← Book details Tabarmar Kashi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 105 OF 171

Sashe 105

Tabarmar Kashi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A firgice ta farka tare da sake qanqame fadeelan cikin zafin nama tana kiran sunanta. Cak ya tsaya yana dubanta cikin mamaki,gaba daya ta firgita kamar ana zare numfashinta ne. Sakar masa fadeelan tayi a hankali bayan sun hada ido,sai ta tsuke fuskarta tana qoqarin gyara gabab rigarta da ya tattare saboda janye yarinyar da yayi yasa ya bude don rigar me santsi ce,saita juya right side dinta tana sake jan duvet din sosai tana lulluba har saman kanta,cikin ranta tana jin haushin yadda kowanne lokaci yake shigo mata daki ba tare da neman izini ba,dole tayi masa magana,ba zata juri wanann ba,a duk yanayin da kake ciki sai mutum ya ganka kenan a haka?. Shima yana gama gyarawa yarinyar kwanciya ya tofeta da addu'a sai ya juya ya fice,tabi bayansa da kallon harara ta cikin duvet din, cikin sa'a ya waiwayo don ya manta bai kashe musu haske ba,tayi hanzarin maida idanunta ta kulle,sai kawai ya basar amma cikin jikinsa tabbas yaji tana kallonsa,ya kashe wutar yaja qofar ya fice,yadda ta firgita da jin ana jan fadeela na tsaya masa a rai,ya sauke sassanyar ajiyar zuciya sanda ya kammala shiga nasa dakin ya zare takalmansa a gajiye ya watsar dasu a gun ya zube saman sofa bed yana dage kansa saman bayan ya watsa hannayensa.

Yana fita ta waiwayo ta jawo yarinyar cikin jikinta,sai yau zasuci gaba da kwana tare,don kullum maji hanawa takeyi tazo,a nata nufin a barsu su sake,kuma fadeela tayi girma da kwana cikin iyayenta. Idanunta a rufe amma tana bitar abubuwan da suka faru wunin yau,bata jima tana wannan dogon tunanin ba bacci yayi awon gaba da ita.

***karfe biyar da rabi ta idar ta farka,a nutse ta sauka daga saman gadon,jikinta ya sake sosai,babu ciwon kan ko kadan,sai dan rashin qwarin jiki dan kadan. Bandaki ta wuce ta daura alwala ta dawo ta shimfida abun sallah,sai data idar sannan ta tashi fadeela,tana gamawa a nan gefanta saman abun sallar ta bingire bacci ya sake daukar yarinyar.

Tayi nisa wajen yin azkar dinta,yayin da gefe daya kuma qwaqwalwarta ke cike taf da tunani daban daban. Wayarta ce tayi haske kadan,ta jawota tana dubawa, afifa ce ta turo mata saqo,murmushi ya subuce mata tana girgiza kai,wato sajjad yana so ya sanyata ta manta da ita,lallai sunci bashi,bari a gama amarcin ta nemeta saita tsigaleta tas.

Tana shirin buda saqon sautin knocking ya ratsa kunnuwanta,ta tsaya tsam daga qoqarin bude saqon da takeyi tana son tantance daga inda sautin yake fitowa,don dai tabbas ba qofar dakinta akewa knocking din ba. Har ta basar jin cewa ba tata qofar ake bugawa ba,ta buda saqon afifa tana dubawa,wanda saqon sannu da jiki ne da kuma ban haquri,saidai har ta gama karantawa ta maida mata reply ba'a daina buga qofar ba. Maida idanunta tayi ta rufe bayan ta kalli agogo,duka duka yanzun qarfe takwas ne da wasu mintu na safe,to waye zai shigo har nan din yana irin wannan nacin qwanqwasa qofar?. A hankali bugun ke qara yawa,qaramin tsaki ta ja,ba kasafai ta fiyason hayaniya da safe ba,ta miqe a hankali tana gyarawa fadeela kwanciya ta nufi qofar dakin nata.

Cikin nutsuwa ta murda handle din ta bude qofar,ta kuma sanya kanta tana leqen tsahon hallway din don ganin me bugun da kuma dakin da ake bugawar. Hakan yayi dai dai da sanda shima ya buda qofar tasa,ya kuma sanyo kansa waje,fuskarsa tayi wani fresh da hasken sallar asuba tare da wani irin tarin nutsuwa da kamala da yake da ita.

Ido suka hada shi da ita,manyan fararen idanunsa da bacci yadan qara musu haske da girma,a tare suka janye dubansu sannan ta sauke kallon nata akan matashiyar dake tsaye gaban qofar dakin. Sanye take da skinny jeans da wata t.shirt da iya tsahonta qugunta,qafafunta dogayen takalma ne masu tsini da igiyoyi a jikinsu,sai qaramin Scarface dake kanta wanda iyakarsa wuyanta,ba wani abu da ya rufe mata,bata iya ganin fuskarta,amma duk da haka zaka iya gane tsananin sirantar da take dashi da kuma hasken fata.

"Yaa moha" ta fada da muryarta me tsananin sirantaka, muryar na dan rawa kadan alamun kuka takeson saki. A nutse ta maida jikinta ta kuma maida qofar dakin nata ta kulle,kwanyarta nason tuna mata wacece ita?. Gefan gado ta koma ta zauna tana qarshe cikon hailalarta da take guda dari duk rana safiya da maraice 200 kenan. Gefe daya kuma yarinyar na mata yawo a idanunta

"Haseena,'yar hajiya qarama" wani lungu daga qasan zuciyarta ya cillo mata amsar,bayan ta gama qirga kwanakin da hajiyan tace mata zata dawo,haka yake,indai lissafinta yayi dai dai kenan. Qaramin murmushi ne ya qwace mata a fuskarta,tadan girgiza kai kawai,wanann itace haseena din da hajiyar keta kururuta zuwanta?,saita girgiza kai kawai,ta sauka a hankali ta dauke fadeela ta maida saman gadon itama ta koma ta kwanta tana jan musu duvet. Dakin ya dauki shuru na wasu sakanni,tana ci gaba da salati qasan ranta idanunta a lumshe,dukka hallway dinma shuru,babu alamun motsin mutum kwata kwata.

Sanda ta maida qofar ta rufe duka akan idanunsa,a nutse yana kuma qarawa fuskarsa rashin walwala ya sauke dubansa akan yarinyar. Idanunta cike suke taf da qwalla,ta ritsashi da idanunta tana kallonsa da kyau,sai kawai ta zame jakar dake rataye a kafadarta ta ware hannunta da zummar rungumarsa. Da sauri yaja da baya yana jifanta da wani kallo

"Meenal,meye hakan?" Ya furta a mugun dake,tsaiwa tayi sak tana kallonsa,hawayen da take maqalewa na gangarowa

"I want to be in your arms yaa toufeeq please" ta furta tana sake sakar masa kuka. Tsaiwa kawai yayi yana kallon ikon Allah,yadda qanqanuwar yarinyar da aka haifa ta taso a gabansa ta zama haka,totally ma ta canza,tun daga yanayin halittarta kawo dabi'unta,tayi wani irin girma kamar sa'arsa,duk da cewa 'yan watanni ne tsakaninsu da nadeeya,amma sai ka rantse gaba take da nadeeya. Ganin baice komai ba sai hannunsa sa ya goye kawai a qirji yana mata wani kallo da batasan inda ya dosa ba,saita sulale a gurin ta duqa saman qafafunta tana sake sabon salon kukan

"Yaa toufeeq,i can't take it anymore,duk tsahon wanann lokacin da naqi kula kowa kai nake jira,na saka raina da duka burina a kanka" sai taci gaba da gaya masa abinda ke ranta kai tsaye ba kunya ko kwana kwana,gaba daya kansa sake daurewa yayi,yaushe ta zama mara kunya haka?.

"Look meenal" ya kirata yana sake hade ransa da kyau,a hankali ta daga idanunta da suka jagale da hawaye ta kalleshi

"Dama ina wasa dake?" Ya fadi da wani irin tone da ya fidda kwarjininsa har ya kusa bugar da ita,qoqarin tattaro dukka dauriyarta tayi,da gasken gaske takeson toufeeq fiye da lokacin baya kafin dawowarta da ganin da tayi masa yanzu,a wannan lokacin da tayi ido hudu dashi,bawai cikin hotunansa da take faman wallafawa ba,ta sake jin cewa a shirye take ta karba toufeeq din daga hannun kowacce mace

"Kaga alamar da wasa nake yaa moha?,kaga alamun wasa cikin soyayyar da nake maka?" Ta tambayeshi idanunta cikin nasa hawaye na sake wanke mata fuska. Abun sai ya koma bashi mamaki qwarai,yayi shuru yana karantarta

"Yaa toufeeq please say something,kayi magana mana,da gaske nake maka,bazan iya jurar rasaka ba,i can do anything a kanka,ciki kuwa harda kashe kaina muddin na rasaka!" Cikin 'yan mintuna qalilan ya gama fahimtar da gasken take fa,duk abinda take fadi din da gaske ne zata aiwatar,shi sai yake ganin ma kamar ba cikin saitinta take ba.

"Muje parlor" ya fadi yana nuna mata hanya,dole tana buqatar guidance and council,ya kamata ta fahimci shi din a matsayin yaaya yake a wajenta bawai masoyi ko mijin aure ba. Kamar ba zata tafin ba har sai da ya maimaita mata yana sake hade fuska,sai tayi gaba tana qoqarin tsaida hawayen nata.

A hankali ta bude idanunta saboda gajiya da tayi da rufesu din,baccin kuma da take sanya ran zuwansa baizo ba,batasan me zuciya da kunnuwanta suke jira ba,sai ta miqe a nutse tana gyara top din rigar baccin jikinta me rubi biyu,ta jawo dankwalinta me santsi daya dace da rigar ta daure kanta ta zuro qafafunta ta sauko daga saman gadon. Gaba daya ta manta da batun shan ruwan duminta,ta zura bedroom slippers dinta ta nufi qofa. Duk yadda taso ta dauke kai daga kallon qofar dakin da a dazun yarinyar ke tsaye amma ta kasa controlling din idanunta. Ba kowa yanzu a qofar dakin,saidai kamar a bude take bawai a rufe yadda ta saba ganinta ba kullum. Batasan dalili ba amma sai ta samu kanta da jan qaramin tsaki,ta juya tana fita a gurin.

Muryarsa a tausashe kunnuwanta suka fara jiyowa,a lokacin da yake magana da haseena cikin son kwatanta mata abinda ke cikin zuciyarta ba me yiwuwa bane

"Ka fahimceni yaa toufeeq,nima ba yin kaina bane,bansan lokacin da zuciyata ta kamu da matsanancin sonka ba,a yanzu kuma ba abinda kunnuwana zasu iya fahimta sai yaren sonka kawai" daidai lokacin idanunsa dana sãahar dake qoqarin wucewa kitchen suka hadu waje daya. Har tsakiyar kanta taji kalaman yarinyar da muryarta me bala'in sirantaka,ta lumshe idanunta tana daukesu daga kan toufeeq din,wani tsanarsa na darsuwa a ranta. Shikenan shi bashi da aiki sai jefa soyayya a zukatan 'yan mata?,su kuma basu da aiki sai zub da kima da martabarsu?,shin wai basajin kunyar roqon soyayya daga gurin namiji?, namijin ma irinsu toufeeq din me zafin kai izza da jin cewa shi din wani ne?.

Bata sake bari kunnuwanta sun jiye mata komai ba ta daga qafarta ta shige kitchen din da dan sauri kadan,sai a lokacin ya dauke idanunsa daga kanta,baiga komai saman fuskarta ba kamar yadda ya saba gani a baya akan fuskar AMEESHA a duk lokacin data fahimci wata mace tana ra'ayinsa,koda kuwa bata furta ba,a ranar babu zaman lafiya ko kuma kwanciyar hankali. Idanunsa dake dauke da wani irin maganadisu wanda ke sake dasa mata kakkaifar soyayyarsa cikin zuciyarsa ya zube mata cikin kowanne lungu na jiki da zuciyarta.

"HUGUMA*

_TABARMAR KASHI_*

Book 02 Page 22

• "Kije ki huta tukunna" ya fadi wa meenal din yanason shawo kan matsalar ta lumana,bayason akai ga ta qure dan garamin haqurinsa a kanta.
Chapter 105 · 0% Book details