← Book details Tabarmar Kashi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 171

Sashe 29

Tabarmar Kashi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zafafa🫶🔥
[8/17, 6:49 PM] +234 806 578 4295: *H U G U M A*

*_TABARMAR ƘASHI_*💔
https://arewabooks.com/u/huguma

Page 25

Wasu hawaye masu zafi taji sun cika mata idanu,qarshen cin zarafi yayi mata shi,FYADE ai ba qanqanuwar kalma bace da furtata zai zama abu me sauqi har haka ba,kadan daga aikinsu me yake nufi kenan da ita?,kawai saita kasa riqe hawayenta,ta barsu suka silalo ko zata samu ganin gabanta da kyau,tun bayan abinda adam yayi mata.....ba wani mahaluqin daya taba mata kalma me tsananin daci zafi da qasqantarwa irin haka ba,sai ta miqe kawai a gaggauce tana fita a kitchen din,har ranta tana jin tsanar shi kansa kitchen din,da kuma dalilin daya kawota.

Tana fitowa a hanya suka hadu da sameera,ta tareta da yanayi ya dan rudani kadan

"Ance kitchen kika tafi,inata qoqarin tsaidaki saboda time ne na shigan sir kitchen din yayi lunch,karkije a samu matsala"

"Ba'a samu ba,gashi na dawo" ta bawa sameera amsa a taqaice tana wuceta.

Toilet dinta ta fada tana sake rage qwallar takaicinsa data sake taruwar mata,sai data kusan minti goma kafin tayi controlling kanta,ta daura alwala ta fito ta tayar da sallah,tana sake jin tsanarsa qwarai a ranta,tana kuma sake tabbatarwa da kanta shi din wani irin mutum ne mara iya mu'amala da gautsin harshe.

Ko bayan ta idar zamanta taci gaba dayi saman abun sallar,duk da akwai sauran ayyukan da takeson gamasu a yau din,a haka miss sameera ta nemi izinin shigowa.

"Boss ne yake neman izinin ganinki" tunda tace boss ta gama fahimtar waye,abun sai ya girmame mata,dr Ahmed da kansa yafi qarfin neman izini wai don zai shigo office dinta,da sauri ta tashi saman abun sallar tana dubanta

"Yafi qarfin neman izini miss sameera,maza bude masa qofa" saita juya a gaggauce tana murmushi,tabbas sãhaar din batasan waye boss ba,da batayi mamaki ba don ya nemi izinin shigowa ba.

Cike da tarin haiba kwarjini da kuma kamalarsa yayi sallama,saita miqe tsaye tana masa sannu da zuwa tare da nuna masa gurin zama,da kanta ta bude qawataccen fridge din dake office din ta ciro masa ruwa da lemo masu matsakaitan sanyi,kasancewar ita dinma ba mai yawan shan abu me sanyi bace

"Na gode sosai diyata" ya fada yana yaba dattakonta,da yadda take da girmama manya tare da sanin kimarsu. Ita kunyar godiyar ne ya kamata,tana neman gurin zama yace da ita

"Ya ayyukan?,ina fatan kina jin dadin aiki da yayan naki?" Qaramin murmushi ta kuma saki,kanta a qasa tace

"Alhamdulillah abba"

"Ma sha Allah,na sanshi sarai,wasu lokutan bashi da kirki,yana da zafin zuciya,amma kuma yana da tausayi" kai ta jinjina tana kokwanton tausayin da Dr yace toufeeq yana dashi.

Ruwa kadan yasha,sanann suka fara tattaunawa kan sabbin ci gaban da aka samu cikin company din,daga bisani yace

"Sajjad ya gayamin,akwai kundin da kika bayar,ya gamsu da ayyukan ciki,ya kuma yimin bayani,amma har yanzu banga an aiwatar da komai ba"

"Tuni na miqa su ga office din ceo muna jiran sign dinsa"

"Kina da copy dinsa a gurinki?" Miqewa tayi a nutse,ta buda computer ta kawo masa gabansa. A nutse ya dinga karanta komai,

"Ma sha Allah,ma sha Allah" kawai bakinsa yake furtawa,baiko kai ga qarasawa ba ya dago kai

"Akwai ideas masu kyau da muhimmanci a nan,zaifi kyau a saka hannun da wuri,inaji a jikina za'a samu cimma gaci yadda akeso" sosai taji dadin yadda ya yaba mata din,har ta rakashi yana mata addu'a gami da sanya mata albarka.

Lokacin tashi yana cika ta baro office dinta,kai tsaye ta sauka zuwa qasa,tana daga cikin sahun farko na ma'aikatan da suka baro office dinsu,don haka gurin ba cikowar masu daukan ababen hawansu. Hakan dama takeso,tayi ta fice kafin wancan mayataccen ya isketa,sam baya yin fushi ko kuma zuciya game da dukkan abinda zata gaya masa.

Sau uku tana qoqarin kunna motar amma taqi kawo wuta gaba daya,abun ya bata mamaki ya kuma daure mata kai,tunda dai tasan lafiya lafiya ta tafi ta barta. Ta gwada dukkan wata dabara amma taqi,dole ta fito ta rufe motar,ta fidda wayarta tana gwada kiran mechanic dinsu,tana masa bayanin abinda ya faru,tare da kwatanta masa kamfanin,kamfanin ba wani boyayye bane,don haka yace yana zuwa nan da minti arba'in zuwa awa daya.

Sauya akalar kiran nata tayi zuwa ga number afifa,bugu biyu ta daga

"Bestie,kin tashi daga aiki ne?"

"A'ah,sai sixs,wani abu ne?" Lumshe idanunta tayi cikin damuwa

"Motana yaqi tashi,baisan meye damuwarta ba,kuma banason fita neman abun hawa na haya"

"Subhanallahi,to ba damuwa,bari zan iso kamar nan da awa daya saina daukeki,kinga na rage time din tashin kada ya zamana na fito da wuri"

"Okay,thanks" ta fada tana tsinke kiran. Da isowar mechanic din dana afifa tana sanya ran yayi lokaci daya,ta dubi agogon hannunta sannan ta sauke tana duban building din,ma'aikata sunata fitowa kowa yana kama gabansa,batason komawa can saman nan,don haka ta yanke ta wuce executive garden dake kamfanin ta zauna ta jirasu a can,da wannan shawarar ta karkata akalarta zuwa can din.

A nutse ta durfafi gurin,yanayin wajen yana sake burgeta,da alama yana samun kyakkyawar kulawa. Sanya qafafunta kenan sautin muryarsa shine abu na farko daya fara ziyartar kunnenta,kafin daga bisani idanunta su sauka a kansa,dai dai lokacin da shima dan motsin da yaji ya sakashi daga kai,idanunsu suka sarqe waje daya,yana daga tsaye hannunsa guda daya cikin aljihunsa yana magana da wasu mutum biyu da bata gane ko su waye ba,saboda suna dan gaba kadan dashi.

Qaramin tsakin da batasan meye dalilin yinsa ba ta saki,kawai dai tasan taji haushin ganinsa a wajen,ya kuma bata mata budget din da tayi na sakewa ta zauna a wajen ta jirayi afifa,saita juya a nutse tana fita a wajen.

Dif maganar da yakeyi ta dauke,ya lumshe idanunsa a nutse yana jin wani irin bacin rai na taso masa,idan har dai dai kunnuwansa suka jiye masa,sautin tsaki ya jiyo,wanda yaga alamun fitarsa daga dan qaramin bakinta data turoshi gaba lokacin da take hada sautukan tsakin.

Ransa ne yaji yayi wani mugun baci,tunda yake zai iya cewa ba wata diya mace data taba masa tsaki,tsakinma mara dalili,haka siddan saboda ganin araharsa?,nan take yaji bazai iya tolerating ba,don ya gama fahimtar kamar tana daukan kanta wani abu,tana da ji da kanta over.

Sam basu lura da barin wajen yakeyi ba har sai da yakai qofar fita,cikin daga murya sajjad yace

"Hi man......ya kamata mu gama kafin mu wuce fa"

"One minute" kawai ya iya ce masa,idanunsa na biye da ita,duk da cewa ta danyi masa nisa kadan. Sai ya qara yawan takunsa,mutum ne ingarma me yawan kuzari,ga kuma tsaho da yake dashi,wannan ya taimaka masa nan da nan ya rage tazarar dake tsakaninsu,wanda sam bata sani ba,ta yanke shawarar ta buda office dinta kawai ta zauna ta jirayesu acan,ko hawa na nawa ne ta gwammace ta koma ta jirasu,akan dai ta sake ganin fuskarsa.

Hankali kwance elevator ta bude mata ta shige,tana shirin komawa ta rufe shima ya shigo,ta koma ruf ta rufe sannan ta fara aikin haurawa dasu zuwa saman.

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070

VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k

*Al'ummar NIJER ku kira wannan number don yin naku pyment din*

+22799643131

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥

*H U G U M A*

*_TABARMAR ƘASHI_*💔

Page 26

Haka kawai taji gabanta yayi mummunar faduwa,kowanne sashe na jikinta yayi sanyi saboda yadda ya zuba mata mayatattun idanunsa,yana jifanta da kallon tsana. Tayi tunanin zata iya jurewa kallonsa kamar yadda ya ritsata da nasa idanun,amma tun ba'a yi nisan zango ba taji ta gaza dauke nauyin zagayyun idanunsan nan masu tsananin haske,kamar ba idanun namiji ba. Gaba daya sai ta jita kamar wadda aka nannade aka jefa cikin wani keji,kamar an sanya igiya an daureta,ta dinga fatan na'urar ta sauketa da inda ta umarceta tayi ta fice ta bashi guri.

Saidai kuma suna isa floor din ya matsa gurin madannan ya sake bata direction na dawowa dasu floor din qasa,a sannan ta waiwayo ta sake dubansa da fararen idanunta karo na biyu,still har yanzu ita yake kalla,kallon dake sake bayyana fushin dake kwance a zuciyarsa. Sake janye idanun nata tayi ta maida dubanta wani wajen,gaba daya kallon da yake mata ya wuce qa'idar da jarumtarta zata iya dauka,uwa uba kuma shirin rikicewa takeyi gaba daya,saboda yadda qamshinsa yake sake cika elevator din. Tattara hankalinta tayi tana jiran jin sun isa,ta riga ta gama ayyanawa a ranta suna isa zatayi hanzarin ficewa,don ta fuskanci kamar ya shirya tayita yawo dasu daga sama zuwa qasa,can can qasan ranta tana tuna tsakin data sakar masa.

Da wani irin hanzari ta nufi qofar da zummar fita,amma kuma kafin ta isa har ya maida qofar ya rufe,ya kuma sake sakata ta lula sama dasu. Wannan karon tsaiwa tayi daga bakin qofar yana lumshe idonta,ranta itama ya soma baci da rainin hankalinsa,ta yaya zayazo ya sameta a waje ya kuma dinga mata wasa hankali?,na meye?,zata tsaya gab da qofa,zataga gudun ruwansa,idan ta fita yasa qarin tuwo ya dawo da ita.

Duk yadda taci buri kuwa suna isa sai gashi tsaye bakin qofar,abun yayi matuqar bata mamaki,batasan wanne irin zafin nama gareshi ba

"Excuse me mana,fita zanyi" ta fada da siririyar lallausar muryarta

"Wa kika yiwa tsaki?" Ya jefe mata tambayar kansa tsaye cikin izza da qasaitarsa kamar wani basarake,duk da yadda yayi mata matuqar kwarjini,amma motsawar tata izzar ta bata qwarin gwiwar amsashi

"Da wanda ya tsargu" ta amsa masa tana qoqarin kaucewa qwayar idanunsa,don har yanzu tana cike da takaicin abinda yayi mata dazu a kitchen.

"Ko?" Ya fadi wani miskilin murmushin gefen baki na subuce masa,duk da cewa ba murmushi bane na kyautatawa ko jin dadi,amma wani irin sirrin taccen kyau ya bayyana muraran kan fuskarsa,fuskarta yake duba,yanason gano daga inda ta samo wannan qwarin gwiwar tsaiwa ta gwada masa rashin kunya,yayi imanin batasan wane shi ba,amma a yadda ya lura akwai quruciya sosai tattare da ita,qaramin abu kawai zaiyi da zai bata zazzafan warning,ta yadda ba zata sake marmarin maida masa martanin magana ba.
Chapter 29 · 0% Book details