← Book details Tabarmar Kashi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 171

Sashe 49

Tabarmar Kashi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*******K'arfe sha daya na safe ta fito daga wanka,daure da babban towel daya rufe jikinta sosai,tana a tsaye gaban madubi tana ware gashinta daya jiqe don busar dashi da hand drayer,tana ware gashin tana kallon fuskarta,tayi fresh sosai ta kuma fara dan cikowa. Cikinta ya shiga wata na uku har ya fara nisa,wannan ya sanya ta fara samun sauqin laulaye laulayen da take fama dashi,taji jiki iya jin jiki,ta gasu,don kusan yafi cikinta na baya bata wahala.

A nutse aka turo qofar dakin nata,ta maida dubanta ga qofar,adam ne ke shigowa da innocent face din nan nashi,yana sanye da shirt turtle neck me dogon hannu da trouser dinta data zauna masa a jiki sosai tayi masa kyau,idanunsa akan sãahar,yana jifanta da wani iri kallo dake cike da tarin soyayya,kamar zai cinyeta.

Har ya iso ya ajjiye madaidaicin tray din hannunsa idanunsa na a kanta,sai daya daidaita zaman tray din saman madubin sannan ya sanya hannuwansa ya jawota jikinsa yana dora kansa a gefan kafadarta

"Qara kyau kike kullum my heart" dan qaramin murmushi ta saki

"Shine kaketa wani kallo na kamar zaka cinyeni?" Ta fada shagwabe sosai,sai ya saki dariya me qaramin sauti

"Bakisan matsayinki bane a zuciyata,da ba zakiyi mamakin irin kallon da nake miki ba" shuru tayi tana jin saukar numfashinsa a wuyanta,kowacce rana sake jinjina soyayyarta dake ninkuwa a zuciyar adam takeyi,a duk sanda kuma ta tuna da incident dinsu na watannin baya sai taji tana sake gayawa kanta tabbas sharrin shaidanne da kowacce irin zuciya bata iya tsallake masa idan yazo da qaddara.

Dan janye jikinta tayi daga gareshi jin shurun nasa yayi yawa,ta waiwayo tana duban fuskarsa,damuwar da take hanga tun jiya ta sake ganinta muraran kwance saman fuskarsa,duk sai taji babu dadi,don ta tabbatar inda shine da tuni ya sakata a gaba da tambaya,har sai yaji menene?,ya kuma tayata sun magance abun koda da shawara ne

"Damuwa naketa gani fa a fuskarka" murmushi ya sake saki yana girgiza kai,tare da saka hannu ya maida gashinta dake son tsole mata ido baya

"Ba wani damuwa fa,kawai sauyin yanayi ne" fuska tadan bata

"Amma ko da ban cika mace ba,mata na rako duniya,almost three years amma ace na kasa gane damuwa a fuskar mijina?, c'mon,tell me kawai,ba'a boyewa abokin kuka mutuwa" ajiyar zuciya ya saki me nauyi dake alamta lallai akwai damuwar sosai a ransa,ya koma gefan gado ya zauna yana goye da hannayensa,idanunsan nan dake cike da wani irin kallo a kanta,sannan ya fara magana

"Momee ce......" Sai yayi shuru yana duban wani gurin

"Uhmmm,me tayi momee din?" Kansa ya girgixa sannan cikin damuwa yaci gaba da magana

"Wai lallai saina canza mota motar da take hawa,jarinta kuma yayi qasa,saboda ta tana kudinta sosai wanna zuwan da tayi Ghana,tana buqatar wasu kudi ta dora jarinta" qaramin murmushi sãahar ta saki,duk da taji maganar wani iri,saboda motar momee din ba wani dadewa tayi ba,hasalima tata ce adam din yake hawa,momee ta nuna sha'awarta,sãahar din tace yabar mata,gif ne ya Saifullahi ya bata. Bataji komai ba,don iyakar kirki matar tana dashi,hakanan soyayyar da take nuna mata ko adam data haifa baya samun ire irenta ma,bata qaunar bacin ranta ko dis!. Uwa uba kuma ita din tana comparing momee da maama dinta,ta tabbatar yadda adam yake sonta yake kuma girmama iyayenta......ba shakka zai iya yiwa abba da maama komai muddin yana da dama

"To meye abun damuwa a ciki dear?,uwa ce fa?,ko ranka tana ce kana so ba zaka iya cirewa ka bata ba?" Kai ya girgiza da sauri

"No heart.....ba haka bane,kinsan a yanzu babu agenda na taba kudaden dake hannuna....infact ma ni banason taba abinda yake ba mallakina bane ni kadai" ido tadan fidda tana kallonsa,sai kuma ta bata fuska tayi kicin kicin

"Kanason gayamin momee bata haifeni ba,kai kadaine danta" dariya sosai ya saki

"Nidai bance ba,kawai dai banason taba kudin ya kawo delay wajen cikar burinmu,inason kafin babymu ya iso duniya,yazo ya samu mahaifinsa wanda yake tsaye saman qafafunsa,sai raɓi inuwa ko alfarmar kowa ba" ya qarashe maganar bayan ya iso gabanta,ya dora hannunsa plate tummy dinta da har yau yake mamaki da kuma tantamar tabbatuwar samuwarsa.

K'awataccen murmushi ta saki,ta dora nata hannun saman nasa,wannan ya bashi damar dago fuskarta yana kalla

"An soso miki inda yake miki qaiqayi ko?,na lura kafuwar kamfanin ma bata dameki ba kamar yadda kika damu da zuwan babyn nan" kai ta jinjina

"Allah ya jarabceni da son yara,inajin ranar dana haihu bazan iya bacci ba,har ina rayawa a raina,wannan tsananin son yaran kada ya zama tawa jarrabawar kenan,na mutu ban haihu ba"

"Komai lokaci ne,gashi yanzu yana hanya?"

"In sha Allah" ta fada tana jin wani farinciki yana lullubeta,ta jarabtu da son wannan cikin fiye da cikinta na baya.

Zame jikinta tayi daga nasa,ta matsa zuwa side bed drawer dinta,ta budeta,sannan ta jawo safe dinta,ta ciro wani bangul guda biyu me kyan gaske daketa daukar ido,ta qaraso wajen adam dake tsaye daga bayanta, hannayensa cikin aljihun wandonsa yana kallonta. Miqa masa tayi

"Abun hannun nan yana da matuqar muhimmanci a wajena,amma duk muhimmancinsa baikai na miji na gari irinka ba,na amince ka siyar dashi,ka siyawa momee duk abinda takeso,idan da saura a zuba a kudaden da suka rage mana na gininmu,koda foundation a fara sakawa na ginin" baya yaja yana zare idanu

"What?, a'ah,ba za'a yi haka dani ba,Allah ya sawwaqe"ya fada yana yarfar da hannu,fuska ta bata tana kallonsa,sai shima ya tsaya ya zuba mata ido yana kallon yadda rashin jin dadi ya ratsa har cikin zuicyarta

"Ni ba kyauta na baka ba,ka rubuta idan komai na kamfani ya kammala zaka biyani" dariya ya saki sosai

"Matata me wayo,to godiya nake" ya fada yasa hannu biyu ya karba yana juya abun hannun,wanda ya tabbatar idan aka kaishi kasuwa kudade ne masu nauyi za'a karba. Ya sani yayi kuma imani sãahar ta dabance ko cikin mata,tana cikin sahun mutanen da idan suka soka qaramin abu bai sanyawa su gujeka,zasu iya sadaukar maka da dukkan farincikinsu muddin zasu samu soyayya da kulawa daga gareka,hakanan idan suka qika,zaiyi wuya wani abu yasa su soka.

Da hannunsa ya dinga bata breakfast din har taci ta qoshi,ya tattare plates din zai fita dasu yana cewa

"Bari na watsa ruwa,inason zan dan fita,sai naga waya kamata ya siya banguls din" miqewa tayi a nutse tana daure lallausan gashinta da wani qaramin scarf kalar english wears din jikinta

"Yaukam ko ladan hada maka ruwan wanka ka barni na samu please" ta fada a shagwabe,kai ya girgiza

"Indai nine na yafe" tsaiwa tayi tana dubansa,kamar me tuna wani abu

"Amma,yau kusan two weeks kana hanani shiga dakinka,why?" Ta fada tana bata fuska, murmushi ya sakar mata,ya kama kumatunta yaja

"Banason kiyi dukkan wani aiki bare ki wahala,idan kika shiga da zummar hadamin ruwan wanka,zakice zakimin gyaran daki ne,don dakin yayi qazanta da yawa,abinda ni kuma bana so kenan" kanta ta kawar gefe cikin nuna tata rigimar

"Wannan gatan yayi yawa,ba'a kaina aka fara samun ciki ba,gidanmu cike yake da 'yan aikin da idan na buqata za'a kawomin,amma banason,saboda me?,aure nazo bautar Allah,ba zaman jin dadi da baiwa zuciya da rayuka abinda sukeso ba,ina fatan samun dacewa" ta qarasa maganar tana zube idanunta a kansa.

Kai ya jinjina,shi kansa shaida ne,gata kyau ko wani matsayi na rayuwa bai sanyata ta dakaki kanta a gidan aurenta ba

"Shikenan,let's go" ya fadi yana bata hanya,saita miqe tana harararshi

"Da ladan kakemin buqulu?"

"Ban isa ba" ya fada yana daga hannu sama alamun surrender.

Koda suka shiga dakin bataga wani datti me yawa da yake magana a kai ba,ta hada masa ruwan yayi wankan a gurguje ya fito ya shirya,tana zaune daga gefan gadonsa suna hira har ya kammala,sannan suka fito tare,sai taga yana saka key yana kulle dakin,abinda ya maidashi dabi'a kenan a kwanakin,to amma da yake tana da nata bedroom din,kuma ba wani abu take ajjiyewa cikin dakin ba,sai bata taba damuwa ba,yayi kissing nata lightly a forehead dinta sannan ya wuce.

Ba abinda zatayi,yau ko aiki ba zata fita ba,don haka tayi zamanta a Parlor,ta kunna kallo,jita jifa tana taba chart a wayarta.

Sallar azahar ce kadai ta tasheta,tayi sallar ta duba fridge ta dauko fresh samosa da adam din ya mata order ya cika mata fridge dashi wai saboda yunwar dare,ta soyata,ta hado da hollandia me sanyi ta dawo ta zauna.

Tana tsaka daci kiran afifa ya shigo wayarta

"Uwar biyu" ta fada cikin salon tsokana

"Allah yasa,tabbas da kin samu kyautar kujerar umra daga adam" zuciyar afifa daga can ta tsinke,batasan wanne suna zata bawa adam ba,har yanzu zuciyarta bata taba nutsuwa da komai na adam ba,ta rasa me yasa?,duk da cewa ya bada dalilai masu yawa da yaci ace kowa ya gamsu ya kuma aminta dashi,amma ta nata bangaren hakan ya gaza samuwa

"Allah yasa" ta amsawa sãahar din

"Kudaden nan sunzo ko?" Kai ta girgiza tana sipping madarar

"A'ah,anya?,banga alert ba"

"Haba?,amma tun jiya da dare fa,kuma sunyi debiting dina,receipt din na manta banyi generating ba"

"Karki damu,zan duba balance,nasan sunzo ma"

"A'ah,duba dai yanzu ki gayamin,amana ce ya zaid ya bani kuma kafin na gaya masa na saka sai nayi confirming ya shiga Account dinki" qaramin murmushin dake qara mata kyau tayi

"Bestie koni kika siyar kikaci kudin kinci halak"

"Na sani,amma yanzun ki duba tukunna" ta fada tana katse kiran,ta ajiye wayar a gefe tana jiran kiran sãahar,akwai abinda takeson takai sãahar din gashi,addu'a kuma take takai gano.

Tana murmushi ta soma checking balance dinsu ta USSD CODE,tayi na farko yayi cancelling,ta sake gwadawa har sau uku yana cancelling,tayi duk wami qoqari na checking din amma yaqi yiwuwa,abinka dame ciki,haka kawai abun ya zafafeta,sai ta soma trying number wani ma'aikacin banking da suke ajiyar.

Sanda ta gama masa bayanin cewa yayi
Chapter 49 · 0% Book details