← Book details So Makamin Cuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 121 OF 132

Sashe 121

So Makamin Cuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun alokacin Jamal da jabir sai suka sha alwashin kare kansu da dan uwan su,
suka kuma nuna masa zasu taimaka masa kota wani hanya ne ko don su wanke abubuwan da suka sashi ya fuskan ta a rayuwa.

Bayan kwana biyu jabeer ne ya fara komawa nigeria ya barsu da kyar aka rabu saboda kaf zuciyan su ya jike da shaukin so su tarairaya little bro dinsu su shagwaba sa da kulawar da da chan basu bashi ba.

Ash sai yaji wani sabon dadi da sanyi a ransa sosai
Nan Jamal ya sashi dole suka dan zauna a mexico bond din family na dada karfafuwa tsakanin su..

Washe garin da ash ya cika 2 weeks a mexico jasmine ne a daki ta kammala wanka tana shirin komawa tayi kwanciyar ta
Don sosai ta gaji da yadda ake mata kallo da tambayar kure a gidan

Ashraf kuma ranar ne ya gama shirin sa akan zaizo mata da magana
Don haka ba ko sallama ya shigo dakin nata ya tsaya durus yana kallon ta.

Tana tsaye jikin mirror fully dressed tace yay Ashraf lpya kuwa?

Bai amsa ba tukun sai da Yayi wannan shu'umin dariyan nasa yace "ke zan tambaya ai yanzu
Lpya kuwa, naga shi dadiron naki baizo ba ne kwana biyu?

Tayi wani irin shegen murmushi mai sauti tace yaya ashraf ai yaya Ash miji na ne.

Yace ohh i seee amma a gidan sa kike yanzu?ke dai kawai kice iskancin sa ke fitar da shi ke kuma jaraban tsiya gindi ba zip bazaki iya hana sa ba, hmmm kin shiga uku jasmine
duk da ma yana da karuwa a waje kuma kin sani sarai kike kai kanki wajen sa wai ance miki shi kadai ya iyayi da mace ne? Yana shirin yace mata gashi anan a gidan yaji in tace zata wulakan tasa sai yace zai gaya ma mamy komai

Amma Sai Tayi saurin tsaresa da tsaki mai sauti tare da cewa what eva,nidaii wallahy ka sake ce miji dan iska zaka ga abunda zan maka anan"sannan
in ka gama sai ka fita min don bana son cika Kunne.
Daganan bata sake cewa komai
Ta haura saman gado ta ja bargo ta rufu half
Waya ta shiga latsawa tana ready in yace zai mata wani abu ta kira mamy.

Shikam Bai daddaraa ba ya cigaba da zubo munanan kalaman batsa akan su gaba daya yana gwada mata ba abunda bai sani game da su ba.

Sai dai yana magana ne ammaa kamar da gawa bata ko motsawa bare tayi magana Abun ya mugun bata masa rai

A dan haukace ya karaso kan gado daf da ita zai mata tsawa tuni ta zugo qamshin turaren sa

Wani jiri ne ya daga ta da sauri a daburce tana tangal tangal ta rasa me ke mata dadi
bayi take so ta shiga amma sai tayi hanyar waje tana jan numfashi kamar mai jinnu

Anan fa shraf ya rude ya rasa meke faruwa da jasmine din
Ai kuwa tana dafa kofar dakin ta rusuna ta zube gwiwa ta soma kwaza amai akasa tana kuka

Ba jira ya yo kanta yana mata sannu don harga Allah ya tsorata da yanayin ta

A sukwane ya soma kiran mamy ,ya hargitsa gidan da ihun kiraye kiraye.

jasmine kuwa kamar ana hura mata wutan aman ne don jin sa akusa da turaren na dada tunzira ta

Kowa ya fito abban ashraf ne kawai baiya kusa
Mamy tun daga ka step da ta hango jasmine idon ta suka ciko da hawaye aranta tace wayyooooo ni hadiza na shiga uku kar dai Jasmine ciki ne da ita?
Take sai ta soma karkarwa ta kasa yin komai idon ta nakan jasmine tana bata close look

Alokacin brain din mamy ya birkice tunanin ta kar dai ace mata ciki ne da jazmine.
Tace To me zan fada ma Ashween?

A birkice ta karaso ta rike ta da kyau lokacin mai aiki na faman taya ta daga jasmine din dake kan amai tana kuka at the same time.

A dan razane mamy tace sannu jasmien wai meke damun ki,malaria ko?jasmine ko bata ko iya amsawa ba ta fada jikin mamy sumamiya.

Anan akayi da ita asibiti ruwa ruwa dukan su suka tafi aka bar mai aiki tana kimtsa wajen

A mota mamy na so ta tambayi ashraf me ya ma kaisa dakin jasmine
Don yanzu komai a zargin sa take yi

Amma sai ta kasa tana dai so a tabbatar mata eh hakan ne ko ba haka bane..

Da aka shiga da jasmine din ma
Suna zaune a asibitin zuciyan ta na kan rudani tace kar dai hana yaran nan zaman auren su ya jefa jasmine wani damuwa har ta bada kanta ma ashraf...

Ta runtse ido ita kadai tace noo.nooo yah Allah kaji kaina yau no
Me zanje ma yaron nan in ciki ne da matar sa da yabaro a hannu na
Wayyooo na shiga uku..

Tana cikin wannan yanayi bata sani ba har doc ya fito
Wanda yayi dai dai da zuwan abban ashraf wajen shima

Sai ma kawai ya fuskan ce sa suka gaisa yana cewa alhamdullhi Alhj,

Ai an Samu karuwa yarku tana dauke da juna biyu na tsawon wata 2 da kwana uku kenan.

Abban ashraf ya ce masha Allah tubarkallah sai yayi murna sosai ya gode ma doc

Lokacin mamy tayi suman tsaye haka shima ashraf.

Sai ta juya a gagagauce ta shiga dakin don ta same ta
Sai Tayo tsaye kan jasmine dake tsuru tsuru da ido kamar ba ita ba

Tace jasmine ena kika samo ciki?

Cikin sanyin muryya tace mamy ciki nake da shi da gaske?

Nan mamy ta daka tsalle ta mata wani ihu saida ta razana ta ja gefe tana bari

Abban ashraf ya kamo ta dam dam yace kull hadiza, kar ki sake kice zaki daga mata hankali ko baki ga halin data ke ciki bane?

Mamy Ta fashe da kuka mai dauke da rudani tace alhaji na shiga uku mena aikata da kaina?

Sai Ya jata shikam har waje ya damka ta ma ashraf yace suje gida kawai shi zai taho da jasmine

Mamy tun a mota take hada ashraf da Allah ya gaya mata gaskiya in shine yayo cikin nan.

Iya rantsuwa yayi amma mamy sai kuka takeyi tana jimami

Bata ma san shima ashraf din a hargitse yake ba
Don gani yake plan dinsa nakan gadan zare saura kadan ya tsinke

don shikam yasan ba tantama cikin ash
Ne a cikin jasmine

Itama jasmine a motar abban kuka takeyi sai yana dan rarrashin ta ba tare da ya tambaye ta komai ba

Don aransa ma dadi yaji koda bai sani ba yasan jasmine dole cikin mijin ta ne a jikin ta ba na wani ba.

*Gud morning people we are pregnant👯🏻‍♀*

*surriem*
[23/08, 05:43] ‪+234 806 071 2446‬: *⚜BRILLIANT WRITERS ASSO🖊*

💔

*SO MAKAMIN CUTA*
_'the sword of evil love'_

_Story and written by_
*SURAYYAHMS*🔥

*DEDICATED TO-*@UMMERHERNY NERSALLAH.

*Page▶86*

Suna isa gida mamy tayi cirko cirko a falo tana jiran shigowar su abban ashrf da jasmine

Shikuwa da suka shigo agaba yasa ta yace maza ta wuce site din sa yana kallo har ta lume ba wanda ya isa ya mata magana.

Ranar rayin mamy ya baci don sosai don taso ayira wuta wuta ne komai ya wuce mata.

Jasmine Gaba daya ranar a site din abban ashraf din ta zauna tsaban tsoro yadda mamy ta birkice ta kasa zama waje daya a gidan ita kawai a fada mata waye uban cikin dake jikin jasmine

Anan ma Ta hana ashraf sakat ta sashi a gaba da bala'i ta daga masa hankali sosai sai da ranshi ya baci har sai da yayi mata kuka kafin ta hakura ta kyale sa

Haka Abba kuwa ya tirje yace sam ba wanda ya isa ya taba jasmine har sai hankalin ta ya kwanta ayi maganan cewar sa kar aje a taba masa jika.

Wannan magana ya matukar bata ma mamy rai musamman da ta fahimci abban ashraf ko ajikin sa bai damu ba..

Shi dai sau daya ya tambaye jasmine din yace mata cikin na waye ne?
Bata ji kunya ba tayi masa bayanin komai sannan tace masa abba wallhy cikin na yaya ne ...
Yace Alhmdullh ,to gobe idan aka tashi magana bana so kiji tsoro ki fada mata komai kinga sai kowa ya huta ko?

Jasmine tace toh,anan tayi zamanta sai chan 10.30 na dare ya sata a gaba yace taje ta kwanta a dakin ta.

sannan yayi kashedin kar yaji wani ya daga ta sai da safe za suyi maganan.
Jasmine kam tun a asibiti data ji maganan a bakin mamy ta gode ma Allah yafi abun a kirga a zuciyan ta .

Yanzun ma Ta so ace ta gaya ma ashween halin da take ciki amma sai ta nemi layin sa iya nema amma shiru baya tafiya

Cikin daren tayi nafila ta dada nuna godiya ma ubangiji tare da dada nuna masa nadamar ta na kuskuren data tafka da kyautar da ya bata na farko

Tsaban murna hannun ta akan cikin tana shafawa ciikin tunanin mijin ta har bacci ya dauke ta.

Tun safiyan Allah mamy ta zo ta turje a bisa dikkan alamu kamar ko bacci batayi ba,
Ita dai duk damuwar ta yau ita mai zata fada ma Ashween game da cikin?

Abban ashraf haka yaki cewa komai ya ringa waina ta har saida aka ci karfe 10 na safe kafin yace ayo zaman..

Jasmine sanye da doguwar riga ta shigo falon abba sai ta zauna a a kasa daf da shi ta sunkuyar da kai kasa.

Mamy sam ta kasa hakuri tace ehem ena jinki ?
Nace Daga ena kika samo juna biyu jasmine

Jas tayi shiru tana tunanin yadda zatayi bayanin satan hanya ta keyi tana fita har aka samu

Sai mamy tace magana fa nake miki ko sai na tashi na miki dukan tsiya zaKi gaya min?

Sai ta soma kuka a hankali, tace kiyi hakuri mamy dan Allah kiyi hakuri

Mamyn ta tashi ta tsaya a tsaye idon ta har sun kawo ruwa don firgici tace ki kace nayi hakuri?ni ban san shi ba, Bayani kawai zaki min uban wa ya miki ciki agidan nan.
Chapter 121 · 0% Book details