← Book details So Makamin Cuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 131 OF 132

Sashe 131

So Makamin Cuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Amma sai taga ba hakan bane ,gaba daya sun bata assuarance zasu kula da ita kuma suna tare da ita

A haka har ta samu tayi shiru ,sannan aka soma shiri aka koma masaukin su.

Da shike yanzu ne lokaci na farko da dukkan su suka hadu a waje daya

Sai jamal ya kawo shawaran su dan yi hutun musan juna a babylon city tunda waje ne na tarihi da abun mamaki masu girma

Anan suka yada zango ,jabir da familyn sa jummai da salim
Jamal da new wife dinsa sarah
Sai ashween da jasmine da kuma zahida

Duk waje daya suke awani katon estate na shakatawa sai dai part daban daban

Zahida ta kasance har yanzu ashween kawai ke iya controlling din ta
Ko kuka takeyi idan ya zo ya bata hakuri da kanshi sai ta tsinci kanta da jin sauki a ranta
haka ma abinci muddin bai sa baki ba bata iya wani ci sakamakon kullum tana fama da tunanin yadda zata fuskanci rayuwanta a yanzu da bata komai sai arzikin ta da yan uwan ta .

Don haka ne ma jasmine ta yanke hukuncin su dawo da zahida kusa da su sosai cikin flat din su ita da ash
saboda tafi sakewa kuma shivkadai ne ke sata samun nitsuwa daga jefa kanta cikin wani halin tunani

Yau ana sati na biyu kenan Ba laifi zaman zahida da su jasmine a flat daya ya sa ta soma mancewa da abubuwan dake damun ta.

Musamman da jasmine ta ke janta a jiki suna hira wani lokaci abun dariya
Wani bin duk neman gafara ne.

A haka suka soma sabawa sosai sai dai zahida kullum ta kanyi fighting da abunda ke damun ta akan ashween

Ji take kamar shi kadai ne ruhin ta,
Ta kasa zama ita kadai tasan presence dinsa da kulawar sa ne ya sa ta soma samun sauki har haka ba wani abun ba.

har cikin zuciyan ta bata son haka don tasan hakan halaka ne mai grima

Allah ya riga ya haramta mata shi amma zuciyanta yaki ya barta

Ranar ma haka ta kasa bacci gashi ana neman wajen 1.30 na dare
Amma tana fitowa cikin daren sai tayi gamo da su A sitting room

yasa white 3qrt ba ko riga ajikin sa yana kwance jasmine tana tsakiyar kafar sa da wani guntun bomshot na jeans iya rabin cinya da dan fingililallen vest sharara wanda yake bayyana katoton cikin ta kanta na kan kirjinsa
Sai ta mike kafa suna hirar su cike da so da kauna sai kissing din face dinta,da neck ko ena ma yake suna dariya gwanin sha'awa

Kallon su a hakan yasa Sai taji wani iri sosai ta koma dakin ta a sulale basu lura ba.

Kuka ne ya kufce mata amma ta rasa na meye ne
Ta yi makanta gargadin ashween haramun mata har abada amma ena tasan vazata iya denaying har yau tana jin zafin ganin shi da wata ba
musamman yadda yake nuna rayuwar sa gaba daya na jasmine ne yanzu.

Zahida tayi kuka sosai tana tausaya ma kanta
Gashi bata iya sallah ba bare addua oi
Sai abubuwan suka taru suka mata yawa a zuciyan ta

Anan a kasan dakin ta ta kwana tana kuka daga karshe sai ta yanke ma kanta wani hukunci wanda take ganin hakan ne kadai mafita a gare ta.

*Ku biyo ni muji hukuncin da zahida ta yanke*

*surriem*
[23/08, 05:43] ‪+234 806 071 2446‬: *⚜BRILLIANT WRITERS ASSO🖊*

💔

*SO MAKAMIN CUTA*
_'the sword of evil love'_

_Story and written by_
*SURAYYAHMS*🔥

*DEDICATED TO-*@UMMERHERNY NERSALLAH.

All tanks to my co Brilliant writers i hrt ur supports
*Meelat musah*
*Real me dambu ce*
*Ummerhny nersellah*
*Asmeenat zeeyan*
*Halima leemah*
*Meemah mohd*
*Ummu farhana 'kakus*
*Umman sayyaed*
*Halima20*
*Asmaluv*
*Maman mamy*
*Oum muhammd*
*Ummu ahmd*
*Halima bamalli*
*Ummu affan*
*mamn hibbah*

My sweet sisters
*Feenah bae*
*Princesss ayisa*

*My honourable WHATTPADIANS @surayyahms is not forgeting u thanks much💋❤🌹*

End🔚🔚🔚🔚🔚🔚

*Page▶92*

A haka zahida ta zauma wajen tana kan fighting abubuwan da ke damun ta har safiya yayi bata sani ba

Wajen jasmine kuwa sam sai ta kasa tashi dama dauriya kawai takeyi amma ba karamin ciwon baya ke damun ta tun zuwan su

amma sai bata son ta sanar da shi don
Kar ya ce zai fasa zuwa wannan re-union din.

Tana daga kwance a hakan ta najin Yana wanka a bathrum
Sai ta daddafe ta dan tashi tayi waje da niyyar ware kafarta kafin ya fito ya gane halin da take ciki

A hankali take tafiya tana
Saukowa kasa
Amma sai ta sha mamaki gashi har karfe 10 yau zahida bata fito ba kamar yadda ta saba
Kullum anan suke samun ta

Hakan ya sa jasmine ta kama hanya zuwa dakin ta ta duba ko lpya.

Knocking ta dan yi tana cewa aunty, amma shiru
Ta dada yi,tayi yakai sau uku amma shiru sai ta tura kofar a hankali ta shigo

Kwalabe ne dake tsakiyan dakin suke faman gangara akasa jasmine tayi saurin bi a hankali tana kamawa
Tabbas giya ne don warin sa gaba daya ya gauraye wajen.

Da sauri ta ajiye tana cewa aunty wanka kike yi ne? Nan idon ta yaci karo da dan karamin note manne a jikin mirror wanda yace:
```Im gone ASH, dan Allah ku yafe min am just a curse in your life dole na tafi na barku har abada you don't derseve me ni kaina ena tsoron kaina ..kuyi hakuri bazan iya ba.
Zahida abdl rod```

Da sauri jasmine ta yarda paper a razane ta soma dube dube
Tana yaye curtain sai tayi ido hudu da bayan ta chan kasa bakin gate tana dab zata fice bata ko juyawa.

Duba da ciwon da cikin ta yake mata amma hakan bai hanata saukowa da gudu ba
Ko sauraran komai bata yi ba ta bi bayan ta a bakin gate

Ganin ta shiga taxi cap har ya sha kwana
ya sa itama ta bi wani taxi din suka bi bayan su.

Akwai rata tsakanin su sosai amma hanya daya suke bi

Gaba daya hankalin jasmine ya tashi sosai gashi ba takalmi kafanta bare waya

Nan zahida kuwa ta sauka gaban wani tsohon bridge achan nesa da cikin garin babylon.

Wajen na da kyau na fitan hankali ga shi ana yayyafi ko ena shiru ba jama'a
Sai taxi da ya kawo ta.nan ma ta sallame shi
Aka bari ita kadai ce awajen sai rairayin da yayafin ke sukowa da shi awajen.

Nan ta shiga saukar da hawayen da ta dade tana danne su tun a gida
Ta nufi kan wannan rafi ta tsaya akai tana kuka.

Tace mutuwa ne hutu na,hutun yan uwana.
Allah ya jarabce ni da kaunar kanina,
Gashi Bazan iya sake zamowa wani abi marar kyau a rayuwa ba.
Sakamako na kenan da iri soyayyar da na hana shi da shi zan mutu kamar yadda lailah ta mutu,lallai fansan soyayyar lateef da lailah akwai tsada ga shi ita ce ta kasa bari na yau mutuwa kawai ta zaba min.

Dai dai nan jasmine ta karaso ganin halin da zahida take ciki ya sa ta saukowa a guje ta na cewa zahida pls don that wait...
Zahida sai ta dada fashewa da kuka jin hannun jasmine ya damko kafar ta sosai tana kuka itama

Cikin masifan karfin hali tace jasmine baki ji ko?
Wa yace miki kizo nan.
Ke wata iri ce ba nace zan barku bane ?ko baki son shi ne.

Cikin kuka jasmine tace aunty ena zaki je ki bar mu,meyasa zaki kashe kanki bayan muna zaman mu tare please kar kayi mana haka na roke ki.
U still have chance to be happy please give urself d chance,

Nan zahida ta dan tsaya da kukan nata ta dan juyo tana kallon jasmine dake kasa ta riko kafar ta.

Tace ena son farin ciki ne shiyasa na zabi mutuwa jasmine
I cant lie to u ena jin Ashween a raina har yanzu i realy want to die so that bazan taba cutar da ke ko shi ba
bani da mafita jasmine dan Allah ki barni ki tafi gida kinji?
Kije ki kula min da kanina
Nikam na san haramtaccen son shi da ke zuciya na shi zai yi ajali na.

Jasmine dake kukan fitan rai gaba daya sai ta rasa me zata fara furtawa daga abubuwan da ke son fita abakin ta

Yau ne rana na farko da ta fara jin da zahida ba yar uwan ash bane da ta hakura mata ya aure ta.

Amma abun ba haka bane ,dukan su sai suka taru suna kuka kafin tace
Zata ce aunty ,nan cikin ta yayi wani irin murdawa
A hujajan ta fasa ihu amma sai ta kasa sake kafar zahidan

Tace innalihhi wa enna ilaihi rajiun wayyo Allah na ciki na.

Nan zahida ta soma dawowa senses din ta ta juyo da kyau ta na kallon jasmine din tana dan fincike kafar ta tuni jasmine ta sulale kasa ta riko cikin ta sosai tana kuka tana washhh washhh.

Sai ta sauko daga kan bridge din a hujajan tayo kanta
Tace lpya kuwa cikin ki ne ke ciwo? o.m.g some one help us tafada da karfi tana waige waige.

Ganin waje na dada yin shiru ya sa zahida kara rikicewa da alamun ciwon nakuda ne ya taso ma jasmine bazata ga ruwan sama na so ya tsanan ta.

Ta rasa meke mata dadi ga jasmine sai rolling take a kasa tana rike bayan ta maran ta gaba daya ta birkice

Anan ta jawo ta ajikin ta ta shiga calming din ta a hankali tana waige waige ko zasu samo taimako.

A gida kuma gaba daya Ashween ya daga masu jamal hankali cewan baiga zahida ba bare jasmine ga kuma letter da ya tsinta a dakin

Gaba daya sun duba ko ena har kasuwa ba su gansu ba.
Jummai dake gida ita ma sam ta kasa zama sai ta fito bakin gate

Anan ta tambaye mai gadi duk dama bata jin turancin su sosai amma shi ya gama fahimtar halin da suke ciki.

Wajen akwai security sosai don haka sai ya hada ta da number mai taxi din da ya dauki jasmine.
Chapter 131 · 0% Book details