← Book details So Makamin Cuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 132

Sashe 31

So Makamin Cuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Luiiii jasmine tayi zata kai kasa,
Amma suka riko ta,idon ta dishi dishi nan take jikin ta ya mutu, sai zazzAbi daya rufe ta nan take
' Tangal tangal ta somayi har ta isa gaban gawar ammyn tana mata wani irin kallon ena ma ace mafarki ne in tashi
Sannan ta kamo hannun ta Gam gam ta rike ta tana bin ta da wani irin kallon razana
Nan ta kife ta soma wani irin kukan zuci......tamkar bata hankalin ta

Ashween ko Dan siririn Hawaysn sa ya goge ya tashi tsaye ,don bakin sa ya dauke magana tamkar kurma haka ya dawo lokacin
Da kansa ya tashi ya riko jasmine din
Da ta soma fizga tana kwacewa a hannun sa "tana kuka"" ammy kimin magana mana
Please ammy,kar ki tafi ki barni take cewa cikin kuka amma sam bata cikin senses dinta..maimakon abun ya sassauta sai dada hawa take tana maganganu kamar zararriya
Shima dai ya rike ta ne kawai amma shi kadai yasan meya keji aransa
Da kyar ya daure yace jasmine!!!!!!! da dan karfi"
Nan ta dago ta kalle sa a daburce,,sai charaf suka hada ido da sauri ta fada kirjin sa ta sake wani irin razannan kuka"tare da kankame sa...tana kiran ammy

Hjiya hadiza ma da kyr ta fice ta isar ma mijin ta sako don a yi a kaita makwancin ta
ita gani take a halin da ake ciki ashween bazai samu gwarin gwuiwar yin komai ba tukkunna,

Dam suka rike juna kamar zasu shige cikin jikin junan su alokacin kowa da abunda yake ji na zafin rashi....a hankali yake rarrashin ta yana dan bubbuga mata baya don ta sassauta kukan nata,
Shikam tuni idon sa Suka Vushe ya makance ce baya so ma ya sake kallon ammyn
Don ya tabbata komai nashi dai motsi kawai yake amma na karfin hali
....
Jasmine dake hannun sa tayi lumui tana sheshheka Haka har ya mika ta ma mamy dake kokarin shigowa da mijin ta da abokin sa da ashraf .., amma ashween haka ya daure ya danne zuciyan sa kamr da wasa yaje akayi niyya aka kammla komai yadda ya kamata
Sannan suka kai ammyn makabarta ...
Nan ma Still hawaye bai sauko masa ba saida ya sa ta cikin rami da hannun sa
Nan ya ji gaba daya duniya ta juya masa baya, zuciyar sa ce ta soma ce wa
' Yah Allah kai kadai ka rage min yanzu banda kowa' ena rokon ka.. ka mata rahma ka kyutata makwancin ta fiye da yadda ta kyutata rayuwa Ta'
Na rasa uwa,uba da yar uwa da farinciki na gaba daya yau, Allah kai kasan dai dai,kasa chan ya fi mata nan..kaji kanta ya rahmanu
Sannan ya karashe da wasu adduoin..ya share hawayen sa .

Jasmine kam zazzabi ma ya hanata jin hayaniyar masu zuwa gaisuwa tun daga ranar farko
ashwenn bai bari ta sake fitowa ba don bata dawo ba...
Haka ma Kwata kwata ya raba ta da dakin ta ya kaita wajen sa inda ba mai shiga
don mutane suna mata magana saita firgice ta soma maganganu alaman bata cikin senses dinta har yanzu

Haka suka cigaba da zaman makoki abu kamr wasa
Bayan kwana uku kamal yayi shirin komawa shima bayan kammala sadakan uku...

Tare suka jera ba wanda yace uffan har saida ya kaisa bakin motar sa
Kallon da kamal ke masa ya sa shi
Da kyr ya kwakwulo murmushi yace
" saura inkaje kar ka isar ma amarya sako na,im so grateful naga kokarin salma data zo cikin danyen amarci" gashi bamu samu daman halartan biki ba ya karashe da dan fuskan damuwa

Dan karamin scuf kaml yayi don har cikin ransa ya san ashween daurewa kawai yake yana magana
Sosai damuwa ya bayyana a jikin sa da fuskan sa don har yayi fayau kamar mace mai sabon shigan ciki

Yace Kar kadamu ash,bakomai wallhy salman ma ta fahimci hakan "
Dama kuma kaga auren one time ne ba abunda akayi ,abun tsakanin family ne kawai kwana biyu duka duka aka dauka aka kammala
Gashi bata samu ta gana da kawartan ba ma,
Ya jasmine din take yanzu?

Tare da sauke ajiyan zuciya yace " alhmdullhi,
Nasa ta taci wani abu yau dai ..she will be fine
Ya fada cikin sigar tausayi
Dan dafa kafadar sa kamal yayi
Yace " nasan zaka iya ash, ka kula da kanka da yar 'uwar ka.
Shes all yhu got now
Dan gyada kai yayi yace hakane kamal..na gode
Nan har sukayi sallama
Ya juyo ya nufo cikin gida

Site din da su haj hadiza suke ya je ya dan leka su enda take sanar masa da yanzun ta baro jasmine din sai amai take amma da jikin da sauki..

Ba jira shima ya mike ya nifi site din san kwance ya tarar da ita ta rungume hoton ta ita da ammy tayi luf da ido kamar mai bacci....

😔🤝🏼

*surriem*
[23/08, 03:02] ‪+234 806 071 2446‬: *⚜BRILLIANT WRITERS ASSO🖊*

💔

*SO MAKAMIN CUTA*
_'the sword of evil love'_

_Story and written by_
*SURAYYAHMS*🔥

*DEDICATED TO-*@UMMERHERNY NERSALLAH.

And.
*UMMu FARHANA*
*MEEMAH TA*
*HALIMA LEEMAh*
Da kuma
*MOMyn MUFeeda*

*Kulli nafsin za'ikatl maut...Allah ya sa mu cika da imani*

*Page▶18*

Shiru shiru Basu ga dawowar ammy ba bare samun takamammen bayanim enda take..

Daga asibiti kuwa Har kusan karfe goma saura kafin aka cire ammy cikin life supporting machine
Sannu ,,sannu hajya hadiza ke jera mata
Da kyar ta daga ido tace
Hadiza karfe nawa Ne yanzu?

Tace Karfe goma saura ne tace tana duba agogon bango.. yunkurin mikewa ta somayi amma saita kasa nan tace
"ki kaini gida hadiza..ki kaini wajen yaya na ..kinga mun dade anan yaran nan nasan hankalin su a tashe yake yanzu

Shiru hjy hadiza tayi tana bin ta da kllaon tausayi
Chan sai ta kira likita aka daura ammy kan emrgency wheel chair suka nufo gida ba don taso hakan ba

Ganin ba motar ashween ya sa ta danji sanyi a ranta tunanin ta baidawo ba ma daga office
Nan suka shige daki a gaggauce ba wanda ya san da dawowar su"
Talatu ce ta shigo tana mutsil mutsil da jiki alamn bata gane meke tafiya ba nan dai
Ta soma zuba musu gaisuwa don sam kanta ya kulle da rashin lpyar ammyn lokaci guda

Ena jasmine?cewr ammy tana dubar ta

Tana chan sama dakin ta ,tun dazu take xaga nan bata ganki ba ,
Barin je na kirata enaga bata san kindawo ba

Ah ah,bari kar ki kirata tukunna, ena shi kuma yayan nata ko bai dawo bane?

Nan ma talatu ta shiga bayani 'Uhmmmm,ai oga baije ko ena yau ba,,shima wai baida lpya dan naga dazu jasmine takai mas magani a dakin sa
Ammy tace what? Baida lpya kuma?
Kinga ni ko hadiza ,kwana biyun shima hakan yake ta kananan zazzAbin nan..sai yace min gaban sa na yawan faduwa
Toh yanzun ena yake ta maida Kallon ta wajen talatu fuskanta dauke da damuwa

Ai ya fita tun 6 Yace dai zaije nemoki halan ma gidan hajy yaje

Ok shikenan Jeki ...
Ni bari na kira ashraff naji ya abun yake hjiy hadizan ta fada don ko hankalin ammyn zai kwnta
Bugu daya ya dauka a handsfree ta sa kowa naji
Bayan gaisuwa tace
Nikam ashween ya zo ne?
Ashraf Da kamar bazai amsa ba don yatsani jin sunan ashween din bare kuma shi kansa
Chan kasan makoshi yace
Yanzun nan ya fice enaga gida ya koma
Batace komai ba ta kashe wayar ta

Ta juyo ta kalli ammy dake maida numfashi sama sama tace Alhamdullhi,yanzu zai dawo insha Allah

Ammy tace hmm Dama nasan za'ayi haka
Kwana daya kenan basu ganni ba,enaga ace bana duniyar
Takarashe a sanyaye

Haba hjy shahida,ki dena furta wayannan kalaman mana dan Allah
Ena tare da ke insha Allahu zaki samu lpya

Gyada kai kawai tayi ta sake murmushi tace
" nagode hadiza
Banda kamar ki a duniya,
To Ni zan kwnta yanzu
Ko da sun shigo kice musu kawai nayi bacci..gobe su dawo

Toh ,cewar hajiy hadiza tana lullube ta ita kanta yana so ammyn ta huta ko jikin zai sassauta
Daura da haka cikin minti 30 ashween ne ya soma shiga dakin kai tsaye
bai kula ba ya nufo kanta kamar wanda yayi shekaru dari bai ganta ba
Amm..ammy ..Ammy? Yace yana lalubata a haukace
Cikin azama hjya hadiza ta mike lpyarka kuwa
Ashween?
Ammyn ai bacci take ko?

Nan ne hankalin sa ya dan dawo jikin sa
gefe yayi yana dan sosa keya alamn jin kunya yace toh sai da safe mamy.
Uhm Dama nayi ta neman ta ne bangan ta ba, ince dai lpyar ta lau?

Wani murmushin tausayi ne ya kufce mata musamman data lura da jasmine a rakube jikin kofa tana jin su
" sannan ta kalle sa tace kalau take,
Itama haka nan take ta tambayar ku kamar wasu kananan yara" sai kuje ku kwanta gobe ai kwa dawo ku ganta

Murmushi ya mayar mata baice uffan ba ya mata sai da safe ya fice abunsa

Buuut.... itama jasmine ta juya cikin sauri ta nufi dakin ta don ma bata bukatar ta sake haduwa da shi
Duk zuciyan sa yaki kwanciya amma sai yaji dama dama ganin ammyn a kwance ..don haka ya nitsar da kansa yayi baccin sa

Da sassafe karfe 5 saura ya dawo amma sai yaji gam kofar dakin don haka ya wuce sallahr asubahi abunsa

Zaune take kan sallayar sai habon jini take amma haka saida takai raka'atanl fajr din ta hade da sallahr asubahi
Amma kuma ta kasa tashi daga kan sallayar donji take kamr lokacin ta ne yayi
Hankalin hjya hadiza ba karamin tashi yayi ganin yadda jikin ya tsanan ta
Ganin damuwar kan fiskan hjy hadiza yasa ta "juyowa ta riko hannun ta
Nan wasu xafafan hawaye suka soma sauko wa a idanun ta " kiyi hakuri hadiza,..ki karfafa imaninki don yanzu make zan damka amanata " yara na,farin ciki na,rayuwa ta..
Na bar miki su hadiza,ki zama musu uwa duniya da lahira ...ki.....

Hjy hdiza da tuni take Girgiza kai nan ta shigayi tana kuka amma ta kasa cewa Komai gwanin tausayi
Chapter 31 · 0% Book details