← Book details Tabarmar Kashi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 171

Sashe 81

Tabarmar Kashi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ba abinda kukayi mata,ko bata tafi ba daman zan sallameta,saboda bata dace ta rayu daku ba" maganganun nasa sai suka zame mata tamkar zubar dafi tsakiyar naman zuciyarta,tana da muradin ko sau daya ta waiwaya ta sake kallon fadeelan dake kuka iya qarfinta saboda ita kadai,amma kalmarsa ta sanya ta lanqwasa zuciyarta taci gaba da takawa ba tare data waiwayo ba. Tsawar data sake ji ya yiwa fadeela karo na biyu ya sanya qwallar dake magale a idanunta qarasa gangarowa,zuciyarta na kwarara da wata matsananciyar tsanarsa,sai ta qara sauri tana ficewa a gidan,lokacin da ya sanya hannu daya ya dauketa cak ya nufi cikin gidan,ta qwalla garar kiran sunanta full, abinda bata taba yi ba

"Anty saahaaarrrr" kamar zata shide,sai ya dageta ya rungumeta tsam a jikinsa zuciyarsa na wani irin bugawa a mugun jargiy,yana jin kamar ana yankar naman zuciyarsa.

Duk yadda taso riqe qwallarta cikin mota amma abun ya faskara,sai tasa tafukan hannayenta kawai ta lullube fuskarta tana sauke hawaye masu dumi qwarai,ba abinda ke dawo mata cikin kwanyarta sai sautin kukan fadeela da yadda ta qwalla kiran sunanta har zuwa sanda sautin ya dusashe daga kunnuwanta. Sanda suka isa qofar gidansu ta cire kudin ta miqawa me napep,yana fadin

"Hajiya ga canjinki fa" ko waiwayowa bata iyayi ba ta daga masa hannu,ya fuskanci me take nufi sai hau zabga godiya yaja macnine dinsa yayi gaba

Baaba habu ne ya karba mata kayan,yadda yake mata sannu da zuwa yaji batace komai ba sai ilkinsa ya bashi akwai matsala,don haka bai sake cewa komai ba ya migawa jamilu luggage din yace ya garasa mata ciki da ita.

Can gasan magoshinta tayi sallama,falon nasu ba kowa kaman yaushe,yana nan a tsaftace da qamshinsa,da kuma ac dake bada iska me sanyin dadi,sai gamshin sanwar dare dake sirarowa kai tsaye daga kitchen dinsu.

Baaba rabi ce ta fito daga kitchen din sai taci burki tana cewa

"Ah ah,maraba da farar diya,kece yanzun nan akan hanya?" Kai ta gyada muryarta can qasa

"'Nice baaba rabi,barkanmu da yamma"

"Yauwa barka kadai" daga haka tayi hanyar bedroom dinta tana tambayar maama

"Basu jima da fita ba ita da afifa"

"To yayi" abinda ta fadi kenan ta wuce shige dakin nata.

Saman gadonta ta zube kamar wata kayan wanki tana qoqarin samarwa kanta saugin abinda takeji a zuciyarta,tayi lamo idanunta a rufe tana jin yadda zuciyarta ke gonewa. Inda ace ta san wannan gidan nasa ne,inda tasan ace wannan ahalin nasa ne inda ace tasan wannan diyar tasa ce.....to babu shakka,duk yadda zuciyarta zata kai ga tausayinta ba zata taba rabarsu ba.

Duk iya yadda yake tunanin zai iya lallashinta ko kuma ya bata baki amma abun ya faskara,har ya gaji da lallashin,ya koma bakin window din dakinsa yayi tsaye yana duban farfajiyar gidan, zuciyarsa na masa mugun zafi. Me yasa suna zamansu lafiya suna lallaba rayuwarsu zata shigo ta hargitsasu?,bayajin fadeela ta taba kuka irin wannan,koda kuwa ranar data rabu da mahaifiyar da tayi silar kawota duniya ne. Wai me yasa ne su mata basu da tausayi?,basu da imani?,a duk sanda zuciyoyinsu masu cike da ra'ayoyin qeta da son kai ta mosa musu,tabbas sai sun shiga rayuwar dukkan wanda suka hara sun aiwatar da koma meye sukayi niyya. Bayajin zai saurari kuka ko rigingimun fadeela,zata gaji ta haqura ta bari, dole ta koyi rayuwa babu mutanen da zasu zame mata baraza ko matsala,kamar yadda suka tashi shi da NADEEYA,suka rayu kuma a hakan,babu kuma wani abu da ya canza kalar qaddararsu,gasunan cikin qoshin lafiya da wadatar Allah.
Bismillahir rahmanir rahim

*HUGUMA*

*_TABARMAR KASHI_*

Book 02 Page 01

A ranar cikin su hudun säahar nadeeya taoufeeq da mai gayya me aiki fadeela babu wanda yayi wani cikakken baccin dadi, nadeeva ranta a jagule zuciyarta fal tambayoyi tare da neman dalilin tafiyar sãahar din lokaci guda,sai kuma yadda yaga zallae bacin rai daga fuskar ya moha,idan har kunnuwanta sunji mata dai dai da bakinsa yake gayawa fadeela

"Let her go,zaki ci gaba da rayuwa ko babu ita.." Sake juyawa nadeeya tavi tavi rub da ciki tana sake nazarin matsalar,a yadda idanunta suka karanci yaa moha din,kamar wata alaqar sanayya a tsakaninsu,to amma a ina ya santa ko kuma a ina sukasan juna? ,shine dai bata sani ba. Iska ta furzar daga bakinta,fatanta dai Allah yasa ba wani abu me muni bane va hadasu kwatankwacin na Ameesha. Sai ta girgiza kai da sauri tana gayawa kanta A'AH.

********Duk da kumburin idanuwan da basu samu bacci ba,da kuma ciwon kai da yakeson taso mata kadan kadan,amma hakan bai hanata shiga kitchen taya maama hadawa dr breakfast dinshi ba. Tana aikin amma yau so silent take,ba kamar baya da takanyi hira da masu aikin nasu ba. Afifa tun sassafe ta fice asibiti,saboda samun marasa lafiya da akayi daren jiya wadanda sukayi hadarin mota.

A daki ta iske maaman,ta gaya mata ta gama

"Ki shiryawa abbanku a dining na sashensa,fita zaiyi yau din yana da baqi,yanzu zan iso sashen" amsawa tayi da to ta juya tana fita, maaman ta bita da kallo. Tun jiyan datayi mata sannu da zuwa bayan dawowarsu da afifa ta karanci akwai wani abu dake damunta,to amma tasan halin kayarta da shegen zurfin ciki. Sannan tana zaune ma afifa zata gano musu komai. Sau da dama tana iya gayawa afifa damuwar da ita bata iya gaya mata ita,wannan din kuma wani haduwar iini ne da zumunci me qarfi a tsakaninsu fiye dasu iyayensu.

Ta gama shiryawa tsaf ta juya zata fita muryar dr girema ta sauka kunnenta,cikin kamilalliyar muryarsa yake sallama a falon.
Sai da gabanta ya fadi,amma ta tattara dukka nutsuwarta waje guda ta amsa masa sannan ta rusuna tana gaidashi

"Zauna muyi magana" ya fada maya shima yana laluben wajen zama,sai ta zame ta zauna daura dashi kanta a qasa.

"Jiya akacemin kinzo,ina fata ki dawo kenan,saboda ba zaki sake komawa ko ina ba,ladan da aka samu Allah ya amfanashi" a ladabce tace

"'Eh,na dawo kenan abba,ina godiya kuma da dukka damar da aka bani"

"Bata haka nake buqatar godiyarki ba ummi na" sai ya gyara zamansa sosai yana dora hannunsa saman hannun kujerar

"Zuciyata ta gama nutsuwa da aminta da yaron nan,don haka ina me shaida miki,muddin kin bani dama kamar yadda musulunci ya tsara mu nemi izinin bazawara,to zan bashi damar turo magabatansa,yazo ayi a gama komai a wuce gurin,kema ki tattara hankalinki waje guda"

"Na baka izini abba" ta fada kanta tsaye, zuciyarta na qeqashewa,tana jin yanzun bata da sauran mafaka kuma,guje gujenta ya qare,babu wani abu da ya rage mata,
MAHMUD GANA yayi winning.
shuru dr girema yayi yana son karantar fuskarta,yadda tayi saurin amsawa yadan daure masa kai,saboda ya riga ya ajema ransa ko yaya zai ta dan ja,amma karon farko babu jaa babu komai ta sallama?. Kai ya gyada

"Shikenan kije,Allah yayi miki albarka,ko meye ake ciki zan sanya mahaifiyarki ta sanar miki"

"Ameen abba" ta amsa tana migewa, kowanne sashe na jikinta na qarasa sakewa yana mutuwa dukkan wani qwarin gwiwarta yana zagwanyewa,qarshen tika tiki tik,mai afkuwa zata afku a kanta.

Da gyar ta tattara nutsuwarta tayi wanka,batason duka wannan bacin rai qunci da damuwar da take yawaita samun kanta a ciki,ga tunanin fadeela cunkushe cikin zuicyarta,duk wani motsi da zatayi sai taji kamar sautin muryar fadeela ne keci gaba da kiranta. Wannan ya sanya ta shirya ta nema izini wajen maama,ta wuce gidan yaa muhyi ta dauko khaleefa,daga nan suka zarce gidan ya Saifullahi ta dauko fadeel,ta sauka gidan yaa zaid ta dauko zaahid. Tana Sanya ran kasancewarta tare da yaran zaiyi matuqar debe mata kewa,duk da cewa yara maza ne ba mata ba,amma tana da yaginin zai dauke mata damuwa me yawa,ya kuma rage mata zaman kadaici.

********Dukka manyan idanunsa ya ware a kanta,yana ci gaba da sanya spoon din abincin a bakinta cikin tsare gida tare da sake tsuke dinkakkiyar fuskarsa. Hakan ya qara ta'azzara rashin fara'arsa tare da garawa fuskarsa kwarjini.

Duk sanda zata karba abincin saita kalli idanunsa sannan,ya sake kawo spoon din bakinta,sai taqi bude bakin bare ta amsa.a maimakon haka ma ruwan hawaye ne ya biyo baya.

Ajiye spoon din yayi yana tsareta da idanu

"Meye kuma?"

"Anty N" ta fada hawaye na sake sauka a idanunta. Sosai ranshi ya sosu,don ko sunanta bayason yaji daga bakin fadeelan

"Idan kika sake yimin maganarta.
.. saina zane
bakinki tas" ya fada yana zare idanunta cikin
baraza

"Oya,gate up" muryar sajjad ta ratsa tsakaninsu ya fada yana migawa fadeela hannu. Da hanzari ta miga masa hannun nata hawayen da suka magale suna garasa zubowa,ya tayar da ita tsaye yace

"Muje ki gayawa sister nadeeya ta canza miki kaya,ki barshi yaci kansa shi daya,ya
Allah.
..ina rogonka ka danqara masa
soyayyarta azababbiya naga ya zaiyi da wannan zafin kan da zafin zuciyar" ya fadi maganar yana wucewa gaba abinsa.

Ji yayi kamar ya tashi ya shago sajjad ya nannausheshi,adduar da yayi masan yazun jinta yayi bata da maraba da mutumin daya rogar maka saukar ajalinka a kurkusa. Shima sajjad din yasan me ya aikata,don haka ya dauki fadeela cak suka fice da sassarfa daga sashen,yana jiyo muryarsa yana sake kira masa wani alkaba'in na zurmawa soyayya.

Sumar kansa ya shafa yana furzar da iska,zuciyarsa tana gogarin bashi nutsuwa ta hanyar jaddada masa babu ta yadda zaiyi a yanzun yaso wata diya mace, babu wata d'iya mace da zata iya galabar tsallakawa takai ga zuciyarsa,an gama yiwa ruhi da zuciyarsa barna,bazai kuma sake bari hakan ta faru ba,kai kwata kwata ma yanajin cewa a yanzun babu wani abu waishi SOYAYYA dake existing,zaifi kyau a canza masa suna da sha'awa ko son zuciya.

A lokacin ne ya samu damar shiga toilet yayi wanka,duk yadda yaso ga yaci jerin abincin alfarmar da Jacob ya saba dafawa ha ajiye masa amma yau ya kasa dora komai saman harshensa,kukan da fadeela keta faman yi a kwanakin ya tsaye masa a rai,yau ta bugaci wani abu da yakejin bazai taba iya bata shi ba,sai kuma rashin walwalar nadeeya,duk gidan sun maidashi wani so silent, damuwa ce fal cikin zuciyarsa,wadda har sai data taba kuzarinsa.
Chapter 81 · 0% Book details