshe duk wani kafa ta tunaninta,dole ta jawo qafafunta ta fita a motar don ta bawa driver din damar rufe motar,saidai a ranta tana jin ya kamata ta kira

hajiyarta ta gaya mata ko ita din zata gano abinda ta gaza ganowa.
Da daren ranar suna saman gadon fadeelan,bayan ta tabbatar ta bata magungunan da afifa ta rubuta ita kuma ta fita da kanta ta siyo. Ta shiryata cikin kayan bacci,kan fadeela na kwance saman cinyarta,gashinta me tsaho da santsi irin na saahar din ya baje saman gafafun sãahar din,ta nace wai sai sãahar din tayi mata kitso.
Itama ba iya kitson tayi ba sai kalba,don haka kalbar taketa qoqarin kitsawa amma tana warewa, kunnuwanta suna kan fadeelan daketa complain din rashin kiranta da Abby din nata baiyi ba. Kusan duk wayar da zaiyi matan tana gurin baaba ramatu,a can suke wayarsu su gama
"Abby yayi busy ne tabbas,amma ayi masa uzuri kinji,ki daina complain da yawa fadee,he cares about you fadee,you have to appreciate his efforts kinji" ta fadi ne don kawai kwantar mata da hankali tare da nuna mata muhimmanci haquri da kau da kai. Kai ta gyada a sanyaye,bata sake cewa komai ba.
Kamar jira kuwa akeyi tayi shurun sai tab din ta fara gara, zamewa tayi da gudu ta dira a gadon ta nufeta,ta iya karatu sosai,don haka ta karanta sunan me kiran
"Aunty,budemin google meet dina,abby ne a nutse ta sauka a gadon,ta dauko mata headphone da fold up stand,ta fara bata headphone din ta saka a kunnenta,sannan ta ware fold up din ta dora mata tab din a ciki don taji dadin amsa wayar,ta koma daga bayan camera din ta saita mata Google meet din.
Cikin qawatacce kuma tsararren balcony din nasa yake a zaune,wanda aka rabashi sassa biyu lounge and eating area qawace yake da wasu irin stone tiles da kuma couch masu tsananin laushi hade da table din dake da kujerunsa guda hudu,sai swing bench daga can gefe guda daya dake mahadin furniture din. Da wasu irin fitilu aka yiwa gurin ado,hakanan aka wadatashi da potted plants a kowanne sago da kuma qasan gurin,tsirran dake iva garawa gurin kyau iska me dadi da kuma qamshin furannin dake magale dasu.
Pajamas ne a jikinsa,farare tas tas dasu,rigar me gajeran hannu ce qwarai,v shape neck dake iya baka damar hango lallausar gargasar dake kwance lambam a girjinsa,hakanan gajartar hannun rigar yasa kake iya ganin dantsensa dake da wasu irin muscles,daga can gasa zuwa tsintsiyar hannun kuma gargasa ce itama me santsi baga sidik.
Wandon jikinsa iyakarsa gwiwa,yayi crossing gafafunsa yana jiran kiran da ya yiwa halittar mafi soyuwa a gareshi ya shiga,hannun damansa coffee dinsa yake sipping kadan kadan. Duka duka bai cika awa guda da dawowa daga office ba,ya sake maida kansa busy qwarai da gaske da tunanin hakan shi zai zame masa abokin debe dukka wata damuwa da kewa.

Miskilin murmushi ne ya subuce a labbansa sanda innocent face din fadeela dake zaune tsakiyar gado da hargitsatsen gashinta ta bayyana
"Assalamualaikum abby" sallamar tata ta ratsashi qwarai,ta kuma dace sosai da muryarta
'Waalaikumus salam,daddy's angel ta girma da gaske,an iya sallama da kyau‚barakallahu fiik"
"Abby,aunty nanny ce ta koyamin" sai ya jinjina kai yana murmushi
"Tace min tafi lada akan ace hello"
"'Da gaske ne" ya amsa mata yana gyara zamansa,ya buda baki zaice wani abu,saidai kafin yace komai din ta rigashi,ta barke da bashi labarin aunty nanny,abubuwan da take koyamata,abubuwan data hanata yi da wadanda ta gyara mata,karatunta da sauransu. Shuruuu kawai yayi yana bin bakinta da kallo tare da sauraren bayananta,yana tsintar abubuwa masu yawa game da labarin nanny din da take bashi,a hankali ya samu kansa da furta
"Alhamdulillah" a gasan zuciyarsa,tana sake gaya masa abubuwan da suke gudanarwa nutsuwa na sake saukar masa game da hannun da diyar tasa ta fada a wannan karon,abinda yake ta taraddadi kenan,sai ya gara sakewa sosai ya bata dukka hankalinsa yana sauraronta,cikin ransa yana jin mai yiwuwa Allah ne ya dubeshi ya share masa damuwarsa ya hada sanyin idaniyar tasa da nanny ta gari
"Kanason ka ganta? daddy na nuna maka ita?" Tayi gasa gasa da muryarta harda dan sunkuyowa screen din wayar alamun quima,tana maganar kuma tana satar kallon säahar dake tsaye bakin mudubi tana
taje kanta tare da gogarin hadeshi cikin
ribbon,fadeelan ce ta watsa mata kan a dasu garin cewa lallai saita koyi kitso itama a kanta.
Yadda tavi maganar da sunkuya da yin qasa qasa da murya ya bashi dariya,ya daga hannu yana shirin dakatar da ita,amma
inaaa... bata tsaya jin ta bakinsa ta juyar da screen din zuwa sashen da sãahar din ke tsaye tana daure gashinta da ya zuba har bayanta.
"aunty na juyo miki da camera kizo ku gaisa da abby na..." Wani muguwar faduwa gaban sãahar din yayi,tamkar wadda aka dasa taci gaba da baiwa camera din baya ba tare data juyo ba,ba abinda take tunawa sai kayan jikinta,inda Allah ya taimaketa doguwar rigace sakakkiya a jikinta,amma duk da hakan tasan tudun mazaunanta da kuma gashinta dake sake a baya yana lilo bazai kasa ganuwa ba,lallai ta yarda quruciya na damun fadeela sosai, banda haka ba wanda zaiyi irin abinda tayi.

Da sauri ya janye idanunsa daga kallon abinda baiyi niyyar gani ba,ya dunqule hannunsa sosai yana fadin
"Angel,move the camera,basai mun gaisa ba" kasancewar akwai headphone a jiki ya sanya ita daya take jin abinda yake fada,saita kyabe fuska tana fadin
"Anty na dauke camera din,yace basai kun gaisa bama" ido ya zubawa fadeelan sosai yana kallonta,can qasan magoshinsa yana qogarin harhada abinda zai fada mata,saboda ta sanyashi kallon abinda bai shiryawa ganin ba,dole ya mata bayani cikin hikima yadda zata fahimta,don ya fahimci ita kanta matar batasan zata juyar mata da camera ba. Zama yayi sosai yana fuskantarta,ya maida fuskarsa serious da zummar mata bayani da kyau,kada wataran ta sakashi ganin abinda baiyi niyya ba

"Fadeela"

"Abby"

"Kina iina?"

"En daddy"

"Daga yau idan na kiraki,idan bance ki bawa wani waya ba kada ki sake yin hakan kinji?" Kai ta gyada a sanyaye

"Kome zaka yima mutum saida izninsa,kinga yanzun ba hijab ko dankwali a jikinta,kuma ba kyau aga mutum a haka,kin saka mata camera,kinga ba zataji dadi ba ko?" Kai ta sake gyadawa da alamu jikinta ya mutu

"Good girl,idan mun gama waya ki bata haquri"

"In sha Allah" sai murmushi ya sake subuce masa,in sha Allah din kamar a bakinta aka radata,bai taba jin ta fadi ba,kamar wata babba,amma yanzun data fada sai yaji wani sanyi a ransa

"Khairan in sha Allah" ya fada a ransa yana jin hope sosai akan sabuwar nanny din fadeelan.

Tunda ta fahimci ta janye camera din sai ta koma gefe ta zauna tana maida numfashi, wani abune da bata taba zata ba shi yasa ta razana,wayarta ta jawo ta buda don rage zaman da bugawar da zuciyarta keyi akan abun,tana danne danne tana kiran sunan
Allah,har batasan fadeela ta kammala wayar ba,saijin mutum tayi tsugunne gabanta

"Aunty,am sorry,abby yace na baki haquri,na juya miki camera without your permission" ido ta zuba mata,sai ta murmusa ta sanya hannunta ta dagota ta dorata kan cinyarta

"Abby yace babu kyau kada na sake" kai ta jinjina

"Abby dinki is a good person,gaskiya ya fada,na haqura nasan kema ba kina sane bane ko?"

Kai ra gyada mata tana murmushin jin dadin yabon da ta yiwa mahaifinta,riqe hannunta tayi suka miqe
"Oya,muje a kwanta,gobe da school,next week kuma zaku fara revision,sai C.A then exams ko?

"Yes" ta fada tana murmushi

"Abby yamin alqawura da yawa,yace ya gaji da ganin third position,da second yakeson ganina,if possible ma first,idan na kawo first din kuwa,sai ya gyada kai,nasan abby naidan ya gyada kai baice komai ba.....hmmmmm,zai baka mamaki ne,anty ki tayani addu'a na samu first position" ta garasa maganar tana
marairaicewa dai dai sanda sãahar ke lullubeta
da duvet.
Murmushi ta saki,ta kama hannunta ta rige
cikin nata
"Kiyi karatu sosai kiyi addu'a da yawa,you will pass in sha Allah, kuma duka zan tayaki fadee"

qanqameta tayi tana dariya cikin jin dadi
"Na gode aunty nanny"

Shuru yayi idanunsa akan system dinsa
bayan sallama da fadeelan,hannunsa rige da
dan qaramin spoon yana ta juya tea din da
already ya riga ya gama juyuwa,ya rasa me
yake tunani,hirarsu da fadeela....abubuwan
da yaji.
.ko abinda ta nuna masa bai shirya
gani ba?, Sai kawai ya zame hannunsa daga
tea din,ya mige yana zuba hannuwansa dukka
biyu a aliihun wandonsa yana furta "La haula wala quwwata illa billah" tattaki yayi kadan ya matsa gaban balcony dinsa,ya zube idanunsa a gurin yana kallon jerarrun tsirran dake gurin suna rayuwarsu hankali kwance,duhun dare da hasken fitilu suna sake qawata ganin mutum. Qarar wayarsa ta sanyashi waiwayowa,ya zubawa wayar ido yana karanta sunan NADEEYA cikin ransa,sai data kusa katsewa sannan ya daga ya sanyata a kunnensa yayi shuru ba tare da yace komai ba.

*HUGUMA*
Chapter 71 · 0% Book details