← Book details Tabarmar Kashi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 156 OF 171

Sashe 156

Tabarmar Kashi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kamar zuciyarta zatayi tsalle ta fito haka taji,ga maji ga mahmud again ga kuma toufeeg, toufeeq din da sannu sannu take kallo yana komawa qarqashin iko da mulkin maji din ta ruwan sanyi,sai ta girgiza kai,wannan babbar asara ce da tabewa a gareta, ba zata taba yarda wannan abu da ya fara afkuwa yaci gaba da wanzuwa a haka ba.

Tana wani shan qamshi ta shigo dakin, ta samu waje ta zauna Dr mahmud na tambayar ta fito

“Eh, ai naga ba kasafai kuka fiyawa tunawa da kun aje mutum a dakin ba" dire cup din hannunta maji tayi ba tare data dubi sashenta. Ta shirya sauya taku don haka ta hadiye wani abu da ya tsaya mata a wuya tace

"Barka da safiya matar yaaya" wani kallo maji ta ajewa hajiya garama, a hankali ta sakarwa hajiya qarama din murmushi, a kallo daya tak ta fahimci inda maganar ta dosa

"Barkanki fauziyya* ta smisa mata a taqsics taria barys dubanta daga kanta.

Duk yadda toufeed yasi controlling carisa gaidata don ya sake binneta ya pra isovar fariar da /5 gayawa duniya wace ita, da fiddata a rayanarsa fitsrea ta har abada da kuma sarin hukuncin da yay imani sal yali kowanne hukunci yi mata cio a rayura sai ya kasa.
Tsar ya mique abinsa, yanata cocarin had ye bein fan dake taso masa a duk sadda ya kalli fuskar ha, ja garama, baya ga amneesha itace mutum ta biyu a durija da tayi masa abinda zai koma ga manaliccinsa da tabonsa.

"Zuwa nayi na gaya maka inason na koma gida,zan yank. ticket zuw anjima in sha Allah" hajya carama ta fada tana hadiye wani abu me daci da ya tsaya mata a wuya,ciwo kan ciwo,duka kan duka,yadda toufeed yayi watsin ruwan tsarki da ita ta karanci hakan. Tayi laluben duniya ta gano wanne laifi ta aika masa data cancandl yayi mata wannian rashin arzigin a matsayinta na wra kuma uwar goyo a gareshi?. Abu daya zuciyarta keta nanata mata,sãahar ce kawai ta shiga tsakaninsu, ita ta avatar da kornai,shi yasa batajin zata sassauta miata. duk randa ta tashi miga hukuntata,sai ta san ya yarinyar tayi dana sanin saninta a rayuwa,sai ta saryata ta zama izina ga kowacce diya mace dare shirin sake shiga rayuwar toufeeq din,ciki harda uwar data haifesa

_uhmm, kifi na ganinka me jar koma_

"Ki gara haquri duka saura kwanaki biyar mu wuce gaba daya har da ita fadeelan,zan saka a yau din a duba mana ticket da zai maidamu gida lokaci daya" sai data hadiye wani abu a gasan ranta sannan ta dauke dubanta ta mayar ga yayanta

"Yaaya, vanzu lalacewata yakai toufeeq ya wuce ba tare da ya gaidani ba?, hakan ba 'yar manuniya bace ga matarsa tayimin duk wani diban albarka da taga dama?" Dan dubanta kadan maji tayi, sai ta mige a nutse ta fice tabar musu dakin. Cikin ranta takejin indai toufeeq din bai gaidata ba bai kyauta ba da gaske, koba komai ganwar uba uwa ce komai lalacewarta ita da Dr din duka ba wanda ya lura da hakan. Reception ta wuce tana fidda wayarta ta kirashi tace ya sameta a can.

Ba jimawa ya taddata, ta nuna masa guri ya zauna

"Moha ban zaci samun dabi'ar raina na gaba daga gareka ba,ko meye a tsakanina da fauziyya ba huruminku bane wannan wani abu ne dava shafemu,me yasa baka gaida fauziyya ba?" Qas yayi da kansa, ya rasa wacce amsa zaya bata, ya sani ba Dr ba,ko ita da yayi imanin tasan halinta ciki da waje sai ta girgiza idan taji abinda hajiya qaraman ta aikatawa jininta gudar jikarta, yanzun kuma bayason yacewa kowa komai,so yake su isa gida ya gabatar da komai da hujja

"Bazan iya gaidata bane maji, kiyimin afuwa" ya furta a hankali vana daga idanunsa zuwa kan majin. Kafeshi tayi da kallo tana mamakin yadda tashi guda kamanninsa da launin idanunsa suka sauya, idan ma idanunta sun gane mata dai dai harda kwanciyar hawaye a qasansu.

Zafafabiyar

"HUGUMA*

_TABARMAR KASHI*

Book 02 Page 63

"Me yasa Mohammed?" Ta jefa masa tambayar a mamakance tana karanto tsantsar duhun bacin ran dake qasan zuciyarsa, tana son karanto zuciyarsa kai tsaye, inn karatun da cikakkiyar uwar da tasan abinda takey, takewa yaron cikinta komai girmansa. Dauke dubansa yay ya maida gete ransa yana soyewa

"Zakiji maji a gaba, kiyimin afwa" shuru dukkansu sukayi shi da ita,jilkinta ya bata tabbas akwar wani gagarumin abu da ya faru,duk da ba'a shaidar dan yau amma ita din tayi amanna da Muhammad din d'ari bisa d'ari

"Shikenan,Allah ya rufa asiri" ta fada a sanyaye

"Ameen" ya amsa. Har ya miqe tace

"Ka dauki matarka ku wuce zan saki dakin dana Kama din tunda babu amfani, ruwanka ka taimaki likitocin Kan taimakon da sukayi muku don ku samu ganin diyoyinku, ruwanka kuma ka wargaza aikinsu" sai a sannan yaji kunya ta kamashi,yasa hannu ya shafi lallausar sumar kansa yana murmushi cike da jin kunya

"Allah ya saka da alkhairi ya qara girma". Kai kawai ta girgiza bayan wucewarsa, har ranta tana jin wani farinciki yana saukar mata,nutsuwa tana gauraye rayuwarta,ta tuna da darensu na jiya ita da Dr jarma din, komai nashi dare zuciyarta ya koma sabo. Yadda a ajiyan ya dinga bayyana mata bazai taba samun wata mace da zata maye masa gurbinta ba Itama tayr imanin hakanne a tata zuciyar, kawai tana ja masa aji ne saboda ya sake sanin muhimmancinta, tabbas, dan adam abun toro ne, kuma sharrinsa abun neman tsar ne.

_ya ubangiji dukkan wanda zai nufemu da sharri cutatarwa ko quntatawa ga rayuwa da farincikinmu,ya rabbus samawati ka shagaltar dashi da damuwoyinsa,kayi mana tsakani da shi tsayin nisan tazarar da bata da yaka don hasken fuskar annabi muhammad S A W.

*******
Qwarya qwaryar honeymoon suka gudanar a
Germany din tsakanin toufeeq da saahar. Wata irin narkakkiyar soyayya ce me matugar tsayawa a ral ke huda zuciyar kowannensu. Wani irin so me matuqar qarfi da tasirin karya kowanne qarfi kafiya zati da turjiya na zuciya. Karon farko saahar din ta koma masa tamkar wata raqumi da akala,gaba daya ya sauke mata tunaninta,ya goge haddar kanta tasss!!' ,ya tsiyayar mata da man kai babu wani abu da yayi saura cikin zuciya ruhi da gangar jilkinta sai MUHAMMAD TAUFEEQ din.

Gwarzon namijin da cikin lokaci qalilan ya tabbatar mata da karin maganar nan ta hausawa da suke cewa MAZA SUNA SUKA TARA Kuma KOMAI LALACEWAR AL' UMMA AKWAI NA GARI. Yayi nasarar cisge kowanne mummunan tunani a ranta damuwa da bad memories dake damunta,ya maye gurbinsu da wata zazzatar qauna soyayya da zallar kulawa. Irin nau'in kulawar da ta sanya ta dinga hango tsananin wauta da sokonci da take kallon abinda adam ke mata a baya da sunan KULAWA,sam sam babu hadi tsakaninta da wanna kulawar ta ainihi da toufeeq yake nuna mata. Sassanyar soyayya me tafiya da imanin diya mace, duk kuwa da cewa bashi da damar shiga gonarsa yayi ban ruwa,amma a hakan daga ita har shi cikin wani irin aminci suke.

Baisan lya adadin sau nawa bakinsa ya furta godiya ga ubangiji ba,wato inda Ubangly bai cire ameesha daga rayuwarsa ba haka zai tabbata cikin quncin kurkuku da sunan AURE?,haka zai dawwama cikin mayaudariyar soyayyarta wadda bata da ma'ana ko gardi ko kadan?,cikin kwanakin KHADIJATU SAAHAR ta zame masa ALJANNARSA TA DUNIYA kamar yadda taci alwashi. Komai nata a nutse yake da want inn tsari me tsayawa a zuciyar namiji,tana da want irin Kula da takatsantsan a komai nata da sanya farincikinsa a gaban nata. Sun hadu sun kulle sun dinke sun zama cikakken abu guda.

_RAMIN KARYA kurarre ne_*

karfe uku na rana jirginsu ya sauka a filin sauka da tashin jiragen sama na mallam aminu kano dake garin kano. Jirgin da yayo dakon iyalin DR MAHMUD JARMA da kuma surukansa. Toufeeq da sahar,dr din da kansa
• da sarautar mata maji, afifa da hayatee dinta sajjad, sal kuma sister nadeeya da shalelensu fadeela, daga gefe kuma hajya qarama ce dake ankare da takun kowa,cikin ranta da zuciyarta kuma tana jin duk wannan scenes din ya qare tun a Germany,dukkansu sun gama cin gaajiyar soyayyarsu, a yanzu lokaci ne da kowa zai girbe hukuncin data tanadar masa.

Duk da haka babu abinda ta tsana irin idanunta su sauka akan maji da Dr, ko kuma säahar da toufeeq,basu ba hatta nadeeya ta sakawa ranta wannan karon ba zata sassauta mata ba,ita kanta afifa saita fita daga da'irar danginsu tunda ta silar saahar ta shiga family din.

lauranin masoyan guda biyu,zaka rantse da Allah saboda hutunsu da jin dadinsu yasa aka shirya tafiya garmany, daga toufeeq din har saahar sunyi wani irin kyau sunyi fresh cikin sati biyun da suka qara akan kwanakin da suka shirya tahowar. Saahar ya hade mata da yanayin cikinta wanda ya samu cikakkiyar kulawa da tabbacin zamansa dai dai bisa mahaifarta, ya kuma sake zuba mata wani irin kyau kamar 'yar sarkin aljannu.

Toufeeq kuwa zai iya cewa kafff! Tsahon rayuwarsa bai taba samun nutsuwa makamancin wannan a rayuwarsa ba,nutsuwa ta ainihi tun daga gangar jiki zuwa ruhi.

Ko da soyayya bata burgeka kana kallonsu zasu baka sha'awa ta kowacce fuska,sai nan nan yakeyi da sahar din tamkar sarauniyar matan duniya, o yaya ta motsa sar ya tambayeta

"Me kikeso ne moonbeam?" A sannan dumin jikinsa kadai take bugata,amma tana jin kunya da nauyin nuna masa,ta tsinci kanta a wani yanay na tsananin son kasancewa dashi. Sanda ta fahimci hakan hankalinta ya tashi,ba da wanda zata iya maganar dashi sai bestie dinta.

Dariya afifa tayi sosai kamar zata kifa akan dan matashin cikinta,har sai da saahar da zuciyarta yanzu yanzu zakaga tazo kusa tace da ita

"'Ki yarfani yadda kikaso,dama aini na kawo kaina ko?"

Rigo hannunta afifa tayi tana qoqarin saita kanta

"Ki yafemin Bestie, Allah bazan ya riqe dariyata bane, nasan wannan yanayin zar yiwa moha dadi qwaral,ashe akwai wanann lokacin zaizo?"

"Ban sani ba,sakeni"

"Zauna kiji" ta fada tana daidaita dariyarta,sannan ta zauna tana fuskantar saahar din.
Chapter 156 · 0% Book details