← Book details Tabarmar Kashi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 171

Sashe 79

Tabarmar Kashi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"To bama dole kiyi kumatu ba? don Allah ki gani,da safen nan an tasheki ke daya kina cin kayan dadi ke kadai abinki" dariya kawai suka saka mata

"'Ke da baki tashi da wuri waye zai rage miki?"
Saahar ta fada tana goge hannun fadeela da tissue. Hamma nadeeya tayi

"Yanzunma wallahi yaa moha ne ya tasheni don Allah coffe zaki taimaka ki bani na kai masa da sauri,kada yace ya fasa sha nayi jinkiri " kai sãahar ta daga tadan kalli nadeeya tana mamaki a ranta,don anyi jinkiri kawai sai mutum yace ya fasa shan abu?

"Indai sauri kikeyi to yanxun kam sai milk tea wanda na dafawa faddee,babu coffee"

RA
"Ya salam....a zubamin nayi shahada,idan kuma nasha maruka to kin jawomin tare zamuyi jinya" ta fada tana zare ido.

Miqewa sãahar tayi cikin fuskar mamaki

"Maruka kuma? haba dai"

"Allah ba komai bane wajen yaa moha,yaushe ya daina ne? tafiyata karatu fa" maganar sai tadan daure mata kai,to amma batason tsawaitawa tunda ba huruminta bane,don haka fadeelan na biye da ita tana bata labarin tsaurin yaa moha din har suka isa kitchen, itadai tana saurarenta harta gama zuba milk tea din a wani siririn qawataccen silver flask, qamshin flavour din da yakeyi da su cardamom gaba daya ya cika kitchen din

"Yawuna ya tsinke Allah,wannan wanne irin tea ne? don Allah anty N ki ragemin" dariya nadeeyan ta bata,yadda tayi maganar da gaske cikin marairaicewa

"Ya rage miki,bana zaton zai iya shanyewa" dukka ta zaro fararen idanunta waje

"Wa? niii?yaa moha din zance ya ragemin abu?,idan kin ganni a lahira kaini akai" da mamaki ta juyo tana dubanta

"Wanne irin mutum ne shikam haka?"

Abinda takeson cewa kenan,amma saita maida maganarta ta hadiye. Idan ta saba yin hakan da nata yayyun,nan din ai ba gidansu bane,kowa da irin tsarinsa da nasa ra'ayin,so ba huruminta bane.

Yana amsa waya ya fito daga dakinsa,yayi fes cikin wasu fararen kayan still, da alama zabinsa kenan farin abu ko kuma abu me haske,musamman idan ka duba vanavin furniture din dake qawataccen falonsa. Da ido ya tsire tea din har ya kammala wayar,ya kashe ta ya ajjiye wayar a gefe yana hada hannayensa guri daya,kafin ya maida dubansa ga nadeeya

"Me ya hau kanki ne?,wannan yanzu coffee ne?ko dama inashan tea da madara?" Tasan dama tsaf hakan zai iya faruwa,don haka ta sake maida fuskarta kalar tausayi

"Ba wancan yaaya...amma please kasha wannan,idan baiyi ba Allah na rantse, kayimin hukunci"

"Ya isa,Gate out" ya fada calmly,da sassarfa ta juya ta fice tana dafe qirjinta saboda arzigin data auna yau bata shiga ukunsa ba.

Kaman bazai sha ba kamar dai jiya,sai qamshin ya buwayi hancinsa,a daqile ya dauki cup din idanunsa akan TV ya kurba. Kasa wassafa komai yayi a ransa, saboda qamshi da gardin madarar daya kai masa ko ina,karon farko bayan shekaru masu dama ya samu tea din da yafi masa coffe dadi.
_tom,nikam nace tun yanzu MR JARMA?,WAI YA HADUWAR ZATA KAYA NE? KOWA NA YABON DAN UWANSA BA TARE DA YASAN WAYE SHI BA.MUJE ZUWA_
*DON ALFARMAR ANNABI MUHAMMADU
ME FITARWA KIYI HAKURI KIBAR MANA
KAYANMU*

*HUGUMA*

* TABARMAR KASHI *

Page 70

. Baisan ya akayi ba,shidai ya tsinci hannunsa riqe da empty cup,ya maida a hankali ya ajjiye yana tunanin rabonsa da shan madara a tea,sai gashi yanzu ya shanye ta tsaf,har yana jin buqatar qarin wani tea din,to amma bayason ya aika din,zaidai binciki yadda ake sarrafashi.

*********A tsaye suke suna fuskantar juna,duk da cewa ita din bashi take kalla ba hakanan akwai 'yar tazara a tsakaninsu. Irin kallon da yake mata kadai zai gaya maka zallar yadda zuciyarsa ta narke da soyayyarta

"Zan tafi.don Allah ina roon kici gaba da bani dama"

"Allah ya kiyaye ka gaida gida" ta fada tana
Juyawa,zuciyarta a quntace saboda abubuwa biyu,na farko tasa yasa an tilastata ta bashi damar zuwa zance gidan mutane,taso ta furje amma Dr girema ya kirata da kansa,yayi masa irin fadan da bai taba mata irinsa ba,sannan kuma ya tabbatar mata wa'adin sati biyu kacal ke gareta,ruwanta ta bashi dama ta bude masa zuciyarta ta fadada tunaninta su fahimci juna,ruwanta ne kuma taqi. Maganganun dr sun daga mata hankali sosai,don bai taba mata magana da salon fada da bacin rai irin haka ba.

•Ci gaba da kallonta mahmud yayi har zuwa sanda ta bacewa ganinsa,ya sauke hannunsa yana furzar da iska daga bakinsa,sannan ya juya yana nufar inda gurd dinsa da ya masa rakiya yake. Hakan yayi dai dai da shigowarsa ta qaramar qofar gidan,yana sanye da wani lallausan yadi da aka yiwa dinkin african kaftan na maza,fuskarsa ta cika da wani irin kwarjini,elyas da jibril na biye dashi.

Dawowarsu kenan daga masallacin layinsu wansa aka gudanar sa taro da akanv duk sanda aka samu dama,kusan duk wan ke muqami ko babba a unguwar yana halartar taron. Lokaci guda idanunsu suka sarge ana juna,murmushi mahmud ya saki cikin hanzar ya maida akalarsa zuwa gabansa

"Sir" ya furta yana saluting nashi cikin murmushi,fuskar toufeeg ta motsa kadan alamun murmushin shina yayi, ya migawa mahmud din hannu
"Barka da yamma sir"

"Barka,kana lafiya?"

"Lafiya alhamdulillah,kwana da yawa sir,tun a
Singapore,ban zaci zamu sake haduwa nan kusa ba"

"Gashi Allah ya nufi hakan" ya fadi yana maida hannunsa ga aljihunsa fuskarsa a dan sake ba kamar yadda take ba

"'Gaskiya ne,ina fatan zamu sake haduwa anan kurkusa"

"In sha Allah" ya fada yana gyada kanshi

"Nazo ne wajen qanwata da kuka riqemin a gidanku"

"A nan din?" Ya fadi cikin mamaki

"Yes sir" ya fada yana waiwaya hadi da
duban inda sãahar ta tsaya a dazun. A ran
toufeeq din ya danji mamaki,me kuma zaya
kawo qanwar mahmud gana gidan?,ko cikin
qawayen nadeeya ne?,shine tunanin da yafi
kwanta masa

"She's my soulmate,inata qoqarin ganin mun
dai daita ne,she's my wife to be in sha Allah"
sake daurewa kansa yayi,har ya kalla ainihin
sashen cikin gidan ba tare da ya shirya ba,sai
ya gyada kai yana sake bashi hannu

"Allah ya taimaka" ya fadi ya zame hannunsa
bayan sunyi musabaha yayi ciki.
Dab da zai shiga sashensa nadeeya ta
fito tana laluben sãahar sabida shurun da taji
tun bayan fitarta,tayi masa sannu da zuwa
ya amsa yana tambayar fadeela,sai tace
masa tayi bacci yanzun nan bayan ta gana
jiran dawowarsa,yana wucewa ciki yana gaya mata ta kawo masa cottee nan da kamar awa daya, murmushi ta saki gain yadda ta zama addicted da coffee din nanny,shi da baya cin komai a hannun kowa. Har ya zarta ya dawo da baya yana tambayarta waye yayi bago a gidan?

"Nanny N ce,ko ba mahmud ba?" Kai ya jinjina,sai kuma yayi gaba ba tare da ya sake cewa komai ba,amma can qasan ransa cike yake da mamaki,mahmud ke son nanny din gidansa?,abun sai yaji baiyi making sense ba,so amma shi din ba mai damuwa da shiga rayuwar wasu bane,don haka tun bai isa sashensa ba ya tattara lamarin ya watsar.

Sai daya gama komai ya sauya kayan jikinsa zuwa wata shirt,v neck ne daya fidda sirrin ginannen girjinsa me yawan gargasa,sai dogon wandon joggers pants,qafarsa saye da socks da baya rabo da ita yawancin lokuta.

Farfajiya ce ta musamman da akayi mata gofa daga cikin falonsa, wanda aka qawatata da wasu irin sofas masu retractable canopy a samansu,wanda zasu baka daman zama comfortable kamar kana kan gado,samansu ya zauna yayi relaxing sosai sannan ya kunna system dinsa bayan ya duba lokaci ya tabbatar lokacin da suka sanva don yin meeting dinsu through video call da directors na companies dinsa dake gasashe daban daban lokacin ya cika,ya bude system din ya saita komai sannan yayi group call in general.

Ba jimawa kusan kowa ya daga din,mutanene da sukasan muhimmancin lokaci da kuma na aikinsu,don haka komai suna yinsa ne akan lokacin da aka tsara zaa yi din. Cikin salo da qwarewa da sanin makamar aiki suke tattaunawa,da zallar qwarewa a harshensa na furta kalmomin yaren turanci,a haka suka cinye awa guda cif,wanda basu qara ba kuma basu rage ba aka tsaida taron,suka sanya wani lokacin da zasu sake haduwa su tattauna.

Sake zama yayi saman sosai saman sofa din,yana gyara rumfar dake saman sofa din. A yanzun yana jin aminci da nutsuwa sosai akan kasuwancinsa,dukka directors dinsa amintattu ne,ya tabbatar koda babu shi zasu iya gudanar da kamfanin fiye ma da yadda zaiyi.

Wayarsa ya ciro ya lalubi number nadeeya,bugu daya ta daga

"Yaa gani nan,kana ta baya ne?"

"Yeah be hurry"

"Okay tom" ta amsa masa,tana maida dubanta kan säahar dake hada coffe din zata dora masa

"Don Allah yafi na ko yaushe,zan tambayi wani abune, inaso a bani da wuri,kinsan yaa moha shi da girki two and one ne" murmushi tayi tana girgiza kai,tuni ta fahimci hakan al,yanason laflyayyen abincihakanan baya shiri da yunwa.

Tun kafin ya kashe kiran da ya yiwa nadeeyan yaga kira nata shigowa wayar tasa baisan number din ba bashi da niyyar picking,saidai yana gogarin katse kiran nadeeva din kiran ya shigo ya daga lokaci guda ba tare da ya shirya ba,dai dai lokacin kuma true caller dinsa ya nuna masa sunan me kiran AMEESHA!.

lya sunan kawai ya haifar da wani irin bala'i cikin zuciyarsa,lokacin da sautin muryarta kuma ya baqunci kunnensa sai ya ja fikinsa ya sauko daga saman sofa din yayi tsaye,kowacce jijiya ta jikinsa tana miqewa

"Ina fatan kana lafiya,babu wata doguwar gaisuwa,don na tabbatar ba amsamin zakayi ba.....inason naga 'yata,inason a bani lokaci nazo na dauketa tayimin hutu,tunda nasan zuwa sati me zuwa zasu fara exam,upper kuma sun gama..

"'Stop!" Ya tsaidata a tsawace, yanajin wani abu na masa tururi tun daga zuciyarsa zuwa saman fuskarsa

"Lokaci na farko kuma na qarshe da zanyi warning dinki,ki cire a ranki cewa kin taba haihuwa da toufeeq jarma,ki cire a ranki cewa kina da 'ya a duniya tare dani,wannan shine gargadina gareki" yayi maganar yana nuna gabansa cikin wani irin fushi da deepness a cikin muryarsa

"Ta yaya? ka taba ganin an raba uwa da
'yarta?,laifin dana aikata tsakanina da ubangiji na ne,so bai shafi alaqata da dangantakata da

'yata ba,inata kawaici,inata dannewa,ina tsoro da fargabar kiranka,for what! fadeela yata ce, kuma har abada ba'a taba canzawa tuwo suna"
Chapter 79 · 0% Book details