← Book details So Makamin Cuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 132

Sashe 9

So Makamin Cuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin zuciyar ta take rayawa"
Hmm lallai abunda shafiu(mijin ta na karshe ) ya mana ya taba mummy, ita dai damuwar ta kar arziki ya ragu sai dai ya karu"hmm just 1 mistake amma har yau tana min masifa akai..ikon Allah
Daga bisani ta dago tace
Jamal pls talk to her tunda kai bata fadi laifin ka ba
Ni fah gaskiya sai na auri ashween

Dan murmushi jabir yayi yace "Hmm dama baza ace yayi komai ba ai
ba yana kare ta a koutu ba

Shikam jamal Mikewa tsaye yayi
Ya ce ure unbelivable guys
In zaku sauke girman kai ku bata hakuri zaifi muku
Kowa dai yasan wacece mummy so suit urselfs ya fada yana lumewa site dinsa shimaa

Tsuka taja "Ba kunya ta mike ta shige site din mummyn kai tsaye ..nan ta soma lallaba ta
Da kyr suka samu fahimtar juna don kuwa zahida girman kaine da ita sosai

" ok fine mummy tace amma
Ba zaki aure yaron ba sai jamal ya kammala min bincike na akan sa inkin yarda fine,

Dan shiru tayi daga baya ta ce toh shikenan..na yarda

Wani makeken hotel aka kama domin hidiman domin tun a daren suka soma karban bakin musamman friends din sa daga kasar waje
Gayu ne tubarkallh kowa naji da kansa ga kudi..
Wasu sunzo da matar su wasu da yan matan su
Sosai aka qawata wajen
Yayi kyu sosai kamr an zana da hannu

Duk da partyn strikly on Iv ne waje tam ya cika da manyan Mutane kowa na dokan hancin kowa

Musamman atmosphere filin ranar ya sauya tsaban hidima da harkokin dake gudana a wajen
Karfe biyar aka soma red carpet, photo artist kala kala abun kwanin sha'awa
Ko wa ya zo sai an fadi title dinsa sannan ayi pic a bashi mazaunin sa

Daga cikin gidan ko Su biyu ne kacal a dakin ita da salma
Sai artist wacce ta specialisng wajen make up
Gyran gashi da duk wani harkan tande jiki
" haddadiyar red gown mai design din black stone gefe guda akayi sliding da wata bakar net mai kyaw
Colour kayan kusan iri daya wacce hudayya fadoul ta yi designing musu
Sai dai da shike salma batada jiki sosai flair gown aka mata wanda ya mata das das kasar kuwa ta bazo kamr sarauniya
black head suka sa kowacce ta kamo suman ta ta baya
Sosai sukayi kywu don kuwa kafin su fito sunsha pics ba adadi a dakin
Cikin surutun nasu Mai aiki ce ta leko ta ce
Jasmine madam na kiran ki
Ba bata lokaci ta bi bayan ta don da shike sun kammala shirin su dama tsaf

" simple suit yasa cool royal blue wanda daga ganin kasan ba na kana na bane
Sosai kalar ta dauke sa
Sai wani sheki yake kamr ba mutum ba
Ko da ta sa kai sai famar jan jelar gown din ta take tana tafiyar mai dauke hankali bata kallon gabanta bare baya

Gefe ya koma da sauri ya tsaya ya kura ma kyakkwar halittar ta kallo
" tubarkalh yace yana lumshe idon sa
Take wani abun da baitaba ji aransa ba ya ziyarce shi " sai yaji bazai iya bari ta fice wani waje a hakan ba

Da sauri ya bi bayan ta zuwa site din ammy
Kwance ya same ta jikin ammyn
Tana dariya dan ba karamin zugata tayi ba
" shigowar sa ya sa suka sassauta dariyar na su

Ammy" yafada fuska ba yabo ba fallasa
Come here, tace tana masa hannu
Ba musu ya shigo ya zauna gefe
itako ammy ba irin nasiha da bata musu ba
Don azuciyar ta
Tamkar ranar auren su haka takeji
" Jasmine jeki ki wajen su hajiya hadiza ki gaya musu sako na kinji

Toh ammy tafada ta wuce
Ya bita da kallo

' dan kallon sa tayi a nitse tace Yadai hero
Naga kamr hankalin ka baiya nan

Nop Yana nan ammy
I just have 1 request kuma nasan zaki min
Ya fada a marairace
Uhmm enajin ka
Amm' uhmm"
Ammy kice mata ta sauya wannan kayan ya fitar da shape dinta dayawa kuma fa cikin mutane zamu shiga yanzu

Sauya kaya kuma ashween? Tafada cikin mamaki
To wanne ZAta sa?
Chab jasmine ko anya zAta yadda m
Kaduba dai kaga yadda kayan ya mata kyuw ajikin ta

Ohh Ammy kiji abunda kike cewa fa?
dama sai ta yarda ne
ni fa wallhy banson Abunda
Zai bata min raine da sai na sata ta cire da kaina
Don dai ba zata fito haka ba kam, .

Batayi dogon musi ba tace "Toh naji bari ta dawo sai na sa ta sauya jeka kaima karkayi latti

Murmushi yay ya mike
Dan peg ya manna mata yace dats like yhu ammy
Ena jiran ki
sannan ya fita...

Karfe biyar da wajen rabi ashween da ammyn sa suka fito yana damke da ita
Nan aka dauki hotuna kala kala yan uwa da abokan arziki
Cikin wannan ribibin ne wata benz sport ta dosu wajen wanda kusan ya so ya janye hankalin mutane
Golden brown italian gown rabin gwuwarta ta sanya mai sliding hands sai sheki yake
Duk da shigar ta bai nuna alakar ta da tarbiya ba ba wanda ya isa ya kushe haduwar ta
Murmushi ta sake mai cike da jan aji tana tahowa ahankali
Yayin da kamal wanda shima tsaf yake ya daura sunglases a idanun sa ya karaso ya mata jagora

Tsaba rigima da jiji da kai dake dauke a fuskan zahida ya sa mutane ke binta da muzurai

Ashween da tuni ya ganta saibya dauke kai" ko ajikin sa yana tare da bakin sa sunata surutu ana dab za'a fara programes
Karar Shigowar tex din kamal ya sa shi cewa
Excuse me sannan ya nifo su
tun kan ya iso ta takure tana kallon sa" wow hes sooooo cute
Ba kunya ta juya tana kure sa da ido har ya iso daf
A lokaci guda suka sake ma juna murmushi "yace
Ure highly welcome zahidarod!
Thnks handsome im honoured "
cikin rigima ta amsa

Be my quest pls, ya fada yana mata jagora
chan sama wajen seat dinsa ya ajiye ta sai yauki take

Ba a dade ba aka soma introducing dinsa enda aka fadi matsayin karatun sa da kuma achievemts dinsa so far
Tafi ne ya dau wajen
Enda zahida take jin wani sabon shaukin kaunar sa musamman data ji yadda yaja kaya wajen harkan dukiya da muammala na rayuwa

Cikin ranta tace" Shine miji na ' hes mine
tafada makanta ta sake maimaita wa
Sai sake murmushi take ita kadai

Bayan kammala dan takaitaccen jawabin da yayi na godiya da sauran su
Nan aka soma perfomance na artist ,comedians da cultural events wanda ya bala'in sa kowa wajen nishadi
Sosai shagali yayi shagali zahida sam ta kasa zama waje daya duk enda yayi tana nan makale da shi duk da yana kau da kai . ..

Daga Cikin gidan shiru ba kowa sai sheshekar kukan dake tashi daga dakin jasmine
" toh ki kashe kanki mana, haba jasmine
Wani irin rarrrashi zan miki dan Allah ni wallhy kin fara ban haushi fa
Cewar salma cikin damuwa da tashin hankali "

' an tsane ni a gidan nan
Kowa na chan nine za'a wani ce min na zauna anan kamar wata karamar yarinya?

Kai jasmine ,kema kinsan Akwai dalili kibi abun ahankali mana

Uhm uhm salma ko don banyi kywu bane basu su na fita da su

Ke ma kinsan ba haka bane
Nidai zanso ki musu uzuri
da kike cewa anbar ki ke kadai
Baga ni ba
Tashi ki sauya kayar naki sai mu ci abinci ni yunwa nakeji

" ba musu ta dan sa hannu ta wiping ragowar hawayen ta tace
Barinje na dauko mana toh

Minti 15 ta dawo dauke da tray, mai aiki na biye da ita da sauran kayan kwamulashe
Nan suka baje suka sauka kan abinci
Suna hira kadan kadan har salma tayi nasarar kaucer mata yanayin datake ciki

"
Gefen su ashween kuwa sosai ammy tayi amfani da damr ta wajen nuna masa mutanen ta
Sannan ta yi signing din dukka companyn ta da sunan sa ta damka masa a matsayin tukuwici da amanar data bar masa duniya da lahira
' it was realy emotional don speech din data bayar sai da ya sa kusan rabin wajen kuka duk jikin su ya mutu
Nasiha ne mai ratsa zuciya da kwawalwr mai tunani
Shima Ganin maganan nata na neman masa illah yasa shi zamewa cikin dabara ya dawo gida straight ya wuce dakin sa
Bathrum ya nufa ya kure madubin dake bango da jajeyn idanun sa da suka gauraya da jimamin maganganun ammyn masu ratsa zuciya

Wani sabon kaunar ta yake ji na ratsa shi
Lokaci guda

"kusan minti 15 ya dauka sannan ya saita kansa ya kimtsa ya fito
Hanyar baya ya bi saboda kar agane fitar sa daga gidan kamr yadda ya shigo
Yana murda kofar yaji wani irin kara da ya kusa razana sa

Jasmine ihu ta sake tare da kankame sa gam tana maida numfashi jikin ta tuni ya soma rawa

'yana tsaye bai dau wani mataki ba saida ya nitsu ya lura da tsorata tayi ganin sa ta wannan hanyar
ga shi duk ta zubar da plates din gaba daya sun tarwatse a qasa

Lumui tayi Har yanzu tana kyrma hannun ta da ya kankame rigar sa sai karkrwa yake
Tsintar kansa yayi da shafo sumar kanta data bari ba dankwali a hankali yana saisaitata batare da yace uffan ba
' saida ta sauke wani nanauyan ajiyan zuciya sannan ta soma kokarin kwace kanta daga kan kafadar sa
Baiyi gardama wajen sake ta ba
Sai Binta da yake da kallo kamr wanda yake so ya tambayeta wani abun
' y'am sorrry ""tafada kamr zatayi kuka tana kallon kasa yadda plate suka farfasahe suka watsu

Binta kawai yyi da ido yace" Its ok..meyasa baki daura dankwali ba ?

Cikin Hanzari ta dago ta kallesa dan batayi xpecting wannan tambayr ba

Uhm dama zan kai wayyanan kitchen ne sai na sauya kayan jiki na

'har kin gama naki hidimar kenan? Ya tambaye ta kamr baisan bataje ba

Dan shiru tayi sannan tace
Ai ammy ce ta hanani zuwa
Chapter 9 · 0% Book details