Sashe 163
Tabarmar Kashi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Suna gaban madubi yana busar mata da gashinta,wata sassanyar hira suke a madubin ta cikin qwayar idanuwansu ba tare da baki ya furta komai ba.
Dan garamin tsaki yaja gain yadda aketa neman izinin shigowa hallway din nasu ta garamar na'uarar dake magale a bedrooms dinsu. Cumb din hannunsa ya anivya zaro abayarsa ya zura yana fadin
"'Ina zuwa" ya juya a nutse ya fita.
Murmushi ta saki tana satar kallonsa har ya fice din,ta maida idanunta ta kulle tana jin yadda soyayyarsa keyin yadda taga dama a zuciyarta yadda take kassara kowacce gaba ta jikinta. Wani irin sassanyan mutum ne da ya iya cusa zazzafar qaunarsa a zuciyar iyalinsa.
Adadin yadda mu'amalar aure ta hadasu,adadin yadda yake sake ratsa zuciyarta da wata irin zazzafar soyayya,yasan yadda ake tafiyar da mace over and over, batasan yadda bakinta zai iya fasaltawa ba.
Nadeeya ya gani a tsaye sai ya jefa mata harara cikin salon tuhuma da kuma tsare gida
"Am sorry yaaya‚police ne suke nemanka"
"Shine zakizo kiyita disturbing mutane?" Ya fada hankali kwance
"Yi haquri" ta sake fada. Sai a lokacin yaga kamar akwai alamun tashin hankali kan fuskarta
"Are you okay?" Kai ta gyada tana hadiye yawu da ayar,sai ya kewayeta kawai yana ficewa ta bio bayansa
"Kibi ta daya qofan ki koma cikin gida" yace mata ganin akwai maza da vawa a wajen harda ma'aikatan gidan.
Cikin nutsuwa da kamewarsa ya garasa gurin.
Dukkansu sukayi saluting nasa saboda fuskar da basu zata ba suka gani. Babbansun ya matso ya miga masa hannnu sukayi musaba
"'Sir......na shiga tantama da kokwanto, da gaske a nan din meenal ya'agoub aji take?"
"Meenal?" Ya maimaita sunan cikin tantama
"Oh,right eh nan ne" ya fadi bayan kuma ya tuna wace me sunan. Juyawa yayi kadan ya kalli yaransa sai ya karba wata takarda daga hannunsu ya migawa toufeeq yana cewa
"Am sorru to inform you tayi commiting suicide,ta kashe kanta"
"Subhanallah, subhanallah" toufeeq din ya furta yana maimaitawa tare da karbar takardar yana duba tabbacin gwaji ne na mutuwarta da kuma shaidar kashe kanta tayi din.
"Zamuje tare ku sanya hannu sai mu baku gawarta"
"To babu damuwa, bari na sanarwa da family na"
"Zamuyi gaba sir,sai ka samemu a Murtala Muhammad specialist hospital"
"Ba damuwa" waiwayawa yayi ya kira libril yace ya fiddo mota,ya juya cikin gidan da sassarfa
Sassansu nadeeya ya wuce yana sallama ya samu fadeela zaune tana cin indomie, gefe ga cup data cika da madara, cartoon take kalla a mbc 3. Da mamaki yadan bita da kallo,wasa wasa ta kama abinci sosai tunda akayi aikin fiye da wanda takeci lokacin säahar.
Murmushi ya wadata kan fuskarta,ta ture plate din tana migewa hadi da fadin
"Good morning daddy"
"'Bazan amsa ba, gaisuwarki tazo late" kai ta langabe
"But daddy, banason zuwa na tada ku a bacci fa,nasan anty N a gajiye take sosai,tun kafin ayimin aiki bata bacci, kullum addu'a take kwana tana yimin, inason tayi bacci sosai yanzu don ta haifa min ganne masu garfi da zasu dinga taremin fada" a bisa dole murmushi ya kubce masa,yasan wanna sharrin surutun nadeeya ne, har ya fesa mata kenan, ita kuma bilhaqqi qanne takeso shi yasa take kiyayewa
"Good girl" ya fada yana saluting nata da hannunsa.
Sake gaidashi tayi ya amsa, ya tambayi nadeeya da baaba ramatu tace
"Suna kitchen,abby ka duba abincin da suke bani don
sunga anty N bata kusa" ta fada tana nuna masa abincin da baki. Murmushi ya sake subuce masa,gaba daya yarinyar kamar an sake bude bakinta ne da komai nata
"'Ayyah,zamu kai gara wajen AUNTY N"
"Eh dama na fada,nayi missing abincinta sosai, please
daddy yau tayi mana dinner mana?" Kanta ya shafa
"Nima navi missing abincinta angel, amma sai ta warke sosai zata dafa mana muci ko?"
"Ni ko bata dafa min bama, indai zata kawomin qanne na 1 mu dinga wasa shikenan" dariya ta bashi duk da yanayin zucivarsa babu dadi amma sai da ya sake murmusawa
"'In sha Allah, kiyita mata addu'a yadda tayi miki kema"
"Zanyi daddy,i promise"
"That's good my angel,yanzu jeki kiramin su" da gudu ta cilla tayi kitchen din cike da farinciki, tana wassafa yadda zata kula da nata gannen itama, zata yita bawa 'yan class dinsu labarin qannenta itama yadda kowa yake bata labarin nasa,dama ita kadaice bata da.
Rudewa dukkansu sukayi, nadeeva na hawaye baaba ramatu tana salati
"Relax please, banason SAHR taji yanzu saboda yanayin da take ciki, please take care with her" ya qarashe maganar yana kallon nadeeyan, saboda yasan itace sarkin raki. Kai ta jinjina ya juya yana fita daga sashen.
Batasan me yake faruwa ba,taga dai ya shirya a gaggauce,yayi kissing hannunta yana cewa
"Zanje na dawo,ki kwanta ki sake hutawa kafin anima na sake tara miki wata gajiyar,yanzun bana bugatar kiyi komai saidai ki bani kulawa, idan da hali ma bacci nakeso kiyi" kafada ta maqale a shagwabe
"Kada ki damu,i will handle it with care and softness,it would not be harmful".
Haka ya fita ya barta da tarin tunaninsa a kanta,murmushi kuma fal fuskarta. Ta gaji da zaman,don haka sai ta shirya ta gyara sashen tsaf sannan ta sake gyara jikinta ta fito,don tana sin ganin fadde dinta, tana kewarta.
Hankalin maji yayi masifar tashi da jin labarin mutuwar haseena, ba kuma wai mutuwar ce abun tashin hankalin ba,hanyar da tabi wajen salwantar da rayuwarta.
"Ka shaidawa mamanta ne?" Maji ta tambayi toufeeq
"I think tana asibiti, nidai na gama nawa gawar tana asibiti maji". waiwayawa maji tayi ta dubi Dr jarma da aka gama rubutawa sallama
"Abba,haqqij yi mata sutura yana wuyanku,saidai bansan ta yadda za'a gayawa fauziyya rasuwar ba tunda bata da lafiya itama"
"Dole ta sani ai,ko don ta roqawa 'yarta gafara ko?" Ya fada yana sauka daga saman gadon hadi da duakan wayarsa.
Toufeeq sajjad dr har da maji suka isa asibitin da hajiya qarama ke jinyar.
"Dama muna shirin neman 'van uwanta mu sallameta ne,saboda babu me jinyarta, abinda ya hana mu bata sallama ma ba'a biyamu bill dinmu dake kanta ba" wata nurse ta fada cikin girmamawa sanda taga dr mahmud hadi da toufeeq,wanda kusan ba boyayyu bane kusan kowa yasan fuskarsu.
"Sannan sir,kamar akwai abinda yake shirin taba qwaqwalwarta,akwai magana da yawa da takeson fada ma amma kuma ba'a iya jin abinda take fada sosai,a shawarce a fara ganin likitan qwaqwalwa kafin abin yayi nisa". Shikam toufeeq zame jikinsa yay yabar wajen,don baya jin sisinsa zai iya sanyawa wajen neman lafiyarta.
Zafafabiyar
"HUGUMA*
•_TABARMAR KASHI_*
Book 02 Page 70
A haka aka kinkimeta sukayo gida da ita, duk da Dr jarma vaso kafewa akan ba za'a koma da ita cikinsu ba
"Abba yayi gaskiya maji, ki barta kawai" toufeea ya fada cikin I don't care manner. Dubansu tayi duka su biyun
"Inajin babu wani hukunci da kuka isa kuyi mata kamar wannan da Allah yayi mata,ba lafiya babu dukiya diyar da takevin fadi tashin tara komai da mallakar komai saboda ita ta kashe kanta da kanta, banda Allah wa ya isa ya hukuntata haka?, saboda haka ku barta taji da nata, kuci gaba da fatan ku bar sararin duniya lafiya,kada Allah ya jarabceku da son zukatanku har takai ku aikata abinda ta aikata din" wannan maganar ta sanyaya musu jiki dukkansu saidai har yanzu TOUFEEQ bayason koda kallon fuskarta,gashi ita din ta nace da kallonsa bakinta dake zubda miyau yanata motsi, da alama akwai maganganun da take fadi amma ba'a iya jin ma me take cewar.
Abinda yayi gudu kusan shi ya faru,bayan isarsu gidan gain gawar haseena ya sanya hajiya garama tayita kwarara ihu,ihun da iya shi kadai ke fita ake iya jinsa, amma muddin magana zatayi komai baya fita.
Wanann shi ya daga hankalin sãahar sosai, uwa uba mutuwar data tabbata haseenan tayi,ya sake saka mata tsoron Allah da kuma tsoron duniya, da gaske budurwar wawa ce, kuma babu mayaudariyar aba irin duniyar yanxun nan zata daura aure da kai,yanzun nan zata sakeka,waccae shekarar iwar haka hajiya qarama din nata tsara yadda wannan shekarar zata kasance mata cike da cikar burikanta da haskowa kanta tarin nasarori da kuma ci gaban rayuwa,amma a ayanzun sai gata a kanannade cikin keken guragu, ba gafa ba hannu babu baki,ba lafiyar ma dukanta,babu dukiya ba miji babu diya,lallai ba shakka babu abinda yafi aikata alkhairi dadi a rayuwa,KOWA YAYI NA GARI KANSA kamar yadda bahaushe yake fada, kuma hakan take.
Ganin tana neman birkice masa sai va dauketa
gaba daya ya kaita bristol ya kama royal suit kamar yadda ga saba sukayi zamansu a can. Katafaren gidan da yake kan ginawa ya tayar da qarasa ginin,cikin. sati guda komai ya kammala. Babu abinda suka dauke daga wancan tsohon gidan sai suturar jikinsu. Ana ya goben zasu tare ya kaita gida yace ta kwana wajen maama
"Zaki zama full house wife, idan kika shiga MY KINGDOM ban miki alqawarin fita ko yaushe ba,ki kula da ni ki kula da abinda zaki haifa min for the rest of our lives shine burina".
Ranar da zasu tare din dr iarma na zaune a parlor dinsa suna yin dinner tare maji na serving nasu ya kalleshi
"'Diyarka kadai zaka dauka nima dauke tawa diyar zanyi"
Dr jarma yace da toufeeq. Kansa ya daga yana duban maji ko zata shiga maganar sai yaga ta fuske, da suka hada ido sai ta kauda kai
"Ai gaskiya ya gaya maka,ka sakata a gaba ba batun aure bayan ta gama isa munzali har tana shirin wucewa aurar da ita zamuyi muma"
"'Kodai kunason ku shaqata ne maji?" Ya fada qasa qasa yadda Dr bazaiji ba.
Spoon din hannunta ta jefa masa tana cewa
"'Qaniyarka,me yasa ka maidani kakarka ne?" Dariya ya saki yana kaucewa
"Afwa ni ba wani abu nake nufi bafa".
"Bar dan nema, ka dauka tsufa mutuwa ce?" Dariyar da yake rigewa ya saki yana hada hannunsa guri daya
"Ayimin afuwa,na tuba". Har qasan zuciyarsa yakejin rayuwarsa ta sauya, yana mugun jin dadi idan yazo yaga maji da Dr a tare guri guda suna hidimtawa juna da sunan miji da mata