← Book details Tabarmar Kashi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 171

Sashe 28

Tabarmar Kashi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sun jima kafin daga bisani suyi sallama,ta kawo masa wayar,fuskarta qunshe da murmushi

"Daddy,wai a ina maji take?" Ta jefa masa tambayar da baiyi zaton jinta daga bakinta ba

"Bata a nan qasar angel"

"Tana ina?" Ta sake tambayarsa,da alamar da gaske tanason jin a inda take din

"Algeria"

"Yaushe zamuje daddy?,tanason ta ganni nima inason na ganta" ta tambayeshi a shagwabe. Ido ya zuba mata sosai,shi kansa a yanzu bazai iya kai kasa kai tsaye inda maji take ba,tun haihuwarsa har girmansa bai taba zuwa,a baya yana da kwadayin zuwan,amma a yanzun kwata kwata babu wannan cikin ransa,baisan kuma yaushe hakan ta faru ba,kawai dai ya tashi ne dare daya yaji yayi loosing interest akan dukkan abinda ya shafeta,kafin daga bisani kuma ya yakan yawaita samun mantuwa akan komai daga danganceta.

"Zamuje angel"

"Daddy yaushe?" Ta sake tambayarsa tana kafeshi da idanu,idanunsa ya janye daga kanta,murmushi kadan yana subuce masa,ya fuskanci rigima takeji

"Wata rana" ya bata amsa yana sanya hannuwansa ya dauketa cak hadi da cewa

"Muje muci dinner" zata sake magana ya dora yatsansa akan lips dinsa gami da cewa

"Shshshsh,ya isa" duk da qanqantarta amma tana gudun abinda zai bata masa rai,tana matuqar jin maganarsa fiye da tunani,saita kwantar da kanta a kafadarsa,a haka suka qarasa dining room din.

Sallamar cook din nasa dake jiran ya iso yayi serving nashi yayi,da kansa ya zuba musu iya abinda zasu iya ci shi da fadeelan yabar sauran.

*********Karfe daya na rana ne,lokacin da kowanne ma'aikaci dake qarqashin company din yake morewa lokuttansa na break. Dai dai lokacin da sãahar a cikin nata office din ta duqufa wajen ganin ta gama hada dukka bayanan data samu daga financial team na company,tana duba yiwuwar yin magana akan document dinta dake office na CEO,batason tayi aikin banza,tanaso ta aiwatar da dukka tsare tsaren da tayi,don ta tabbatar zai kawo gagarumin ci gaba da kuma sauyi cikin company din.

Buda qofar da akayi ya sakata daga fararen idanunta tana kallon bakin qofar,mr sameera ce,ta bata izinin qarasowa bayan ta janye hannuwanta daga kan system din

"Ranki ya dade,sir hamza ne ya sake dawowa" idanunta da suka dan daure saboda kallon allon system din tadan juya kadan,qaramin tsaki taja,hamzan yanason shiga rayuwarta,kaf fadin company din a yanzu bata da wata matsala saishi,yaqi fahimtar inda tasa gaba,gaba daya sake shige mata yakeyi a kowanne lokaci,don kawai office dinta yana da alaqa da department dinsa,don ko yanzu report din da take dubawa daga office dinsa ya fito,banda haka da tuni ta yanke dukkan wata alaqa da zaya bashi damar ganinta

"Ki gaya masa ba yanzu ba,aiki nakeyi,ya tura kowanne saqo ta email din office,zan duba sanda na zama available" jinjina kai sameera tayi,ta juya ta fice.

Cak ta tsaya da aikin da takeyi tana sake jan wani dogon tsakin da yafi na farko,saita tura kujerarta baya tana dan fidda iska daga bakinta,da alama wani tunani ne ya darsu a ranta lokaci daya. Yatsunta tasa tana murza goshinta dasu,tana tuna shigowarta company a safiyar dazu,yadda ta tadda employee a dan hautsine,sakamakon korar wasu ma'aikatan guda uku da ceo yayi a safiyar

"wanne irin mutum ne shi?,me izza da dagawa?,he doesn't give excuse to anyone?,abu kadan kora?,kowa ma yana iya kora ko yayi masa fada?" Tayi maganar can qasan zuciyarta,haushinsa da kuma tsanarsa suna huda zuciyar tata,abinda ta lura dashi ma,gaba daya yafi zafafa al'amuransa akan mata. Sake jan wani dogon tsakin tayi karo na uku,gaba daya tuna abin da ya farun yasa tayo loosing interest akan aikin,ta duba baqin agogon dake daure a tsintsaye hannunta qirar kamfanin Casio,akwai ragowar mintuna talatin kafin lokacin komawa bakin aiki yayi,coffe take da buqata,amma batason takura mr sameera,don haka ta tsugunna a hankali ta daura igiyoyin baqon takalaminta daya mugun haska farar qafarta me dauke da dogayen yatsu,ta miqe a nutse ta dauki iya wayarta ta fita a office din.

A nutse take takawa a farfajiyar gurin,cikin girmamawa ma'aikatan ke gaidata,saboda Suna respecting nata sosai,duk wanda yayi mu'alama da ita kuma kusan sai ya fadi halinta ya kuma yi mata shaida me kyau.

Ko kusa ko alama bata ga koda inuwarsa ba,saijin maganarsa tayi a bayanta

"Ranki ya dade,barka sa fitowa" mr hamza kenan,wanda ke biye da takunta yana son ya cimmata cikin zumudin da katarin ganin fitowarta da yayi. Kadan ta waiwaya ta aje masa kallo daya

"Ya kake?" Ta fada a daqile,hamza na daya daga cikin mutanen dakeson zame mata barazana cikin company din,tare da yi mata kutse cikin walwalarta da al'amuranta,duk wani hanya da zatayi avoiding nasa tayi,amma ta karanci kamar baya fahimta,da alama yana sahun mazan dake da shegen naci da kafiya ne

"Lafiya amma ba qalau ba,please ki taimaka ki gayawa secretary dinki,ta daina min shamaki da ganinki,wallahi it really hurts me" sunzo bakin qofar kitchen din,kuma bata da buqatar yaci gaba da binta,don haka ta dakata,ta juyo gaba daya tana dubansa

"Excuse me mr hamza.....ko zaka taimaka ka juya,saboda banason ka shigarmin lokacin nawa hutun,na gaya maka idan maganar office ce ka tura ta email zan duba,idan kuma bata office bane, please i beg you,banason wani abu da bashi ya taramu a nan ba ya hadani da kai,bama kai ba,koma waye bana buqatar wata hulda ko alaqa" da hanzari ya buda baki zai maida mata da martani,amma sai taji yayi dif,batasan dalilin daukewar wutarsa haka lokaci guda ba,amma koma meye sanadi ita ba damuwarta bane,don dama tafi buqatar shirunsa akan amsarsa,don haka ta juya ta shige kitchen din kanta tsaye.

Wayam din data gani a kitchen din babu kowa da kuma qarancin haskensa bai sanya ta zaci akwai wani abu ba,saboda wannan shine karon farko data taba shigowa kitchen din. Coffe dama kadai tazo nema,don haka ta nufi mini coffee maker din data gani a jone,data duba sai taga akwai saura a ciki,don haka ta ciri mug guda daya,ta cikashi dashi,yawunta yana tsinkewa,saboda wani qamshi da taji yanayi na musamman,uwa uba kuma kana kallonsa zakasan ya hadu iya kwadayinka da shan coffee.

Dan qaramin murmushi ta sauke,saita gyata tsaiwarta tana kai mug din bakinta,dai dai sanda ta juyo. Babu zato ta saki mug din,cikin razana taja baya,fararen idanunta suna sake girma hadi da fitowa waje. Tsoratar da tayi yasa bata iya tsaiwa ta tantance waye ba tayi qofar waje da sassarfa,saidai kuma tana dab da isa ya rigata isa gurin,ya saka hannu ya tura qofar ya rufeta bam,taja birki a mugun hautsine tana sauke dubanta a kansa,sai a lokacinne ta gane waye.

MT jarma ne da kansa,cikin shigar suit dinsa ta ko yaushe,saidai kuma a yau din babu suit jacket din a jikinsa,alamu suna nuna ya barota a office,hannun rigar ciki da ya kasance dogo ya tattareshi ya barshi iya gwiwar hannunsa,wannan ya bawa murdadden hannunsa dake cike da gargasa da wasu irin jijiyoyin da yawan shiga gym ya haifar dasu. Kwantacciyar sumarsa me santsi a dan hargitse take kadan,lips dinsa sundan sake yin jaa saboda zazzafan coffee din da yake sipping a hankali.

Ko a yanzun ma da yake tsaye ci gaba yayi da sipping abinsa cikin nutsuwarsa da kamewarsa,kamar bashi ya tsorata ta ba,sanann yasa hannu ya garqame musu qofa haka kawai ana zaune qalau. Ranta ne taji yayi mummunan baci,tadan motsa fuskarta kadan saboda yadda zafin coffee din data saki ya dan taba qafarta yake mata zafi kadan kadan,wannan wacce irin dabi'a ce zai samu guri ya zauna a kitchen,a corner din da ba lallai kai ka iya ganinsa ba?,saita janye idanunta ta taka zuwa qofar don ta bude ta fice,don bata qaunar hada rufi daya dashi bare taci gaba da zuqar qamshin turarenta da yake neman sanyaya dukkan wani zafi data dauka akan abinda yayin.

Table din dake daura dashi ya matsa kadan ya dora cup din,cikin zuzzurfar muryarsa dake cakude da wani irin amo me ya soma magana

"You must learn saying salam a duk wajen da zaki shiga,saboda nan din mudai musulmai sunfi yawa......sannan bari na taimakeki na tuna miki wani abu daya,nan masana'anta ce,kayi aiki a biyaka da gwargwadon wahalarka na wata daya,ba waje bane da aka bude saboda soyayya ba,saboda haka ki kiyayi bawa wani damar ganinki a office da kebantacciyar buqatarku wadda bata da alaqa da company,idan ba haka ba,you will loose your job" ya qarasa maganar yana dora hannunsa a mariqin qofar,ya budeta sannan yace

"Dont try to do this again......inda kin fita a yadda kikaso fita,wani ya ganki me kike tunani zai zata" bai jira amsarta ba ya taka zai fita, zuciyarta tazo mata iya wuya sosai. Yama gama raina mata hankali,yaso qona mata qafafuwa,sannan kuma ya bita da wasu sharuddansa marasa amfani a gurinta,tunda dai ai ita ba yarinya bace,tasan meye ya dace da ita. Ji tayi idan ya fita ba tare datace masa komai ba tabbas yaci bulus,duk da zuicyarta na qoqarin tuna mata maganganun yaa Saifullahi da yaa zaid na ta girmamashi,gaba yake da ita

"Shi kuma wannan kullemu da kayi fa?,idan wanin ya gani yace me?" Ta fada tana jin takaicin yadda tayi dogon zama a guri daya dashi,harta shaqi turarensa da kyau,ya shiga kowacce kafa ta hanci da kwanyarta.

Waiwayowa yayi ya zube mata manyan kewayayyun idanun nasa dake da wani irin magnet da kwarjini,har sai dataji kamar zata zube,yayo taku biyu ya dawo baya kadan

"Kina iya gayawa duk wanda ya tambayeki..... nayi raping naki ne,don wanann din kadanne daga aikinku".

"Ya salam" ta fada can qasan zuciyarta hade da wani mugun bugawa da zuciyar tata tayi,ba kuma tare data shirya ba ta koma da baya ta zauna saman kujerar dake kusa da ita,wanda tayi yaqinin banda taimakon Allah kujerar tana kusa da ita lallai zata iya faduwa qasa. Kamar baice komai ba ya juya a nutsensa ya fita a kitchen din.

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070

VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k

*Al'ummar NIJER ku kira wannan number don yin naku pyment din*

+22799643131

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Chapter 28 · 0% Book details