← Book details So Makamin Cuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 98 OF 132

Sashe 98

So Makamin Cuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana cikinn jirgin ma tana kuka, duniya ya mata zafi sosai
Cikin ranta tace" i just lost evrything ba family,no friends,gashi ni kenan babu wanda yake so na na gaskiya a duniya? Babu mahaifina
An kashe min mahaifiya ta shine take neman raba ni da ashween?
No, ai na gwammaci na zauna da shi har na mutu ena saukar masa dakai tunda naga shi kadai ya san mutunci na a duniyan nan koma wani irin laifi na masa ,

Ashween shine masoyi na na gaskiya da amana cos he neva lives me duk munin hali na.
Yau ko zanje ya dinga kunna min wuta ne a jiki na na amince da na zauna da muguwa azzaulamar matan nan.
Cikin wannna halin ta isa yola.

Ko kafin ta isa gidan ma tuni wani zazzafan zazzAbi ya sake rufe ta.
Bacci kawai take yi in ta shi ta sha giya ta sake komawa aikin kenan sai ta dawo bata damu da kowa ba.

Har tsawon kwana ukun ana yau su jasmine zasu dawo,
Shima ashween yau ne yayi niyyar fada ma jasmine komai akan zahida in suka koma gida

Don sosai jasmine ta warware ta samu sauki.
Jirgin karfe 9 na safe ya dawo da su nigeria..

Yau da aka sanar ma zahida ash zai dawo sai ta shirya tsaf din har ta zube cikin kwana ukun fuskan ta ya lotse kadan alaman ba adai dai take
ba.

Haka tayi zaman diris tana jira ya shigo gidan ta samu wanda zatayi sharing worries dinta da shi ko zata samu sauki saukin abun aranta.

Kullum wutan daukan fansa ke huruwa aranta gashi ta kasa daga waya tayi magana da madam hidayat gani take zata iya kwaba komai intaji muryan ta.

Tun a hanya doc yake kiran Ashween akan ya kawo masa medical history na cikin jasmine
Komai da komai kamar yadda ya bukata.
Don yana so dama yayi employing home nurse wanda zata na zuwa jofa jifa tana kula masa da lpyar su.

Wani sabon kwanciyar hankali jasmine take ji musamman da taga yana nuna kulawar sa kanta sosai har da kari.

Sai dai ta matsu taji meye yace zai fada mata in sun zo gida.
Don tun jiya da dadddare yake maimaita mata akwai muhimmin maganan da zasuyi da ita.

Suna isa gida Baibi ta kan kowa ba yayi sauri ya sake ficewa don yayi muhimman baki a office din sa,ya ce ma jasmine ta huta
In yadawo zasuyi maganan
Anan dakin ta kwanta tana hutawa cikeda tunanin lovely memories din da sukayi sharing da shi cikin kwanakin
A hankali take shafa cikin ta tana lumshe ido cikin godiyar Allah da kaunar mijin ta

Yana fita da mota a gidan nan zahida ta farga ta sauko da gudu don ta tare sa ta ko don ma ta gwada masa ai ta dawo gidan amma da shikd sauri yake sai bai ganta ba.

Anan ta tsaya ta dan ciza yatsa wani abun yace mata ki shiga kawai ki jira shi ai zai dawo gidan.
Tana kaiwa one step taji an sake bude gate

Juyowa tayo taga wani motar ne daban ya shigo sai ta tsaya

Doc ne ya fito, tana kallon sa har ya karaso sai suka gaisa
Yace madam na zo ganin oga ashween ne.

Tace oh ai yanzu ya fita.i think he's in a rush
Lpya kuwa?

Doc yace lpya lau dama na kawo masa files din dayayi requeasting ne na medical history
Bata bari ya karasa ba tace ok ,bani na ajiye masa ai nice matar gidan

Shi dai doc baiga kamar ta da pasport din jasmine ba amma sai ya mika mata ya juya abun sa ya fice

Dakin ta ta nufa straight da shi da har zata ajiye ta fada wanka ,sai ta dawo ta dauka
Ita kanta bata san meya sa ta bude ba, ba ta jira komai ba sai ta soma karantawa a nitse

Gani tayi, sunan jasmine da nashi an cike su ga pasport din ta a manne
Ashween As father da jasmine mother na unborn baby 6weeks old
Sannan ta karanta komai information daya biyo baya Har da date in haihuwa kaf ta gani..

Kafim ta gama dama ta soma diga da hawayen hannun ta na karkarwa
Kanta ta rike,tana jin wani mutsa mutsan hauka na hargowan subuce mata,

Ta kalli gabar ta kalli yamma a haukace Tayi wani irin firo da abun akasa ta channa wani firgitaccen ihu ta dire kasa tana birgima kamar zarrariya.
Cikin bala'in kunan rai ta ce ""Ash ka cuce ni,ma yaudari yau sai na tarwatsa ka
Ta sha numfashi mai zafi kirjin ta na dagowa sama sama

Ta mike tsaye tana zare horrible and furious eyes din ta tace :Yau sai na nuna maka ni ba kanwar lasa bane Ashween.

Da sauri ta fito fuuuuhhh kamar zata tashi sama zuciyan ta ya kafe tana cewa yau kowa zai san wacece zahida a gidan nan,kowa sai ya dandani azaba yau bazan kyale uban kowa ba a gidan nan......

*nikam bana nan ooo🤷🏼‍♀🏃‍♀🏃‍♀🏃‍♀*

*FILIN NAZARI*

*nace ba,amma fans ya kuke ganin ashween zai kare kansa da jasmine a hannun zahida after dis tangible proof ?wai shin in akace ya tona asirin kansa wa zahida agaban jasmine,.. jasmine ta tsira kuwa?*

*To inya ki tonawa ita matar sa ce har ila yau wani hukunci jasmine zata dauka musamman da baisamu dama ya sanar da ita wacece zahida ba?🤔🤔🤔*

*surriem*
*⚜BRILLIANT WRITERS ASSO🖊*

💔

*SO MAKAMIN CUTA*
_'the sword of evil love'_

_Story and written by_
*SURAYYAHMS*🔥

*DEDICATED TO-*@UMMERHERNY NERSALLAH.

*Page▶71*

'Zahida ta fito Ba kowa a wajen sai mai gadi da driver suna hiran su

Ba takalmi a kafanta sannan idon ta sun kafe sunyi ja zir da hawayen bakin ciki da kunci..jikin ta na bari tana kyarma ta kira su a gagauce ta ce ma driver ena zata samu hot acid?

Ya gwalo ido cikin mamaki yace madam babu anan kusa gaskiya
Sunayi suna dar dar don yanayin ta ya nuna alaman ba lpya ba

Tace toh kaje ka bude gareji ka bude motar uban koma waye
Ka hado min ruwan batir yanzu tafada da commanding voice.

Cikin tsananin tsoro dukan su sukayi shiru suna kallon ta basu motsa ba
Cikin Wani razannanen tsawa tace me kuke jira ne?look na baku 10 mints in ba haka ba harbe ku zanyi yau a gidan nan .ta ja gefe ta tsaya

Ba musu suka bar wajen
Kowa jikin sa na bari hanjin su na kuka don tsoro

Duk sun sani cewa ruwan ba3 wani bin ma yafi hot acid illa domin kuwa zallan concentrated sulphuric acid ne wanda ko ma ginin block aka zuba sai ya narke ya zube kasa bare mutum..

,a yanayin zahida ko da ba'a fada musu ba sun san ba alheri za'a aikata da ruwan bat3n ba

Nan driver ya shiga kunce kunce ya soma hada ruwan ba3
Ganin yadda abun ke watso musu wani mummunan wari mai hatsari ma numfashim dan adam ya sa mai gadi yace wallhy wallhy nikam zan kira oga
Don Ba zan iya wannan aikin ba

Driver yace ka rage murya kar taji ka
Kayi sauri kayi hakan don nima bansan me zance ba in wani abu mummana ya faru.

Nan mai gadi ya boye bayan bishiya ya ci kirar ash bai daga ba
Chan hikima ta zo masa sai ya tura masa tex massage.

Suna gama hada ruwan ba3 ta karbe bata ko sauraran zafi da hargowan da yakeyi sai ta ajiye a dai dai kan step daya raba site din gidan

Ta kamo hanya ko ajikin ta sai sauri take ta tayo dakin jasmine.

Idar da sallar ta kenan ta zauna tana lailaya cikin ta duk hankalin ta ya koma kan yaushe ashween zai shigo don tana mugun jin missing dinsa.

Zahida ta banko kofa tayi Wani munafikin murmushi ta bangaje kofar sai dayayi kara
Kallo daya zaka mata kasan bata cikin hankalin ta

Jasmine ta mike tsaye a dan razane tace mata lpyar ki?

Dariyar hauka ta bushe da shi gashi kafar ta ba takalmi kanta ba dangwali sai uban hawayen takaici da ya bushe a fuskan nata.

Tace " yi min shiru munafuka karuwa, yar iska mai raba gindin ta a titi, yau ni zahida zan koya miki tarbiyan da uwar ki bata baki ba

Jasmine tace ahayye, kaji masu neman motar kano a china'wani tarbiyan ne dake wai goggo yaga gaban liman ?kije dai kiyi makarantar tarbiya ma kanki dan yanzu kece tababbiya,jaka.jahila anan wajen...

Zahida Ko sauraran wani magana daga bakin ta batayi ba tayi wuf ta chakoma hannun ta ta damke su duka biyu damka mai tsanani

Da shike ita kanta zahidan ba acikin hankalin ta take ba ta riga ta harba dokin zuciya wani karfi take ji da shi ma masifa..
Jasmine ta soma kokuwar kwace kanta a hannun zahida amma kamar bata komai

Sai jawo ta take a zuciye zata kaita enda ta ajiye ruwan batry ta watsa mata.

cikin bacin rai jasmine tace ki sake ni,

Shiru bata amsa ta ,ta cigaba da zagin ta tana cewa sai ta hada ta da yayan ta,

Nan ne ma ta juyo da murdadden fuska ta kalle ta "tace yaya indeed,
Wanda kika gama ware ma sa kafa ya dura miki dan shege ?
Wawiya,slut,ure a hoe jasmine dama naga take taken ki kaikayi kashin gindin ki keyi kuma kin ci nasara an sosa miki har kin dauka,
Ta dada zare mata furious eyes dinta tace
Amma ki sani da ga yau ba zaki sake aikata ma wani haka ba bare ni zahida..

Nan ne Jasmine ta soma kukan bacin rai tace enough,
Pls leave me alone zahida bana son tashin hankali.kije chan kiyi dashi bada ni ba
Chapter 98 · 0% Book details