← Book details So Makamin Cuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 105 OF 132

Sashe 105

So Makamin Cuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani bangaren cikin asibitin kuma mamy ne da ashraf dA yamman suna tsaye hankalin ta duk ya tashi ganin halin da jasmine ke ciki.

Tun ashraf yana calming dinta har ya yi shiru ya kyale ta.ta gama kawowa aranta cewa stressed ne da depression din rabuwa da miji ya sa jasmine take bijera wa abinci har ya mata illah haka.

yau mamy ji tayi kamar ranta ake cirewa ganin yadda jasmine din tayi ta suma ba adadi a gida.

Daga kan gadon asibiti ta bude ido dishi dishi ta hango likita a kanta,
Docton bature ne, sai sosai ya nuna tausayawan sa akanta Cikin sanyin murya yace mata ya ki keji yanxu?
Ta soma hawaye a sanyaye tace meke damuna doc?ka fada ma mama na?

Yace a'a dama basu sani bane ?
Amma ai ke ya kamata ace kin sani
Sai tayi shiruuu ba tace komai ba

Sai yace toh ki huta ni bari nayi magana da su, a hujajan ta daddafe ta damko sa ta fashe da kuka,
Yace lpya dai ko?

Tace doc dan Allah kar ka fada komai na roke ka
Kar kace na zubda ciki am going trou alot ka taimaka min pls

Abun ya basa mamaki sai ya dakata yana kallon ta tana kuka gwanin tausayi""

Yace ohh, dama da sannin ki kenan kike so ki kashe kanki?kin sha maganin zubda da ciki ya kuma zube
Kinsan muddin jini daga mahaifa na zuba mace na bukatar kulawa na musamman shine kika bar kanki ba ci ba sha? Ko su da suka baki maganin basu fada miki ana bukatar kulawa bane?so kike ki kashe ka kanki ko?

Ta dukar da kai kasa gwanin tausayi tana kan rokon sa ita dai ya rufa mata asiri kar ya fada ma kowa
shi dai baisan meya faru ba
Amma daga gani Ya san tana cikin matsala sosai"

Ya mata fada yace banji dadi ba da ya kasance kinsani sarai kika kwabar da cikin ki
duk da ma bansan dalilin ki ba, amma fa kisani
Abortion Ba abu bane mai kyau sai ya zama dole, u have no idea irin dumbin matan da suke yawo suke neman haihuwa da iya karfin su da imanin su amma Allah bai basu ba..kar ki sake yin haka, shi Allah daya baki shi zai raya miki sannan ya fitar dake da ga duk wani halin da kike ciki

Ta ce hakane doc nayi kuskure amma dan Allah kar kace mata na zubda ciki

Yace gaskiya bazan iya ba ,is againts my oath as a doc nayi miki wannan aikin karyan ,

ko ma ba don komai ba ai bazan so na sake jefa rayuwar ki cikin hatsari ba dole asan kin zubda ciki saboda a baki kulawar da ya ce

Ta daura hannu akai tace na shiga uku,nan ta shiga rusa kuka tana roko har yace calm down to ki saurare ni,zan miki alfarma daya in kin mun alkawari zaki bada hadin kai wajen Tattalin lpyar ki

Da sauri ta gyada kai tace nayi alkwari doc

Yace to shikenan ,zan gaya musu kinada ciki ne kuma ya zube baki sani ba.ke kuma sai ki tabbata kin basu hadin kai sun kula dake.

Tace zan bayar na gode doc,
Yayi mata murmushi sai ya fita,

Nan ya tarar da mamy wanda already bpn ta yana kokarin hawa duk bata jin dadi sosai
Sai ya sanar da ita yadda suka shirya da jasmine

Sosai abun ya mata ba dadi a ranta, sam bataji dadin rasa cikin jasmine ba sai tausayi ya gama balbale mata zuciya .

Amma a fuska sai ta nuna madallah da cikin Ya zube kawai ita a sakar mata yarta.

Ashraf kam har ranshi yake jin dadin abun don dama jira yake kiris ta fashe musu

Mamy tabi bayan doc akan itama a duba ta sanan ta umarce shi da ya fara yin gaba da jasmine kafin ta taho

Ba musu ya amsa mata ya shiga dakin
Tana kwance ta kau da kai tana kuka, yanzun ne take mugun jin nadaman abunda ta aikata ma kanta.

Ya tsaya yana kallon ta ,chan yace
Hmmm, ai dama wanda baiji bari ba ,

Ta juyo a hanakali tare da dakatar da shi
Ta ce ya isa haka yaya ashraf,bana son surutu

Yayi murmushi mai kama da dariya yace toh muje na kaiki gida ,nidin da aka ki dole za'a dawo min
Ta masa shiru ta daddafe
Zata sauko ya soma yunkurin kawo hannun sa
Ta kauce ba bata lokaci ta fice ta barsa a wajen

Bai damu ba yana biyota a baya yana gaya mata magana son ranshi

Gefen su ash kuwa an kammala komai an tabbatar musu he's normal sai dai a kiyaye na gaba

Amma sai yaki sam a cire mai bandage din sedative' din da aka jona masa akai don yana soothing jijiyan brain din nasa .

Kamal yace malam ance fa yanzu ka warke ka cire mana muga sarari

Ash yayi yar dariya yace ka bar min abu na ni ena so a haka.

In fact bari ma na dada gyarawa ya juya jikin wani washroom jikin madubi yana dada gyarawa.

Sauri takeyi tana so ta kauce ma ashraf dake binta da maganan banza
Ga kwarnafin amai yana so ya dago mata gaba daya taji cikin ta na yatsunewa sanadiyar ba komai aciki sai magani da dari darin ruwan allurai..

Ta kasa daurewa tayi saurin shiga washroom ta shiga kwaza amai bata lura da shi a gefen ta ba
Sai Ya dawo daf ya kunna mata ruwa bisa ga dukkan alamu amai mai daci ke fita don da kyar take fitarwa

Hawaye ke sauko mata ganin shi din ne
Sai ta soma tunanin ko dai imagining dinshi kawai take, har suka kammala tare.
ba tace komai ba
Ta mike Zata bar wajen
ya kamo hannun ta ya jawo ta jikin sa sam ya runguen ta ya kwantar da kansa a kafadar ta
Cikin sanyi murya yace,ya jikin ?.

Sai ta lumshe ido tana kan zubda hawayen takaicin komai da ya faru
Ya kara cewa forgive me for not being there for you,ba son raina na barki cikin wannan wahala ba.

Maganan san nabkashe mata karfin gwiwa Ta soma juyowa a hankali da niyyar masa tambayar'ya gaya mata me zaice mata ranar yanzu tana so taji,"
Sai dai suna hada ido
Kasa bude bakin tayi tana kallon sa ko da ba' ace ba tasan ya sha wahala sosai shima.
cikin haka ashraf ya banko kofar wanda ya sa ta dan janye wa ajikin sa tayi gefe

Ya watsa musu harara yace ohh dama abunda kikeyi anan kenan ko mamy tace ki fito maza
In kuma zama zakiyi ki yanzu naje na gaya mata tazo da kanta.

Ba musu ta fice ta barsu a wajen don harga Allah tagaji da ganin wannan fitinan

Tsaki ashraf yayi ya juya yana dariya kasa kasa yace an daiyi asara
Dai dai lokacin kamal ya shigo
riko Ash Yayi don ya hana shi tankawa har ashraf ya bace

Kamal yace relax dan Allah kar ka tada ma kanka hankali mana
Yace kamal magana zata min i see it in her eyes
Kasan ko wani abun ke damun ta ? Ni gaskiya zanje na duba lpyar ta ai matata ce, ya bangaje sa ya fice a gagauce

Kamal ba yadda ya iya haka ya kyale shi ya fita
Gani yayi gata chan gaban motar ashraf yana jan su sunkai kusan bakin gate

Ba jira ya shiga mota shima ba yadda kamal baiyi ya bashi tuki ba amma yaki roughly yake yi har Suka sha kwanan anguwar su mamy

Tunda ashraf ya lura da biyosu yake yi, yake faman tsokanan ta da mugayen maganganu

Yace 'madallah, dama karshen rashin ji kenan
Aure da dan iska kuma ai kadan kika gani,
Hakki na ke bin ki da mani kika bada jikin ki da bazan ci amanan ki ba
Ya sake juyi ya kalle su daf ya dan yi dariya mai ban haushi yace " sunan wata wai anci biredi an yada leda..

Jasmine ta kifa kai ko jinsa batayi ...bare ya dameta wani strange guilty concience ke cinta arai game da ashween amma ta rasa meyasa

Daf da bakin gate din ash ya wani wawan u turn ya sha gaban su
Ashraf ya kwashe da dariya sosai sai ya kashe motar sa shina ya fito a xafafe ya tamke fuska yana masifa

Yace wannan wani irin hauka ne kai mahaukacin ina ne?

Kamal bai iya taro sa ba don ko rufe door din motar baiyi ba ya dosu inda jasmine take abunsa
Dai dai setin kofar ta ya sa hannu zai bude kofar ashraf ya damke hannun
Yace kar ka sake ka taba min mota na wawa matsayaci,kai wai wani irin jarabbabe ne bakayi ya ishe ka ba, ai cikin ma ya zube sai kabarmu mu dana muma,
bai hankara ba yaji naushi a bakin sa
Ash tunda ya juya ya chakumo sai da ya masa jina jina kamal da kyar yayi ceto ya damke shi sosai

Sai ya fizge a hannun kamal din ya zo daf da ita don tsoron tashin hankalin nasu ya sa ta fito da niyyar barin wajen
Ash ya karaso daf ya juyo da ita y rike kafadun ta tana fuskantar sa.

Yace ,im here jasmine dan Allah ki zo mutafi kinji?
I dont want to leave u here bana son ana bata miki rai kina kuka ,i love you...
Ya kamo hannun ta ta dan janye kadan cikin bori
Kan yace zai sake bude baki ya hango mamy dake kusa daf cikin mota tana mika musu mugayen
Kallo
Nan ya dada zafafa maganan
Yana kallon ta yace jasmine dan Allah ki zo muje kar ki barni ni kadai
U know i wont hurt u i want to xplain myself to you kuma nasan kina so ki saurare ni.

Sai ya mika mata hannu ya marairice fuska alaman ta zo su tafi..

Mamy na kokarin parking
Ashraf sai yayi wuf ya iso wajen shima yace ki zonan ki wuce gida

Itako har ta gama karaya, tayi sanyi zata mika ma ashweenn hannu su tafi,

Ashraf ya chakuma hannun ta na hagu daga gefe sai Ash shima yayo saurin rike hannun da take shirin mika masa
Chapter 105 · 0% Book details