← Book details Tabarmar Kashi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 101 OF 171

Sashe 101

Tabarmar Kashi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Waye yace ka dinga shiga gonata?,ba haka mukayi da kai ba,munyi da kai kowa zaiyi rayuwarsa ne ba yare da ya shiga rayuwar dan uwansa ba..
tunda nazo kagan na.
bata ida garasawa ba saboda wata muguwar ba zata da yayi mata,dumu dumu ta tsinci harshensa cikin tsakiyar bakinta wanda shine ya toshe sauran maganganun da tayi niyyar gaggaya masa. Wani irin zuqa yakewa bakin nata yana hadawa sa lips dinta cikin wani irin salo da zata iya cewa ta mugunta ce kawai.
Cikin sakanni gaba daya kwanyarta ta birkice da tsananin tsoro gami da firgicin abinda yake faruwa din. Kaf rayuwarta babu mutumin data taba hada baki dashi irin haka baki cikin baki,gefe guda kuma yadda labbanta suka dauki radadi ta gama saddaqarwa sun tsage ne kawai. Duk yadda take tunanin zata iya tureshi ta kasa,sai kawai hawayen da suka tarar mata suka budewa kansu da kansu hanya suka fara sauka,danshinsu ya gangaro zuwa kumatunta ya fara taba skin na fuskarsa.

A hankali yaja da baya qafafunsa na wani irin sanyi da laushi,ya kalleta lokacin da take dugewa a waien tana cusa kanta tsakanin gafafunta tana sakin kuka a hankali don kada ta tashi fadeela dake baccinta batasan ma wainar da ake toyawa ba, yatsuntsa biyu saman lips din nata da ko da bata kallesu ba tasan sun tasa sosai

"Idan wancan karon na takeki wannan karon bakin tsiwar zan cinye gaba daya,kuma bani zan hadiye ba karnuka zan sa a kaiwa,as from today karki sake cewa zaki sakamin wata doka taki,nine gaba dake so nine me sanya kowacce doka nayi niyya,ko zaman dadiro nake da mace bata isa ta kafamin doka ba bare sadakina na biya,ki aje a ranki bazan taba neman komai daga gurinki ba idan ma shi kikewa,don nafi qarfinsa,ko yanzun bakina da kika lasa saikin biya hakan" daga wannan ya juya a hankali ya fita a dakin.

"HUGUMA*

* TABARMAR KASHI_*

Book 02 Page 18

Hawaye sosai takeyi tana shafa labban nata da suke mata zugi, anya ba baki afifa tayi mata ba? ‚idan ba haka ba me yasa yake mata kwarjini har haka?
"Martabar aure" amsar da zucivarta ta sake nanata mata kenan kamar yadda afifa ta gaya mata. Motsin fadee ne ya sanyata saurin share fuskarta da daidaita kanta. Ai tana hada idanu da sãahar din ta wantsalo gaba daya daga saman gadon ta qanqameta tana kiran

"Anty N,good morning" rungumeta itama tayi sosai cikin jikinta,a hankali takejin wani farinciki, bacin ran dake lullube a zuciyarta ya dinga zagwanyewa. Sun jima a haka sannan ta dagata tana kallonta

"Chubby fadeela ina wanka?" Kai ta langabe a shagwabe

"Sai kinzo ke zakiyimin" dariya tadan saki

"Kin fara girma fa,muje na gani" sai ta riqe hannunta suka wuce toilet din.

Sanda suka fito tana tsane mata jikinta aka tura gofar aka shigo. Baaba ramatu ce suna hada ido da sãahar ta tambayeta

"Ya akayi baaba" dab da ita ta iso, ta dan waiwaya ta kalli bakin gofa ta tabbatar a rufe take sannan ta warware bakin zaninta, wata leda ta ciro tayi saurin migawa sahar,sai sãahar din tasa hannu ta karba tana jinjina kai

"Kome ya tafi dai dai, tun bayan tafiyarki wannan magungunan take sha, ina lissafawa a cikin wadancan ina cirewa ina zubarwa kamar vadda kika kwatanta min, amma an samu matsala daga dawowar hajiya" baaba ramatu ta fada fuskarta tana canzawa, tadan sharce gumi, sãahar ta zuba mata ido gabanta yana faduwa

"Matsalar me baaba?"

"Daga dawowar matar nan da kanta take sanya fadeela a gaba da magungunan nan,yau kwana biyu nata take bata tana sha,duk wata hanya da zanbi na kauda afkuwar hakan wallahi nayi amma baiyuwu ba" baaba ramatu ta fada hawaye yana cika mata ido, tana jin bacin rai har cikin ranta na vadda tsahon shekaru tana zaune ana wasu abubuwan amma rashin ilimin zamani yasa bata fahimta. Sosai säahar taji hankalinta yayi mugun tashi,ta dinga jinjina kai tana jin tsohon bacin ranta yana motsawa, a lokacin ta'addancin da adam yayi mata sa qwayoyin magani ne suka dinga dawo mata, ba zata bari ba kuwa haka ya faru tare da innocent fadeela ba

"Zan yiwa tufkar hanci" ta fada a sarari, cikin zuciyarta tana jin zatayi amfani da nata power din da take dashi a yanzu na matar uban fadeela, duk da bawai tana tutiya da wannan matsayin bane.

Kwanaki biyun da maji ta qara cikin gidan säahar gurinta take wuni, tun daga ranar basu kuma haduwa da toufeeq ba saidai a wajen maji,idan ya shigo din ba wani dogon zama yakeyi ba,sosai ta fuskanci abubuwa da yawa,kamar rashin sabo da sakewa tsakaninsa da maji din,duk majin tana bakin qoqarin gain ta jashi a jikinta amma wasu abubuwan basu yiwuwa. Gurinsu maji take yini tare da fadee dinta ga nadeeya,rana ta uku majin ta gama shirin tafiyarta,a safiyar da zasu wuce
airport, dukkansu suna gaban motar da zasu wuce da
rakiyar nadeeya fadeela da toufeeq.

Su libril ke shirya komai,toufeeq din yana sassansa
bai kammala fitowa ba,suna tsaye dukkansu gaban
motar cikin alhinin tafiyar maji,ji sukeyi kamar su hanata
tafiyar, säahar a cikin jiki da zuciyarta takejin babu dadi
qwarai. Hannun säahar maii ta kamo tana murmushi

"Karki damu d'iyata,bazan dauki dogon lokaci ba zan
dawo, dawowar da nake kyautata zaton zan jima ban
koma Algeria ba,akwai kasuwancin da na fara
processing nasa a nan, bana tunanin zan wuce wata uku
ko biyu ma ban dawo ba" wannan albishir din shi yafi
komai faranta ran säahar, ta rige hannun maji sosai tana
murmushi dai dai lokacin da yake takowa zuwa gurin.
Sanye yake da wani baby cashmere da aka yiwa
lafiyayyen dinki wanda yabi jikinsa ya dace da
yanayinsa, ya kuma fitar da structure dinsa sosai yau din
ya saka hula saman kanshi, abinda sãahar din bata taba
gani ba kenan,hakan sai ya sake canza fuskanshi,ya fito
a cikakken shuwa dinsa ya tashi daga launin larabawan
Algeria. Ido suka hada,sai ta janye daga kallonsa tana
hade rai,can gasan ransa ya murmusa a karon farko
bayan da ya karanci wani abu saman fuskarta. Ta kalleshi
ne ba tare da kowa ya tilasta mata ba,amma kuma bayan ya ganta tana kallon nasa sai ranta ya baci tana tuhumar
kanta da kanta. Yau kwana biyu cur bai ganta ba,baisan
a wanne bigire zai sakata ba, amma tuni ya fara karantar
wasu halayen nata,bayan tsiwar da ya samu ya rage mata run randa ya yuwa labbanta wawan kamu,ya fahimci tana kafiya taurin kai da tsaiwa akan ra'ayinta.
Zarmewa idanunsa sukayi da kallon labbanta,sun koma normal,wasu irin soft and tiny lips, masu wani irin pinky color me dan duhu. Idonsa yayi hanzarin daukewa yana lumshe idanunsa tare da budewa duka lokaci guda cikin kaucewa gamuwar idanunsu, kada taga yana kallonta ta rainashi.

Isowarsa gurin ya dawo da hankalin maji kansa,ta saki garamin murmushi lokacin da yake duqawa har qasa saman gafafunsa yana gaidata,abinda ya sanyawa guard dinsa saurin juyawa suka basu baya. Ido itama sãahar ta dauke tana jin wani abu yana ratsa zuciyarta,karon farko da bataji feeling na rashin burgeta ba tattare dashi.

Dabi'arsa guda daya da zata iya zanawa tace me kyau ce,daga kan maji har dr jarma ba zatace ga lokacin da taga ya gaidasu a tsaye ba. Fadeela ce ta matso tayl kissing kumatunsa dake da wani kwantacciyar qasumba me laushi wadda bata cika yawa ba,tana ta fitar d qamshin hair mist da kuma qyallin mayukan da tasha gyara dasu,sai ta zame ta tsugunna tana gaidashi kamar yadda taga ya yiwa maji,dama kusan tun bayan zuwan sãahar gidan ta dorata akan hakan

"Barka da asuba abby" ta fada da salon da sahar din keyin gaisuwa, murmushi ya saja yana dan jan kumatunta

"Barka da asuba abby, a ina kika canza yadda aje gaisuwa?" Tana dariya ta kalli sahar da sam tagi tsaida idanunta a sashen

"Aunty N ce, haka take gaida mutane" basarwa yayi kamar bashi ya tambayu fadeela ba. Hannunsa maii ta kama ta migar dashi, tasa daya hannun ta kamo hannun sãahar,rigota din da tayi shine ya sanyata waiwayowa tana duban maji din. Hade hannayen nasu tayi guri daya,lallausan tafin hannunsa ya sauka cikin nata tafin hannun me wani irin taushi da dumi. A take tsigar jikinsa ta zuba wani irin dumin hannun yana ratsa jikinsa da wani gudu kamar gudun jini a kowanne sashe na jiki.

Itama motsa hannun nata tayi saidai ba damar ta janye saboda maji ta lullube nata hannayen da nasu tana duban idanun kowannensu

"Na baki amanar d'ana da jilkata na baki amana" sai ta waiwaya ga toufeed

"Na baka amanar diyata, ka kula da ita ka kula da mutuncinta, ka tsare mata dukka
buqatunta,mutuncinta naka ne, amanar Allah ce a wajenka daga gurin iyayenta kamar yadda abbanka ya gaya maka". Dukkansu babu wanda baiji ta dora masa wani nauyi ba,ba wanda jikinsa baiyi sanyi ba a cikinsu. Karo na biyu hannuwansu suka sake gamuwa wajen qoqarin da kowa keyi tsakanin shi da ita na budewa maji qofar mota, sahar dince ta fara janye hannu kamar wadda wuta ta jata, tayi gefe da hannun tana yarfarwa,ya ganta amma sai yayi kamar bai ganta ba,saida maji ta shiga ya sakewa nadeeva gofar suka shiga ita da fadeela. Da hannu ya yiwa elyas magana, sai gashi ya matso da sauri ya bashi key din motar,ya shiga seat din driver duk sai sukaja baya,don haka yana nuna musu da kansa zai tuga mamarsa
kenan.

"Yayi wuri ki fara fita diyata,da sai nace kema ki shigo." maji ta fada tana murmushi, cikin alkunya sãahar tayi qasa da kanta taja baya tana daga musu hannu sanda motar ta fara fita a gidan.

Ana kammala rufe makeken gate din gidan ta juya cikin jin kewa,muryar daya daga cikin masu aikin gidan taji a bayanta

"Madam hajiya garama tana kira" da mamaki ta waiwayo tana kallonta,mamakin kiran da take mata na meye? batajin zata iya taka sassan matar bare ta saurareta,gaba daya babu wata daraja tata data rage mata yanzun a idanunta sai 'yar kadan, ita dinma ta dosaneta ne a dalilin martabar dr jarma

"Kice mata zan shigo" kawai iya abinda ta fadi kenan ta wuce sassan su fadeela tana juya kiran a ranta.
Chapter 101 · 0% Book details