← Book details So Makamin Cuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 132

Sashe 77

So Makamin Cuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shikan sa baisan lokacin dayayi complying ba fuskan sa cike da kaunar ta
Ya tallafo ta kadan Tuni ta dan fada jikin sa da dabara tana sauke wani susutaccen nishin shagwaba tana dan kakkame shi
shikuma bainkula ba ma aka barsa da ce mata sorry yana lallashin ta a dabaran ce,ya dauka ko zafin ne har yanzu

Lokacin Bakin zahida a bude yake tsaban mamaki tana binsu da ido, gashi ba halin tayi magana don ta sani sarai inyaga dama zai ce zai haura mata and she knows deep can cikin ranta ba dadi, she is already chocked up abu kadan zai iya sa tayi bursting yanzu

Ganin bazata iya tsayawa tana ganin sun ba , ta karaso Cikin wani shakurraren Murya tace baby,, c'mon ure doing so much, kabari mana na taya ka kula da ita, i think zata fi jin dadi in mace yar uwan ta tana kusa ko? Wai Me amfani na anan wajen.

Baice komai ba tukun Ya dada gyara ma jasmin zaman pillow ta jingina bayanta sannan yace ma zahidan ok fine, amma
Zaki iya bata a baki? Kinga zafi take ji har yanzu bata warware ba, she cant stress ya dan kashe ma jasmine ido da wayo ,tayi murmushi

Zahida ko Fadan hakan dayayi yasa Ta watsa masa hara bazata tace ,uhm naji,ai sai ka tashi kuma ni anan zan zauna ai

Ba don ya so ba ya ja gefe tayi saurin maye wajen sa daf jasmine ta zauna

Jasmine bata ce uffan ba ,don ta riga ta gama hada abunda zata mata cikin ranta
Nan zahida ta zauna ta soma yunkurin dauko abincin sama
shikuma ya ja gefe yana kallon abunsa yana binta da murmushin kauna tana cafkewa.

Zahida Kamar bazata deba abincin ba don idonta ya gama cicikowa da tsaban haushi da kunan rai

Nan dai ta dangwalo abincin dan kadan zata bata a bakin jasmine tayi sauri ta kau da kai gefe tana yatsine kamar taga kashi...
Nan yayi saurin cewa meya faru kuma jasmine? tace bana son wannan fingers din nata ne yaya zai cakke min ido..ta karashe cikin muryan kuka

A fusace zahida ta dangwala spoon din ta sunkuyar da kanta cikin takaici ta na kallon well polished nails dinta daya ji cotex yayi kyau
sai tayi shiru tana calming kanta ranta na kuna tana maganan zuci, wallhy mum kin cuce ni da kika ce kar na ci uban yarinyar nan, bura uba..hmm"
Ta tabe baki a hankali

Nan Maganan Ash ya dawo da ita yana cewa jasmine yi hakuri ba zai cakke ki ba, ba ga spoon ba c'mon eat kinji?

Ta turo baki cikin shagwaba ta juyo tana fuskantar zahidan alaman ta hakura,

'Jiki ba kwari zahida ta sake debowa wannan karon da dan yawa acikin spoon din
sai ta kai zata bata a baki ba laifi jasmine ta bude bakin zata amsa

Ai kuwa Zahida na kaiwa kan harshen ta tayi saurin tofarwa ta bi ta watso mata shi a fuska tuf tuf,tufff,,sannan ta hau yin tarin karya

A hujajan zahida ta sake spoon a kasa ta channa ihu ta riko idanuwan ta dam tace ouchh my eyeesssss.. '
Tuni ta danyi gefe cikin radadi tana jimamin barkwano a idon tan

Shiko ena ma ya san ena take ,tarin da jasmine take yi ne kawai ya ruda shi don haka ruwa ya rarumo a bottle ya yo kanta yana mata sannu jasmine 'cikin kula yace da barkono ko,? Im sorry yanzu za acanza miki wani

Ta langwame ta dan damko sa ta nayinbtarin kadan kadan tace yaya bni ba barkwano bane da zafi ne, ya kone ni ne sai tabishi da sassanyar kallo innocently.

Ba shiri Ya zauna a gefe Ya tallafo ta da niyar ganin bakin nata daya kone bai sani ba har ya ture zahida dake fama da idon ta agefen su cikin azaban radadi

Tana ji Ya shiga lallashin jasmine din kamr zasu gogi juna.

A lokacin Wani irin jiri ne ya ke neman rufe zahida ga zafin barkwano a ido ga jasmine ta bi ta narke gaba daya ta susutar da shi sai hakuri yake bata

Chan abun daya ishe ta sai ta sake ta tsala ihun sunan sa,cikin bacin rai tace baby ido na faaaaa

Nan ne ya juya kadan yace toh kitashi mana ki wanke idon zahida
Nan Tayi saurin hadiye hawayen ta tace pls baby help me bana gani

Yayi ma kamar baiji ba yana rike da hannun jasmine din da tayi shiru tana dariyan abun aranta, har zahida ta sake cewa babyyyy magana fa nake ..yace oooooooh zahida pls ki tashi mana ke karamar yarinyace kam i hate dis fa? Ya bi ya dan daure fuska sounding very annoyed.

Nan Bakin ciki ya gulle ta Duk abun duniya ya cunkushe mata arai sai tayi yunkuri a daddafe ta tashi tsaye hannu a ido tana tangale Ta galla masa harara a fusace ta shige bath room din sa kamar mayya

nan ta soma wanke fuska tana goge wa a hankali sai uban Azaba datake ji

Ta kai mint 10 cikin batrum din ta rasa me zatayi musu guda daya sai kawai ta fashe da silent kuka cikin ranta na kan tafasa,
Tace wannan wani irin abun kunya da cin zarafi ake min, ta kalli jajjaywn eyes dinta a mirror tace wallhy yau da badon badan ba,ko son da nakeyi wa ash bai isa ya hana ni tarwatsa rayuwan yarinyar nan ba.
I hate her, i hate her sooo much ...ta fada tana dunkule hannu tana dada kallon kumburaren idon ta dayaji yaji yay ja

sukam Kafin ta fito har sun koma dai dai shiru kakeji aahweeen har ya dawo ya zauna a position dinsa yana famar bata abincin a baki Tana karba a nitse

Bude kofar bathrum din zahida tayi a hankali ta tsaya tana binsu da kallo musamma shi ashween dom alokacin ji take kamar ta je ta shake shi ta huce,

Da gefen ido jasmine take duban ta amma sai tayi kamar bata san da shigowar tan ba, dai dai ya kai mata a baki ta karba sai ta dan riko hannun sa ta karbw spoon din tana murmushi ta debo dayawa shima ta bashi abaki cikin kula har tana taya shi rike habansa kadan alaman sauran kar ya zubo waje

Ta dube sa tayi murmushi shima ya mayar mata don shikam harga Allah bai san zahida ta riga ta fito ba

Boyayyen hawayen nata ne suka sauko tayi saurin goge su Nan ta zame a hankali za ta bar musu dakin

Da sauri jasmine tace" laaah yaya har zata tafi ne baka ce mata sory ba fa? tayi nuni da zahida da dan yatsa
cikin kunci zahida ta tsaya chak don batayi tsammanin jasmine zata ce hakan ba

Nan ne ya juya cikin mamaki yace ohh baby, sory fa ya idon?
ba tare da ta juyo ba
Sai da taji wani sabon takaici ya gulle ta A kirji tayi shiru alaman ranta yayi mugun baci
jin ta masa shiru shima sai ya dauke kansa.
Bai farga ba jin rufowar kofan kawai sukaji da karfii,.alaman ta fice

Kallo daya yama closes doors din ya dauke kai A hankali ya sauke ajiyan numfashi ,

jasmine ko tana shiru a ranta tace wow, ashe gaskiyan salma ne ,,sai yanzu nagane.. Hmm wato duk yadda akayi dai asalin matar gida itace mata ,kuma kwanan nan kuwa angulo zata koma gidan ta na tsamiya mswww,
ni da miji na mutu ka raba takalmin kaza.
sannan tayi karamin murmushi dube sa tace yaya yau kafasa zuwa ko ena ne naga kamar lokaci ya kure?

Ya gyada kai, ya riko hannun ta yayi kissing
Fuskan sa dauke da annuri, yace na ma isa na tafi na barki bayan ban cire zafin nan ba'
Tayi saieinbboye fisanta dan kunya
yayi kayataccen murmushi ya shafo gashin kanta cikim sanyin murya yace im so happy jasmine.

even morw happy da kika daure kika dan ci abinci....cikin idonta yake duba yace tell me evrything u neeed i promise zan miki im here for you bana motsawa ko ena

Wani dadi ke ratsa zuciyarta ta tayi murmushi ta lafe kadan a jikin sa ,
Tace as long as urw here bana bukatar komai yaya bacci kawai nake ji ,

Ba bata lokaci Nan ya hauro sama ya zauna gefen ta da kyau,
Ya jawo ta jikin sa ya dan rungomuta suka cigaba da dan hiran su har tayi baccin.

Shima sosai yake jin baccin don dama bai samu yayi ba sai ya jona ta
Basu da tashi ba sai wajen 12.30 to 1 na rana

Hakan ma Zafi jikin ta ya sake hadawa sosai don haka still saida ya tsaya ya tayata ta kammala komai,sukayi wanka, tayi sallah sannan ya bata maganin da likitan ta bayar ta sha, nan ne yace mata ta jira shi anan yana zuwa.

Ba musu ta kyale sa ya fice ,
Ajiyan zuciya tayi Ta lumshe idon ta tana jin sanyi a ranta.

a bangaren zahida ko Kuka sosai taci amma sai ta kasa kiran mrs rod ta fada mata abunda zuciyan ta ke raya mata
Anya kuwa ash bason jasmine yake ba?

Anan tana kwance Tayi juyi tayi juyi ta rasa wanda zai tayata calculations din ta samo amsa
gashi ba halin kiran madam hidayat don tasan wani zaagin zata sha.

Yau din Sosai taji kishin yadda Ashween yake lailaya jasmine kamar kwai agabanta har bai damu da barkwanon da ya shige mata ido ba.

Yanzu kam Ba musu zuciiyan ta ya riga ya aunata mata jasmine ta dabance a wajen ashween sai dai ta kasa fahimtar meyasa hakan toh, isnt she his ordinary cousin sis?
Son ta yake yi shima? Ko kawai hes protecting her ne as yar uwan sa?,
Cikin wannan tunanin taji an turo kofar ta nan suka yi ido hudu da shi

Duk da ma haushin sa take ji ama saita ji dama dama daya biyo tan altho ba akan lokaci ba.

Tuni ta juya baya ta dauke wuta, shiko kamar baisan ma tanayi ba ya zauna a gefen gadon
Ya nitsu Cikin sanyin murya yace baby ya idon naki?
Chapter 77 · 0% Book details