← Book details Tabarmar Kashi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 161 OF 171

Sashe 161

Tabarmar Kashi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tunda uwarta ta haifeta bata taba ganin tashin hankali tozarta da abun kunya irin na yau ba,sanda take tafiya zuwa dakinta jiri ne yake angizata daga gaba zuwa baya. Meenal tana biye da ita itama cikin kukan,kukan nata da yake da nasaba da hango rasa toufeeq rashi na har abada. Yadda gaba daya parlor din ya rude ya birkice ya sanya dole maji ta gayyato juriya da dakiya irin ta uwa ta azawa zuciyarta da ruhinta, don dukkansu a yanzu suna bugatar wanda zai jagoranci tunaninsu ya kwantar musu da hankali

"Dauko mota Muhammad mu kaishi asibiti, nadeeya kira baaba rabi tazo takai sãahar daki ta huta, ki cire damuwa daga ranki, jarrabawa ce mun ganta kuma mun cinyeta a yanzun in sha Allah alhamdulillah, Allah dai yayi nufin sai mun gani ne kawai ki cire damuwa saboda abinda yake jikinki" dai dai toufeea ya dawo a gaggauce, ya kama Dr jarma wanda yaketa ambaton sunan Allah sanoda vadda numfashinsa da girjinsa suka rige va fita dashi zuwa harabar gidan. Sai da maji taga baaba ramatu ta kama hannun sãahar sun wuce daki da ita,tace fadeela ma ta zauna gudun shiga tunani sannan suka wuce asibitin.

Falon ya zamana babu kowa,hajiya qarama aneesa hajiya mansura da labiba sune suka rage.

Wata shu'umar dariya mansura ta saki, ta hada hannuwanta dukka biyun ta tafasu da kyau, tayi taku biyu ta tsaya gaban hajiya garama

"Tabbas abinda malam ya fada haka yake, faduwa guda biyun tawace da taki, nasara kuwa ta maji ce,a yau na tsinciki kaina banji takaici ko baqincikin yin nasarar wani ba..... Fauziyya kin dauka kai kadai ce kika iya shu'umanci? kin dauka ke daya aka yankewa tuggu cibiya a gabanki? kina tunanin zan zauna ne haka. sasakai kara zube ba tare da na tanadi mkaman gare dangi ba? bayan na san wacece ke?,ai duk makahon da kaii vace ayi wasan jifa to ya taka dutse ne.….na rasa mijina kin rasa dan uwanki!"

"Kin tafka babbar asara mansura butulu" dariva ta kece da ita

"Ashe? da kunya a idanunki har kina da bakin kiran wani butulu? ,kawai butulu sama dake? wadda taci amanar dan uwanta? taci amanar 'ya'yan dan uwanta? tunda kikaci amanar maji to tabbas ba wanda ba zaki iya butulcewa ba gwara ni.....kishiya ce kome nayi a kanta hada miji mukayi"

"Ke da gamawa da duniya lafiya har abada!" Hajiya garama ta furta a birkice tana jin kamar qwaqwalwarta zata hautsine

"Ke kuma idan aka leqa wuta ba'a ganki ba garwashin wuta ne ya rufeki fauziyya!"

"Dalla malamai ku gara gaba,yanzun ba wata sauran alaqa tsakaninmu daku" haseena da duka wadan nan maganganun basa gabanta ta fadi, don abu daya ke damunta a yanzu,ta yaya zata samu toufeeq?.

"'Me kike ci na baka na zuba meenal ya'aqoub aji?, awanni kadanne kuma suka rage muku a gidan nan yadda kuma ban samu toufeeq ba kema ke dashi saidai a hoto" labiba ta fadi tana jin sassaucin tashin hankalin data shiga a dazun, saboda tayi imanin ita da meenal dukkansu sun rasashi kenan.

"Zo mu tafi mommy bakin alqalaminsu suma ya riga ya bushe musu" labiba ta fadi tana damgar hannun hajiya mansura suna ficewa daga falon. Dukkansu ita da labiban zucivar kowannensu cike take da tashin hankali, komai sunayi ne kawai saboda idanun haseena da hajiya garama,amma sunyi amanna watan fara sanin wahala a rayuwarsu ta kama.

Kuka meenal takeyi sosai tana biye da hajiya garam cikin fushi da fusata da kuma tashin hankali, bata damu ko kadan da zubar hawayen idanun hajiya qarama din ba

"'Ni duka bance kije ki aikata wannan abun ba,kinyi ne kawai saboda son ranki da biyan buqatarki,ni ba damuwa ta bane koma meye zai faru, kawai ni ki cikamin algawarin da kika daukarmin,ni toufeeq nakeso,na riga na tsarawa kaina da shi zanyi rayuwa" kalaman 'yar tata yayi mata tsauri da yawa, tana juyowa ta kwashe haseena din da mari

"Ban taba sanin baki da imani ba sai yanzu, kome da ake tuhumata akai fiye da rabi na aikata shine saboda jin dadin rayuwarki da kuma inganta rayuwar taki amma baki ganib..." Kafin ta rufe bakinta siraran yatsun haseena masu azabar zafi sun samu lafiyayyen muhalli akan fuskar hajiya garaman. Wani mugun shock ne ya shigeta har fitsari yana ballewa a wandonta,da gyar ta tattaro yawun bakinta ta hada kalaman

"Ni kika mara haseena ni uwarki da na dauki cikinki wata tara na haifeki?"

"To sai meye? don kece kika haifeni ai ba kece kika halicceni ba,ga mari ga tsinka jaka? ga duka ga rashin biyan bugata?, to tunda ke sauna ce kin kasa aiwatar da komai ni zan samawa kaina farincikin da kika gaza bani din" saita kewayeta kamar zafa bangaji kafadarta ta wuce dakinta da gudu gudu.

Sulalewa tayi ta zauna saman kujerar da tafi kusa da ita tana dafe da dukkam kuncinta guda biyu tana jinta kamar ba cikin duniya take ba. Tunda take a rayuwarta duk tashen gin jin maganarta taurin kai da* shaharar da tayi wajen iya garya da shirya makirci ko yayanta bata taba mari ba bare akai ga mahaifiya, sai gashi yau itace yarinyar data haifa,ta gwadawa gata fiye da kowa cikin duniya,taketa fadi tashin tara mata dukiyar da ko bayan ranta ba zata wulaganta ba,take ta yunqurin samar mata nagartaccen miji, yau itace ya shimfidawa fuskarta mari?.

Qarar jan luggage dinta ya sanya hajiya qarama din daga kai. Ta shirya abinta kamar yadda tazo cikin gananun kaya. Da sauri ta janye qafafunta wanda banda hakan tsaf zata murjesu tabi ta kansu ta miqe tana kiran sunanta

"Haseena baki da hankali ne? ina zaki haseena? wa kika sani?" Ta fada tana tarar gabanta cikin jin tsoron kada halayyarta ta tsananin fushi ta sanyata ta aikata abinda ba dai dai ba

"Dalla matsa ki bani guri,ni yanzu baki da amfani a gurina, toufeeq shine rayuwata, kuma na rasashi, tunda kuma na rasa shi a shirye nake na rasa komai nawa" ta fada tana jifanta da wani wulaqantaccen kallo sannan ta gogi kafadarta tana wucewa.

Tayi taga taga kamar zata fadi ta samu ta tsaya
kan gafarta, ta bude baki zata sake gwada yunqurin
tsaidata din sai sautin data sanyawa dukkan alert
massages na bankunanta ya fara tashi a jejjere. Da sauri ta miga hannu saman dan table din data ajjiye wayar dazu kafin ta fita tana dubawa, mamaki yana cikata na shigowar massages din a jejjere babu qaqqautawa.

"Na shiga uku......na lalace….meye haka?......kai jama'a
wayyo Allah na ku kawomin agaji….Zasu yasheni.......zasu talautani…..wayyo Allah wai ba kowa
ne a gidan" ta fada cikin budaddiyar murya tana kwasar hanya da mugun gudu tana fita daga sashenta.

Zafafabiyar
"HUGUMA*

_TABARMAR KASHI_

Book 02 Page 68

Dai dai lokacin da alert na qarshe ya shigo wayarta,wanda aka cire ragowar millin uku last amount da ya rage a bankinta, kuma qarshen abinda ta mallaka kenan duk duniya,don ta saida komai nata ta hade kudin cass cikin account dinta zata sake sabuwar order na dukkan shagunanta,har a ciki take sanya ran gyara da same bungasa plazas dinta da wuta tayi musu mugun ragargaza. Tsaiwa tayi cak a wajen,sai ta dafe kanta ta daga qafa da mugun gudu tana fitowa harabar gidan a birkice kamar wadda take da tabbacin barayin da sukayi mata aika aikar suna
tsaye a qofar gidan. Saidar tana gara daga qafarta wata muguwar hajijiya ta debeta ta watsar da ita,sai gata tayi d'ai d'ai warwas a qasa. Amma hakan dai bai hanata miga hannu tana son yin kururuwa ba, kururuwar da babu damar fitarta daga bakinta saboda karkacewar da bakin nata yayi,sai wan! kakkauran yawu data fara zubarwa ta gefen bakin nata.

Caaaa ma'aikatan gidan sukayo a kanta, sai suka rasa yadda zasuyi da ita,saboda sunga fitar masu gidan yanzu. Daga qarshe dai bayan kusan awa daya daya daga cikin masu aikinta tayi gundunbala ta shiga bedroom dinta ta dauko key din motarta. Acanne taci karo da kit na sarqoqin gold dinta rankacakaf data fitar dasu a dazun bayan dawowarsu da zummar zata saidasu saboda taji yadda kudinsu yayi daraja ta aikawa gawarta kudin dake dubai ta siya mata sabon design.
Key din motar kawai ta miga musu ta wuce sashen masu aikin gidan ta hada kayanta zakara ya bata sa'a ta falle, cikin zuciyarta tana fadin

"Allah ne yayi da rabona, muguwa kina samu amma ke kadai kike amfana,saidai mu mu qare ayi miki bauta" ( shawara a gareku masu ma'aikatan a gurin
Sana'a ko kasuwanci ki cikin gidajenku de sauransu,sanda mutum yake zaune qarqashinka yake maka hidima,a duk sanda Allah ya buda maka,kaima kayi goqarin buda masa ku taru duka kuyiwa Allah godiya,wannan shine abinda zai dawwamar da soyayyarka a zuciyar ma'aikatan ka,da wata iriyar mana ta gaske da zaiyi wuya a hada baki dasu a cutar da kai, ko suna ji suna gani su bari a cuceka, Allah ya bamu ikon kyautatawa dukkan wanda muke tare dashi ameen summa ameen).

Private hospital aka kaita kamar yadda sukasan duka iyalin gidan suna zuwa,babban asibiti ne da suke cazar kudi bana wasa ba,sanda aka isa asibitin da ita
likitan da ya fara dubata ya tabbatar zaiyi wuya bata
samu matsala ba,saboda jininta ya hau sosai, hakanan
barin jikinta ya daina aiki, daya barin ma ya tabu sosai
amfanin da zaiyi mata kadanne, duk wani abu dake daya
sashenma totally ya daina amfani, kama daga idonta
kunnenta hannu qafa da sauransu
Sun tsaya anyi mata komai da komai ba don
halinta da dabi' arta ba. Bayan komai ya kammala akayi total na kudin asibitin kwanciyar da zatayi da sauran bill na abubuwan da zata ci. Elyas na daya daga cikin wadanda suka tallafa aka kawota,don toufeeg din bai fita da kowa ba,daga shi sai maji din sai Dr suka wuce dashi asibitin.

Bayan ya gama duba bili din wayarsa ya ciro yayi
kiran toufeeq,cikin rusunawa yayi masa bayani

"'Kana jina elyas?"

"Eh sir"

"Sisina daga abinda na mallaka da kuma abinda
mahaifina ya mallaka ban amince ka cire ka biya komai
ba,ku batta da su tana da gwarin qwiwar yiwa kanta

komai,ka jini?"

Kai ya gyada cike da biyayya

"'Yes sir" sauke wayar yayi daga kunnensa yana furzar da huci daga bakinsa,shi kansa baisan wanne kalar hukunci ne va dace da ita ba.
Chapter 161 · 0% Book details