← Book details So Makamin Cuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 103 OF 132

Sashe 103

So Makamin Cuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abun duk ya ishi mamy, cikin tsawa tace bazaki wuce ciki ba ko sai na zo wajen ?
Nan ta shiga ture sa a hankali cikin karfin hali amma yaki ya matsa jikin ta
Har sai da mamyn ta zo da kanta ta janye hannun ta da karfi daga nashi,

Firgici ya somayi yana fizgeewa a zuciye yana cewa jasmine i love you, pls don't leave me give me a chance na roke ki pls dont leave .dan Allah dan Allah.

Jasmine na so ta dawo gare shi amma sam tsoro ya hanata tantance ko gaskiyan hakan takeji aranta ko tausayin sa ne kawai.

Mamy ta rirriko shi amma sam yaki sai ya shiga kokuwa ya birkice mata zai bi bayan jasmine
Cikin azama ta tallafo sa ta wanka masa mari mai sauti.

A hatsale ta juya tace ke kuma ki bace min anan wajen kafin na taka ki

Duk da ma zuciyan ta ya karaya sosai da halin da ta ganshi a ciki da gudu ta juya ta shige ciki tana kuka

Ya dafe kuncin sa gaban mamy yana hawaye yayi shiru bai sake magana ba
Gaban shi ta tsaya tace "ka bani mamaki ashween
Sai yanzu ne zaka zo nan kana min wani hauka?
Sa 'ar ka daya da ban zo har gida na samu ita tababbiyar budirwan naka ba wallhy kuwa da sai kasan wacece hadiza.

Ashe baka da imani?
Marainiyar Allah amanar wacce ta zame maka uwa da uba a duniya ?
Ka ci amanar kyautatawa kaci amanan yarda,kuma kaci amanan shahida,

Nan ya dago da kyar ya kalli mamy yace ,kiyi hakuri ki daina fadan haka mamy wallhy ena son jasmine
Ban taba yin wani abu don na cutar da ita ba belive me..
Na roke ki Dan Allah ki saurare kiji mai zan fada

Tace kayi min shiru,to me zaka fada din da baka fada gaban shahida ba kafin ta mutu
Ai sai kace mana kaifa bazaka iya rike mana ita ba kana da wanda tafi mu daraja awajen ka ita zaka aura dole,meye ma a ciki
Ga na Allah dayawa ai kasani jasmine is a woman of all standard,ba zatayi kwantai ba kwanan nan kuwa zaka ji na aurar da ita..
amma kam bazan taba bari karamar yarinya marainiya ta zauna cikin wannan bakar wahala da kunci da kake sata ba kayi karya.tana nan gidan
Sai Kaje chan ka zauna da wanda kake so din.

Ya rusuna kasa kan gwaiwar sa cikin kukan yace mamy kiyi hakuri mana,nasan nayi laifi
Bata bari ya gama ba
Sai ta fashe da kuka ""tace mutuwa mai tona asiri. mai bayyana hali,ai dama sai baka raye zaka san waye asalin masoyin ka na gaskiya

Lokacin ashween ya kasa motsi idon sa na kasa sun dena kasa ruwan hawaye sai yaji mummunan ajijiya na deban sa

Mamy naci gana da kuka tana kan cewa
Shahida har kika mutu kina alfahari da wanda baki isa da shi ba,butulu ,daman naganin ido kawai ya miki soyayyar ..gashi yau yana neman taiyyara rayuwar yarki kwalli daya a duniya akan wata ya mace na daban.
Ta daka masa wani tsawan tace Just get out of my site,ni bana son ganin ka,.. kaje chan dama bamu da wani dangi da kai, wanda na hada yau ma na raba..

Kuma kasani The next time da zamu sake haduwa da kai takardan sakin yata zaka bani ta juya a fusace ta barshi a daskare a wajen

Tun kan mamy ta shigo jasmine tayi saurin barin enda ta labe yana jinsu tayi dakin ta da gudu ta fada kan gado ta shiga wani sabon kukan.

Ashween yakai minti 20 sannan ya tashi a tsaye kansa a kasa bai dago ba hawaye nakan bin kuncin sa.
Da kyar yayi ajiyan zazzafan numfashi ya juya a sanyaye ya nufi motar sa

Kuka yake yi yana tuki a hankali kamar hannun sa bai taba kan stiring, gaba daya zazzabi sai ya rufe sa kansa na bugawa kamar zai haukace haka yake ji

Gidan ammyn ya nifa
Ya buga horn aka bude masa gate.

Bai ko iya amsa gaisuwan kowa daga ma'aikatan ba ya ajiye motar ya fito a rikice

hannun sa a akai ua rike tsaban bugun daya keji akansan yana bari yana sauri har bai rufe motar bama ya shiga tsala ihun kiran ammy,

Da karfi yake kirar kamar wanda akace masa tana ciki kuma zata amsa shi

Kukan ya ki fitowa sai hawaye gaba daya muryan sa ya dishe sai ruda waje yake yana neman ta tare da kiran sunan ta.

Sama ya haura da gudu site din ta tun kafin ya bude kofar dakin ta yake bugawa a zafafe yana kan cewa ammy, ammy......

😟😟😟.

*surriem*
[23/08, 05:43] ‪+234 806 071 2446‬: *⚜BRILLIANT WRITERS ASSO🖊*

💔

*SO MAKAMIN CUTA*
_'the sword of evil love'_

_Story and written by_
*SURAYYAHMS*🔥

*DEDICATED TO-*@UMMERHERNY NERSALLAH.

*Page▶74*

Tun tafiyar ashween mamy ke kuka sosai a dakin ta dama dauriya kawai tayi don aganin ta hakan ne kadai zaisa ta karbe ma jasmine yancin ta nan gaba.

Abban ashraf ya shigo baice uffan ba ya dawo gefen ta ya zauna.

Dama yana cikin masallaci ake hayaniyan amma da shike itace ke da alhakin su duka biyu sai ya zuba mata ido yaga kalar nata hukun cin.

Kuka take yi kanta a kasa kamar wacce tayi laifi sai yace kiyi hakuri hadiza kukan ai ya'isa haka

Its so obvious that u cant hurt sumone witout hurting urself,
Ni aganina hadiza anya harshen ki baiyi tsauri akan yaron nan ba?

Wai Duk akan ya kawo wata mata cikin hidiman ...gaskiya banji dadin kalaman ki ba .
Na dauka zaki bi abun a sannu ai ashween yaro ne
na tabbata ko shahiida na raye yau bazata taba furta masa haka.kiyi tunani dai

Nan ta dago murya a sanyaye tace nasani alhj,na sani.

Amma kuma hakan nayi niyya nafi so nagaya masa hakan shyasa kuma na fada.
Kaiwa nan ta tashi ta fuce abunta

Girgiza kai kawai yayi yace toh Allah ya kyauta

Gefen ashween kuwa a lokacin Ya turo kofar ammyn ciki da karfi idon sa sun rufe baya ma ganin gaban sa sai ya soma tahowa enda shimfidar ammyn yake nan ya zube gwuwir sa a kasa yana kan kuka mai cin rai.

Koran sunan ta yake Tamkar a gaban ta yake.
Yace" dan Allah ki dawo ammy nasan zaki saurare ni,come bak to me mother i ne..e.d you.
Nan ya cigaba Ya fada ya sake maimai tawa

Har ya kife kansa akan gadon"bai fasa ba can kasan makoshi yake cewa ke daban ce ammy nasan ba zaki taba rabuwa da ni ba har abada kina so na ,ke kadai kika san ena kaunar ku baki daya kuma bazan taba butulce miki ba bare na ci amanan ki,

Bakin sa har na rawa yace i love her ,ena son jasmine ammy ki zo ki fada musu, pls come bak bazan iya rayuwa na a hakan ba
.
Babu ke babu jasmine banda farin ciki
today i feel so guilty an scared
Ki taimaka min ki dawo mana

,.. sai ya lumshe ido yana dada matso zafafan hawayen sa yana jan katifan da hannun sa cikin tsananin tashin hankali da firgici bai masan meya keyi ba

A Brain dinsa Ya rasa maganan wanne daya cikin jasmine da mamy zai dena tunawa don ya samo sauki ma zuciyan sa.

Duk da ma yasan maganan mamy yafi masa ciwo amma har yanzu yana jin tsananin bakin ciki kufcewar jasmine a rayuwar sa.

Wani Bacci mai nauyi ne bazata ya dauke shi a wajen a tsugune kan gwiwar sa.

Cikin baccin yake jin yadda ake shafo suman kansa ana calming dinsa amma Allah baiyi zai iya juyawa ya ga waye ba ne
Tsaban yadda yake jin dadin yadda ake calming dinsa sa shafowar kan ya sa shi jin dama dama a ransa.
Amma sai ya shiga cikin zulumi to waye yake rarrashin sa haka.

Sai ya budi baki yace ammy na ke ne?shiru baiji an amsa ba.ya dan ja ajiyan zuciya yace pls come back to me mother ki zo ki saurare kice mamy ta bani mata ta wallhy ena son ta ... Bayan nan shiru yayi kamar wanda aka ce masa yayi

Chan kuma sai komai ya dauke masa kamar film firgit ya bude idon sa yaga sarari ashe shika dai ne ba kowa

Wani perfect silence ne ya dada ratsa dakin aka barshi da rarraba ido a tsugune a kan kafar sa,

Nan wani mummunan Jiri ne ya debe sa ya zube kasa a take baya ko
motsi.

Kamal na jirgi amma sam hankalin sa bai kwanta ba
Yayi iya kokarin yaga ya samu wani information akan meke faruwa sa ash amma shiru

Gashi Tun karfe 6 yake jirgi daga chan yankin antactica daura da north america wurim akwai nisa sosai da africa sai ana neman 5.30 pm ya diro nigeria

Layin ash still Ya kira ya kira amma shiru ba a dagawa
Nan ya dada birkicewa jikin sa yayo sanyi yasan ba lpya ba.

Inda salma take ya soma zuwa ya danyi refreshing kansa ,ita ma duk ta sa abun arai daurewa kawai takeyi take masa smiles don karfin hali

Yana cin abinci a gaggauce yace mata ki kwantar da hankalin ki, zan je na dubo sa yanzun
Na san endai har jasmine bata saurare shi yau ba bazai hakura ba and i know where to find him

A sanyaye Salma tace pls do,
Allah kadai ya san ya yake ji yanzu na tausaya ma yaya ash baka yadda yake ba ne dazu.

Koma meye ne i dont think jasmine zata tsawwala wannan hukunci akansa its so unfair.

Kamal yace, hakane mine..ya muka iya?ai ku din ne sumtimes zuciya baya barin ku.
Ya tashi tsaye yace"Let me be going in na same shi zan kira ki ko?
Ta gyada kai ya mata light kiss ya fice.

Ba tantama ya nufi hanyar gidan ammy lokacin daf 6pm na yamma.
Ganin motar sa a parker ko rufewa ba'ayi ba ya sa yayi ajiyan zuciya tace thank God

Shima Yayi saurin parking ya shige cikin gidan.
Chapter 103 · 0% Book details