← Book details Tabarmar Kashi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 122 OF 171

Sashe 122

Tabarmar Kashi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kwana biyu,kwana biyu ko?"' Ya fada qasa qasa, tasan me yakeson fadi ,yanason sakayawa ne saboda meenal dake cikin motar. Da sauri sukaji an bude murfin motar kuma a wani irin fusace,bata iya tsaiwa ba ta kwasa tayi cikin gidan da mugun gudu, abinda ya yanke tsaiwar hajiya qarama a gurin,tabi bayan meenal din cikin sassarfa.

Tashi yayi ya koma mazaunin driver yana sakin murmushi
"Ko kishin kanki baki dashi? a gaban idonki na bawa wata lift?" Ya fada with softness yana shirin kunna motar
"Kishi? god forbid" kadan ya waiwaya ya kalleta, kaman zaiyi magana sai ya fasa murmushi ya sake kubce masa
"Alright,zamu gani, amma dai yanzun ai na taimakeki da korar miki ita,ko banza kya shaqi numfashi me kyau" kasa amsa masa tayi saboda gaba daya ya yamutsa ta a fakaice,kuma batason taci gaba da amsa masa fadeela ta fahimci wani abun. Kawai dai abu daya ya bata mamaki driving da yakeyi yau da kansa abinda bata taba gani ba, sai daya fita sauran motocin suka taso suka rufa musu baya,biyun kuma sukayi gaban tasu.
A yau din bayan sun isa company,su biyu kadai suka wuce zuwa ciki. Dukka ma'aikatan kowa goqarin gaidashi yakeyi cikin girmamawa,abinda yadan basu mamaki shine yadda yake amsa gaisuwar tasu a yau kadan kadan, musamman ma'aikata mazan. Hatta cikin elevator su kadai ta dauka har zuwa building dinsu. Baya yaja yana kallonta,fa fahimci abinda yake nufi tayi gaba kenan, dauke kai tayi gami da noqewa kamar bata fahimci abinda yake nufi ba. A nutse ya tako ya garaso kusa da ita,ya sanya hannunsa ya rigo nata hannun yana hade tafukan hannayensu guri daya. Cikin sauri ta daga kanta ta kalleshi,ta kuma fara yunqurin zare hannunta daga nashi. Jifanta yayi da wani irin kallo sannan ya girgiza mata kansa alamun a'ah,bai sake saurararta ba ya jata a tausashe suka fita daga elevator din.
Kusan duk inda suka gifta sai idanun jama'a sun bisu da kallo,wani irin mugun matching sukayi a safiyar tare da wani sassanyan kyau dake cakude da annuri saman fuskar kowannensu. Wanna kallon da ya lura ana binsu da shi ya sake jagula masa lissafi,sau uku yana canza mata side,from left to right, from right to left.
Cikin kamalarsa yayi sallama cikin lobby na office din nasa, mazaunin saima kenan. Da kuxarinta ta dago tana amsawa, harda gyara zamanta, saidai kuma kafin takai ga garasa amsa sallamar komai ya magale mata a wuya,da qyar ta tattaro kalmomin
"Good morning sir"
"Morning" ya amsa mata yana wucewa kai tsaye ga office dinsa,har a lokacin kuma bai sake mata hannu ba "Sir,kowa kai yake jira,dukka suna hall din" saima tayi qarfin halin fada tana jin wani abu me daci saman harshenita. Sai a wanna karon ya waiwayo,kallo yayi mata irin wanda ya saba yiwa kowa, amma sai taji wani dadi a ranta,saboda takan jima bata samu wannan damar ba
"Monday ne dama?" Ya tambayeta cikin kokwanto. Sai data hado wani murmushi saman fuskarta sannan ta gyada masa kai tana lumshe idanu
"Yes sir" tana gama fada jibril yayi knocking ya nemi izini sannan ya shigo
"Sir, kowa yana jiranka"
"Okay" ya amsa yana gyada kai

"HUGUMA*

• TABARMAR KASHI*

Book 02 Page 36

A nutse da wani irin sanyi ya maida dubansa gareta,wani sashe daban take duba bashi ba. Har gasan ransa yaji bazai iya tafiya ya barta cikin office din ba, kamar bai gaji da kallonta ba
"Madam" ya kirayeta da wani irin amon sauti me laushi da sanyi. Tsigar jikinta tadan zuba saboda canzawar sautinsa a yau din, amma sai ta fuske kamar bata jishi ba.

Ya matsu ya Kalli qwayoyin idanunta,yanason yabar mata wani saqo me nauyi da narka zuciya,kamar yadda ya sani, sauran mata ma suka sani, idanunsa nada wani irin mugun tasiri da maganadisu me qarfi dake narka zuciyar mata da yawa,ya kuma tafi da tunaninsu. Uwa uba yana matuqar qaunar idanunta, tun a shekaran jiya daya qure musu dukkan kallo harda wanda ya wuce qa'ida ma idan akwai,kallon cikin idanunta na tuna masa yanayin da suka shiga gaba daya shi da ita a wancan ranar,yadda komai ya canza cikin lokaci qanqani. A ranar ya fara tabbatar da kyawun qwayar idanun nata.

Hannunta ya saki kawai sai ya rigo qugunta, sai gata
tsaye a gabansa suna fuskantar juna. Kanta kawai ta
sunkuyar ta hanashi kallon fuskarta bare akai ga idanunnata, abinda ya hanata kowanne yunquri na qwatar kan ta shine Karantar da tayi saima tana wajen

"Da mutane fa a gurin nan" ta fada qasa qasa wai don
kada saima din taji, saidai abinda bata sani ba,yadda tayi
cooling voice dinta ya sanya yaji tsigar jikinsa gaba daya
ta tashi,yadan ja wani numfashi hade da sheshsheqa

"| know, just i want to look into your eyes......please" jin
abinda ya fada ya sanyata maida idanun nata ta kulle
gam, tana nufin ba zata bashi wannan damar ba,har cikin zuciyarta abinda tayi niyya kenan, indai idanunta yakeson kalla zai bushe a wajen saima ce kawai ta zalunceta data ci gaba da zama a gurin, tana pretending kamar bata ganinsu,ita kuma tayi imanin dukka hankalinta yana kansu,banda ita da tuni ta tureshi daga riqetan da yayi.

Zanen fuskarta ya shiga kallo daki daki, tun daga
kyakkyawan eye brows dinta,miqaqqen hancinta mar
tsaho da tudu, shape din idanunta da kuma eye lashes
dinta masu tsaho ya dire zuwa kyawawan lips dinta da
suke yawna fuzgarsa,duk yadda yaso ya daure ya kasa

"Your lips look so lonely, would they like to meet mine?" Babu shiri ta bude fararen idanun nata tarr bisa fuskarsa da suka cika da tsoron kada ya aikata din. Qaramin murmushi ya subuce masa. Fuskarta ya kama ya hade fuskokinsu guri guda, abinda ya Sanya saima ba shiri cikin rawar hannu ta kwashe takardun da bata gama tabbatar da ingancinsu ba ta bude qofa ta fice

"Am dying to have my lips on yours one chance please!"

Duka garfinta ts tattaro ta turashi tana yin baya,numfashi take maidawa hadi da sanya hannunta daya tana gyara zaman hijabinta

"Why all these ne wai?, why?" Ta tambayeshi cikin zafin rai, zuciyarta na gaya mata shi kuma jikinta kadai yakeso, sha'awar ta kawai yakeyi, bashi da aiki sai burin son taba jikinta?.

Da baya da baya yaja ya jingina jikinsa da bango yana rufe idanunsa, tuni kowacce jijiya ta jikinsa ta amsa

"You stole my heart" ya fada can qasan
maqoshinsa,labbansa kadai sune suka motsa. Itadimma lallabawa tayi ta zauna zaman kujerun dake gurin, tsahon wasu mintuna shuru ba wanda yace da kowa komai,yayi ta maza yana qoqarin binne komai a ransa ya mige ya tsaya saman qafafunsa ya fara takawa

"Let's go" ya fada a taqaice, sai ya kasa ci gaba da tafiya sanda ya isa bakin qofa,ya tsaya har ta qaraso. Lalubar hannunta ya sakeyi ya hade da nasa,ta ja zata fincike yace

"'Kina cirewa ban yafe ba" laqwas taji zuciya ds gangar jikinta tavi, bata da wani sauran zabi sai ci gaba da binsa da tayi.

Kamar ya koma haka yaji lokacin da suka isa hall din, bai dauka zaman meeting din da mutane da yawa ba haka idanu sukayi caa a kansa shi da ita dukka suka mige suna masa barka da zuwa. Da ka ya amsa yana jin nutsuwarsa na raguwa. A nutse y jawo hannunta ya jawo kujerar da aka tanada saboda zaman CEO ya matso da ita gabanta,ya zaunar da ita a kai sannan ya koma bava ya tsaya yana dafe da kujerar, tamkar yaron gidan da uban gidan nasa.

A schedule na meeting din one hour ne meeting ne, amma cikin mintuna talatin ya sallamesu. Yadda suka shigo yanzunma haka suka koma office din yana riqe da hannunta,wannan shi ne ya zama muhimmin topic na tattaunawa a cikin company din a ranar.

Tunda suka dawo duk bavan minti dava zuwa biyu sai ya daga kai ya kalleta. A duk sanda ya kalletan kuwa sai wani abu mai qarfi ya fusgeshi tattare da ita. Wasu lokutan har sai ya tsaida abinda yakeyi ya zuba mata idanu yana kallonta cikin wani irin nutsuwa da wank lamari me matugar qarfi kaifi da kuma zurfi cikin zuciyarsa.
Bata fahimci komai ba, kawai ta fuskanci yau din yana ta sanyata zurga zurgar dauko wancan ajjiye wannan.
Yayi amfani gwarai da wannan damar wajen samun damar morewa kallonta ta yadda ranshi yakeso.

A karo na barkatai ya sanyata dauko masa wani book cikin tsararriyar book shelf dake gefen table dinsa,saidai akwai tazara tsakaninsa da ita. Sanda ta miqe don isa gurin sai ya daga kansa gami da ajiye biron dake hannunsa,a hankali yake sake qarewa tafiyarta kallo, komai nata unique ne, bai taba cin karo da mutum me uniqueness irin nata ba.

Ta maida hankalinta sosai tana duba masa littafin da
ya aiketa ta dauko din,ba kuma wai don zaiyi karatu bane,a'ah,kawai yanason yaga wannan kyakkyawan takun nata. Yadda take tura baki da bata rai saboda bataga book din ba ya sanyashi sakin murmushi yana jin wata gajiya da kasala suna bin sassan jikinsa,wanda shi kansa yasan ma'anar hakan a tattare dashi. Ya miqe a nutse yana sanya hannayensa a aljihun wandonsa, har ya isa gareta bata sani ba. Daga bayanta ta tsaya, dab da ita,tazarar data rage a tsakaninsu duka baifi taku daya rak ba.

Muryarsa ya sassauta sosai ya kuma rage tsahonsa yana son daidaita kanshi da ita ya dawo da kansa saitin kafadarta,cikin laushin murya tamkar wanda yake a buge yace

"Am so tired,can you give me a hug pleasssssse" cak ta dakata daga abinda takeyi tsigar jikinta tana tashi,yadda yayi maganar saitin kunnenta ta shigeta sosai,sam sam bata tsammaci tsaiwarsa a wajen ba,saita qame a tsayen, bata juyo ba bata kuma ci gaba da neman littafin ba. Ragowar taku dayan da ya rage shi ya qarasa, cikin sanyi da tashi ya zura hannuwansa ta saman cikinta.va kuma jawota a mugun slow ya manneta da jikinsa. Kamar wadda aka yiwa allura ta zabura tana juyowa da sauri da nufin kufcewa,saidai kuma babu damar kuncewar saboda yayi mata zobe gaba da hannunsa. Kai tsaye idanunsu suka jone guri daya,ya lumshe nasa idanun tare da budesu lokaci daya yana sakin wani lafiyayyen siririn murmushi da ya sanyata kasa jurewa kallonsa saboda wani tsalle da zuciyarta tayi ta kuma ce mata
Chapter 122 · 0% Book details