← Book details Tabarmar Kashi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 171

Sashe 46

Tabarmar Kashi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kamar daga sama taji qarar waya,a mamakance ta waiwaya tana duban daga inda sound din ke fita. Wayar adam ce a wajen,tadan zubawa wayar ido tana mamakin yadda akayi yau ya manta wayarsa,shi da kwana biyun nan baya sake da waya,ko yaushe tana hannunsa,bini bini ya dauka ya duba,har wani sabon suna ta saka masa saboda maitar riqe waya daya koya,ko cikin dare idan ta farka da yake a kwanakin nan bata fiya kwana da qoshin lafiya ba sai ta ganshi riqe da waya,tun tana daukan abun da wasa har taga ya zama gaske,tayi masa complain sai yace akwai wata sabuwar harka ne da yakeson ya gwada shiga,so ana wayar masa dakai ne yadda business din yake,wanda kuma yake masa bayanin ba qasar nan yake ba,yana china, akwai tazarar 7hrs tsakaninmu,darensu shine ranarmu,lokacin shi kuma yana office bazaiyu ya maida hankali ba akan waya ya ajiye aiki,ranarsu kuma shine darenmu,a sannan shi yana da chance nayin chart,shi yasa yake tashi a daren.

Ta gamsu,saboda ya yarda da adam din,bata taba kamashi da wani laifi da zai sanya zuciyarta tayi ɗar ko rawa a kansa ba.

Kira bayan kira haka ya dinga shigowa,hakanan taji qarar wayar ta dameta,saita yanke shawarar sanyata a silent,don ita din ba gwanar daga masa waya bace,koda za'a kira wayarsa sau dubu bazata waiwaya ta kalleta ba,ada har qorafin hakan yake mata

"Idan kirane mai muhimmanci ko kuma samuwa ce kinga shikenan ta wucemu" dariya kawai takeyi,saboda bata jin zata iya,tana da dabi'a na tsame kai daga abinda ba huruminta bane bai kuma shafeta ba.

Da sauri ta koma ta zauna sanda ta miqe da nufin cimma inda wayar take saboda wani hadadden ciwon mara na tashin hankali da taji ya soketa,ta runtse idanunta ta kuma dafe mararta da kyau tana kiran sunan Allah tana jujjuya kanta saboda azaba. Akalla ta kusa kwashe minti biyar a haka tana juya kanta hagu da dama,gefe guda kuma qarar wayar naci gaba da cika mata kunnuwa. Ta bude idanunta a hankali bayan ciwon ya lafa tana share gumin daya tsatstsafo mata a goshi,qafafunta babu cikakken qwari ta miqe ta nufi wayar.

Tana isa wayar ta danyi blinking light alamun shigowar saqo,ba inda idanunta suka sauka sai kan fuskar wayar. Da sauri ta zare idanunta daga fuskar wayar tana lumshe su,gabanta na wani irin dokawa labbanta na furta

"Ya hayyu ya qayyumu bi rahmatika astagis" tana fatan ta bude idanunta taga ba abinda suka gane mata bane da farko. Saidai a wannan karon data sake bude idanun nata abinda ta gani ya zarta wanda ta gani da farko,dukkan jikinta ya dauki rawa,taji a sannan bata da sauran zabi da ya wuce ta dauki wayar.

Tana daukan wayar qafafunta suka gaza daukarta,dole ta zame ta koma da baya ta zauna saman kujera, hannuwanta kamar ba zasu iya riqe wayar da kyau ba,ta fara qoqarin gwada password din dake kan wayar.

Duk password din da ta saka sai yace mata wrong,daga qarshe ta gwada saka qarshen number wayarsa,a take ta bude,saqon da bai gama fitowa ba ya bayyana muraran.

K'azaman kalmomi masu munin gani bare kuma kunnuwa su iya jumurin sauraronsu,wani gumi mai zafi ya shiga tsatstsafo mata ta kowacce kafar gashi dake jikinta,zuciyarta ta ninka bugunta kamar zatayi tsalle ta fito daga qirjinta,kanta yayi wata irin sarawa ta fara gani dishi dishi sanda ta fara bin charts din dake inbox din da number wayar da babu suna a kanta. Wasu irin qazaman saqonni da ko ita da take halalin adam bata tunanin sun taba musayar irinsu a tsakaninsu,hotuna na kowanne sashe na jikin yarinyar,harda muhallin da ko mahaifiyar yarinyar tana tunanin zaiyi wuya ta sake katarin ganinsa tun bayan da shari'a ta hau kanta. Ganin abun take kamar al'mara,ganin abun takeyi kamar ba adam dinta bane,kamar ma ba wayarsa bace,ba abinda ke kaikawo cikin kwanya da zuciyarta da sunan adam din da kuma fuskarsa. Video na qarshe da idanunta suka gaza kalla wayar ta sulale a hannunta ta fadi tare da wani hadadden ciwon mara da bata taba jin makamancinsa ba,sai kawai ta cure a wajen tana jin numfashinta na shirin barin gangar jikinta.

Wannan yayi dai dai da bude qofar falon da adam din yayi cikin gaggawa,har yayi nisa ya tuna yabar wayarsa,duk da yasan baida matsala,kuma bashi da haufi matarsa bata taba wayarsa,amma haka kawai yau din yaji ya kasa samun nutsuwa,yaji bashi da gamsuwar tafiya,dole ya juyo da kan motarsa ya dawo ya dauki wayar sannan ya koma.

Sam bai lura da inda ya aje wayar ba,idanunsa akan saahar dake cure guri daya kamar alkaki suka fara sauka. Da hanzari ya qaraso yana kiran sunanta,duk da azabar ciwon da takeji a mararta amma hakan bai hanata daga kai ta watsa masa wani kallo da jajayen idanunta ba. Sosai yasha jinin jikinsa amma zuciyarsa na gaya masa komai normal ne,ya miqa hannu gareta,ta tattara dukka ragowar qarfinta ta miqe tana jin mararta kamar zata rabe biyu

"Kada ka yarda ka tabani,karka qaraso inda nake......" Bata kai ga qarasawa ba numfashinta ya soma sarqewa,tana jin wani abu me dumi ya ratso ta jikinta ya soma bin qafafunta yana gangarowa,duk da yanayin gushewar hankali da take kan gabar yi,amma hakan bai hanata qoqarin ganin abinda ke faruwa da ita ba,idanunsu shi da ita suka sauka lokaci daya akan jinin dake malala saman tiles din falon,bai jira cewarta ba ya qarasa gareta da hanzari yana riqeta,zuwa lokacin itama tuni ta qarasa ficewa daga hayyacinta,saboda qarin tashin hankalin fitar jinin da ta gani daga jikinta.[8/29, 2:05 PM] KYAUTA: *H U G U M A*

*_TABARMAR ƘASHI_*💔
https://arewabooks.com/u/huguma

Page 41

*******Daga lokacin data fahimci cewa ta farka,ta dawo cikin duniyar da batayi tsammanin dawowarta ciki ba,sai ta fara qoqarin bude idanunta don ta tabbatar da inda take din. A lokacin da kwanyarta ta fara yi mata bitar al'amari na qarshe daya faru da ita saita rasa dukka qwarin gwiwa karsashi da kuma sha'awar bude idanun nata,ta sake runtse idanun nata cikin jin zafi,wani abu me tsini na sukar qirjinta kamar an fiddo zuciyarta an shanyata tsakiyar qwalleliyar rana.

Hannunta data daga a hankali takai saman cikinta ta shafa bayan ta tuna yadda taga jini yana bin qafafunta a kallo na qarshe data yiwa jikinta. "Saahar,kin farka ne,sannu" muryar anty labiba matar yaa saif dake zaune a gabanta ya ratsa kunnuwanta,bayan zuwa yin salla da maama ita da afifa suka fita yi. "Sannu saahar" anty labiba ta fada tana riqe hannunta dake saman cikin
"Ki daina motsa hannun, cannula din dake hannunki zata goce" ta fada cikin matsanancin jin tausayinta,daga yadda taga tana shafa cikin lallai shine abu na farko daya fara zuwa mata kenan a rai bayan ta farfado din,wanda tuni ya fice daga jikinta ta cikin jinin data dinga fitarwa me yawan gaske.

Tare maama suka shigo ita da afifa,dukkansu rige rigen isowa gareta sukeyi

"Menene abun kukan kuma?,Allahn daya baki shi zai sake baki wani" abinda maama ta fada kenan cikin muryar lallashi,a nata zaton saahar din ta fuskanci babu cikin a jikinta.

A mugun karye ta daga kai ta kalli maaman,xancan yayi mugun dukanta,wasu tawagar hawayen masu zafi suka kunno kai,saita maida idanunta kawai ta lumshe,abinda ya bawa hawayen damar saukowa da kyau.

Tsahon zaman da sukayi tare da ita suna lallashinta idanunta na a rufe ba tare data iya budesu ba,taji ciwo sosai na rasa gudan jininta da tayi,amma a yanzun hankalinta yafi karkata ga mummunan ganin data yi a wayar adam din. Ciki tasan ubangijin da ya bata shi zai sake bata wani,ko a kusa ko a nesa kamar yadda ya kawo mata wannan,to amma kuma wannan baqon al'amari daya shigo rayuwar adam fa?,wanda kai tsaye zata iya kiransa da neman mace koda bata ce neman mata kai tsaye ba,iya maganganunsu kawai ya gama gaya mata adam ya jima da yarinyar,sunyi mugun sabo,kuma sun saba kasancewa da juna da irin mu'amalar dake iya wakana tsakanin ma'aurata
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" ta furta har ta fito fili ba tare data ankara ba,sai sautin muryar maama da tace

"Yauwa,ita zakiyita maimaitawa" sake motsa bakinta tayi a karo na biyu tana sake maimaita kalmar,hawayen na sake bin kuncinta.

A matuqar sanyaye afifa ke sanya tissue tana dauke mata hawayen,saahar dinta jaruma ce da take da wani irin juriya dakiya da kuma cinye abu,irin tashin hankalin da take gani dimuwa da halin qunci sai take ganin kamar ya zarta yadda ya kamata ace an gani a fuskar macen data jima bata samu haihuwa ba ta hadu da miscarriage,saidai bata ga wani abu guda daya da zai dasa mata kowanne irin zargi a zuciyarta ba bare ta sanya ayar tambaya.

Dai dai lokacin likitan yayi knocking qofar ya kuma tura ya shigo shida wata nurse dake riqe da file na saahar din

"Yauwa ta farka?"

"Ta farka dr" anty labiba ta amsa masa

"Ma sha Allah" ya fada yana tsaiwa daga gefan saahar din

"Sannu ko?" Ya sake fada yana duban fuskarta,sai a sannan ta bude idanunta a hankali da suka tasa saboda hawayen daketa fita daga cikinsu akai akai

"Ya da kuka kuma madam?,sorry for the lost.....kiyi addu'a,next year kamar war haka sai kiganki saman gadon nan rungume da babynki alive and healthier" idanunta ta mayar kawai ta lumshe,abinda takeji cikin zuciya da qirjinta ta tabbatar babu me iya fahimta,da rufaffun idanuwan nata ta amsawa likita dukka tambayoyin sa,sai ya rufe file din nata yadan dubi afifa

"Idan me gidanta ya shigo a turomin shi,inason magana dashi kafin na fita duty"

"Okay,in sha Allah" ta amsawa likitan bayan ta daga kanta daga wayar da take dannawa, zuciyarta duka babu dadi,duk sanda daya daga cikinsu ya shiga damuwa ko tashin hankali,kusan su biyu suke raba wannan damuwar da dukka sakamakon da zai biyo baya.

Yanayin yadda taga kukanta yana tabasu tare da sake sanyasu damuwa ya saka dole ta tattara abinta ta cinye ta hadiye tana kiran sunayen Allah can qasan ranta,don ita kadai tasan qunci da bala'in da zuciyarta take ciki,dukkansu sun sanyata a gaba kowanne tambayarta yake me takeso?,me yake damunta?,bisa taimakon afifa da anty labiba ta shiga bandaki ta gyara jikinta tayi wanka,ta fito afifa ta shiryata sannan ta zauna yaa zaid yana ajjiye mata plate din abinci a gefanta
Chapter 46 · 0% Book details