← Book details Tabarmar Kashi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 100 OF 171

Sashe 100

Tabarmar Kashi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kamar yadda suka saba toufeeq ya gaidata,tayi gogarin gagaro murmushi

"'Lafiya lau ango,idonka kenan?" Gaisuwar da sãahar ta migo ita ta katse tuhumar da take masa ta sigar tambaya a fakaice. Wani irin shu'umin kallo tayi mata,tadan kada qafarta kadan

"Amarsu,lafiya ya kwanan baqunta?,koda yake
ma ai 'yar gida ce na manta" ta furta tana sakin wani murmushi me dauke da ma'anoni da dama,gasan ranta kuma zuciyarta ke
sake cika da alwashi da algawura iri iri akan sãahar din,sai ta biya baqincikin da ta sanya ta kwana dashi a jiya sanadiyyar maida mata maaganganun da tayi. Maida dubanta tayi ga
yayan nata Dr jarma tana gaidashi.

*HUGUMA*

* TABARMAR KASHI_

Book 02Page 17

Amsa mata yayi yana tambayarta hidimar da aka qare jiya

"Alhamdulillah, duk da wata tana tafe in sha
Allah nan kusa,saura kwanaki shida kacal meenal ta dawo,karatu ya qare sai aure in sha Allah" tayi maganar tana murmushi,kai dr mahmud ya jinjina

"To Allah ya zaba abinda yafi alkhairi"

"Ameen ameen,tuwona mai na in sha Allah" da kyau sagon ya isa kunnuwan maji,sai ta saki wani qaramin murmushi tana sake juya kanta gefe. Fauziyya ta riga ta makara,tayi makarar da bazata sake yin sammako ba daga nan har illa ma sha Allah,ta rigata isa gaban Allah,ta rigata kuma shiga kotun Allah,ranar yanke hukunci kawai take jira.

Hamdala dr jarma yayi sannan ya fara da yiwa toufeeq nasiha hadi da tunasar dashi nauvin da ya rataya a wuyansa

"Amana ce ita muka karbo maka,sai kayi qoqarin sauke haqqin Allah a wuyanka,duk da cewa ba wai yau ka fara aure ba" shikam gaba daya wa'azin dr jarma mamayarsa kawai yakeyi,duka abubuwan da yake lissafa masa a yanzun kamar an buga masa gudumar mantuwa,sai yanzun da yake masa bita suke dawo masa a kai, gaskiya ya fada,babu yadda za'a yi suyi wasa da Allah,shi kuma aure koda wasa akeyi,koda wasa aka daurashi to ya dauru kenan. Sai yaji lema tana tsatstsafowa daga gaban goshin sa yasa tafin hannunsa ya gogeta. Kan sãahar ya koma,itama yayi mata abida duka zai gayawa nadeeya,sai da ya kammala sannan yace

"Komai na kamfanina ya gama dai daita kamar yadda nake zato sanadin tubalin ginin aikin daku kuka farashi,so saboda haka nayi hiring naku duk da ban tuntubi ra'ayinku ba,zaku je kuyi conclusion na aikin da ku kuka kafa harsashinsa na wata guda,ku tabbatar da gyaruwar komai din,saiku miga ragamar ga sabbin shugabannin da zan nada kuyi tafiyarku,zaka riqe matsayinka na CEO,ke kuma diyata zaki taimaka masa ne a matsayi
PA dinsa saboda ya samu saugi da saurin kammala komai kada na riqeku da yawa a company din,hutun sati biyu kacal gareku na hutun aure kafin ku fara aikin"

Kusan a tare suka kalleshi,sai ya
sakarwa kowannensu murmushi yana gyada kai alamun tabbatarwa. Maida kansu sukayi ba tare da kowa ya iya musa masa ba,saidai ba abinda qirjin sãahar keyi sai bada wani fat fat. Ya tana qogarin nesanta kanta dashi amma al'amura nason sake kawo kusanci a tsakaninsu?

Duk yadda hajiya qarama taso daurewa ta gaza,suyar maganar takeji har tsakiyar zuciyarta,tayi gyaran murya sannan tace

"Amma yaaya, kana ganin hakan ya dace kuwa?,ya zaa yi harka ta dukiyar iyali a dauko bare a sakata a ciki?, next week haseena zata dawo,sai nake ganin ita tafi dacewa da wannan matsayin" sosai zuciyar maji keson maidawa fauziyya martani amma ta dakata taji wace amsa mahmud zai bayar? ya canza ko har yanzu ita ke riqe da akalar steering na rayuwarsa kamar yadda yake faruwa a baya?

Dan qaramin murmushi ya saki sannan
yace

"Banda abinki fauziyya,ya zaa yi mutum ga matarsa ta sunnah kuma da ita aka fara aikin,tasan makamar aikin sosai sannan a ajjiyeshi a hadashi da wadda ba matarsa ba?" Mamaki ya kama haiiya caramar hadi da rudani, dama sãahar din ma'aikaciyar MT JARMA GLOBAL ce?,me ya kawota aiki cikin gidan?,anya anya ba turota akayi ba?,dukka wadan nan abubuwan dake faruwa ba shiri bane ba kuwa?.

"Yaaya,naga tuwona mai na mukeson ayi,hakan ai zai gara musu ma fahimtar juna yadda komai zaizo da sauqi ko?" Ba maji data karanci fauziyya shekaru masu yawa ba take kallonta fes a tafin hannunta ba,hatta dr jarma yayi mamakin yadda take iya furta wannan maganar a gaban saahar,amaryar da kwananta daya tal a gidan miji akewa zancan kawowa kishiya nan da wasu watanni KO satittika?. Toufeeq ne mutum na farko da ya fara miqewa,don ya gaji da jin soki burutsun hajiya qaraman. Ba tun yau ba ta sani shima ya sani,ba kowacce magana tata yake iya bawa muhimmanci ba tun dazun da taketa zubarta baima gama fahimtar inda ta dosa ba sai yanzu,ta barshi yaji da danyan hukuncin da abban ya yanke masa na komawa company har na wata daya,kuma wai shi da yarinyar da ta riga tabar company din a gaban kowa,a yanzun zasu koma shi da ita a mazaunin miji da mata?.
Iska kawai yake furzarwa a bakinsa,ya akayi komai yakeson ya dinga juyewa daga ainihin yadda qwaqwalwarsa ke wassafa masa zai tafi?, matsalar hajiya qarama da dukka maganganunta bai daukesu a bakin komai ba,don ita kanta haseena din da take magana a kanta bai dauketa wata cikakkiyar mace ba bare wani wasan kwaikwayon hajiyan ya tabbata,damuwarsa yanzun yadda yarinvar ke gara kusantoshi cikin lamuransa,ya gama da case din maji na tafiya honey moon ashe wani yana tafe. Qaramin tsaki yaja,sai ya sauya akalarsa zuwa dakin fadeela ya dubata,yana jin baccin da akace tana yi din yayi yawa,yasan ba kasafai ta fiya baccin safe ba.
Baice da kowa komai ba ya taka a hankali ya fice daga dakin,maji ta waiwaya ga sãahar da kunya ta hanata motsawa

"Tashi kibi mijinki kinji, Allah ya yiwa aurenku albarka,ya tsone idon asara da hassada qyashi mugunta d mugun abu". Cikin ranta sai data yiwa maji addu'a sosai data bata damar barin wajen. Ajiyar zuciya me sanyi ta sauke tana lumshe idanunta,tanason ta zauna tayi bitar abubuwan da suka farun amma kanta ya dauki zafi,ba yanzu take da bugatar hakan ba, saita waiwaya sassan dakin fadeela tana duban qofar dakin,qaramin murmushi ta saki,tunda tazo gidan bataga fadeelan ba,tayi kuma kewarta sosai,don ba kadan ba tana jin yarinyar qwaral a zuciyarta,sai ta soma takawa zuwa dakin itama ba tare da tasan yana ciki ba.

Da gaske baccinta take lakadan hankali kwance,da alama tayi nisa sosai kuma tana jin dadin hakan,a tausashe ya zauna daga gefanta ya sanya hannu ya kama hannuwan ta yana kalla,kusan komai nasa ta daukeshi banda kamannin fuska da wani lokacin take yanayinsa,wani lokacin kuma yanayi take da maji. Sake damqe hannun nata yayi a tausashe yana sauke numfashi me zurfi daga hunhunsa,ko meye yake faruwa yanzun da shi ta sanadinta ne,lalurarta jarrabawa ce a gurinsa daya tabbatar akwai abinda Allah ke nufi a gareshi,kuma koma meye yana fatan ya zame masa kaffara da nasarar rayuwa.

Cikin jikinsa yaji alamun an bude gofar,da yake dakin ba wadatar haske nadeeya ta kashe mata kowanne fitila sansa zasu fita sal ya sanya bata hangeshi a gurin ba sam.
Ta gefen idanu yake dubanta sanda take takowa cikin dakin,sassanyan turarenta yana kwararowa tare da cika dakin. Sanda ta ganshi already ta iso tsakiyar dakin,taja ta tsaya dai dai sanda ta mige a nutse,saita juya da nufin fita a dakin,don ba zata iya zama dashi daki guda ba.

Batasan ta ina ya iso ba,batasan yaushe yayi dogon takun da ya rigata isa bakin qofa ba,ta dai ganshi yana maida key din jikin gofar yana kullewa. Batason ta nuna tsoro ko firgita,sai tayi kamar bata ga abinda yakeyi din ba,taci gaba da takawa zuwa bakin qofar,ta
Kama key din zata bude,wanne tudu wanne gangare sai ji tayi an mata wata wawiyar fusga an ajiyeta tsakiyar dakin. Yadda ta tsorata yasa gudun numfashinta ya qaru sosai,ta fidda idanunta waie tana kallonsa sosai sanda yake tsaye a gabanta hannuwansa cikin alihun wandonsa,ya zuba mata narkakkun idanunsa dake cike fal da bacin rai. Qara taku yayi gaba ya fara hade Gap din dake a tsakaninsu,sai ta fara ja da baya tana dubansa cikin zallar mamaki

"Meye haka?,ka bani hanya na wuce" ta fadi ganin ta qure bangon babu kuma sauran inda zata sake goce masa. Kamar da kurma take magana,bai fasa nufota ba yana dubanta da tsimammun idanunsa,miskilar fuskar nan tasa a mugun hade cikin rashin walwala. Idanunta ta mayar ta runtse sanda ya qaraso dab da ita taku daya kacal zaiyi ya hade da ita. Cak ya tsaya yana kallon yadda fuskarta ta soma yin ja,soft lips dinta suke shacking kamar tanason furta wani abu daga dan mitsitsin bakinta na rashin kunya amma tsoron da taji ta kasa fadin komai. Sannu a hankali idanunsa suka sauka kan qirjinta da yake a cike sosai a kuma tsaye,bugun zuciyarta na nuna alamun ya qaru ta yadda qirjin nata yake sama da gasa da sauri,ya lumshe idanunsa saboda yadda dumin numfashinta dake gauraye da qamshin jikinta ke sauka a wuyansa,wani abu yaji kaman ya fusgeshi,sai yayi taku uku baya a hankali yana jin jikinsa yana saki. Irin wannan yanayin ya taba ganinsa sau kusan hudu cikin mafarkinsa,sak kamar irin haka,irin wannan dukiyar fulanin da yasha kai hannu zai taba amma mafarkin ya katse a dai dai wannan lokacin,ko a yanzun sai daya murza hannuwansa dake cikin aljihunsa da kyau,yaja numfashi sosai yana son daidaita kansa,cikin husky voice dinnan tasa dake da wani irin kwarjini yace

"Open your eyes" a hankali ta fara bude idanun nata har ta kammala budesu gaba daya

"Ke wacce irin mara kunya ce?,ban gaya miki banason tsaki ba,kinyimin tsaki kin harareni me navi miki? ni sa'anki ne? ko don na aureki shine garamar qwaqwalwarki take gaya miki yanzun dai dai muke kamar yadda take gaya miki a baya?" Ya jefa mata tambayar yana tsareta da kallon nan nasa me ladabtar da kowa ba tare da yayi magana ba. Kalaman da ya gaya mata sai suka tunzurata,ta danne tsoratar da tayi din ta sake galla masa harara
Chapter 100 · 0% Book details