← Book details So Makamin Cuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 132

Sashe 13

So Makamin Cuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Uhumm u cant wait wato kin gaji da ni ko?
Nan ne ta danyi murmushi
Tace ah a, kin taba jin yadda mutum ya gaji da rayuwar sa ammy
Ke ce fa rayuwata ta karshe a shagwabe tana dan fadawa jikin ammyn

Hmmm toh Allah ya bar min ku baki daya
Haka ma yayaN ki ashweewn ke min wannnan shegen taka.

Dum zuciyar ta yayi jin sunan sa ma da ammyn ta kira
Hakan ya saa bata ce komai ba
' ammy bata fasa ba ta cigaba da cewa
Wai nikam in na mutu ya zakuyi? kuna nufin zaku shashantar da rayuwar ku kenan ko me

' mutuwa fa kika ce ammy?. Ta dago tana kallon ta
Ai in kika mutu hmm" sai tayi shiru bata karasa ba
Dukar da kai ammyn tayi tace
Jasmine , kulli nafsin zaikatul maut ,sannan shi mutum kamr matafiyi ne a duniyan nan
Cikakken mutum shine wanda zai yi imani da qaddarar Allah..ena so ace kin shirya zuciyar ki da tunanin wata rana babu ni ,ko ke din ma.. ko ma yayan ki" fatan mu chan ya fi mana nan ako yaushe ..
Kusan minti biyar ta dauka tana bulbulan hawaye sakamakon wani zafin da ,zuciyar ta ke mata
Haka kawai taji maganan ammyn na yau ya sosa mata zUciya tunanin mutuwar daya daga cikin sun yasata jin komai nata ya tsaya
Ba shiri ta mike zumbut cikin sauri zata fice

Jasmine ..jasmine
Ammy take kiran ta hankali a tashe
'amma ba amsa sai kukan data keyi tana tafiya cikin sauri abunta zata nufa dakin ta
Wanda yayi dai dai da shigowar asheewn cikin falourn
Wucewar bayan ta kawai ya gani
Sai muryan kukan da ya danji sai dai bai tabbatar hakan ba ne

Lpya dai ?Ya naga kin tsaya haka, whts wrong ammy ya karaso wajen ta fuskn sa dauke da alaman tambaya

Da kyr ta kakalo murmushi
Tace
Bansan me na mata ba take kuka
Ko dan nace mata tayi imani da wata rana zn mutu ne?
Lumshe ido yayi shima
Cikin wani yanayin
Ya kamo hannun ta ya zaunar da ita
DN kallon ta yayi fuskan sa a sanyaye yace
To ai duk laifin ki ne ammy

Laifi na kace ashween?

Ehen meyasa ke dai kullum ba dama muzo jikin ki sai kice mana wata rana zaki mutu
Wa zAi so yaji hakan?
Ni ne ko jasmine eh?

Shiru tayi tana kallon yadda ya daure fuska kuma ya shgawban ce lokaci guda

Toh dama bazan mutun bane

Eh zaki mutu mana nayi imani da hakan amma muma ai zamu iya mutuwan nan ko kafin ke ko?
What baka da hankali tace tana dan zungurin kansa
kar ka sake kira ma kanku mutuwa at dis young age ku nemi tsawon rai wajen Allah don ku daukaka alummar annabi (s.a.w) sannan ku mana addua kafin naku tazo
kul, kar na sake jin kana fadan haka kaji na gaya maka..
kallon ta yayi ya ce
Ohhhhh ashe ba Dadi kenan'
Ni dai na fada maka dai tace tana dan daure fuska
Tare da sauke ajiyan zuciya yace toh fine.
Ni yunwa ma nakeji ammy na do something

Ba musu ta mike
Tace' tashi mana ko anan zaka ci
Baice uffaN ba ya bi bayan ta kamar yadda aka saba suka nufi dinning room

After 1 month

Cikin wata dalleliyR mota ta fito tana tafiya tana waya Alaman kwana biyun nan rayuwan ta nakai mata sosai' kwalliyar ta ma na daban ne sai sheki take tana takon ta cikin qasaita
' jamal na fada maka ya kamata ku hadu da shi pls"
Kai kaga yadda yake Pampering dina kuwa
And Kar ka so kaga yadda yake taimaka min wajen juya clients a company na
bakaga am bauncing bak ba?ta karshe maganan da karamin dariyar nishadi

Um gaskiya ne zahida i can see
im impresses sis, ai naga har kin soma sabbin contract cikin lokaci kadan"i must say,surkin namu akwai gari a hannun sa

Of cous bro,ai nafada ma mummy wannan shine asalin match di na
Ga kyw
. ga kudi .ilmi...ga aji..shyasa ma amince kuyi binciken ku nasan karya kuce baiyi ba

Karamar dariya yayi yace" gaskiya an dace kam'
Ni gashi har yau ta kasa amincewa na auri wata
Yau ace wannan baiyi ba gobe ace wancan baiyi ba
Am so tired...

Tare da dan sauke ajiyan zuciya tace
Kasan mummy ai
Muddin mutum bai cika sharuddan ta ba bazata bari ya shiga rodriqeuz Family ba
Kyw,kudi,ilimi ko power
In ba su kai ba komai bane wajen mummy

Yh nasani ..call yhu bak enada case zan shiga sharia
Blowing kiss tayi masa ta wayar sannan tace gudluk bro
Nan suka dakata

Ko da ta shiga beauty spa din
Ma'aikatan wajen Kowa a tsaye yayi yana kwasar gaisuwa kamar yadda Suka saba Wanda ko kula wa batayi
Har ta kammala dube duben ta Da hidimar ta da customers dinta wanda mafi akasari qasaitattun mata ne masu ji da kansu ke zuwa
Ta kai kusan rabi
Ta juya da fara'ar ta tana kallon yadda dayan maikaciyar ke lailaya gashin wata mata wanda fuskan ta bai bayyana mata ba
Gashi baki wuluk ga cika ga tsayi sai taje shi akeyi qwanin sha'awa alaman an kusa kammala gyran

Ummm wow" waye haka so beautifl tace
"amma yau bakowa mu kayi ko ta karkato tana takowa cikin rangwadi saitin wannan matar
Dukar dakai tayi " Hello, cewar ta tana kokarin leka fuskan ta cikin dabara

Wani' Duummmm taji kirjin ta ya buga batare da bata lokaci ba ta daga kai tare da sauke wani zazzAfan tsaki
Itama mikewa Tsaye tayi cikin wani irin juyin bunkasa ta kalle ta
Sama da kasa

Ke ..ta daka ma ma'aikciyar tsawa
Je ki kira min security incharge yanzunan

Ya zaku bar mahaukata suna shiga min shago'
Tattaba machine din ta somayi tana cakuda fuskan ta kamar zatayo amai
Tace A fitar min da wannan abun anan
I cant stand it..wari yake yi'
ai aka sake sa ma wata customer sai aga sun soma hauka

" Kan bala'i? Ga ki babbar mahaukaciya ' ?i curse today for showing me ur ugly looking face "bitch" tania tafada akan fuskan zAhida tare da watsa mata wasu mugayen kallo

Wani dariya ta fashe da shi kafin tace
Kalle ni da kywu ..igiyan rakumi yayi nesa da kasa ... Juyi ta shigayi tana rausaya Jikin ta "nice kyw,sunana ne kywu don shi kuma aka halicce ni
Idan wani abun kike ji da shi a kanki
Mu hadu yau
ta ciro iv ta wurga mata
" im inviting u to my litle kingdom party
In kin cika marar kunya kizo wajen
Im sure tarihin ki daga ranar zai gushe a doron kasa trust me '

Tsaki tania tayi ,ta tsuguna ta dauko ivn
' cikin wani irin kallon banza tace dan halak ka fasa sannan ta ja jakar ta ta fice abun ta

Wajen kowa ya sa ido yana kallon dramar hatta securityn da aka kira su
Fada sosai ta shiga musu cikin cin mutunci da kaskanci wanda har ya sa customer din da
ta ke lailayawar suka soma shan mamakin hali irin nata'doka mai tsanani ta bayar kan cewa duk randa tania ta sake shigowa zata sa ama mutum daurin shekara 10 a gidan yari
a fusace ta ce da Allah ku bace min anan kowa ya koma kan aikin sa bunch of idiots...

Sum sum kowa ya bace nan itama tafice rai a bace tayi hanyar office din ta
Kamar zUciyan ta xai fashe sakamakon kiran data keyi wa ashween bai daga ba
Take ta soma jin wani azabbaben quna aran ta
Ena ya shiga ?tafada tana zirga zirga ita kadai cikin offishin ta
A karo na goma sha biyar ta ajiye wayar a gefe
Ruwa ta tsiyaya mai sanyi a distiller ta kwnkwada tana lumshe ido kamar wacce ke shan madaci
"Gwam ta ajiye cup din kan desk da karfi ta saida glass din ya dan tsage
Chab lallai duniya juyi juyi "Ni ne yau zan ta kiran wani namiji bai daga wa?
Wtf! Ta ja tsuka
Dan lumshe ido tayi ta koma ta zauna kan sliding chair tana juyi kadan kadan
' why me? Meyasa nake jin kamar yanzu ne karo na farko da soma soyyaya a zuciyata why? Girgiza kai ta shigayi tana fadin he's mine'

Ashween is mine ba wanda ya isa ya sha min gaba...ta koma tana maida numfashi wanda yayi dai dai da budewar kofar office din

Take taji ta mance da halin data ke ciki zumbut ta mike zatayi kansa
Tana narkewa "na gode Allah da ka zo why arent yhu picking up kasan zan damu ko?
Riko hannnun ta yayi fuskan sa ba alaman wasa
Yace ' me kika ma wa tania yau?
Wani kasallen kallon takaici ta bisa da shi tana yarfe hannun ta
Me zan mata kuwa ? She bumped into my spa nikuma na kore ta ai ba na uban ta bane tafada ranta a dan bace

" ohh really
Good,,.yace a takaice ya juya da sauri ya fice

"Sarawa kanta yayi lokaci guda ta bi bayan sa tana kwalla masa kira
Ba ita da kamo sa ba sai da suka yi dab cikin jama "a ,
Ganin kowa ya dauke kai ta soma masa mgana a hankali
' haba ash,yanzu akan ta ne zaka zo kana kumbura min fuska
Wani munafurcin ta je ta hada min
huhn? Yarinyar nan so kawai taga baka tare dani

A fusace cikin dagon murya yace "just shut up
Zahida kina ban mamaki
After all im doing for yhu
Na fifita ki akan tania hakan ba yana nuna bana kaunar ta bane

Amma har zansa ta hakura taje wanke kai wajen ki ki tozarta ta ?
Sau nawa zance miki magana ya kare tsakanin ku
Huh tell me? ya fada cikin razanannan tsawar daya so ya firgita ta

Tam idon ta ya kawo ruwa ganin yadda ma'aikatan ta ke bada hankali a dabaran ce wajen kallon abunda ke faruwa
Wani kunya ne da takaici ya lullube ta ace da isar ta da kyuwn ta namiji' namijin ma karamin yaro kamar asheewn yana dakata mata tsawa gaban mutane akan wata mace?
Chapter 13 · 0% Book details