← Book details So Makamin Cuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 116 OF 132

Sashe 116

So Makamin Cuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mrs hidayat ta tsaya shiru gashi angama chinchirindo a kansu ana kallon ta,, ranta a bace yake amma cikin zuciyan ta ta kudiri niyyar duk ritsi sai ta fada ma zahida maganan nan amma ya za'ayi tafada wannan Babban magana agaban mutane? Take tayi kasa ta zube kan gwiwar ta ta kamo kafar zahida don tasan zahidan tan akwai rauniin zuciya

tuni saita sauya murya kalar tausayi tace haba zahida ,ni fa uwa ce
duk da nasan na cancanci duk wani wulakanci awajen ki.
Amma ena so ki daure ki saurare ni na gaya miki abunda ke tafe dani dan Allah..
bazan iya fada Anan bane don ena kaunar ki sosai har yanzu yata ki tuna fa nina raine ki na kula da ke pls beauty ki saurari mum din ki mana..

Zahida da tuni abun ya ratsa ta amma sai fiske ta dada daure fuska, tana so ta saurara amma Sai ta kasa yanke hukunci don sam sam bata jin ko digon yarda tsakanin ta da mrs hidayat yanzu..

Kawai sai ta juya zata koma ciki abun ta mrs rod tasake dukar da kai kasa tace zahida pls dont go and leave me here ki saurare ni kiji

Zahidan ta ja tsaki amma abun na dada damunta ta sai dai takasa furtawa,
Ko da ta juyo
Bata ce ma mrs komai ba
kawai sai ta sauke bala'in akan mutanen da ma'aikatan da suka taru suna kallon Draman

Cikin seconds kowa ya watse itama ta shiga ciki sai da ta shiga office ta zauna sannan tace aje ace mrs rod din ta shigo

Tayi murna sosai don har ta fara tafiya ganin zahidan taki aminta da ita..
Nan tabi bayan security aka kawo ta gaban zahida.

Tace nagode yata daman nasan kinada imani gurbata ki ake so ayi..

Tuni zAhida ta mata wani banzan kallo tare da mata hannu tace dakata malama
Na baki minti 5 ki fadi abunda zaki fadi kiyi waje bana bukatar bata lokaci na dake..

Gum tayi da bakin ta tana wani hadiyan bakin yawu nan bada bata lokaci ba ta soma bata labarin komai har da yadda tayi da saminu har da ce ma zahida ai tinda ya munafice ni kema zai miki shyasa dole ya muti ko ya ta?

zahida na shiru har ta soma bada labarin na ashween
da yadda tayi ta gano ashween ne lateef sannan ta soma kokarin kawo mata wasu alamomi tana dada zuga ta,tana cewa ki duba dai da kyau ki gani zahida Ashween shine lateeef fansa kawai ya zo dauka akan ki..

Still Zahida na shiruuuuu tana kallon mrs rod, da ta gama sakankan cewa tana dada koro bayanai don sosai ta shirya maganganun ta dama

Chan sai Zahida ta jingine baya tare da lumshe ido nan ta sake Wani mahaukacin dariya mai sautin ban mamaki

Tayi sosai har hawaye na droping tana nuna mrs hidayat da hannu kamar kashi take kallo ajikin ta amma dariyar kawai take bata ce komai ba

Mrs hidayt tuni ta ja baki tayi shiru don harga Allah ta kasa gane kan dariyar zahidan izit for her?ko againts her.?

Ta dai daure tace zahida pls believee da gaske na
Ke fada miki wannan magana, kar ki ji komai ena tare dake bazan barki ba,zan taimake ki plz zahida

Nan zahida ta yanke dariyan chak ta taso in full ta karaso gaban mrs rod daf da daf

Tace sake maimaita min naji?
Kikace wai lateef shine Ashween? Ba tantama
Mrs rod tace eh shine, sai fas zahida ta dada wanka mata mari akan bakin ta

Abun yayo mata zafi sosai ta kame bakin sai ta dago jajayen idanun ta nan taci karo da na zahidan shima wanda babu alaman wasa aciki

Tace tufff da bakin yawo munafuka makiran mata, ashe bazaki saduda ki bar min rayuwata ba?
Why did u hate me so much mena miki a duniya ta fada a raunane idon ta suna shirin cikowa"

A daburce Mrs hidayat ta budi baki zata yi magan a
Zahidan ta daka mata wani mummunan tsawa tace" amma kin ma cuci ashween da kika hada shi da mummunan danki nakasashhe,? Tirrrrrr Allah ya kiyaye
Dube ki? Oh din ana miki kirarin kin haifi kyawawa is dat why ure now claiming my man?
To ai ba sai kin masa sharri ba wai to Meya sa zaki rabani da shi bayan kin rabani da iyaye na?

Look,U must be a fool da zaki sake tunanin ni zahida zan yarda da ke da kuma wayannan ridicoulous tales dinki na karya da munafurcin da kika shiryo, am tired of ur lies hidayat just get out of my life..tayi mata nuni da hanya a fusace

Mrs rod dake cikin wani yanayi na kunci da rudani ta kasa motsawa sai hawaye sai ta dukar da kai kasa gwanin tausayi tace kiyarda dani zahida ashween dan uwan ki ne he's just fooling you..

Abun ya ishi zahidan don gani take duk dan kudin ta mrs rod ta hada wannan plan Din .
Sai ta ja cheque book ta rubuta kudi mai yawa ta wurga mata

Tace ki dauka ki fita nasan damuwan ki kena if not dont blame me in nayi miki wulakancin da dani dake ba za muji dadi ba and listen ke ..baki da mahaifar da zaki haifi ashween,domin yayi miki nisa har ki mutu bazaki haifi kyakkwan yaro kamar sa ba.
Ga hanya
...ta dan tura mrs rod da tayi zugum tana kallon kasa kalar tausayi

Sai itama ta dan fizge cikin bacin rai tace zahida nagode da kika ki yarda dani afterr all i did to u.ba kunya ta tsuguna ta dau cheque din ta ce toh na barki da Ashween zahida ya kashe ki in yaga dama, but ki saurare ni da kyau wata rana ke da kanki zaki zo ki nemi ni kuma kice na gaya miki...kaiwa nan ta juya zata tafi

Zahida tayi wani wawan yinkuri ta shagaban ta tsaya..
Ta bi ta da munanan harara kafin tace,..wannan duk ba damuwa na bane,so listen and listen carefullly ki sani duk maganan da mukayi da ke gasu nan anan ta mata nuni da recoder da secret cameras tace to walhy wallhy hidyaat ciwon kai ya taba Ashween zan miki wanin irin kisa wanda za'a kafa tarihi da shi a duk duniya

..na rantse miki in har kin ga nida hannu na ban tarwatsa ki ba to tare muka tarwatse..
Get out and neva come back forever ta gaya mata cikin idon ta..

Tsaki kawai mrs rod tayi ta kama hanya ta fice abun ta..

Zahida ta zauna kan chair tare da sauke ajiyan numfashi don bawai maganan bai shige ta bane amma sam ta kasa ganin alakar Ashween da lateef sai ta yanke kawai hauka da son zuciyan ne ke damun hidayaat ba wani abun ba..

A gefen jasmine yau ma tun safe ta bar gida ba wanda ya sani
Da shike site din ta akwai enda zaka sauko ta balcony kayi kasa ta bayan gidan
Sai ya zamo in ta yi niyyar ganin mijin ta sai kawai ta saci jiki ta fita tayo iya yadda take so sannan ta sake satar jiki ta shigo baki shiru..

Ashraf a dakin sa yana kwance ba abunda ya damu dashi sosai kamar change of behaviours din nata gashi tunda mijin ta ya dawo rayuwar ta duk wani rama da fuskan damuwa sai ya kauce ya bar ta a asalin jasmine din ta.

Shi burin sa yanzo ya shawo kanta ya sami biyan bukatar sa amma ya rasa ta ena ma zai fara.

Tunanin me yayi oho sai ya tashi ya fito ya kama hanyar dakin ta ya tarar a bude kam amma ta bai ganta

Cikin dabara sai ya zo ya tambayi mamy sai ta ce mai ai jasmine na daki tun tuni.

Nan ya fahimci cewa hala ta fice ne ba da sanin kowa ba amma where could she be?
Gashi ana neman 9.44pm na dare

Waje ya fita shima ya zauna cikin motar sa a asalin bakin gate inda ba wanda zai gansa

Ko minti 10 baiyi ba ya yaga dosuwar mota amma bai san nawaye bane'
don tuni ash ya sauya fita da wani motar da ba wanda yasan shi da ita don idan jasmine ta saci hanya ba daman daukar motan gidan mamy a napep take zuwa wajen shi.

a hankali suke tafiyar su don haka sai ashraf ya dada sa ido da kyau ga duhu ya soma yi baya ganin waye aciki da kyau

Dan daura da gidan ya tsaya charaf sai ya hango ta gaban motar alaman tana magana ne da wani sai langwamewa takeyi a jikin sa yana kissing dinta har suka rabu ta fito..

Tafiya take yi kamar bazata yi ba tana juyawa tana kallon sa don dama in ya ajiye ta har sai ta shiga sannan shima ya bace

Hakan kuwa akayi a idon ashraf sai ya daura hannun sa akai baki bude yace innalihh, tabbbbbbbbbb lallai jaraba ya kai jaraba ..yana dada leke yace ashe haka yarinyar nan take da bin maza shine ni take raina min wayo ?
Karuwan ci ashe take zuwa da Auren nata sai ya karashe da dariya mai ban mamaki...

Chan ya tabe baki kawai ya shiga gida ya kwanta a dakin sa yana nazarin yadda zai ga waye ne wannan da jasmine take fita dashi a sace ba a sani ba.

*Thnks for ur time*

*suriem*
[23/08, 05:43] ‪+234 806 071 2446‬: *⚜BRILLIANT WRITERS ASSO🖊*

💔

*SO MAKAMIN CUTA*
_'the sword of evil love'_

_Story and written by_
*SURAYYAHMS*🔥

*DEDICATED TO-*@UMMERHERNY NERSALLAH.

*Page▶83*

Tun ranar ashraf ya qudiri niyyar sa na sa mata ido don ya fahimci kan abun da kyau.

A ganin sa in har ya kama ta dumu dumu da wani namiji toh tabbas zai yi amfani da wannan dama yama razanar da ita cewa zai gaya ma mamy har ya samu biyan bukatun sa.

Ashween yana komawa gida cikin daren zahida ta kira sa don tun zuwan ta sai yau suka sake waya da shi.
Chapter 116 · 0% Book details