← Book details Tabarmar Kashi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 104 OF 171

Sashe 104

Tabarmar Kashi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Ki sameni gida yanzu" abinda ya fada kenan ya gintse kiran. A hankali ya koma saman hannun kujera ya zauna,har yanzu yana jin zuciyarsa na masa quna,ya daga hannunsa ya kalli tsadajjen agogon dake maqale a lafiyayyar fatarsa. Yana da schedules da yawa yau dinma,akwai baqin da yasa aka ajjiye a tahir guest palace amma cikin jikinsa yakejin kamar bazai samu zuwa ba. Kamar kuwa jibril yasan abinda yake saqawa sai ga shigowar kiransa,ya kalli wayar da kyawawan fararen qwayoyin idanunsa,sai ya daga wayar ya saka a kunnensa

"Sir,i think kamar ka manta,we have an important with the guest who is staying at the guest house,sunce morning flight zasu bi gobe,seven pm dot,They asked me to tell you, if you don't mind, the conversation should be over tonight" kai ya gyada

"Alright,kazo ka daukeni after one hour,banason rakiyar kowa"

"Yes sir" jibril ya amsa masa cikin girmamawa. Yana sauke wayar dr raheema na shigowa. Kai tsaye yayi mata nuni da hallway na dakunansu. Nauyi taji sosai,saboda bata taba yin nan gefan ba hasalima part din nasa yaune karon farko data fara shigowa,so sai abun yayi mata kwarjini da yawa.

"Don't mind,ki shiga tana ciki" ya furta calmly

"Okay madam ce?" Tayi tambayar tana murmushi,kai ya gyada mata,sai ta gyara box din kayan aikinta tana cewa

"It's better to let her know first sir kafin na shiga" kansa ya daga a hankali yana duban hanyar,ya yadda da idea dinta,don haka ya miqe a nutse yana maida wayarsa aljihu ya nufi hanyar.

Tana jingine da fuskar gadon idanunta a lumshe,zara zaran gashin idonta sun yiwa idanun nata rumfa da kyau,sau daya ta bude ido ta kalleshi ta mayar ta kulle,ya qarasa kanta ya tsaya yana dauke dubansa daga kanta

"Ki shirya ga dr nan zata shigo,ki gaya mata matsalarki,i don't want rudeness" ya qarasa maganar yana turawa Dr raheema gajeran tex akan ta shigo. Bude idanun nata ta sakeyi a hankali ta sauke a kansa,me ruwansa da rashin lafiyarya da zai kira mata likita,saboda tsabar girman kai da izza kuma yazo yana kafa mata dokoki kaman ita ta buqaci ganin likitan?.

Tare da nadeeya sukayo sallama da fadeela duka a tare.

"Oh sannu anty N" nadeeya ta fada cikin nutsuwa,tana gudun kada tayi misbehaving yanzu a sendata waje. Qaramin murmushin data fusgo da qyar ta sakewa nadeeya tana gyada kai,ta miqa hannu a hankali ta sanya hannun fadeela da duk take a dame cikin nata,ta tabbatar lokacin dawowarsu baiyi ba,tayi yaqinin fadeela ce taqi sakewa,ta gayawa nadeeya ita kuma ta tattarota suka dawo.

"Sunnu madam" Dr raheema ta fada cikin murmushi tana sake yaba kyan da sãahar din ke dashi

"Dama MT JARMA din sai mata irinku" ta fada a ranta tana murmushin gulmarsu da tayi.

"Yanzu ukhtie fadeela ta yaya za'a duba maman naki ehnn?" Dr raheema ta fada tana murmushi ganin yadda ta kafa ta tsare ta nannade hannun sãahar da kyau

"Karkiyi mata allura please dr" ta fada a shagwabe,dariya tadan saki

"Ah.....wai da allurar zanyi mata fa,kika sani ko qani maman naki zata baki ko bakiso?" Wani tsalle tayi hadi da sakin hannun sãahar da maganar Dr din ta sanyata kasa bude ido. Tuni fadeela ta maqale toufeeq tana dariya

"Da gaske daddy?,wai nima anty N zata haifo min qani?,daddy nima na daina wasa da teddy sai da qanina?" Gaba daya nauyi ya saukar masa,yasan halin Dr raheema ba wai tun yau ba,tana da mugun barkwanci da kuma kirki,amma haka kawai saita hada masa gwarama,ta qala masa abinda bai taba attempting aikatawa ba harda su wani ciki?

"Fadeeeeela" toufeeq yayi kiranta ganin ta dauki abun serious. Yadda yayi kiran nata ya sanya ta nutsu tana dubansa

"Ki nutsu za'a duba mara lafiya. Nadeeya come and take her,ku zauna a waje ku jira" ya fada yana wani basarwa saboda kallon da yaga nadeeyan tana masa,haka kawai zata janyo yara su rainashi,yadda yaga nadeeyan tana kallonsa itama tayi believing ne da abinda Dr raheema ta fada bisa alama.

"Kodai anyi abunne?" Ta fada qasa qasa tana duban idanun sãahar bayan ficewarsu nadeeya

"Da wa?" Sãahar din ta fada kai tsaye tana duban dr raheema din,don ko dazun da tayi zancan ciki bacin rai kawai ta dasa mata. Tambayar sai ta saka Dr raheema murmushi,tana zaton kunya kawai sãahar din takeji. Ga toufeeq kuwa ya fahimci sarai ma'anar amsar data bawa dr raheema din sai yayi folding hannayensa a qirjinsa yana duban fuskarta,zarginsa ya saje tabbata sanda ta juya kadan ta jefa masa wani kallo

"Ba maza ai a gidan" ta fada qasa qasa hankali kwance bayan ta dauke kai daga dubansa ta maida idonta ta lumshe. Dr raheema batace komai ba,ta bawa ranta zafin zazzabin daya fara hawa mata ne.

A nutse ta gama dubata,sai ta fidda PT strip

"Ko zaki kawomin fitzarinki zanyi pregnancy test,saboda nasan magungunan da zan rubuta miki" kai tadan juya kadan

"Ki rubuta maganin directly kawai" murmushi ta sakeyi mata kamar yadda yake nuna al'adarta ne hakan

"Sorry madam,indai matar aure ne dole tayi gwajin kafin karbar magani saboda gudun matsala ga qaramin cikin da ba'a san dashi ba" siriryar iskar ta furzar daga bakinta,itakam ta gaji da zancan cikin nan da taketa jawo mata shi d baki a gaban wannan dan izzar wanda ko a yanzun yana tsaye qyam kamar tsohon soja yana danne danne a wayarsa,sai ka rantse da Allah babu shi a dakin kwata kwata,ko kuma baisan abinda yake faruwa ba

"Am on my period " ta fada qasa qasa cikin jin takaicin tona asirin kanta da tayi da bakinta. Duk yadd tayi qasan da muryarta sai da yaji din, sauke wayarsa yayi saboda shigowar kiran jibril

"Zan fita yanzu,thanks dr,zan saka elyas yayi magana dake"

"Thank you sir,Allah ya bata lafiya"

"Ameen" ya amsa sannan ya maida dubansa gareta

"Take care" ya furta softly wanda sãahar ta tabbatar na ganin ido ne,bai tsaya jiran respond nata ba ya juya cikin nutsuwar nan tasa yana ficewa a dakin.

*H U G U M A*

*_TABARMAR ƘASHI_*💔
Book 02
Page 21

Ta kusa mintuna talatin tsaye a bakin window dinta tana jiran feedback na abinda ta shirya,first plan dinta kenan. A gaggauce ta sauke labulen tana amsa sallamar masura me aikinta data aika ta sanya mata ido akan abinda zai biyo baya. Shuru tayi har masura ta gama labarta mata,taja wani numfashi me tsaho ta fesar da me zafi

"A taqaice kinason kice ba wani rashin jituwa daya gilma a tsakani?" Kai ta gyada

"Dukka ma suna sassan nasa,harda Dr raheema,kamar ma batajin dadi ne"

"Tashi kije" ta bawa masura umarni,sai ta miqe tsam ta fice. Hannunta ta dunqule tana dan dukan daya tafin hannun nata dashi. Tayi missing target dinta,a gobe meenal zata sauka a gidan kuma tun a yau taso ta haifar da gagarumin rikici gami da rashin fahimta a tsakaninsu,to amma ya akayi ta kuskure?. A mganganun data gaya masa game da yarinyar tayi zaton har sai ta shiga maganar wajen sasantasu.

Mamakinta da daurewar kanta ya sake qaruwa lokacin da taji tashin motarsa,ta sauke labulen nata ta koma ta zauna saman sofa din dake falon. Tayi nisa a tunani har bataji lokacin da me aikinta ke gaya mata ta gama gyaran dakin meenal ba har sai data maimaita

"Good,ki wuce sashen su nadeeya,cikin dakunansu ki sake gyara mata daya a can"

"Okay hajiya" ta amsa mata a ladabce tana fita. Tayi hakanne saboda ta samar da kusanci na mussamman tsakanin meenal nadeeya da kuma fadeela data tabbatar itace ruhin toufeeq.

Qarfe sha biyu saura na dare ya samu dawowa,sanda ya shigo falon babu kowa,har qwayayen lantarki duka a kashe sai masu qarancin haske da aka bari kada duhun yayi yawa. Dining ya duba,kusan a yanzu bazai iya cin komai ba,amma kuma yunwa yakeji,dole ya zauna ya tsakura abubuwan da basu cika nauyi ba,su dinma baici da yawa ba ya ture,inda zai samu wannan hadin coffee din da yafi kowa murna,zuwa yanzu ya fara fita a kansa,saboda yasan idan ma ya hada baya masa dadi kamar nata,abun ya zame masa kamar jarrabi.

Cike da gajiya data qarawa tafiyarsa nutsuwa yazo zai wuce,idonsa ya sauka akan qofar dakin nata. Tunda ya tafi meeting din hankalinsa ke a rabe gida biyu wanda shi kansa baisan ainihin dalilin hakan ba. Har ya gota sai kuma ya dawo,ko ba komai haqqinta ne a kansa ya kula da lafiyarta kamar yadda take qoqarin kula masa da lafiyar diyarsa.

Haske ne sosai a dakin,da alama bacci ya dauketa ne ba tare data shiryawa hakan ba,don fadeela na kife ne saman cikinta,hannuwanta zagaye da bayan fadeelan. Gabansu ya qarasa ya tsaya sosai yana kallonsu,suna rungume da juna tamkar uwa da 'ya. A hankali ya zame ya durqusa daga gaban gadon inda suke kwancen,idanunsa saman fuskarta da take looking innocent cikin bacci,bayan a idanu biyu cikakkiyar matsiwaciya ce,sassanyan kyan nan nata da babu abinda ke sanyawa ya gushe shinfide akan fuskar tata. Da sauri ya dauke idanun nasa daga kanta ganin yadda suka fara yawo saman pink lips dinta,kwanyarsa nason tuna masa abinda yaji a wancan lokacin da ya nada lips din nata da nashi. Har zai miqe yaji alamun fitar numfashinta kamar ba dai dai ba,alamu suke nuna fadeela kenan tayi mata nauyi,sai ya zare duvet din data lullubesu dashi,ya soma zare fadeelan daga jikinta.
Chapter 104 · 0% Book details