← Book details Tabarmar Kashi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 171

Sashe 20

Tabarmar Kashi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Koma ka zauna,ku qarasa kada lokacin tashi yayi" yadda yayi masa sallama haka itama sãahar,cikin girmamawa da ganin kimarsa,ya juya ya fita a office din,yana jin farinciki har cikin zuciyarsa.

Shuru ne ya ratsa office din tamkar babu sauran wani me rai,shi din yana daga saman kujerarsa,yayin daya dora sambala sambalan qafafunsa akan leg rest na jikin kujerar,yana kuma sarrafa computer dinsa cikin qwarewa da hannu daya. Ko sau daya bai dago kai ko yayi wani motsi da zai nuna yasan da mutum cikin office din ba,dai dai lokacin da sãahar ke zaune don cika umarnin dattijon,wayarta itama take sarrafawa,lokaci lokaci tana duba agogon hannunta,tana jiran kuma lokacin data dibawa kanta ya cika tabar masa office dinsa.

Kowanne a cikinsu jin kansa ya hanashi ya fara tankawa dan uwansa,cikin zuciyar sãahar tsanarsa da haushinsa ne fal suka danqare mata,ba tun yau ba tasan baisan darajar diya mace ba,bai martaba kimarta sam,a nasa sashen kuma ji yake sam batayi masa ba,tunda suke da Dr bai taba ganin mutumin daya jawo jikinsa har haka ba,farat daya ya maidashi tamkar ahalinsa,ya bashi dukkan yarda ya bude masa sirrinsa,yasan halin mata sarai,basu da kirki ko kadan muddin suna da wata manufa akan abu......tofa basa ji basa kuma gani harsai sun cimma muradinsu,suna iya komai,hakanan suna kuma iya jure komai har sai sun cimma gaci,musamman akan KUDI DA DUKIYA,suna sa masifar son kudi,tamkar wata halitta ce aka dasata cikin jininsu,basayin komai don Allah,bayason shi ko wani nasa ya sake fadawa MASIFA DA TARKON MACE,wannan wani HUKUNCI ne nashi da ya jima da yankewa akan kowacce mace idan ka debe MUTUM UKU RAK cikin rayuwarsa.

Sai da ya mula don kansa sannan ya janye hannuwansa da idanuwansa duka daga kan computer din,ya sarqe yatsunsa cikin na juna yana fitar da sassanyar siririyar iska daga bakinsa,ya maida shanyayyun idanunsa dake da wani irin qarfin fusgar hankali a muhallin da take sai kuma ya janye yana jin wani qyashi yana kamashi,dai dai sanda take miqewa a nutse cikin nata jin kan,ta zura takalmanta a nutse ta fara takawa zuwa bakin qofa

"Hey,da alama bakisan policies na aikin kamfani ba" ya jefa mata magabarya nutse ba tare daya kalli inda take ba,tsaiwa tayi cak,sautin muryarsa data tsana tana ratsa kunnuwanta,kamar tayi gaba,sai taga ya kamata atleast ta tsaya ta fuskanci wannan izzar tasa,don haka ta waiwayo cikin nutsuwa ta zube idanunta fes cikin nasa

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070

VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k

*Al'ummar NIJER ku kira wannan number don yin naku pyment din*

+22799643131

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥

*H U G U M A*

*_TABARMAR ƘASHI_*💔

*Arewabooks:Huguma*
https://arewabooks.com/u/huguma

Page 18

"Eheenn" sãahar ta furta a taqaice da alamun dake nuni da neman qarin bayani takeyi,sake zare hannunsa yayi daga kan system din,ya sanya idanunsa cikin nata a hankali kamar masu narkewa,wani abu me kama da fushi yadan ratsa ta tsakanin zagayayyun qwayar idanunsa

"Waye ya sallameki?" Ya fada kansa tsaye yana qanqance idanunsa cikin nata. Sai data kalli agogon hannunta sannan ta amsashi,tana jin kamar ta bude idanu taganta ba cikin office din ba,inda yasan yadda ta tsani hada hulda da maza da bai bari ta zauna tsahon mintunan da tayi a tare dashi ba,tana qoqarin hadiye fushinta ta amsa masa,saidai hakan bai boye tata izzar ba

"Lokacin daya kamata naci gaba da zama ya cika,inajin babu wani sauran abinda ya kamata na sani,inda akwai da ka sanar dani din" yadda take maganar with confidence ya bashi mamaki,karon farko da wata diya mace ta taba tsaiwa a gabansa cikin nutsuwa irin wannan ta bashi amsa takai tsaye,ta kuma amsa masa da abinda ya fito kai tsaye daga zuciyarta. Hannu yasa ya jawo wani file dake gefansa

"Inason nayi alerting naki abu daya,ki tsaya iya matsayinki,kada maganganun Dr ya rudeki,kina da naki limit din,so do not exceed that limit,right?"

"Don't bother" ta amsa masa a taqaice,duk da tanason ta gaya masa sama da hakan,to amma a yanzun bata da buqatar doguwar magana,sannan bai kamata ta take maganganun dattijon da bai dade da gama gaya mata su ba,bata sake bata koda second biyu ba ta juya ta fice abinta ba tare data tsaya jiran abinda yakeson gaya matan ba.

Sanda ta koma office sai abubuwan suka yita dawo mata,tanason taci gaba da aikin,amma kuma abinda ya faru cikin office din yana ta dawo mata a rai,a hankali sai zuciyarta ta fara zafi,ta dinga jan tsaki a jejjere,daga qarshe ta tabbatarwa kanta ba zata iya ci gaba da aikin ba,sai ta ture komai ta fara hada tarkacenta,ta dan debi wasu files da take tsammanin may be zata iya dubasu a gida,tabar office din bayan ta yiwa miss sameera umarnin ta rufe,ta dan bita da kallo tana mamakin yadda ta tashi abinda duk da lokacin tashi baiyi ba,bayan qaqqarfan jan kunne da CEO ya ajewa kowanne ma'aikaci akan makara da kuma tashi kafin cikar lokaci,a taqaice ma dai a kwanakin kusan kowanne ma'aikaci yana d'ara lokacin tashinsa,saboda yadda kowa ya maida hankalin wajen kawo daidaito da gyaruwar lamuran kamfanin.

Tana driving a hanya zuciyarta tana dada yin zafi,ta yaya zata iya aiki da wannan mutumin?,ta yaya zata jure aiki dashi?,kwata kwata nashi da manners,baisan darajar mutum ba,koda wayeshi,kowanne irin matsayi yake dashi,itakam ba zata taba jure ya takata ba,ba zata dauki kowanne banzan hali daga wajen kowanne d'a namiji ba yanzun.

Da wannan fushin da zafin zuciyar ta isa gida,tayi parking ta fito tana tattaro files din data taho dasu,fuskar nan a dinke na walwala taji takun afifa.

Ta cikin motar ta daga kai ta dubeta sanda take tahowa tana amsa waya,sanye da wata free gown,da alama tun dazun ta taso daga nata aikin,saita maida kanta taci gaba da abinda takeyi.

Tana isowa gurin ta gimtse wayar tana dariya qasa qasa

"Oyoyo mr president,bari na kwashi tabarraki" ta fada tana murmushi tare da qoqarin karbar folders din hannun nata,batayi jayayya ba ta sakar mata,ta fara kulle motar,afifa na gyara zaman folders din a hannunta tace

"How was your day today?" Yi tayi kaman ta cilla mata harara amma sai ta fasa,ganin cewa ba ita takar zomon ba,don haka ta amsa mata cikin miskilancin nan nata

"Bad" ta fada a taqaice tana soma takawa zuwa ciki,afifa tabi bayanta da hanzari

"Kaman yaya?,your first day at work fa" kai ta jinjina mata kawai tana lumshe ido ba tare da tace mata komai ba,sai afifan itama bata qara tambayarta ba,sukaci gaba da takawa zuwa ciki.

Maama ce zaune cikin falon,saman cinyarta wani dan bowl ne dake dauke da strawberry tana gyarawa,cikin kulawa ta amsa sallamar tasu idanunta akan fuskar diyar tata

"Barka da gida maama" sãahar ta fada tana isowa gabanta gami da duqawa,ta kuma dora saman cinyarta kadan. Murmushi ta sauke tana dubanta,gaba daya jiki da zuciyarta sun nuna gazawa xda gajiyawarta,saita zare hannunta daga cikin strawberry din ta dora saman kanta

"Barka kadai president dinmu,ya aikin?" Tabe baki tayi kamar wadda zata saki kuka,itako sunan batason a tuna mata,don da alama yaa muhyi ya bata aiki me wahala qwarai

"Ba dadi maama,ya muhyi yayi punishing dina ne kawai da wannan aikin" dariya afifa ta saki yayin da maama tayi murmushi

"Ba haka bane,da sannu dai zaki saba,qila ma ki dinga jin dadin aikin nan gaba kadan fiye da yadda muke tunani" miqewa tayi tana dan tura baki

"Anya maama zanso wannan aikin?"

"Ba wanda yasan gobe sai Allah" kai tadan jinjina

"Abba bai iso ba?"

"Ya kusa,inajin sai an idar da sallar magrib".

Zasu wuce baaba rabi ta iso zata karba strawberry din da zata markada,cikin fara'a da girmamawa ta amsa barka da gidan da sãahar tayi mata

"Barka dai farar d'iya,tun dazun nake dakon isowarki,abincinki ya kammala"

"A shiryamin dan kadan,bamai yawa ba,ina fitowa yanzu"

"A fito lafiya ummin abba" ta fada cikin nuna kulawa,maama dake zaue ta kalleta

"Rabi kece kike sake sakalta sãahar naga alama"

"Idan bamu tattalawa alhaji diya ba hajiya ai bamuyi halacci ba" sai kawai maaman ta bita da murmushi,kasancewar itadinma ba maison yawan magana bace.

Tare suka shiga dakin ita da afifa,ta zube mata takardunta a kyakkyawar kusurwaf da aka shiryama wani kyakkyawan table da kujerarsa,dan qaramin study room a maqale da bedroom din nasu,gurin an masa shiri na musaman da zaiyi dadin karatu,ta koma parlor ta barta a dakin.

A nutse ta cire kayanta ta watsa cikin laundry basket,ta daura wani lallausan farin towel,gab da zata shiga toilet din wayarta ta soma tsuwwa,dakatawa tayi tana duba number dake yawo saman screen dinta,zubawa numbers din dake jere reras idanu tayi,sai taja da baya ta wuce bandaki abinta,saboda number tayi mata kama da number mahmud,wadda a qalla kusan kullum tana ganin gilmawarta cikin wayarta da tarin saqonninsa da ko sau daya bata taba tsaiwa dubawa ba bare ta bashi amsa.

Mintina kusan ashirin da biyar sannan ta fito,ta tsaya gaban madubi ta tsane jikinta,ta shafe lallausar fatarta me sulbi da mayuka sannan ta mutstsike jikinta da turarukanta masu taushin qamshin da kwantar da zuciya.

Wani budadden cotton trouser ta saka,da wata free over size shirt me taushi,ta kama gashinta ta daure da band,idanunta suka sauka ga fuskarta da tayi wani irin fresh,babu alamun tabo ko qwarzane ko daya a kanta

_"ki tsaya iya matsayinki,kada maganganun dr ya rudeki,kina da naki limit din_" ido ta lumshe tana jin maganar na mata zafi kamar yanzun ya furta mata su,waye ya gaya masa buqatar kanta ce wai ta kawota companynsu?,baisan aikin tamkar wata tursasawa bane da karan tsaye ne da aka yiwa rayuwarta ba?,batason shafe maganar dattijon,hakanan batason zubda yaa muhyi a idanunsu,dole wani abun ta kauda masa kai,amma bafa komai ba,kuma muddin zasuci gaba da hada hanya da guy din ta tabbatar babu jimawa zasuyi batacciya,don ba zata iya shanyewa irin wadan nan halayen nasa ba,yadda yakema mata ita ba zata iya dauka ba,don ba abinda take nema daga wajensu.
Chapter 20 · 0% Book details