← Book details Tabarmar Kashi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 171

Sashe 77

Tabarmar Kashi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kwantacciyar sumarsa da tasha gyara take a kwance luf cikin wani tsari da gyara me daukan hankali sai glowing takeyi,hakanan eye glasses din da yayi amfani dashi ya sake fidda kyawawan qwayoyin idanunsa dake da wani yawa.

Ko sau daya bata daga qafa ba wajen sauke tata gafara a duk inda ya ajjiye tasa ba,tana yi tana shagar qamshin lallausan turarensa daya zama abu na farko da ya fara jan hankalinta game dashi,duk bayan wucewar kowacce daqiqa sai taji kamar zuciyarta zata narka a kansa, tsahon awannin da suka dauka kadai a jirgin a tare tana jin kamar zata zauce a kansa,duk da cewa ko kalmar ZO bata hadasu ba,hasalima bata zaton ya ganta. Tana yawan ganinsa a shafukan MEENAL YA'AQOUB
AJI,amma batasan cewa hotuna rage masa kyau da kwarjini sukeyi ba sai yanzu data ganshi physically

"Hi mr man" ta fadi tana dan qara sauri don ta cimmasa,ganin baiko san tana biye dashi ba. Wani faduwa gabanta yayi lokacin da ya waiwayo ya zube mata idanun nan nasa dake da wani irin kwariini da maganadisu "How can I help you?" Kalmar sai tayi mata nauyi,taji kuma ta muzanta,abinda yasa tadan diririce kadan kenan,tayi gyaran murya sanda yake juyawa zaici gaba da tafiya ganin bata da abin cewa

"Mmmm..... ammm,kamar nasan fuskar nan taka,idan ba damuwa....may i get your phone number?" Wani irin haushi da takaici ne ya kamashi,ya tsaya cak har ta cimmasa,ya waiwayo yana dubanta

"What amount do you need?" Hannayenta ta harde a girjinta,tana dan ware idanunta kadan akan fuskar sa,cikin zuciyarta tana jin wannan din dama ce me kyau a gareta,don haka ta saki murmushi kadan

"Five hundred thousand to one million" waiwayawa yayi yana duban jibril,hannunsa daya a aljihun trouser dinsa

"A bata" va dawo da dubansa gareta

"Wannan va zama shine lokaci na farko kuma na garshe da zaki yarda magana ta sake hadamu" daqa haka ta kewayeta yayi gaba cikin qasaitaccen takun nan nasa,ransa yana sake baci,zuciyarsa na motsuwa,yana in tsanar mata da halinsu gaba daya,ya gama yarda kudi yana gaba da komai a wajensu!,kuma tabbas zasu iya aikata komai akan kudi. Yaja tsaki har baisan adadi ba,zuciyarsa na sake quntata a duk inda ya gifta ya tsinci idanuwansu suna binsa da kallo duk da bawai kallon nasu yakeyi ba,amma yana ji a jikinsa, kyakkyawar fuskar yarinyar na dawo masa

"Ya tsani mace me kyau,hadari ce,ya yadda da wannan" ya sake jaddada maganar can qasan zuciyarsa.
*HUGUMA*

* TABARMAR KASHI_*

68

Tun daga nesa da ya hangi angel dinsa bacin ran ya fara narkewa,saidai wannan miskilar fuskar tasa na nan a hade,murmushi bai kubce mata ba sai da yayi hugging fadeelan,wani sanyi da nutsuwar ruhi na saukar masa,hancinsa ya zuqi daddadan turaren sãahar da take amfani dashi,qamshin ya cika masa zuciyarsa da kwanyarsa gaba daya. Zamewa tayi sannan ta duga har qasa tana gaidashi tare da yi masa maraba da zuwa,sosai murmushi ya wadaci fuskarsa,yasa hannu ya kamota yana amsawa da lallausar muryarsa dake nuna zallar gaunar diyar tasa "Waye ya koya miki angel?" Murmushi ta saki

"Anty N"

"she taught her a lot" nadeeya dake tsaye tana dubansu ta qara masa haske ita kanta tana jin alfahari da sãahar din.

Miqewa yayi tsaye yana kallon nadeeyan,fuskarsa a dan hade,saita langabe kai tana dubansa,abinda yasa ya zare hannunsa daga aljihun wandonsa ya miqa mata,dariya ta kubce mata itama ta bashi sukayi musabaha, she's very proud with him,ta yarda yayanta miskili ne na qarshe,yana da wuyar sha'ani wasu lokutan,musamman idan kayi masa bahaguwar fahimta,amma kuma mutum ne me tsananin kula da damuwa da duk wanda yake alhakin hakan yana rataye a kansa,a yanzun tasan fushi yakeson ya gara nuna mata,amma ta karya lagonsa. Haka suka jera su uku,sun sanyashi a tsakiya,yana riqe da hannun kowa a cikinsu sun baibayeshi da surutu. Duk da rashin son magana da hayaniya irin nashi amma yana qoqarin bawa kowa hankalinsa,har suka isa inda motocinsa suke jiransa,daga daga cikinsu BMW sabuwar qirar shekarar Jason ya bude musu suka shiga ya maida murfin ya rufe.

Har yanxu hannunsa na cikin na fadeela yana mamakin yadda tayi kumari,ta ciko sosai ta murie, ta gara haske gashinta ya qara kyau da tsaho,komai nata ya canza sosai

"Abby baka tambayi anty N ba....bata jin dadi,tana bacci ma muka fito, sister nadeeya tace a ayaleta wai" saita karyar da kanta gefe bayan ta gama bashi labarin. Kanta da tun jiya sãahar ta gyareshi tsaf ya shafa

"That's right ‚ku barta ta huta,she will be okay in sha Allah" sai ta magaleshi da kyau tana murmushin jin dadi.

"ya kamata ayi doubling salary dinta ko?" Yayi
maganar yana duban fuskokinsu. Murmushi
nadeeya tayi tana gyada kai
"Yaa salary din da har yau ba'a taba karbarsa
ba?"

"Like how?, Ya mata kadan ne?" Kai nadeeya ta
girgiza

"Bana tunanin haka,tunda mommy qarama ma
kafin tayi tafiya last week naji tana tambayarta
tana bugatar qari ne da taqi karbar salary
dinta? amsar dai kawai No ce,tace bata bugata
ne a yanzun,tafi sha'awar kula da fadeela
kyauta,wannan ya qaramin qaunarta da ganin
girmanta sosai yaaya" ta qarashe maganar
tana kallon fuskarsa. Shuru yayi yana juya
maganar nadeeya a ransa,zuciyarsa sai yaji
sam bata aminta da tsarin ba

"She must collet her salary,coz banga muhallin kulawa da ita a kyauta ba,we can afford all her needs da abinda muka mallaka,basai anyi mana aiki kyauta ba" dan murmushi kadan nadeeya tayi,ta karanci har yanzu akwai wannan zafin cikin ransa bai gushe ba

"Kyautatawa ce fa yaya" waiwayo yayi ya kalleta,kamar zaice wani abu sai kuma ya fasa ya maida hankalinsa ga hanya,cikin ransa da zuciyarsa ya soke tsammani ko ganin kyautatawa daga dukkan wata macace muddin ba wadan nan jinin nasa ba.

Kamar ko wanne lokaci idan ya dawo tafiya irin haka,yakan dauki wasu mintuna a farfajiyar gidan,saboda dukka ma'aikatan gidan masu masa barka da dawowa,ya bincika wasu abubuwan ya tabbatar komai haqqinsa ne ya sansu sannan ya wuce ciki nadeeya jibril da fadeela na biye dashi. Jibril ya ajjiye duk wani abu daya danganceshi ya sallami jibril din don shima yaje gida ya huta,su elyas zasu kasance dashi nadeeva ma sai ta wuce sashensu don ta kammala masa komai don yace abinci zai fara ci,yau kam tace nasu zaici,tacewa jacon yau duk abincin daya shiryawa ogan nasa saidai yayi haquri,yana dariya kasancewarsa me saugin kai, kuma yasan barkwancin nadeeya yace babu komai

"Amma madam,ya za'a yi da abincin?"

"Kaie dashi kuci kai dasu Jason kafin su wuce" cikin farinciki ya dinga juye musu abincin yana fita dasu,duk da cewa dukkan wani dake aiki a qarqashin gidan yafi qarfin ci sha da kuma suttura masu kyau,toufeeq yana daga parlor dinsa yana jinsu,baice komai ba,amma kuma zaiga wacce rigima ce ta sanya nadeeva bayar da kyautar abincinsa bayan yunwar da yakeji,kuma tasan baya son missing abincin
Jacob din,ya yarda dashi da girkinsa,expert ne sosai ta wannan fannin,shi yasa salary dinsa yake na daban. Sai daya sallami fadeela da wasu daga cikin tsarabarta dole saboda yadda ta matsa masa ta bashi guri ya samu ya shige bedroom dinsa din ya watsa ruwa kafin ya zauna cin abincin.

Kowa taqi kulawa a gidan da tarin kayan wasanta da bata gajiya da tara shirginsu,ta wuce kai tsaye dakin säahar.
A nutse ta maida murfin gofar ta rufe,ta qarasa gefan gadon ta ajiye kayan tana kiran sunanta,ganin bata motsa ba sai ta haye saman gadon tana janye duvet din data qudundune a ciki

"Anty N,abby is back,kinga abinda ya siyamin,yace sai ya huta zai daukomin sauran" wata miqa tayi tana jin dukka jikinta yana mata ciwo,dole ta yaye bargon ta miqe ta zauna tana karbar kayan wasan.

Kusan dukka basuyi mata ba,saboda yanayin lafiyar fadeela da take kiyayewa,ta zabe wadanda basuyi ba a ciki tace mata

"Wannan ki ragesu ki ajjiyesu ba yanzu zakiyi amfani dasu ba,saikin qara samun lafiya da kyau soon in sha Allah" kayan tabi da kallo,da alama tanason kayan,to amma tana bin maganar sãahar qwarai,duk yadda tace mata tayi abu ko ta bari tofa zata bi ne. Dole ta miqe suka wuce dakin fadeelan,ta tayata jera na jerawa,sannan ta dawo dakinta ta sauya pad dinta,ta daura alwala yadda zataji dadin jikinta ta fito parlor dinsu.

Da baaba ramatu da nadeeya duka suna kitchen suna kacaniyar hada komai yadda zai dace da tsarinsa,a can ta taddasu

"Yauwa anty N,yanzu nake shirin shiga naga ilkin naki"

"Karki damu,alhmdlh,naji sauqi" ta fada tana karbar shirya abincin,nadeeya ta koma baya tana kallonta,har ta kammala shirya komai tsaf,cikin burgewa nadeeyan ta kasa shuru

"Wow.ma sha Allah,anty N,anya ba catering kikayi ba?" Murmushi ya qwace saman fuskarta data dan canza kadan saboda baccin
da tayi

"Aikin maama na ne da anty farheen"

"Nice name" nadeeya ta sake fada tana
murmushi, zuciyarta kuma na mata kokwanto
akan sãahar. Kota wanne bangare a waye take
matuqa,kuma ta iya komai fiye da yadda ita
din zatayi,ta zarta a abubuwa da yawa,bataga
wata alama ta bugatar yin aikin nanny ba sam tattare da ita, komai nata na nuna wayewarta
da zurfin iliminta,to amma she's very kind,suna
in dadin zama da ita dukkansu,sai sukejin
kamar wani gibi ne dake cikin rayuwarsu aka
cike musu shi da ita,she's nice person,batason
tayi mata wata tambaya da zata bata mata
rai,ko tayi silar da zata tafi ta barsu.

Ba yadda nadeeya bata juya ba akan
tazo suje su gaisa da abby din koda ba zata
zauna cikinsu suci abinci ba ta girgiza kai

"Saurin me kikeyi sister nadeeya? munafa gida daya,kuma yau yau ya dawo shima,yana bugatar ya samu isashen lokaci daku,zamu gaisa ne" da haka ta doje tayi zamanta kitchen tare da baaba ramatu dake shirye shiryen yi musu tuwo yau,hakan ya yiwa sãahar dadi,don ita kanta tayi missing dinsa kwana biyu

"Yadda kike maqalewa wannan bagin abun,ban zaci kina iya cin tuwo ba ai" baaba ramatu ta tsokaneta sanda take kunna gas tana dora ruwan tuwon a tukunya. Janye coffee din tayi daga bakinta tana murmushi

"Inaci sosai baaba,tuwo abincine me sirri al a cikinsa"

"Tabbas,amma mutan gidan nan basu sani ba,zuwanki yasa fadeela ta fara ci,amma ada idan nayi saidai naci abina ni kadai,ya kamata ki rage shan wannan bagin abun ko zakiyi kumari" murmushi ta sakeyi
Chapter 77 · 0% Book details