← Book details So Makamin Cuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 132

Sashe 19

So Makamin Cuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dan tabe baki tayi ,
Tace hmm
Jamal ya saya makan sa wahala
En nine shi kawai zAn cigaba da aiki na ba sai nayi suna ba

Mummy kam dama In kana da shi kaine nata amma inbaka da shi ure useless".

🤓

*surriem*
[23/08, 03:02] ‪+234 806 071 2446‬: *⚜BRILLIANT WRITERS ASSO🖊*

💔

*SO MAKAMIN CUTA*
_'the sword of evil love'_

_Story and written by_
*SURAYYAHMS*🔥

*DEDICATED TO-*@UMMERHERNY NERSALLAH.

*Masoya A duk enda kuke surayyahms tana kaunar ku* 💋❤💯

*Page▶11*

Zaune suke a karkashin wani open air cool down,suna shan drinks sai kyalkyelwa sukeyi da dariya kamar kananan yara
Amintaka irin na kamal da ashween tamkar jini daya ne ya hada su
Duk da ma a secdry achl suka hadu ba wanda zai iya cewa hakan
Domin savuwr tasu yayi kama da wanda suka tasu tun suna kanana..

'lallai yaron nan ,
Ka tabbatar min da zaka iya jefar tsuntsu goma ma da dutse daya

Dan murmushi kaqai ashween yayai yace
Nothing is impossible bro
Sun dauka abun wasa ne ,
dama mutanen da suke kallon rayuwa a irin wannan madubin ba wahala zasu fada cikin kowani irin tarko,
Wht yhu need is ka nuna musu abunda suke so, to shikenan ka gama da su

Kaml ya nitsu yana jinshi " Hmm amma Allah ya dai sawwake ,to ena ilimi da power ? Ba basirah mswww
Yanzu shi jamal ka gama da shi tashi ta kare tunda yan jarida ma naga sai dada hura qutan abun suke' yanzu sai kuma waye next?

Uhmm bari fa ai jamal hakki mutane ke binsa sai dayan wawan ,,shikam ai one blow ne zan masa muje zUwa
Don Yanzu bani da wani matsala sosai tunda na samu shiga wajen uwar tasu
Sannu a hankali zan durmuryarta da ita da yarta ,amma nafiso komai ya tafi steady
clean bana son nayi garaje ka fahimta

Of cous, kar ka manta ena tare dakai,kasan
Ciwon dayafi zafi shine wanda ba ganin sa sai da aji sa,

Dariya sukayi tare ,sannan ashwewn yace kaga ni zan koma gida kwana biyu ban kula da tsohuwa ta ba duk aikin wayyanan banzayen sun sha min kai,
Ya mike tsaye ,,
Tohh shikenan ash send my regards ,nikam jiya naje ai
Later,suka yi musabaha sannan ya kallesa ya dan kashe masa ido yace
And my princess too
Da sauri ya kwace hannun sa yana harar sa cikin sigar wasa
Kwara ma ka cire my din nan
Princess din dan ma kaine ?

Shikam kamal dariya kawai yake don yasan dole ya amsa shi haka suka rabu kowa yayi nashi hanya

*Bayan wata daya,*

Haka rayuwa ta cigaba wa ashween da familyn rodriquez
Sosai yake samum karbuwa yanzu ya kaiga madam hidayat ta sake masa wasu harkokin ta yana juya mata su

Yarda da so sosai ta soma qallafawa akansa dun dama tun tuni takejin sa kamar dan cikin ta,

Zahida ko hankalin ta kwance sai baza mulkin ta takeyi iya son ranta,
Cikin kawayen ta kuwa har takanyi birgan cewa ta kashe tania ta gaje ashween ma kanta,

Ranar laaraba da aafe misalin karfe10 Zaune tayi gefen sa ta hanasa sakat, shiko sai aikin sa yake baya ma kallon me takeyi
Yana sane da Duk ma aikatan sa ba su samun sakewa musamman inta na offishin
Saboda zahida asalin ta bata san darajar dan adam ba' wani abun ma don tana tsoron ashween ya sa take ragewa

Baby"? Ta kure sa da ido tana kashe muryan ta
Ya akayi,yace a takaice bai dago ba

Sai Yau naga kamar ranka a bace
I mean, lpya kuwa? Yhu look sick ko kwalliyar ma da aka saba min yau ba ayi ba" ta karashe a marai raice

Dan takaitaccen kallo ya bita da shi yace
Kar ki daga ma kanki hankali beauty
Im ok,just need some time alonee
Shyasa ma naga zai fi dacewa kije gida zamu hadu anjima kinji? Ya kau da kai

Ranta baiso ba amma sai ta yi saurin kawo murmushi kan fiskan ta tace
Anything for yhu,
Kar ka manta duk aBunda kake bukata ena nan,
Gyada kai kawai yayi baice komai ba harta fice
'yana jin karar rufuwar kofar ya kife kansa da tebur tuni wasu zafafan hawaye suka soma sauko masa"
Yakai minti 20 a hakan kansa har na hargowa tsaban ciwon dayake ji
Karshe rufe file din yayi ya wuce gida abunsa

Haka ya wuni a daki sai juye juye yake' yaki sanar da kowa yana gidan don kar hankalin ammyn sa ya tashi
Ita kadai ce ta san yadda ya tsani ranar zagowar haihuwar sa
Don tun safe take kafa kafa da shi amma yaki nuna mata komai

Kamal ma ranar shiru bai neme sa ba don ya tsani ganin yanayin ashween a ko wani ranar bufdayn nasa
Gashi duk lokacim da ya so ya shiga al'amarin yakan so ya zame musu sabani,
sai ya yanke hukun cin masa addua da sadaqa duk ranar zagowar haihuwan sa ba tare da ya sani ba ma

Gefen ashween kuwa yayi nafila ranar ba adadi, amma sam jikin sa yaki sake sa,a hankali ya jingina kansa da pillow idonsa a lumshe yace "ya Allah ,kullum dai haka ne...pls ka saukaka min
Sai bai kara cewa komai ba

Tattara kaya ammy keyi bayan ta kammla rubuce rubucen ta ,
Bata hankara ba jitayi mutum agefen ta but

Ke,kaji min yarinyar nan ai sai ke tsorata ni tafada cikin sigar fada ,
Ita kam shiru tayi saida ta kammla karanta dan papern da ta sa mu a kasa sannan ta ce Ammy"
Daga zuwa duba ki sai kimin masifa? , share ta ammyn tayi batace komai ba

Ta rike kogun ta ,sai kiriniya take
Cahn tagaji dan kanta tace
Ammy naje?

Ohhhh jasmine wai ena zaki je ne?

Zaro ido waje tayi tace " tuntuni nake tace wa zanje kasuwa ammy ashe bakki ma jina ?

Ohh sorry ,
Ke da wa?
Nida driver ne kawai

Ammy tace Ok
Ena fatan bazaki dade ba ko don wallhy ba ruwa na tohm
Da sauri ta gyada kai tace " yanzu zan dawo ammy
Toh shikenan ..nan ta fice a gurguje

Wanka ta sha mai shegen kywu cikin atamfa dark green
Ta nufi kasuwa don yo shoping
" zuciyan ta fall take tafiya cikin mall din
Tunanin ta gaba daya me zata siya wanda zai burge yaya ash"
Kiran salma ne ya sake shigowa wayar
Ba jira ta dauka
Tace yawwa dazu muna magana"
Kinsan ban san yau yake bufday ba sai da naje dakin ammy
Naga ta rubuta masa wish a wani paper,ai itama bata san na gani ba na yar mata abun ta
Ta karashe da dan dariya

Hmm jasmine kenan,
Toh me da me kika saya
Ko har kin gama?
Ehmm toh gani nan dai

Huhh,ta yarfa hannu a gajiye tace
Na ma rasa me zan dauka masa salmah
Im so confused
Uhum uhm dont be ,kinga take your time kiy masa abunda ya dcw da shi
Nikam bari na je my prince charming is coming today

Hmmm kaji masu love,to ki gaishe sa,
No wonder bangan shi a gidan mu ba ashe wajenki ya nufa,

Dan dariya salma tayi
Barshi kawai,shifa har yanzu baisan kinsan shine saurayi na ba,

Uhmm ai ni kanwa ce,na masa uziri. Allah dai ya tabbtr mana da alkhairi

Ameen jasmine,ke ma insha Allahu daga yau komai zai daidaita tskanin ki da yaya ash insha Allahu

Karamin murmushi tayi tace" Uhmm toh Allah ya sa ,ta karashe a sanyaye
Nan sukayi sallama ta cigaba da dube duben ta
Wasu haddadun bunches na red roseflower tagani masu shegen kyuw anyi rubutu " "only for my soul" Murmushi ne ya kufce mata lokaci guda takai hannu zata dauka wani

hannun ne mai taushi mai laushi ya sauka akan nata
a tsorace ta juya tare da ja baya,
Murmushi ne kan fuskan sa
Yace im sorry"
Ni ma yamin kyu ne,ashe kuma kin rigani ni"
Batace uffan ba ,sai cahn ta dan kalle sa tace ena wuni yaya ashraf

Lpya jasmine ,ke da waye anan din
Nika dai ce ,tace tana dukar da kanta kasa ' gaba daya mood dinta ya canza
Don ta tsani ganin sa ma amma sam shi baya lura da hakan,

Sa hannu yayi ya zaro mata abun na ta daga sama
Ba kunya ya tambaye ta'
For someone special i ques?
Da kyar ta dago tace
No,
Its mine..

Hmmm toh ko zaki bani ne? I like it yafada yana lura da ita
Shiru tayi batace uffan ba ,
Ta juya zata var wajen

Jasmine, tsaya,. yace amma sai ta juya masa baya
Uhmm Nace ba? Yaushe zan zo na amshi amsa ta ,
Ko har yanzu baki kammala tunanin naki bane
Wani dumm taji a zuciyar ta
Ita kam ma harta manta da wani yataba cewa yana son ta,
Kinji kuwa? Ya sake maimai tawa
Nan ta budi baki tace naji
Ban gama bane yaya,
Tayi sauri ta wuce abun ta,
Lumshe ido ashraf yayi ,don a duniya ba abunda yake kauna kamar jasmine ..komai nata irin na matan daya ke so ne barin ma
Dirin ta dayake dada rikata shi inya ganta
Shiyasa ma bai boye ba ya gaya ma mahaifiyar sa wato hajiya hadiza wacce take aminiya kuma yar uwa ga ammyn su

Itace dai ta dakatar da magana don shi ya so ace ta nema masa izini wajen ammy ya fara neman jasmine tun tuni

Cikin sauri sauri ta kammala packaging iya
Abunda ta samu ta dauka duk da ma taso ace wannan bunces din rose din na ciki
Ana kammalawa ta bar wajen

Gefen ashween kuwa Kamar yadda yake haka nan ba wani canji,white tshirt ya sa da jean yana kunshe a dakin sa ba abunda ya ci ma cikin sa tun safe'sai ruwa da dabino kwalli uku

Wajajen karfe 8 saura bayan ya kammala sallar ishai ya nufo cikin gidan
Nan ya hango ta sanye da hijabi tana tafiya bata ko lura da shi ba

Daga kai da zaiyi don ya hango enda zataje nan ne ya lura da motar dake parke cikin compund din nasu
Haka kawai yaji ransa ta cunkushe lokaci guda
Amma sai ya dake yana kallon karshen zancen
Chapter 19 · 0% Book details