← Book details So Makamin Cuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 132 OF 132

Sashe 132

So Makamin Cuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Bangaren su zahida kuwa jasmine na kuka zahida nayi duk hankalin zahidan ya tashi ta rasa yadda zatayi da ita.

Ana cikin haka sai ga wani taxi ya sauke wata tsohuwa a gigice ta tashi ta kirawo shi tasa jasmine aciki suka tafi asibiti sai sannu take jera mata.

Bayan an samu infomation din taxi nan su jamal suka zo su kuma wajen amma basu same su ba.

Ashween ya daura hannu akai yace shikenan tawa kare yau jasmine ina zata je tabar ni, tunanin sa kar dai jasmine ta fada a ruwan nan ne neman zahida

Don a nace masa nan ne suka taho ya kawo aransa kawai suicide zahida tayi niyyar aikatawa ma kanta

Suna cikin haka wayar sa tayi kara gashi dujlk ruwa ya musu duka alokacin ya soma saukowa da dan karfi

Sai a karo na biyu ya dauka nan zahida tace masa suna asibiti ya taho emargency.

Ba jira suka bar wajen su ukun su suka nufi asibiti sam ya kasa nitsuwa
Me zai kai jasmine asibiti a kirgen su dai yau cikin ta na wata 8 da sati biyu ne

Yana shiga kuwa ya samo har an sauya mata kaya zuwa labour room gaba daya ta kusa galabaita sai innalihhi take jero wa

Zahida ne kawai akanta tana rike da hannun ta tana kuka ,

Ya na isowa yayo kanta shima yace jasmine are you ok? Ena ne ke miki ciwo nan ma a birkice ya soma kwala ma doc kira gaba daya ya ruda wajen da tashin hankali

da kyar ya bari aka dan jira tayi labour da kanta
Da shike su kasashen waje miji yana da ikon tsayuwa akan matar sa lokacin da take labour har sai ta sauka .

Jamal ne ya rufe zahida da fada duk dama hankalin su a tashe yake ganin jasmine a haka.
Gaba daya sai ta rikice tace wallhy bazan kara ba.
Dama bana son na shiga rayuwan su shiyasa na yanke hukunci ,Allah dai yasa kar wani abu ya sami jasmine sanadiya ta.
Haka sukayi tsayuwan su a waiting room su uku.

Ashween yana ciki rike da hannuun ta ba irin sakalci da shagwaban da bata sake masa ba
ko su doctors din da basu jin hausa saida suka fahimci wani abun badon labour ba dadi ba da ba karamin dariya za'ayi wajen ba.

Tana kuka tana nishi tana magana gaba daya sai mutsinin sa take yi
Duk bai damu ba shikam ya rude sai calming dinta yake doc suna aikin su

Kafin wani 40 to 45 mints sai ga shi abun ya dada zafafa nan ta shiga juyi da kanta tana cewa yaya zan mutu ne?,nikam a cire min wannan zafin wayyo Allah na
Yace kiyi hakuri jasmine u will be fine,doc din ma suna taya shi amma ena a haka a haka sai da tasa shi ruwan hawaye daga nan tayi wani wawan yunkuro sai ta sunbudo masa baby daya na bin daya har guda biyu mace da namiji

Nan ma wani murmushin da ya gaurayu da hawayen farin ciki da tausayi ya bal bale sa.

Sai tayi shiru tana maida numfashi tana dada lafewa ajikin sa yana shafo ta yana sa mata albarka har aka gama kimtsa ta fes tare da babies din sa.

Tsaban kyaun halittar babies din sai da dukan wanda zuka karbi haihuwan suka dauki pics dinsu tare
kowa na musu son barka .

Bakin Ash ya kasa rufuwa gaba daya ya birkice da farin ciki,murmushi ne akan fuskan sa ya riko babies din amma hawayen yakasa daukewa musamman daya ke gani baby girl din sa tana mugun kama da twin sis din sa lailah sosai

Haka yan uwan sa suka rungume sa kowa na masa son barka
zahida ta riko babies din itama gaba daya sai taji kaunar su ya rufe ta har ta mance da damuwar ta .

Bayan kwana uku da haihuwan jasmine already mamy da su salma sun takura adawo musu da ita nigeria

don kamal kam ya riga ya taho iraq cikin babylon da safaffen washe gari ya same su.

Ranar da doc ya tabbatar masa jasmine da babies dinsa komai lpya ranar suka dawo abuja dukan su

Duk maitan son yaran sa haka ya kyale ma su zahida da su kamal enda kowa yake nuna nasa maitan son ma yaran.

A gidan ma mamy ke hidima sosai da jasmine
A nata shirye shiryen suna ma yara.

Ranar da Ashraf da zahida suka hadu ba karamin dariya sukayi ma juna ba saboda duk saida suka sha mamakin yadda rayuwa ta maida su.

Abun abun tausayi amma sai suka maida shi abun tsokana ma junan su

Shi yake debe mata kewa
Itama hakan bata jin dadi in baizo sunyi yar tsokanan da shi ba

Haka shakuwa ya fara ninkuwa tsakanin ashraf da zahida tun kafin suna suka dawo real friends
Na ban mamaki.

Tare suka hada nasu hidiman ma babies din su jasmine wanda aka basu inkiyan sunan ammy wato shahida da shaheed.amma a zahiri lailah ne da kamal jnr

Wanda ash already yake kiran ta da ammy, shima baby boy ya dawo wasu sukan ce shaheed wasu suna cewa jnr.

Kamal da zahida suka dawo rlshp din su normal duk da ma tana dan jin kunyar sa
Amma ana wasa da dariya ita ta fara cewa Ba zata kira shaheed junior ba don kar ya dawo black kamar ita da kamal.

Haka suka cigaba da rayuwan su komai na tafiya dai dai
Har aka yi suna cike da gata da hidima nagani na fada

Mamy gaba daya sai taji duniyan ya mata dadi sosai
ganin yanzu kowa acikin su ita yake duba a matsayin mahifiya musamman ma zahida da ta dawo best friend dn Ashraf

yanzu shi yake koya mata addinin ta da abubuwan da da chan ta mance da su a matsayin ta na musulma.

Ganin ya mallake hankali sosai ya sa abba ya bashi damarl ya sake rike musu tatallin arzikin su kamar da chan.

Bayan shekara guda zahida ta dada wankuwa alaman ta amshi qaddarar Allah daya sauya mata halittan ta
Ta koma soma sa kayan mutunci ta dawo musulma tana sallah tana azumi da sauran su.

Sai ta kwantar da hankalin ta tana juya harkokin business din ta tare da yan uwan ta cike da so da kauna da amanan juna .

Da shike yanzu akwai ashraf sai ta mance ma da wani feelings ma Ashween har tana scolding kanta akan shirmen data yi da chan tana rudin zuciyan ta.

Ba da dadewa ba aka soma shirye shiryen auren su da ashraf
Lokacin salma tana laulayin sabon ciki

Ahaka zahida taga uban gata da soyayya wajen su duka
Musamman mamy data bata kula irin na surka da na uwa
Har aka ci taro aka watse aka kai ma ashraf new wife dinsa wato zahrod.

*After 5 years*

Lokacin Labarin mutuwar madam hidayat a prison har ya soma gushewa
A Lokacin Jasmine ta kammala karatun ta har ta kama aiki karkashin arzikin mahaifin ta.

Sai ya kasance kusan kowani wata biyu ko uku in yara sukayi hutu sai an taho abuja don a hadu baki daya as family and friends.

Jummai da salma already suna da yaran su bibbiyu ,bayan Ash junior akwai baby girl jawahir na jumai kuma fatima

Zahida kuma ta haifi baby boy kabeer da kyar don daga nan saida aka cire mahaifan ta kwata kwata
ga cikin ya zo da albarka shi yayi sanadiyar kara fito da sirrin kyau dake cikin sabon salon halittar ta
Shikuma aahraf yanzu an samu yana amfani da eye glasses suna rayuwar su mai dadi mai tsafta.

Frndship din iyayen ya koma kan yayan wato Kamal Jnr da yayan sa Ashween jnr wanda aka kaisu karatun su kasar waje under care na uncle dinsu jamal.

Anan dai jasmine ke fama da laulayin wani sabon ciki ga baby boy din da ta haifa mai suna oumran bayan twins a hannun mamy tana kula da shi.

Haka rayuwa ta cigaba musu cikin jin dadi, bunkasar arziki ,soyayya, fahimtar juna,amana da yarda da kyakkyawan zumunci.happy
One big happy family.

*Wassalamu alaikum masoya na Ayafe ni ayafe ni,in na bata rai wani sanadiyar wannan littafi ayi hakuri da ni*

```Na gode, nagode wanda suka biyoni har wannan lokaci Allah ya muku albarka ya kare ku daga sharri ya sada ku da alkhairi ya baku ladan karfafa min gwiwa har na kammala wannan littafi a saukake cikin jin dadi kaunar ku da kulawar ku.
Jazakhallahu khairan```

*SURAYYAHMS ke muku fatan alkhairi sai mun hade a littafi na na gaba mai suna:*
*🌺SAKAMAKO🌺 not anytime soon amma zan gaya muku kafin na soma rubuta shi NAGODE*

~Im gonna miss u fans~ 😭😭😭
Chapter 132 · 0% Book details