← Book details So Makamin Cuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 132

Sashe 36

So Makamin Cuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dayan tace..ah' a hakan bazai faru ba, don nasan wannan jikar tawar jaruma ce ,daga yau bashi baci ko sha awaje bare ya ji muryan wata mai pure watar ta cigaba..
Ki duba mana ki gani ko da muka shigo dakin nan ya kika ji ?...ai gamshin nasa dakin sai yafi haka ta sannan ta dubi gadon tace """ehen nashi ma sai yafi haka gyaruwa
Har na shirya ganin jikoki na ,
Nan duka suka danyi dariya da guda lokaci daya...
itako ta sunkuyar da kai kawai tayi don kunya. Haka suka ci gaba..
ita dai batasan su ba amma a cikin wasan nasu take tsintar shawarwari sosai gwanin birgewa

Gefe guda Kuma Ashraf ne tsugune sai kukkuni yake hannun sa rike da kuncin sa alaman ya karbi mari mai zafi daga wajen mamy datayi tsayin daka akan sa tana azalzalan sa
" to sai ka hana abunda Allah ya riga ya qaddara mu gani ,ta Balla masa harara
Da Allah fice min karka bata min rai

Ba musu ya tashi rai a dagule ya nufi dakin sa
Zirga zirga ya shigayi
daga baya ya dawo ya kifu da kan gadon sa yana famar maida numfashi...tunani yakeyi sai
Chan ya yi wani wawan wurgi da wayarsa fas ya tarwatse a kasa

kanshi ya rike ya koma ya tsuguna kasa nan take hawaye suka soma sauko masa yana cewa
" no, no ,ban rasa ki ba jasmine,
Bazai yiwu ba yafada cikin wani kara mai tattare da bacin rai..

Wallhy ba a isa a hanani cika buri na akanki ba dik dakon jiran ki da nayi?
A haukace ya ke girgiza Kai yce
Nooo, jasmine is mine,tawa ce
Kuma yanzun kowa zaisan da haka
ya karashhe da wani busashhen dariyan takaici

Gefen su mamy ko an shirya jasmine tsaf cikin kayan ta dark purple din da ashween ya kawo
Sosai tayi kyu duk da kukan ammyn nata datayo sosai kamar bazata bari ba

Wajejn karfe 10n safe aka yi mata karamin walima wanda ya kunshi zallan yan uwa da abokan mamyn

Duk da abun na cikin gida ne sosai ya kawatar... anci sosai kuma ansha ,
Sannan mamy tayi sourvenirs nagani nafada..
Har jasmine ta soma tunanin yaushe duk tayi wannan aikin cikin dan kankanin lokaci .

Misalin karfe 2.30 kuma aka daura auren a babban masallcin garin abuja,
Nan ma ya samu albarkacin dumbin mutanen da suka zo sallahr juma'ah ,
Kowa saida yayi san barka da fatan alkhairi..

Ashraf kuwa Yana daki yana juye juyen sa baije ko ena ba ,
Sai chan ya fito yace
Yanzu kowa zai gane kuran sa agidan nan
Sannan ya nufo dakin jasmine din cikin sanda enda ba wanda ya gansa

Don haka ma ta Baya yabi enda zai sada shi da window
Charaf kuwa ya ganta kwance tasha uban kwalliya alaman bakowa tare da ita tayi luf tana danne danne a waya

Wani murmushin mugun ta ya sake yace alhamdullhi, perfect
yau dai
Da muga waye angon anan ko ni ko ashween....

🙆🏽‍♀😥

*surriem*
[23/08, 05:42] ‪+234 806 071 2446‬: *⚜BRILLIANT WRITERS ASSO🖊*

💔

*SO MAKAMIN CUTA*
_'the sword of evil love'_

_Story and written by_
*SURAYYAHMS*🔥

*DEDICATED TO-*@UMMERHERNY NERSALLAH.

*SURAYYAHMs fans page and groups👏🏻👏🏻*

💋

*Page▶24*

Karar budewar kofa ne bazata ya razanar da shi yayi saurin tsugunawa kasa kar agansa ....bai bar wajen ba don yayi niya duk rintsi yau sai ya nuna musu jasmine nashi ne ...don haka yakai minti 10 bayan window yana jin tana magana alaman mai aiki cevta shigo aika
daga bisani kuma da yaji shiru..ya leka sai yaga bakowa awajen.
Da kyr ya lallaba ya koma daki ya cigaba da hade haden sa..

Gefen ashween kuwa Tare da kamal suke tafe bayan yagama amsa wayar zahida data zage tana neman daga masa hankali cewar ankira ta daga chan porland an gaya mata an daura auren ashween da wata daban...

' da shike tinkiya ce bai dauki dogon lokacin wajen shawo kanta da cewa "ai shine aka daura auren sa ba ashween ba,don ma ya tabbatar mata sai ya tura mata hoton auren sa da salma
Anan ne ta sauko tace..hmm ai ko da yanzu yanzu zan diro kasan nan... karya ne wata ta aure min miji ashween is mine..only.

Kamal yayi dariya sannan yace becarefl kawai ,,kinga gashi an soma baki wrong ..

Ehh haka ne kamal Tace ...ena yake yanzu?

Ashween na nan na jiran ki a yola ,sai kinzo
Da hakan ta gamsu amma tana Allah Allah lokaci yayi jirgin ta itama ya dawo nigeria ta ga ashween ido da ido cewar ta
Kwana biyu da ya shareta basu cummunicating har kuka takanyi don tsaban missing dinsa dake addabar zuciyan ta

Ko kula surutan su da kamal din baiyi ba yana fama da tunani kala kala ,gashi har yanzu da yake jin ya mallaki princess dinsan amma sam bai daina jin haushin ashraf a ransa ba,

Walkiyar camera ya gani wanda ya sashi yin wani kayataccen post bazata

Kamal yace "Wow, kaga ango,yau ko zahida zata kashe kanta sai nayi posting wannan pics din
Gaskiya ka hadu na jasmine ruwa sai antace,

Dan karamin tsaki ashween ya ja baice uffan ba ya koma ya dada jingina bayansa kan sit
Kamal kuma na tuka su a hankali har suka isa gida..
Duka fararen kaya ne ajikin su fadin kyun da sukayi bata lokaci ne

Kai tsaye ya shiga site dinsa ya tattare sauran abubuwan da bai kammala ba don umarnin ammy ne akan ya tafi da jasmine cahn yola asalin gidan sa mallakin kansa bayan aure duk da ma tasan bai cika zuwa chan ba.
Ta fannin Jasmine Dama chan ita kam ba abunda ya dauka mata daga dakin nata ,dan haka yaja ya kulle kofar ya sauko

Shikam kamal zama yayi tunda suka shigo yake waya da salma don har kuka tayi don rashin halartan bikin kawarta
amma ba yadda ta iya uzuri ne babba ya dakatar da ita.

Can suka kammala da kamal, ashween ya ba ma wayar suka gaisa suna hira da salma sama sama har suka shiga mota
shi kuma yana tuka su har suka fice suka nufin gidan iyayen kamal din

Ranar salma cire kunya tayi ta mika Amanar kawarta sosai ma yaya ashween' murmushi kawai yake yana amsa ta
Don Bai ji mamaki ba dama shi da chan tasu ya zo daya da ita..don tana da mugun kama kai da nitsuwa.

Anan gidan su kamal din suke Kamar da wasa har sukayi sallahr la'asar

Nan ma kamal ya shiga masa barkwanci yana nuna masa likes din da hoton ya samu cikin awa daya tal
Bai kula sa ba..shikuwa
Yana cikin scrolling
Ya gano hoton amarya jasmine a shigar da aka mata na daurin aure wato pitch material din nan
Wanda Jide of stola Make up artist din da suka mata kwalliyar walima dana daurin aure duka sukayi posting sai rububin sa ake yi a media

Lokaci guda ya gauraye ko ena amma an kasa ganin futher updates saboda auren ba wani hidima..

Kamal Yasan inyayi wani xclaiming akan kywun datayi mutumin sa zaiji haushi don haka ya danne abun aran sa saida ya kammala hada hoton kamr pics mix sannan yace

" hey look,kaga family photo, su jasmine ansha kuka kuwa gashi kyuw batayi ba'' hmm

Ba shiri ya juyo ya kwace wayar don yaga meke faruwa don ya tsani ace masa tana kukan nan ..

Idonsa na sauka akan hoton Wani kayataccen murmushi ne ya kufce masa
yakai Minti 10 yana gushing din kyunta a duka pics din a ransa

Kallo kawai kamal yake binsa dashi suna hada ido ya tuntsire da dariya
Yace, ango"
Toh tashi muje mana muga amryan namu face to face kaga sai ka kalli original achan

Dan karamin dariya ashween yayi baice komai ba sai da ya mika masa wayarsa yace ai dama dole ne ma mutafi yanzun
Jirgi na karfe 5.30 zai tashi kuma kasan zamu tsaya a adamawa na duba gona kafin mu shiga yola ko?

Ba musu kamal ya ce toh ai sai muje
Kaga nima sai na isa ga baby na naga ya ake ciki da maganan ummah a asibiti...nan suka sallama da gidan suka kama hanya ba bata lokaci

Gefen su mamy tun kafin Wajajen hudu saura aka kammala shirya mata komai tsaf da duk wani abunda hajy hadizan ta tanada mata na gyran mace budurwa,turarruka na jiki na kaya na gida,da kayan tarkace masu amfani ga ma'aurata..
Wasu tuni tasata a gaba tayi amfani dasu wasu ta mata bayani har rubuta mata sai da tayi ...
Sannan daga karshe ta dada jan hankalin ta sosai ta sa mata albarka...

Nan ta bada ba masu shirya ta waje tare da mika musa sabbin kaya wanda ta hado daga bangaren ta

Material mai kama da lace ne farare sol, riga da skirt da mayafin sa
nan aka kwama mata shi aka mata simple make up mai dauke numfashi
Qamshin dake tashi jikin ta har wani jiri takanji jifa jifa....

Dama da alwalar ta don haka bayan an watse
Kowa na kasa ana jiran zuwan ashween

Nan ta dauko qur'ani ta dan soma karatu kusan minti 20 don zuciyan ta yaki dena bugawa tun safe...amma tanayi
A hankali ta soma jin normal komai ya soma sasaauta mata a zuciya lokaci daya,,
"tana kaiwa aya
ta sauke ajiyan zuciya tace Alhamdullh,,
nan ta Dago kai charaf suka yi ido hudu da ashraf tsaye yana kallon ta...

Mamaki ne a fuskan ta tana kallon sa don maimakon taga bacin rai tattare da shi wani munafukin murmushi ya sakar mata
Yana tahowa gaban ta..

Bata motsa ba har ya dakata ,
Murya a sanyaye tace Yaya ashraf

Tuni ya daga mata hannu alaman dakata bana son jin komai ,,nan ne ya daure fuskan sa ya soma huci wanda ya dan razanar da ita ta mike tsaye

Bata fasa ba tace kayi hakuri yaya ashraf wallhy ba hakan nayi niyya ba aurena da yaya ash qaddara ne...i ...i ....i am
Chapter 36 · 0% Book details