← Book details Tabarmar Kashi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 171

Sashe 74

Tabarmar Kashi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sãahar tare da jin nauyin kiranta anty da nadeeya tayi tunda ko a ido kana ganinta zaka san sun kusa sa'anni da ita idan ma zata girme mata to da kadan ne
"Lafiya alhmdlh sister nadeeya,ya karatu?"

Cikin jin dadin sunan data ambaceta dashi da qaramar dariyar farinciki tace

"Karatu ya qare, in sha Allah nan da kwanaki uku ina tare da ku,nazo naga the world talented nanny dinmu" murmushin sãahar ta sakeyi

"Ma sha Allah,to Allah ya amince sisternmu" matsowa fadeela tayi tana sake zayyano mata dame dame zata taho mata da shi. Saahar din zata matsa don ta basu guri nadeeya tace

"Don Allah karki tafi,yanzu kin fini iya ji da rigimammiyar 'yar nan,ki zauna kya tayani lissafa wadan nan kavan wasan da taketa fadi,ta dauka ni abbynta ce da zan mata tawagar kaya?" Ta fada tana dariya. Murmushi saahar ta saki,sai ta koma ta zauna,wayarta na hannunta ta hau watsapp tana duba kwantan sagonni;,lokaci lokaci takan daga kai ta kallesu cikin ban sha'awa da burgewa idan sukayi wani abun,duk sanda zata daga kan sai sun hada idanu da nadeeya,saidai su sakarwa juna murmushi.

******Washegari aka bude daya dakin da tun zuwan säahar din yana rufe,saboda me dakin wato nadeeya din bata nan. Dukka furniture din din ciki aka fidda,aka shirya sababbi,sannan aka maida mata kayanta ciki aka sake gyara dakin da kyau. Fadeela da suke tare da sãahar din ta kasa sukuni saboda murna,dole karatun ranar da ba'a yi ba kenan,sai ta barta.

*******Karfe hudu da rabi na ranar lahadin motar da take mallakin nadeeya ta shigo da ita katafaren farfajiyar gidan mahaifin nata.
Seatbelt dinta ta cire tana duban ilahirin harabar gidan,ita sam banda Dr jarma din yace lallai ta sauka a nan din,da sai ta gama kwanakinta a gida sannan zata zo gaidasu,sam zama a gidan koda na minti daya ne bai taba mata dadi ko kuma ya burgeta ba,bawai don bata samun kulawa ko wani abu na jin dadin rayuwa ba.

Oofar motar ta bude da kanta ba tare data jira tarin ma'aikatan dake yungurin mata hakan ba,fuskarta a sake,kasancewarta mutum itama me fara'a da haba haba da al'umma cikin kuma kulawa take amsa barka da dawowar da kowa keyi mata,bayan tafiyarta karatun data shekara hudu tana yinsa,wanda a shekara hudun sau biyu kacal tazo gida bisa tsarin yaa toufeeq da yace baison yawo,idan karatun zatayi tayi basai tazo musu gida ba

A haka ta gama gaisawa kaf dasu,sannan ta tuqe ga hajiya mansura dake tsaye tana faman doka mata murmushi

"Lale maraba da dawowar diyata cikin aminci"
ta furta tana yunqurin kamo nadeeya zuwa
jikinta. Kadan tadan zame tana murmushin
itama

"'Na sameku lafiya?"

"Wannan gaisuwar sai a ciki za'a yita,abbanku
yana toilet yana qarasawa shiryawa,muje cikin
tukunna" waiwayawa tayi tana bawa masu
aikin umarnin shigowa da jakankunanta

"A'ah,ai basai sun shigo dasu ba,zan wuce
gidan yaa toufeeq ne" fuska tadan bata

"Me zakiyi a can nadeeya?‚ga gidanku?"

"Fadeela nacan na jirana,zanfi jin dadin can
din" ta bata amsar tana takawa zuwa cikin
gidan rungume da wata jaka data sako kaya masu muhimmanci a mazaunin tsaraba wa mahaifinta. Baki galala da kallo hajiya mansura ta bita dashi, cikin ranta tana jin wani irin kishi yana kamata,a fakaice kamar anaso ne ayi wining a kanta,bayan tarin nasarorin da akaci a kanta,har yanzu wannan matar...
..wannan
mutum dayar ta gagara cimmata yadda ya kamata,tsakaninsu kar rasan kar ne, amma har yanzu qudurinta bai isa ga inda taso ya qarasa ba,MUTUM DAYA TAK! Ita ta samu dukka wasu damarmaki da taso ace ita ta samesu,duk da tayi musu nisan zangon da suke da imanin kasantuwarta a cikinsu abune mai wahalar yiwuwa,wannan ya rage garfi da kaifin wasu damarmakin nata ainun WACECE?!

AMSARKU TANA GABA_.

Juya cokali kawai takeyi cikin abincin da hajiya mansura ta gabatar mata,tana kuma amsa tambayoyin dr jarma. Gaba daya hankalinta bai waien, Allah Allah kawai takevi a tashi daga zaman cin abincin da akace an shirya da sunanta don tayata murnar dawowa,cikin ranta tana fata da addu'ar kada Allah yasa dr din yace ta zauna tare da su.

Yana tsame hannunsa itama ta tsame nata tana gogewa da tissue,haiiya mansura ta kalli plate din nata

"Ya haka kuma?,banga kinci komai ba"

"alhamdulillah ‚naci abinci a jirgi"

"Abincin jirgi wani abinci ne? ki zauna ki garasa ci, yanzu zan yiwa su taiba magana su sake gyara miki dakinki" tana gama maganar nadeeya na miqewa,ta goya jakarta tana duban dr jarma

"Abba zan wuce gidan yaa toufeeq,fadeela tun ina hanya tasa ake kirana"

"Alright,ki mintsinemin kumatunta ja'ira,tunda tayi sabuwar nanny ta rabu da zuwarmin, kullum kuma nayi kiranta cikin bani labarinta take,ki gaya mata nayi mata garin salary akan abinda ake biyanta,ina mata godiya da kyau da kyau,don da alama tasan aikinta sosai" murmushi nadeeya tayi,tana jin dadin yadda Dr bai hanata tafiya ba,sanann kuma ita kanta tana jin sãahar har ranta,duk da basu dade da sanin juna ba,amma tana jin tamkar ta dade da saninta.

Sai da taga sun dau hanyar barin gidan ta sauke ajiyar zuciya,koda ta yiwa dr alqawarin zasu zo suyi kwanaki da fadeelan,batajin zata iya wuce kwana daya ko biyu.

Guri hajiya mansura ta samu ta zauna bayan fitar nadeeya

"'Dr inason magana da kai" kansa ya cire daga wayarsa da yake dannawa,daya hannun nasa kuma yana sakace da toothpick

"Nikam nace ba,bai kamata ace kana raye ba amma dukka yaran da Allah ya baka basa rayuwa tare da kai,ka tattarasu ka barsu a wani guri na daban,ni kaina da nake matsayin uwa a waiensu sam babu wata shaquwa a tsakaninmu" a nutse ya ajjiye tsinken sakacen yana dubanta

"Tohhhh...

...yau kuma wajen qarama dinne
ya koma wani guri na daban?,kin manta suna rayuwa ne garqashin gidan da toufeeg ya gina da kansa? nadeeya da ita tafi sabawa,a hannunta ta garasa girmanta, taoufeeq dinma kusan hakane,sannan shi namiji ne wanda banda gaddara da a yanzun yana qarqashin kulawar matarsa ne,so a ciki bansan meye matsalarki ba" ya qarashe maganar yana kafeta da idanu.

Ajiyar zuciya ta sauke,dama tayi zaton hakan daga gurinsa,yadda qarama ta tattare yaran gaba daya ta maidasu qarqashin mulkinta ita kadai yana mugun ci mata tuwo a qwarya,wanann dalilin ya sanya ta tattara labiba ta miga mata ko hakan zai sanya a samu wani sauyi,amma dai jiya i yau babu wani abu da ya canza

"Shikenan" abinda ta fada kenam cikin suyar zuciya ta miqe tana tattare gurin,zuciyarta kamar zata fito ta qirjinta. Binta shi kuma yaci gaba dayi da kallo,yana mamakin yadda har zata iya gaya masa wannan maganar akan qarama,ko ta mance cewa ta silarta ta sanshi?,ta silarta ta zama abinda take a yanzu take kuma amsa sunan da take amsawa na matarsa.

Dukka wannan shi ba damuwarsa bane,abu daya ya sani,duk abinda zai takura yaran ya sakasu cikin qunci zuciyarsa ko qangani bata so,muddin dai wannan abun bai kaucewa hanyar addini da al'ada ba,can qasan rai da zuciyarsa yasha kasa runtsawa cikin dare,he have feeling of guilt akan TOUFEEQ da NADEEYA,saidai har yanzu kwanyarsa ta kasa gaya masa meye ainihin tagamaimen laifin?,idan ya matsa da bincikar kansa kuma sai matsanancin ciwon kai ya saukar masa.

_uhmmmmm hmmmmm_

Turus ta tsaya cikin mamakin ganin cewa ba wani mummunan abu bane ya sameta sanadiyyar ihunta data jiyo tun daga toilet din dakinta. Suna rungume da juna ne ita da nadeeya kamar wadanda suka bace tsahon shekaru sal yau suke ganin junansu.
Nadeeyan ta daga fadeela tayi juyi tayi juyi da ita har babu adadi sai kawai sãahar din ta saki murmushi ta juya ta koma ta garasa abinda takeyi,saboda taga basa ganin kowa sai kansu,masu aikin gidan nata wucewa da kayan nadeeya din zuwa cikin dakinta

"Ya zaki tafi?,ki tsaya mana mu gaisa" muryar
nadeeya ta ratsa kunnensa sãahar dake
yunqurin komawa ciki. Waiwayowa tayi tana
murmushi

"Ai naga baku gama ba" ta fadi tana duban
nadeeva da take sake ganin wasu kamanni
saman fuskarta,tana ji a jikinta kamar ta santa
a wani guri daban kafin wannan lokacin.
Karamar dariya nadeeya ta saki tana
takowa zuwa inda säahar ke tsaye

"Indai nida ukhtie ne wallahi bakiga komai ba"
saita buda hannuwanta tayi hugging säahar
kadan tana murmushi yadda larabawa ke
marabtar 'yan uwansu

"'Fatan na sameku lafiya" ta fada tana janye
jikinta,fuskarta cike da fara'a

"Alhamdulillah"

"Tambaya ta farko,don Allah me uktie takeci ta fara kumatu?" Dariyar da sãahar bata shirya ba ta subuce mata,yadda nadeeya tayi tambayar tana riqe habarta da yatsarta,da alama da gaske abun yana bata mamaki,ko ba'a gayawa sãahar ba alamu sun nuna mata nadeeya mutum ce me barkwanci da faran faran da yawan surutu

"Ki nutsu ki huta,zaki ganewa idanunki" baaba ramatu ta bayar da amsar tana dariya

"En lallai to nima ko dole aci dani, bari na garasa" nadeeya ta fada tana daukar garamar suitcase din data rigo suka wuce ciki tare,saahar ta koma kitchen,fadeela tabi bayan nadeeya.

66

*HUGUMA*

* TABARMAR KASHI_*

DON MARTABAR MANZAN ALLAH ME
FITARWA KIYI HAKURI KIBAR MANA
KAYANMU

To kusan yinin ranar fadeela na tare da nadeeya,har sai da sãahar tayi mata dan biki

"An samu sister nadeeya an manta da ni ko?"
Dariya tayi,ta taho da gudu ta rungume sãahar din ta baya tana fadin

"A'an Aunty,sorry".

Duk da säahar din na dan basu guri tana Kame kanta a dakinta,amma duk da haka nadeeyan bata qyaleta ba,komai saita sanyota a ciki,kota biyota dakin ta fiddota,da dare ma sai gata da dalleliyar kaftan abaya ta mata me kyau da sulbi 'yar saudiyya

"Ga tsarabarki aunty nanny" sosai kyautar ta burgeta,ta kuma yaba tare da yi mata godiya.
Chapter 74 · 0% Book details