← Book details Tabarmar Kashi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 169 OF 171

Sashe 169

Tabarmar Kashi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Inason baby girl me irin fuskar nan sosai, yaushe zaki harama?" Sai taga kamar gatse yakeyi mata,don haka ta zame jikinta tana cewa

"Ni da haihuwa ba yanzu ba" sak yayi yana duban fuskarta sai kuma ya basar yaci gaba da qoqarin shirya kansa. Rashin tankawarsa sai zuciyarta ta
yunquro,shaidan ya dinga raya mata kamar akwai abinda ya taka shi yasa bai damu ba don tace haihuwa ba yanzu ba. Fita tayi tabar masa dakin, kafin ma yazo kwanciya ita ta gama shirya yara suna dakinsu tazo ta shirya itama tayi kwanciyarta.

Mutum ne shi bai matugar bawa dan adam uzuri qwarai da gaske don haka koda ya sameta a kwance sai shima ya shirya yabi bayanta.

Sanda va fara aike mata da sagonni sai ta tankwabe saqonsa,daga qarshe ma ta miqe tana sauka daga kan gadon, mafi munin abinda shi kuma yafi tsana kenan kaf rayuwarshi

"Mun zama second hand fa,a bari amarya tazo,gobe idan Allah ya kaimu zamu wuce gidan maji,sai kafijin dadin sakewarka da yin waya da soulmate din taka® shuru yayi ya zuba mata ido yana kallonta,duk maganganun da takeyi kuma taqi bari su hada idanu,sai kawai ya miqe ya dauki abinda zai dauka ya canza daki.

A daren ya dinga qoqarin cooling down kansa da kansa,har zuwa wayewar gari yana shirin fita sai gata, ta sake shaida masa zasu wuce fa gidan maji

"Ba da vawuna ba" abinda ya fadi mata kenan ya fice.
Yana office maji ta kirashi, ta kuma bashi umarnin ya dauko mata sãahar din da yara ya kawo mata su.
Bai tambayi ba'asi bai kuma musanta mata ba,ya katse duk abinda yakeyi ya koma gida ya daukosu kamar yadda maji ta fadi, saidai abinda ya fara daga mata hankali da taji yana waya,salon wayar da bata gamsu ba,saidai kuma bata gane da mace ne ko da namiji yake wayar ba.

"Zamu tafi" tace dashi tana dubansa sanda ya saukesun,jikinta yana danyin sanyi. Maganganun da ya gaya matan sune suka tsaya mata a rai matuqa

Ajiyar zuciya ta sauke tana jin ranta duka babu
dadi

"Astagfirullah" ta fada qasa qasa, tana hango rashin kyautatawar muraran. Knocking din baaba ramatu taji,sai ta bata izinin shigowa

"Sau uku ina kewayowa amma banji mitsinki ba,gashi dare yayi kuma ba'a dafa komai ba duk da tagwaye basa nan" dan murmushi ta saji,tana jin dadin kulawar da baaba ramatu ke basu

"Yanzu zan fito baaba, tare zamu sbiga kitchen din, a cire nama a freezer danye a zuba masa ruwan zafi"

"To shikenan, saikin fito" tace da ita. Gefan sofa ta koma ta zauna,ta jawo hula ta sakawa kanta,sannan ta miqe tsam tayi kitchen.

Duk da dare ya soma kawo kai, amma haka ta zage a nutse ta shirya masa dinner sassauqa amma ta musamman tare da taimakon baaba ramatu.

Har ta gama bataji shigowarsa ba, itama hakan
yayi mata dai dai, ta kammale komai ta barwa baba ramatu gyaran wajen.

Sai data gamsasa gidan da dukka nau'in turarukan da tasan yana so sannan ta wuce bedroom dinsa. Kintsashi shima tayi,bai wani hargitse ba duk da kwana biyu kenan Bata nan ta sanyayashi da turaren da ta tanadeshi ne kawai saboda bedroom dinsa sannan ta wuce nata dakin.

Kayan jikinta ta cire ta fada toilet, ta zuba man wanke gashi sosai ta wanke sumarta sannan tayi wanka ta fito.

Tanata sage sage tana gogarin busar da kanta a
gaban madubi tana kuma duba agogo, qarfe tara saura na dare, cikin ranta tana mamakin me ya tsayar dashi har kawo wannan lokacin bai qaraso gida ba.

Har ta ajiye Drayer din zata fara taje kanta taji an turo gofar da sauri lokaci guda ana kiran sunanta.

A nutse ta waiwaya,asad ne da as'ad sai kuma fadeela biye dasu. Kamar yadda suka saba, kowa rige rigen isowa gareta yakeyi, murmushi ya qwace mata tana dubansu. A rayuwarta kaf tanason wannan moment din,tana jin babu wata uwa data kaita a duniya.
Murmushin ta yayi dai dai da kallon bakin qofar dakin da tayi.

Zafafabiyar

"HUGUMA*

•TABARMAR KASHI_*

Book 02 Page 76

Yana tsaye bakin gofar dakin sanye da trouser da shirt charcoal color da yayi matuqar haska fatarsa.
Idanunsa a tsaye carr a kanta,yadda sumar kanta ta bazu a sassan fuskarta da farar lalalusar fatar jikinta sai ya zama kamar wani ado ne a gareta, fuskarta tayi fayau tayi kyau sosal.

Shi ya fara dauke idanunsa,ya juya a hankali da zummar barin gurin, zuciyarta sai ta karye

"Sannu da zuwa" ta fada da karyayyar muryarta,bai amsa ba yaci gaba da takawa yana barin wajen.

Sosai zuciyarta ta sake karyewa,banda yaran dake mararin ganinta ba zata iya ci gaba da tsaiwa bata bishi ba. Duk irin tsauri da zafin zuciyarsa zata iya cewa bata taba ganin fushi haka da I don't care manner haka a tattare dashi ba. A daddafe ta zauna ta biyewa shirmensu da hirarrakinsu,sannan ta samu ta tattarawa baaba ramatu sunata cewa

"Gobe zamu koma maii tace a hada mana kayanmu"

"Allah ya kaimu" tace da as'ad yafi kowa dokin komawar.

Cikin nutsuwa ta bude gaba daya closet dinta, idanunta akan kayanta daya bayan daya. Tsaida kallonta tayi akan was kaya,murmushi ya kubce mata, tana iya tuna ranar data sanya masa kayan, cak ya dagata sama ya juyata sosai,babu inda baiyi kissing a jikinta ba kafin labari ya sha banbam.

Tsaf ta shirya cikin kayan, ta tsaya sosai gaba madubi ta yiwa gashinta wani irin gyara me tafiya da hankali,sannan ta fesheshi da sassanyan hair mist.

Kayan abincin ta kwashe ta mayar sassansa, bata sameshi a falo ba, tayi imanin yana cikin toilet yana wanka,abinda bai taba faruwa a tsakaninsu ba kenan.
Kusan ko yaushe wankansu tare sukeyi,koda tayi nata wankan idan ya dawo sal ya batashi,wani irin mutum ne da tara vaara basa hanashi baje kolin soyayyarsa, baya tsufa da soyayva hakanan idanu basa hanashi nunawa matarsa qauna da kulawa. Ta godewa Allah da va bata maji a matsayin suruka,mace me fahimta wadda al'adarta tasha banban data bahaushe, tayi imanin banda hakan da tuni ta fara ganun canjin fuska saboda kukawa gauna da tattali da yake nuna mata. Tana da kawaici qwarai da gaske, a kullum bata gajiya da sake iadda masa girman amanarta dake wuyansa.

Kafin ya fito ta gama kai kawonta tsakanin sassanta da na yaran,ta tabbatar ta sallamesu, kiwa yayi shirin kwanciya dukbda weekend ne goben sannan ta wuce sashen nasa.

A nutse ta bude bedroom dinsa, har yanzu still yana toilet, saboda tana iya jin qarar saukar ruwa. Zare hijabin jikinta tayi ta aje saman sofa. Dakin takebi da kallo _r a nutse,ko na kwana daya ta masa daga dakin sai taji tayi kewarsa,tana mamakin vadda ameesha ta iva rabuwa da toufeeq,yana da shiga rai ya kuma hada dukkan wasu. qualities na miji na gari. Matsawa gaban dressing table dinsa tayi tana gyara turarukan da ya zube akai,gefe kuma qaramar jakar ce me kyau dauke da tambarin company din da yayi siyayyar. Daya daga cikin kwalaben ta daga, favourite turarenta ne, siyo mata yayi kenan?, ta tambayi kanta,duk da yana fushi da ita amma hakan bai sanya ya manta ko ya wofantar da duk abinda ya shafeta ba

"Shi din na musamman ne" zuciyarta ta gaya mata hakan
"Good men still exist one of them is mine" ta fada a fili hadi da lumshe idonta tana rungume turaren a qirjinta.
Baivi zaton ganinta ba sanda ya bude gofar amma maganar da ta furta gasa gada ta shiga kunnensa,can gasan zuciyarsa wani abu me sanyi ya saukar masa, baqin gashinta me qyalli idanunsa suka fara sauka a kai sannan a hankali suka sauka zuwa gadon bayanta da fiye da rabinsa yake a bude fara tas din fatarta ta dace da launin bagar rigar jikinta.

Ta cikin madubin take satar kallonsa,tsayyayen jikin dake gine da wasu muraddun muscles, tashin farko taji kewarsa ta cikata. Wani irin mutum ne shi mai
•r tsayawa a zuciya a kowacce tarayya zakayi dashi.

Cikin sa'a ya lura da satar kallonsa da takeyi ta gasan ido duk da ta fara fusgar hankalinsa amma sai ya dauke idanunsa daga kanta 'yan miskilancin suka motsa.

Qaramin towel ya saka yana goge ruwan sumarsa data jikinsa,sumar kansa mai santsi da laushi duk ta cakude,yaja stool ya zauna gaban dressing table din daura da ita har yanzun kuma bai dubi sashenta ba.

lya maqura haqurinta ya gaza,ta ajjiye kwalbar
turaren hannunta, ta taka a hankali ta zagaya bayansa.

Qaramin towel din hannun nasa ta rige da kyau,suka hada ido ta cikin madubin, saita dage masa dukka girarta biyun. Bugawa zuciyarsa ta danyi yana jin wani abu yana bin sassan jikinsa,ya lumshe kyawawan idanunsa yana sakar mata towel din salin alin, ita kuma ta zare towel din a hankali ta dorashi saman sumar tasa.

Cikin wani irin salo ta soma nutsa yatsun hannunta cikin sumar tasa,a hankali ta soma yamutsata cikin wani irin yanayi da ya tilasta masa rufe idanunsa ruf yana jin duk wani motsi na zara zaran yatsun nata har cikin kwanyarsa.

"i feel bad for making you sad am sorry for making you loose your temper, sorry for being rude and hurting you with my words,i promise not to repeat it ever" idanunsa 5° ya lumshe yana jin zagin kalamanta. Tana da baiwar iya kalami mai sanyaya zuciya da cire duk wani fushi da bacin rai duk da shi dama bawai har vanzun vana fushi da ita bane,a'ah,he want to teach her lesson.

Ci gaba tayi da yamusa gashin nasa tana kuma tayar da kowacce tsiga ta jikinsa. Ganin yayi shuru bai amsata ba sai ta dan bubbuga qafa a shagwabe

"Kace wani abu pleaaaaaaaassssseee.i can go to any extent to make it up to you,am sorry from the bottom of my heart,please better half..... forgive me manaaaa,)
miss your sweet voice, your hug and your smile,sorry for hurting you" still har yanzu ya kasa bude idanunsa,duk da zuciyarsa kamar zata fito daga qirjinsa yakeji wani wata irin soyayya me motsa zukata,tare da tsananin shauginta da yakeji, muryarta kadai na neman rikitashi. A nutse ya bude idanun nasa ya watsasu a kanta
Chapter 169 · 0% Book details