← Book details So Makamin Cuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 132

Sashe 44

So Makamin Cuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gefen jabir kuwa shirye shirye ake na fitar hankali
An sake yin painting gaba daya faundation din nasa ansa komai neat, domin kuwa wannan ne karo na farko da ya samu wani babban daya fishi ya shigar da shi sama wajen world united nations org.
Domin kuwa baban kamal na daya daga cikin wanda ake damawa da su achan,
Shiyasa Jabir din ya sakankance akan zai samu tallafin da zaisa ya tsaya da kansa don ganin yadda mumyn su tayi rashin mutunci ma jamal ya sa wani bangaren zuciyan sa shaukin so ya wuce gaba. ko da ace wani iftila'i zai same sa nan gaba,atleast kar ya wulakanta kamar dan uwan sa jamal,

Zahida, jabir duk basu ji dadi ba duk da tarbiyan gidan su ne amma sumtyms suna jin bakin ciki yadda mrs hidayat take iya saurin juya musu baya musamman in taga daya daga cikin su ya riga ya fada kasa war was a harkokin sa,

Mace ce wanda bata san qaddara ba kuma tunanin ta gefe daya ne,in bakayi ne bani waje bata damu dakai waye bane a rayuwar ta itadai kawai duniya ne Gaba a lamuranta,

Gefen Zahida kuwa bata wani zauna a wajen sa ba yawon ta ta tafi chan cikin gari,
shima ya samu sarari yayi aikin sa hankali kwance yana tunanin rayuwar sa

Chan wajen karfe 5 saura ya tashi bai nufi ko ena ba sai gida don ya matsu ya ji ya jasmine take acikin gidan .

Bayan kamar minti 15 ya isa gidan,nan ya nufi site dinsa straight ya fada batrum yayi wanka ya fito ya kimtsa.
T shirt ya sa baki da blue jeans ya nufi dakin ta.
A hankali ya bude kofar yayi sallama baiji an amsa ba har sau biyu sai kawai ya shiga ciki.
Zuciyan sa ne tayi dum dum ganin bai ganta ba,da sauri ya kira sunan ta yana karasowa gefen bathrum shiru,
Ya duba dressing rum haka ma shiru

Tuni yaji wani zufa ya soma keto masa,
Nan ya juya ya shiga dube dube gashi ya tabbatar zahida bata dawo ba tukunna.

Idon sa har sun sauya don kuwa haka kawai yakejin in bai ganta ba fa akwai matsala
Gashi ya tambaya duk wani mai aiki da ya gamu da shi a hanya sai suce basu ga kowa ba,.

Har ya gama duba posible inda zata iya zuwa bai ganta ba ,nan ya sauko kasa ya nufo waje nan ma baigan ta ba sai da ya zago baya wajen da yafi ko ena sanyin bishiyoyi Da furanni ya hango ta na zaune akan yoga mat ta sa gown na material red da dan belt dinsa baki
ta daura dankwali ma stil baki ta zubo da jelar gashin ta gefe da ta nade bakin sa da jan ribbons.

Annurin fuskan ma'aikatan dake wajen alokacin ya tabbatar masa she's having a friendly time conversation tare da su,

Cook mai suna Nana ce ta soma hango sa don itace a tsaye a gefen jasmine din alamn ta kawo mata wani abu ne a plates irin masu zurfin nan,
Gefe kuma masu kula da flowers ne su biyu da security men a chan gaba daura da su.

Gyran muryan da yayi yasa kowa ya hankalta suka soma sullebewa suna bashi waje,

Ita kam bata ko ji ba ma ,tana faman tambyar cook nana aena ta samu pormanganate(wato ruman) wani fruits ne mai matukar wahalar samu a kasan nan ko a waje ne ma ba safai ake ganin sa ba,
shima yana daya daga cikin fruits din aljanna da Allah ya fada a suratl rahman,

Cook nana Ta kasa amsawa sai murmushi take don suna mugun jin nauyi da fargaban ashween.

Sai da yazo daf ta rusuna tace ,sannu da zuwa boss ta bar wajen .

Ai da sauri ta mike ta sakar masa murmushi
shiko ko ya kula
Yace wayace kifita ne? Yana kallin dresing din nata daya mata kyuw sosai

turo baki tayi tace ai kaki dawo wa ne,shi ne nace a fitar dani na sha iska,

Sauke ajiyan zuciya yayi yace ,toh yayi, sai mutafi ciki kuma ai kinsha iskan right?
Ta make kafada tace uhm, um. ni anan zan zauna ,haka taki fir

Don dolen sa haka ya hakura shima ya zauna
Nan ma bata kyalesa ba ta shiga dura masa fruits din yana ci,gashi bata masa da sauki akai akai take bashi,

Suna sha'anin su ,zahida ne da karime chan sama daga window suna kallon su.
Ta tabe baki tace,kin ga yar uwa mai kamar kishiya ko?
Jiya jiya tazo gidan nan amma na fahimci so take na nuna mata matsayi na a wajen ashween

Karime daga gefe tace haka ne hajiya
' dama yan uwan miji sun fi kishi da matar gida,wannan din ai na lura fitina ne da ita,
Zahida dake kan kallon su bata amsa ba

Sai chan tace ,jeki kawai karime
Nasan maganin ta.

🤒😣

*suriem*
[23/08, 05:42] ‪+234 806 071 2446‬: *⚜BRILLIANT WRITERS ASSO🖊*

💔

*SO MAKAMIN CUTA*
_'the sword of evil love'_

_Story and written by_
*SURAYYAHMS*🔥

*DEDICATED TO-*@UMMERHERNY NERSALLAH.

*ASHWEEN bai auri ZAHIDA ba, JASMINE ya aura, suna zama waje daya ne kawai as tazo kuma zata tafi. so pls stop confusing oda readers👏🏻*
*Labarin nan kuma ba komai bane a kirkire is 80% TRUE LIFE story it has happened da gaske ..so pls just follow quietly and remember ur life isnt d same as any oda person kowa da yanayin life dinsa, .......and 1 more thing... THANKs😜*

*Page▶31*

Gefen su jasmine kuwa sai Bayan kamar minti 40 lokacin ana dab da kiran maghrib sannan suka shigo gida
Suna tafiya ta damke hannun sa tana wasa da shi,

A halin Yanzu kam ashween Baya iya hanata yin komai da shi,kuma baiya son cika tsawatar mata ko daure mata fuska
Don yana ganin kamar ture ta ajikin sa zai iya sake jefa ta cikin tunani da maraicin mutuwar ammyn sun sosai

A Daki ya barta ya nufi masallacin gidan enda suke sallah su ya su yan gidan,
Anan ya zauna bai shigo ba sai da yakai isha'i yayi musu addu' oi duka sannan ya shigo.

Kafin wannan time din zahida ta gama wasan banzan ta da sugar duk sun gauraye dakin, jikin ta bakomai sai gantalallen towel din data daure kirjin ta
sai nishadi takeji alaman ta gamsu sosai

Wanka ta cahn chada tayi kwalliya ta nifi site dinsa...

Turo kofa tayi Ba sallama ta shigo ta zauna gefen sa tana dada gyra zaman suman kanta
A lokacin shima already zaune yake hankalin sa na kan system dake gaban sa

Qamshi take yi sosai sanda ta zauna daf dashi
Nan' ya juya ya kalle ta fuska ba yabo ba fallasa yace ya akayi ne
My baby,

Tace not fine,ba kayi sabuwar baby kamance da ni ba? ta karashe maganan a shagwabe

Nan Yayi murmushi bai kalle ta ba yace zahida kenan,
Kina ban mamaki.

Tace ta yaya fa? Ai naga jiya kawai tazo gidan nan amma gashi yau ko nema na bakayi ba but u have time for her.
Yace ai yawo kika jeand u stayed late.
Cikin son tayi defwnding kanta tace uhm.
I stayed late din ma ai Ko tambaya kaji na dawo ma ka kasa yi!?

Yace ,hmm duk wannan a yau din ya faru kenan?
Tace eh,
Ya kalle ta yace, to amin uziri, me kuma ya kwo maganan sabuwar babyn ai case din naga duk da ni ne

Murya a kasa tana kallon sa tace im geting jelous ne kawai,bana iya daurewa naga wani abu na dauke min hankalin ka akaina

Yay karamin dariya yace" hmm zahida U know im all yours bai kamata kina daga hankalin ki akan yarinyan nan ba fa, ke da kwanan nan zamuyi aure meye matsalar ki?
besides kinsan kin girme ta sosai meye ma naki da shiga hidiman ta? Baki ga nima lalabata nakeyi ba
Ganin ta bada hankali alaman tana gamsuwa da zancen nashi ya sa shi
Ya saukake muryam sa yace
She lost her parents.dan Allah ki fahimce ta kinji beauty na

Nan Tayi shiru kamr tana nazari,daga baya tace hmm bakomai,
Ai naga bata ji ne,gigin yaranta ke damun ta and ni kuma..

Ya dakatar da ita yace "Shhh, ke kuma zaki kula min da ita ,bana son naji wani salon fitina zAhida ki rike girmanki kawai kin gane?

Dan dolen Ta amsa ba don taso ba,

Yace good

Yau Nayi magama da mumyn ku, ashe abunda ya faru sa jamal kenan?

Nan take fuskan ta ya sauya don tana mugun kaunar jamal da jabir a rayuwar ta har bata son tana tuno abun
Nan ta sauke ajiyayyen numfashi tace
"baby im scared shiyasa ban iya maka maganam ba ,wallhy na tsorata da al'amarin sosai
And mum tace ba ita ba shi kaji fa.

Ashween Ya tari numfashin ta yace"Amma ai danta ne kuma yana da right

Tace ehm of cous yana dashi ,amma ai mum bata san da haka ba ,
Ita dai in baka blowing a harkan kudi da al'amuran life to fa baka cikin shirgin damuwan ta..

Ashween din Bai kalle ta Yace ,Allah ya kywta

Ta cigaba da cewa, bari dai muga fitowar sa a prizon din sai muga me Ai faru ,ance wai 2yrs ko?

Ya ce uhm haka nagani, but baby ke bazaki iya sa baki ba ne? wallhy bana son jamal ya zauna a prison,nayi magana da mum din naku da zu akan ko zan sa baki amma bamu samu fahimta ba ya marairaicw fuska yace'beauty.
Jus Think about it, dan uwanki ne fa kikace min tare kuka tashi,
So Just bcos of one silly mistake shine zaku yarda mumyn ku ta juya masa baya?haba,haba,baby na
Wht if daya daga cikin ku hakan ya same shi ya zakuji?

Jikin ta ne ya soma yin sanyi, don harga Allah akwai wannan tunanin a ranta itama amma sai ta ajiye gefw don tasan halin mumyn sun sarai ba sabon fari ba
Sosai ta tausaya ma jamal duk da tasan rashin godiyan Allah da rashin Tawakkalin sa ya dada jefa shi cikin halin da yake ciki.
Chapter 44 · 0% Book details